Showing 267001 words to 270000 words out of 356830 words

Chapter 90 - RAINA KAMA Complete Hausa Novel

12 Oct 2024

185215

hujjoji da muke dasu a k'asa”.
Galadima ya sauke ajiyar zuciya yana jinjina kai, “hakane Baffi, amma akwai dai wasu y'an bayanai danake dasu a hannu yanzu haka, sai dai banida tabbacin dai-dai ne? Kokuwa akasin haka, amma kama SD da mukayi shine zai fito da gaskiyar hasashen nawa”.
“To shikenan, ALLAH yasa muji alkairi”.
“Amin, saidai ni a bayanin Baba Rabilu akwai abinda har yanzu yakemin rawa a zuciya”.
“tofa, minene kenan?”.
“Maganar siyasa dayacemin ya shiga a wancan shekarun, bayan kuma lokacin mulkin sojane, kenan wace siyasa sukayi?”.
Baffi yay murmushi, “wato abinda na fuskanta anan shine, yasako kalmar siyasa ne domin mu mufasa sauran bak'in da kanmu, amma tabbas a wancan lokacin babu wata jam'iyyar siyasa, wayema ya Isa d'aga murya akan mulkine? Saidai bincikena ya nuna Dalilin kafa Group nasu tanderu yanada nasaba da son kafa mulkin farar hula, wato sunason mulki yabar hannun sojoji kenan, saidai a 6oye sukeyin dukkan abinsu, har suka ringa jawo ra'ayin mutane mabanbanta a cikin tafiyar tasu, abinda na kasa fahimta nima shine, shin sunjawo Alhaji Rabilu ne dansu tabbatar Camera na hannunsa? Kokuwa shine yakai kansa garesu domin lek'en asiri? Dole cikin biyunnan a samu d'aya, kodan yunk'urin kasheshi da suka saka Darma yayi”.
Galadima dayay shiru yana fassara zancen Baffi dak'i-daki ya shiga jinjina kansa alamar gamsuwa da bayaninsa, zuwa can yace, “Baffi ka bani kwanaki biyu zanyi bincike insha ALLAH, dan zan tattauna da SD da kuma Harun, sannan akwai yaron da aka saka yay aikin da aka buga a jaridarnan, shima inason yazo hannuna insha ALLAH ”.
“ALLAH ya cigaba da dafa maka, Yakuma tsareka da dukkan sharri, lallai ka ringa kulawa, dan yanzu dukkan wata hanya da zasubi domin cuta maka sun tanadeta, karka d'auka suma basa bibiyar lamarinka kamar yanda kake bibiyar nasu, dan ranar naga Alhaji Abdul- Naseer da wani masanin Computer, saidai shi bai ganniba, nasha jinin jikina kwarai da gaske, amma nikam inamason tambayarka, minene alak'ar Surukinka da senator halluru ne?”.
“kamar dai abokinsa ne baffi”.
“Ok! Ok! To lallai ka sanar masa ya lura, dan Senator Halluru yaronsu tanderune, za'a iya bi ta hanyar surukinka a 6ata mana aiki, tunda sun san akwai alak'a tsakanin kai da shi”.
“wannan gaskiyane Baffi”.
Sun cigaba da tattaunawa akan matsalolin da ayanzu zasu fuskanta, baffi na kuma bama Galadima dabaru a shara'ance Wanda bazai aikata abinda shima zai rufta ba.

