Showing 258001 words to 261000 words out of 356830 words

Chapter 87 - RAINA KAMA Complete Hausa Novel

12 Oct 2024

185387

ban ta6a ganin uwa mara kawaici akan y'ay'an fariba saike”.
Kunyace ta kamani, na 6oye kaina a jikinsa ina murmushi.
Galadima ma murmushin yake yana shafa bayanta.
Sun dad'e a haka sannan na tashi daga jikin nasa gudun kar khalel ya farka ya ganmu a haka, shima ya fahimceni, dan haka bai hanani ba.
Yace, “Addu'arki yake buk'ata da taka tsantsan, dukda ba wayonmune zai hana Ubangiji ikonsa ba idan yaso, sai yakai watanni 6 zai fara ganin doctor insha ALLAH, ya mik'a mamin ATM d'insa, ga wannan dukdai abinda yataso saiki cira, amma a bimin kud'i a sannu ni talakane mai yawan buk'atu, ga Abdurraheem ya k'aru shima, to idan bawa bai nema kud'iba ai yagama shiga uku a wannan zamanin daba kowa ya damu da damuwarka ba, inadai kuma gargad'inki ki kula min da yara, yau zamu koma India, amma kwanaki uku zanyi insha ALLAH na dawo”.
Nace, “ALLAH yabashi lafiya da dukkan al'ummar ANNABI, nagode sosai, saidai kuma inason kawai idan na tafi shi.......”
Hannu ya d'aga min, “karki damu nasan maganar Aurenmu ne, kamar yanda na alk'awarin inhar komai ya fito kan shekara zamu rabu, inkuma ba a samu yanda akesoba shekara biyu inakan Sani, sauran bayani kibani lokaci zuwa kammala abinda ke gabana OK?”. ‘yay maganar yana kallonna’.
Kaina kawai na d'aga masa ina had'iye abinda ya tokare mak'oshinna.
Bai sake cewa komaiba ya mik'e yana kallon agogon hannunsa bak'i, “ku fito”. yafad'a yana ficewarsa.
Da kallo kawai nabisa idonna yana cika da k'wallan dabasan na minene ba.


******

Munaya tasamu rakkiyar wasu daga masarautar, bisaga jagorancin Galadima da suke zaune a mota d'aya, daga ita har shi babu Wanda ya tankama wani koya kalli wani, shi tundama suka fito latse-latsen System yakeyi hankalinsa kwance, itama ta basar gefe tana kallon waje dukda glass d'in mai duhune.
Sun Isa k'ofar gidan k'arfe 5:24pm, bayan su Aunty Mimi sun fita duk suka shige cikin gidan tareda Kuyangi.
Munaya tayi yunk'urin fita amma sai taji motar a kulle, Sarkin Mota ta kalla sai taga harya fice, ta dawo da kallonta ga Galadima daketa aikinsa tamkar ya manta a mota yake.
Shareshi nayi kamar nima bazanyi magana ba kamar yanda ya basar, amma saina kasa, na kuma kallonsa murya a sanyaye nace, “ka bud'emin mana, miye ma'anar zaman namu? Wanima saiya zargi wani Abu ai?”.
Banza yay mani tamkar bazai tankaba, kusan mintuna biyu sannan yace, “idan sun zarga laifine? Naga Sadaki na biya”.
“Hummm”. Munaya ta fad'a kawai tana d'auke kai.
Saida ya gama shan k'amshinsa sannan ya ajiye lap-top d'in gaban motar yana matsoni. da mamaki na kallesa, “yalla6ai lafiya?”.
“ita ta kawo haka”. ‘yafad'a yana wani ciccijewa da jawoni jikinsa’.
Tamkar zan tsala kuka haka naji, dan naji zafi, mukaima juna kallon ido cikin ido, idona da kwalla tafara taruwa sai wani marmar yakeyi, matso da fuskarta yay sosai, cikin magana rad'a yace, “kin fara kewata ne?”.
Baya naja da kaina ina tura baki da yamutse fuska, amma sai hannunsa daya sa ya tokareni ya dakatar dani daga matsawar, yakuma matsowa gaf, numfashin junanslmu na sauka a fusakar juna, a hankali yafara hura min iskar bakinsa saman ido, babu shiri na lumshesu, hawayen da suka taru suka zubo, sai kawai ya shiga sumbata ta.
Tuni nabashi had'inkai babu wani gardama, saida yay yanda yakeso da ni sannan kowa yakoma gefe, wata y'ar k'aramar souvenir bag ya d'ora mani a cinya, sannan ya cire luck d'in motar, saida naja wasu Seconds nasamu dai-daita sannan ta bud'e na fice rik'eda bag d'in daya bani, ban yarda nasake koda kallonsa ba.
Shima harta fice bai kuma kallon nata ba.