Sai dare ya koma masarauta, yinin yau gaba d'aya a tsaye yayisa, shiyyasa duk jikinsa ciwo yake masa, yanayin zirga-zirga amma ba irin wannanba mai cikeda cajin kwakwalwa da rikitar tunani. Ga maganganun Munaya dake cin ransa, ya tabbata duk gaskiya ta fad'a, hakan datake yana kuma tabbatar masa da tasan darajar kanta, inda watace shiru zatayi sai yanda yaso yi da ita, duk kuma abinda zai mata koda Mara k'yaune zata shanye saboda kasancewarsa d'an wani, amma duk da kasantuwarta mace kuma wadda take k'ark'ashin mulkinsu ALLAH bai sakama zuciyarta tsoro ko kwad'ayi ba, itadai kullum burinta shine asan darajarta da kimar ahalinta, sa6anin y'an matan yanzu da duniyar Ce kawai burinsu da son ganinta a tafin hannunsu, auren mai kud'i ko mulki, mai k'yau ajin farko, na nunama k'awaye da yin alfahari a duniya, yasan darajarta kona iyayenta wannan ba matsalarta bace, yanada addini ko kula da addinin shiyya Sani, son gaskiya yake mata ko albarkatun jikinta yakeso batada matsala, ya zube a kujera yana sauke tagwayen numfashi.
Sauban dake zaune yana kallo yakuma kallonsa, yayansu na bashi tausayi, saidai shi taurinkai da rashin yarda da kowansa ke had'ashi dashi, amma ta wani fannin yakan kalli hakan a matsayin gaskiyarsa, dan massarautar tasuce abar tsoro, ba kowane abin yardaba, yanda zaka tantance na kirkin shine mai wahalar kuma.


*******


Na kasa hak'uri da danne maganganun Galadima, hakanne ya sakani yanke shawarar tambayar Munubiya kota Sani, saida mukai shirin barci dukda sharenin da takeyi nadai danne nawa Fushin na zauna kusa da ita tana shayar da Meenat data tashi. Kan yarinyar na shafa sannan nace “Munubiya in tambayeki mana please?”.
Kamar bazata kulaniba sai kuma ta kalleni. Tace, “Ina saurarenki”.
Ajiyar zuciya nayi ina gyara zamana, nace, “dan ALLAH idan namiji yace gonarsa mi yake nufi?”.
Jimm tayi alamar tunani, ta kwantar da meenat tana fad'in “Matarsa”.
Da mamaki na kalleta, yayinda wani sanyi ya ratsa raina, amma na danne.......
Ta katseni da fad'in “Munaya ki fito fili ki sanarmin abinda ke faruwa, kinsan banason kwana-kwana, sirrinki keda mijinkine kawai a rayuwa bazanso saniba, domin ALLAH ya haramta bud'e wannan, saikuma yankin sirrinsa na rayuwa Wanda yarda da matarsane kawai zaisa ya fad'a mata, shima wannan kirik'e masashi, amma Munaya na fuskanci har yanzu babu dai-daito tsakaninki da mijinki, duk da kin sanarmin da manufar aurenku nazata darajar zuri'ar data shigo tsakkiyarku zai kawo muku sasanci Ku manta da wani auren Contract, duk da na fahimci mijinki jinin mulki na yawo a jikinsa, danne Abu a rai da basar dashi tamkar jinin jikinsa yake, kekam nasan halinki mutumce maison a damu da ita, sannan a nuna mata komai a aikace da furucin baki, kema danaki jinkan Wanda bansan gidan uwarwa kika samoshiba, amma mike wakana a duniyar aurenki? Mikuma kuke shiryawa keda surukarki?”.
Shiru nayi nakasa magana, dan banso fitar da wannan sirrinba har zuwa lokacin da Momma ta bani, duk da nima rashin sanarma y'ar uwata yana damuna, dan bamu ta6a 6oyema juna wani abuba, ko akan aurena daga baya kasa daurewa nayi na sanarmata, duk da na 6oye matanne saboda gargad'in da baba mai kanwa yamin......
Kwanciyarta tayi tana cewa, “idan kinga bazaki iya fad'aba kibar abinki arai yayta cinki, daga k'arshe idan kika rufta auren ya tsinke kekika Sani, kinsandai minene wannan gidan da irin mutanenen cikinsa, dama kullum burunsu kenan”.
Idona cike da kwalla na kamo hannunta, “kiyi hak'uri sweetheart tashi muyi magana”.
Munubiya taiyi kamar ta shareta saikuma ta tashi tana share mata hawayen dake bin fuskarta.
Ta gyara zamanta tana fad'in “wato Munubiya.................🤫✍🏻




Kumuje zuwa page nagaba my guys😉🤩.








ALLAH ya gafartama iyayenmu👏🏻😭






ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻


BOOK 3 👉🏻 1⃣3⃣


..............“Wato Munubiya abinda yasa kikaga inata 6oye miki shine, bansan manufar mahaifiyarsa ba kai tsaye, nidai bayan tabani tarihin

masarautarsu takuma rok'eni nabama Galadima gudunmawa wajen saka idanu akan motsin kowa dazai mu'amulanceni, abinda ta lura shi yafi maida hankalinsane ga mak'iyan waje, gani yake kamar a masarautarsu babu mai iya cutar dashi. tace min Galadima bashi da yarda ko kad'an, sannan mutumne mai zama akan ra'ayin kansa, tankwarashi sai ita da baya iya bijirema umarninta”.
    “Na damu kwarai da gaske Munu.. Dan rayuwa da irin mai wannan halin yanada wahala, musamman mutum mara yarda, wlhy nadad'e a gidannan bai bar zargin an turoni Na cutar dashi bane, saida Momma tafara koyamin dabarun zama dashi, tace nadaina jin tsoronsa, inhar yafad'amin magana Na daurema zuciyata Na dinga maida masa murtani, a tak'aice dai nake masa tsiwa. A lokacin da taimin wannan maganar abin yaban mamaki, Yaya uwa za tace aringama d'anta rashin kunya ko rashin raga masa?, kema kinsan bawai bazan iya baneba, amma yanamun matuk'ar kwarjini, bansan kuma miyasaba nakejin shakkarsa a zuciyata, har gobe idan yamin Abu zan maida masa murtani wlhy saina dage saboda tsoro. Saida zamanmu yad'an fara nisane Na fahimci abinda take nufi, inda bana nuna masa banida tsoroba zansha wahalar zama dashi, sannan bazai ta6a aminta dani ba ya saki jikinsa, zaita d'aukatane a y'ar lek'en asiri, Dan babu abinda ya tsana irin karinga masa Abu kana nuna tsantsar biyya da kwantar masa dakai, shi a wajensa kazo cutar dashine kawai. Maganar zuwana wanka itace tadage akan sainazo, sannan tace duk zuwan da zaiyi wajena Na nuna masa cewar.  nifa bazan koma gidansa ba, dan bazan iya da hallayarsa ba, tadai nunamin dukkan dabarun dazanbi Na dinga zungurinsa da zancen, to ni wlhy ban fahimci manufartaba, tunda nasan babuma Wanda yasan mafarin ginin auren namu, daga ni sai shi, saikuma ke dana sanarmawa. yau kuma namasa zancen rabuwarne da nuna masa zan shayar dasu Abdurraheem ne Na wata shida nayi aurena nima, shinefa yahau kaina da bala'insa, wai babu wawan daya Isa shi ya k'etara gona wani yako ra6eta, koda kuwa ace gonar ta jinginace, inkuma hakan ta faru kobaya numfashi bai yafeba”.
      Munubiya ta zaro ido waje Dan mamaki, saikuma ta tuntsure da dariya harda rik'e ciki, galala nayi ina kallonta, danni banga abin dariya ananba.
    Saida tayi mai isarta sannan ta zauna dak'yau tana fad'in “yi hak'uri sweetheart, wlhy mijinkine yabani dariya, amma anya kuwa mahaifiyarsa batasan manufar aurenkuba?”.
       “Ta ina zata Sani Munu.., shidai wlhy nasan bazai fad'aba, Dan nakula yanada masifar zurfin ciki, balle yasan abinda yay bamai k'yau bane, tunda a al'adarmu da addininmu hakan ba tsarinmu bane, nadad'e ban iya fahimtar matsalarsaba, saikuma naita tambayarsa yamin banza, sai daga bayane naringa Neman dabarun samo kansa harya sanarmin da damuwarsa”.