Jiki a sanyaye nashiga gidan, matan gidanmu duk suna falon innarmu gaida bak'i, ina shiga muka rungume juna nida Munubiya muna hawayen da ita Munubiya tana tayani ne, nikuma bansan dalilin yinsuba🤣.
Kowa dai da kallon mamaki ya bimu kawai.

Su Aunty Mimi basu dad'eba sosai suka tafi, anbar laraba anan zata zauna damu.
Samha da khaleel harda kukansu.


******


Bayan komawar su Galadima masarautane yakejin wai ba'aga Harun ba, k'ala bai tofa ba balle nuna alamun damuwa ko jimama.
Saima shirinsa Na tafiya ya fara hankali kwance, yaje yayma mai martaba sallama. Suka wuce airport abinsu, dan jirgin 7:30pm zasubi.............✍🏻
ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻




BOOK 3 👉🏻9⃣➖🔟


..............Kwana biyu Galadima ya k'ara suka dawo Nigeria shi da Sauban, burinsa a yanzu ya fuskanci abinda ke gabansa da iyakar k'arfinsa da basirarsa, bai shiga masarauta ba saida ya had'u da baffi yabashi wasu takardu.
Dole yay barcin wasu awoyi domin samun nutsuwar gajiyar tafiya, sannan yay shirin fitowa, ya lek'a sashen mai martaba dansu gaisa saiya tarar yanada bak'o, jakadiya sarkin gulma ta gutsiri goronta tana kallon Galadima, “Ranka ya dad'e ai takawa yana tare da bak'one, bak'on kuma Na lura Wanda ba'ason sanin dami yazone, dan kullum ganawar sema k'unshe yakeyi da takawa”.
Shiru yamata tamkar bai jiba, danshi mutumne da baya shiga abinda bai shafeshiba, kowa yasan haka a masarautar, shiyyasa Duk makircin masarauta bazaki ta6a samun wani ya sakoshiba, kokuma kawo masa gulmar wani.
Ganin haka itama jakadiya sai taja bakinta tayi shiru.
Galadima ya mik'e yana kallon agogon hannunsa, “Bara naje, zan dawo anjima”. ba tare da ya kalleta ba yay maganar yay kuma ficewarsa.
Da kallon ta bishi tana cigaba da 6allar goronta, tace, “wannan murd'ad'd'en da ace zai saurara dana bashi sirrika da yawa wlhy, amma ina, maganama ta kud'ice a garesa, ka huta wlhy, wai gurgu ya za6i zaman waje d'aya😏”.