         “Eh bank'i ta takiba, amma a ganina koshi bai fad'a mataba kina ganin Muftahu bazai fad'aba? Nifa tun pills daya zuba muku nafara zargin anya bada k'yak'yk'awar niyya yayi hakaba?”.
      “Kai Munu.. ALLAH bana tunanin haka, gani nake kawai itama da tata manufar, Dan batason halayyarsa ta shiru-shiru d'innan da k'untata kansa dayake akan yawan damuwa kodan ciwonsa, Dan tace min ciwonsa Na yawan motsawa a baya saboda yawan shiga damuwa da yakeyi, gashi bazai yarda kowa yasan matsalarsa ba saboda tsatstsauran ra'ayinsa, itakuma bataso Dan abaya yanda kikaga Sauban k'animsa da faran-faran haka shima yake, amma tunda ya fahimci miya kwantar da mahaifinsa saiya canja musu gaba d'aya, maganar ma saiya gadama idan kayi yake amsaka, abinda Na lura yanzu kuma wannan abun yarigada yazame masa jiki gaskiya”.
         “dukna fahimceki Munaya, amma abinda Na lura kamar wata alak'a mai k'arfi da kusanci takeson ginawa tsakaninki dashi, Dan babu wata uwa dazatasa matar d'anta ta ringa ma yaronta rashinkunya, itakuwa tasan halin d'anta ciki dabai, tanada dabarun dazata d'oraki domin shi su k'ayatar dashi harya ringa kallonki a matsayin mata ba auren wucin gadiba,  dukkan maganganun daya fad'a miki d'azun wlhy Na mutumne mai nuna tsantsar kishi, ALLAH ma yasoki dabakizo da kumburarriyar fuskaba wlhy”. ta k'are maganar da sanya dariya.
    Harara Na zuba mata ina fad'in “nikuma kamar wata sokuwa saina zauna ya dakeni, danma gaskiya shiba mutum bane mai yawan saurin hannu, saidai k'asaita da shariyar tsiya, kaita magana yayi tamkar bai jikaba”.
       “Yo Sweetheart ai mulkin kenan ko, wannan shine ake kira sarautar, idan bashida wannan izzar da k'asaita lallai baicika jinin basarakeba, shi nashi ai da sauk'i tunda yasan darajar d'an Adam. Amma lallai ki godema ALLAH da samun suruka irin wannan, to amma ke kina sonsa yanzu?”.
     Harararta nayi, nazame Na kwanta batareda Na bata amsaba, ta d'akamin duka a cinya tana fad'in “Munafuka kema sonshi kike, wannan jan ajin naku dukshi ke cutarku, shi mulki ya hanashi ya fad'a, ke shegen jan aji yahanaki ki nuna masa, basai kuyitayiba har yaranku su taso su ganku a haka”.
      Baki Na murgud'a mata ina Sosa wajen data dokenin, Dan naji zafi, cikin harara nace, “ai ba a haifi namijin dazan fara furta masa ina sonshiba koda ace son nasa zai halakanine, k duk taurin kai da miskilancin Yaa Marwan ince saida yace yana sonki sannan kika amsa masa?, saini kikeson Na zubar da tawa darajar, salonma ya d'auka kwad'ayine ya sakani hakan, zai ru6e kuwa inhar jira yake sainace Sameer ina sonka, bank'i idan naga zan iya nabika ta wata hanyarba, amma shida yace auren Contract shine zai dawo ya gyara kuskuren da yayi da kansa, shiyyasa nake son canja masa tunaninsa ta hanyar tunatar dashi yasan mace tanada daraja,  ba'a sakata lokacin da akaso sannan ayi tunanin cirewa lokacin da akai niyya, wadda batasan darajar kanta bace zata amince da hakan, nikuma bana cikinsu danba Auren kwad'ayi nayiba”.
     Munubiya tayi dariya tana jinjinamin, “yayi k'yau gimbiya matar Sarkinmu mai jiran gado, wlhy kin burgeni dan wannan shine kima, amma dai a sassautama galadimanmu, Dan naga alama shimafa ya zurma fad'arce kawai mai wahala a harshensa, amma mizai hana mubi wasu dabarun Dan bud'e bakinsa”.
      “babu wasu dabaru dazamubi sweetheart, Dan nidai bazanbi ta hanyar talla da jikina ba a gareshi danya soni, randa Na tsufafa? K'yawun jikin ya 6ata ko Na nakasa?, bazanbi ta yaudaraba ko wani kwarkwasa, randa yaga wadda yakeso tsakaninsa da ALLAH fa? komai zan masa bazai birgeshiba, Dan soyayya ta gaskiya daban take, baruwanta da k'yau ko k'yale-k'yale, zandai iya k'yautatama zuciyarsa domin dukkan zuciya tanason mai k'yautata mata, amma son gaskiya nakeson mijina yamin, bana k'yalek'yalen duniyaba, ko tsufa ya kamani bazai bar sonaba, ko nakasa ta kamani bazai bar sonaba, ko babu dukiya tattare dashi bazan gujesa ba, idan ciwo ya kamani koya kamashi zamu tattali juna saoda tausayi da rahamar dake cikin Auren da soyyar gaskiya da mukema juna, ko kishiya yatashimin nasan son gaskiya yakemin bazan ta6a saka kaina a matsananciyar damuwa ba tunda inada yak'ini akan son gaskiya yakemin, bazai ta6a tozartaniba, sannan ban Isa hanashi yaso matarsa ba Dan ni yana sona, nafison amin komai tsakani da ALLAH bada yaudaraba kema kinsani, Dan haka muyitayi inhar bai gajiba nima bazan gazaba”.
      “Duk mace haka yakamata tasan darajar kanta, takumayi abinda mijinta zai sota son gaskiya Munaya, wannan k'arancin soyayyar ta gaskiya da Muke fuskanta ayanzu shineke yawan ruguje rayuwar aure, mafi yawan mazan sukanso macene domin wata halitta ta jikinta, dasun sami nutsuwa dake kuma shikenan haskenki ya dusashe a idanunsu, wasu kuma Matan mai dukiya ne hangensu ko k'yau, da zarar mijin yazo babu saikiga wuta ta tashi, kokuma bashi dashi dama duk k'aryane, dakinje bakiga abinda kika aureshi danshiba babu sauran zaman lafiya kuma, gaskiya muna cikin matsala yanda taron biki yake a wannan zamanin kawai ya Isa ruguza dukkan albarkar aure, amma ni dazakiji ta tawa tunda shima yana sonki kubar wannan 6oyewar mana”.
      “Munu, idanfa bai canjaba nima bazan canjaba, bakinsa daya furta shi nakeso ya gyara da kansa”.
      “lallai to sai kiyita 6oyewar, idan ya nemi kasheku duk zaku fiddoshine kowama yaji, ai nama godema ALLAH da Muftahu dan ta silarsa ALLAH yamuku dabaibayi da yarannan, Ubangiji sarkin hikima kenan, naga Wanda zai iya barma wani ai”.
     Banza namata nayi kwanciyata, harma barci 6arawo ya saceni. Munubiya ta d'auki wayar munaya tana murmushi, tayi abinda zatayi ta ajiye mata abarta itama ta kwanta.



★★★★

       Galadima daketa juye-juye a gado abin duniya dukya ishesa saijan tagwayen tsaki yakeyi ya kalli wayarsa datayi alamar shigowar sak'o, harzai share dai saiya kasa, dan numbers d'in cikin wayar duk masu muhimmancine.
     Jawo wayar yayi ya danna ta kawo haske, hoton y'an uku ya bayyana a screen d'in, saida yad'an ja wasu Seconds yana kallon yaransa sannan ya bud'e massage d'in, ganin wadda ta turo sak'on sai mamaki ya kamashi, Munayar da inhar bashine ya kirataba bata ta6a d'aukar waya ta kirashiba ita, amma yau itace harda message? Dukda baiyi tunamin samun mai dad'iba haka yabud'e dai, yasan bai wuce maganar data damu mutane da itaba...
      Ina fatan ka koma gida cikin aminci da farinciki? Yaranka namaka fatan alkairi da addu'ar samun k'yak'yk'yawar Nutsuwa mai tarin hak'uri.
        ya dad'e idonsa akan wayar yana kuma bitar sak'on, baisan murmushi ya su6uce masaba, watoma yaransa ba itaba?, kai jan ajin yarinyarnan yayi yawa, da ace agidan sarauta ta fito lallai bayi da hadimai sunga takansu, ya ajiye wayar yana gyara kwanciya, jiyay zuciyarsa tayi sakayau, dandanan barci ya d'aukesa, dama video call yayi dasu Momma, dan tun bayan daya sauka bai kuma kiransu ba saboda yau ya yini busy, ga tunani sunma kansa yawa, Munaya tagama saitashi yad'an samu nutsuwa amma shine takuma hargitsoshi da abinda zuciyarsa bazata iya d'aukaba.


..............


    Washe gari

Munaya dai batasan minene ya faruba, dan Munubiya goge sak'on tayi bayan ta tura, da safe kuma ko alamar tayi wani Abu bata nunama Munaya ba.

        Wajen tashin hantsi saiga Aunty Salamah tazo, cikin farin ciki duk muka mak'alk'ale mata, ta rik'e baki tana fad'in “oh ni, ALLAH yabani y'ay'an da basu San sun girmaba”.
       Innarmu tace, “wlhy kuwa salama, baki moreba kam”.
    Laraba dai tanata musu dariya.
   
     Kayan gyaran jiki Na musamman Aunty salamah ta kawo musu, takuma bisu da gargad'in wlhy kowa tazage tayi, harda rok'on laraba ta saka musu idanu Dan ALLAH.
     Gaba d'aya yau a gidan tama yini, hakanne ya d'aukema Munaya damuwar data tashi da ita.


 ★★★★★★*★★★★★★

       Tunda yadawo salla ya koma barci, saboda jiya bai wani samu yin isasheba, wajen 10 ya farka, brush kawai yayi yazo ya zauna yana hada wasu takardu, sosai aikin ya d'auke hankalinsa saboda muhimmancinsa, sauban datun d'azun yay shirin tafiya yagaji da jiran fitowar Galadima Dan haka yazo yaymasa knocking, Dan yanason biyawa wajen Munaya kafin ya wuce.
      Galadima dake zaune bakin gado ya baje takardu yana kuma rubutu a jikin wasu ya d'aga kai ya kalli Computer d'in dake hasko masa dukkan CCTV camera's d'in sashen nasa, ganin Sauban ne sai ya d'auke idonsa yace ya shigo.
         Zama sauban yayi saman stool d'in mirror ya gaida Galadima, hankalinsa nakan aikin dayake ya amsa. yace, “Dama katashi?”.
       “Wlhy Yaya tun d'azun Na tashi, naga baka fito baneba gashi inason kafin Na wuce nabiya Na gaida Aunty gimbiya naga my Triplet's kuma”.
        Galadima baice komaiba, sai had'e takardun gabansa daya shigayi, Sauban yamatso bakin gadon yana tayashi, saida suka gama tsaf, ya shiryasu cikin wani k'aramar briefcase sannan ya kalli Sauban dake zaune,  “Mik'omin System d'incan”.
        Sauban yad'an marairaice fuska cikin tausayawa. Yace, “haba yaa Sam kad'an huta mana”.
       Da mamaki Galadima yace, “to idan Na huta kaine zakamin aiki?”.
     Girgiza kai Sauban yay

Join Our Groups

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login