😂😂🤭
_________★


Kwance yake jikin seat d'in mota idonsa a lumshe, duk yanda yaso ture zancen jakadiya a ransa karyay tasiri ya gaza hakan, sai kaikawo zancen ke masa, tabbas bak'o mai muhimmanci ne kawai zai iya ganawa da mai martaba har cikin turakarsa, to mike faruwa ne haka?, bashida amsa dan haka ya cije lips d'insa, tafiyar tasu yau dagashi sai sarkin mota, ya hana dogaransa binsa, gidan da su Nuren suke ya isa, dukda shi Nuren ma baya nan yaje gida saboda kiran gaggawa da papi yamasa, Muftahu kam dole kullum a Masarauta yake kwana, saida taka tsantsan ma yake zuwa gidan da rana, saboda rashin ganin Harun yanzu motsin kowa lura akeyi dashi. Su Ameer ne suka bud'e musu k'ofa Sarkin mota ya shiga, yanayin parking suka bud'ema Galadima ya fito, cike da girmamawa suka gaisheshi, ya amsa musu da d'an sakin fuska, sannan ya tambayesu Yaya aiki?.
Da Alhmdllh suka amsa. Har cikin falon sukai masa rakkiya, babu kowa cikinsa, amma ko ina k'al yake a gyare, ga k'amshi mai dad'i yana tashi.
Yayi zama yakai Na 10minutes saiga baba Rabilu shida wani dattijo da zai iya girmarsa kad'an, kokuma wahalace ta girmamawa tsufan nashi oho.
shidai Galadima kallon mutumin yake tamkar ya sanshi, amma ya manta a ina.
Zama sukayi, cikin girmama juna suka gaisa, sukaima Galadima barka da dawowa, da d'an guntun murmushi ya amsa, har yanzu dai idonsa akan dattijonnan.
Lura da hakan da baba Rabilu yayi saiya murmusa, yace, “Ranka ya dad'e ka shaidashi ne?”.
Galadima ya hard'e k'afafunsa yana murmushi, yace, “baba rabilu inadai masa kallon Sani kam”.
Baba Rabilu yay k'aramar dariya yana kallon dattijon dake durk'ushe a k'asa shima yana Murmushi, sannan ya dawo da kallonsa kan Galadima yace, “Zaka sansa Ranka ya dad'e, amma gaskiya kana tare da k'uruciya lokacin, Sunansa Badi, mahaifinsa shine mai kula da dawakan Sarki a wancan lokacin”.
Da sauri Galadima ya sauke k'afafunsa daya hard'e, cikin tsantsar mamaki yace, “Baba Rabilu kana nufin wannan Badi ne?”.
Dattijo ya risinar da kansa k'asa alamar girmamawa ga Galadima. Yace, “Nine ranka ya dad'e”.
Rasama abinda Galadima zaice yayi. Sai bakinsane ke motsawa alamun yanason maganar amma ya kasa. Sai ido daya tsurama Badi cikeda tunosa a lokacin da shi yake d'an shekara 5 kacal a duniya, dukda bazai yuwu ya iya tuna komaiba, amma tabbas yasan fuskarsa, yasan kuma shine mai kulawa da barga ta dokunan masarautarsu shi da iyayensa, a lokacin inhar baiyi k'aryaba Badi bazai wuce shekaru 33 ko 35 ba. Amma yau gashi zaune gabansa furfura da girman tsufa duk sun bayyana a garesa......
Sallamar Muftahu ce ta katse tunanin galadima, Muftahu ya zauna suka gaisawa da Baba Rabilu, sannan ya gaida galadima, idonsa dai nakan Badi shima.
da k'yar Galadima ya amsama Muftahu gaisuwarsa.
Badi dakema muftahu kallon sani ya gaisheshi cike da girmamawa (Dan ALLAH yayisa mutum mai yawan rik'o).
Muftahu dai kasa hak'uri yayi, ya kalli baba Rabilu yana neman amsa.
Murmushi baba Rabilu yayi, ya gyara zamansa yana fad'in, “Yalla6ai baka ganesa bane?”.
Muftahu yace, “Banma ta6a ganinsa ba alhaji”.
Badi ya kalli Muftahu sannan yay k'asa da kai. Yace, “Nikuwa kaga Na ganeka yalla6ai, dan bazan manta sanda kukan rako Yarima ba idan za'a fita da shi bakin ruwa shan iska, ka kan nace sai a doki d'aya zaku tafi kai da sauran abokan nashi”.
Murmushi Muftahu yayi, ya kalli Galadima dayay shiru yana kallon Badi kawai, yasan yana tuna bayane, kuma akwai tambayoyi fal ransa sai dai ya kasa furtawa, janye idonsa yayi ya maida ga Badi, yace, “Amma Badi minene ya faru da kai harka bar masarauta? dan bazan iya tuna wani abuba a wad'ancan shekarun namu, yanzu kuma daga ina kake?”.
Zama Badi ya gyara. Yace, “lallai labarine mai tsawo da Nisan zango, amma a tak'aice dai abinda zan iya cewa shine.....”.

“Bayan kwanciyar mai martaba adalin sarkinmu jinyar da ba'asan mafarinta ba da wata biyu kacal ranar wata lahadi da tashin hantsi munje kasuwa ni da mahaifina mun sayo abincin dokuna mun dawo, muna tsaka da sauke kaya a barga saiga wani mutum a tsakkiyar harawar dokunan cikin a kori kurar da muke zubo kayan kenan, dagani har mahaifiyata da mahaifina mun razana matuk'a, harma k'anwata taso tayi ihu amma mahaifiyarmu ta toshe bakinta saboda rok'on da mutumin kema babanmu akan muyi shiru Dan ALLAH, a razane matuk'a mutumin yake dan ko ina Na jikinsa mazari yake, yace a taimaka masa da ruwa yasha zaimana bayani, iya mahaifiyarmu ta nufi d'akunanmu dake cikin bargar dagacan gefe ta d'ebo masa ruwa a randa cikin kwanon sha ta kawo masa, babana ya taimaka masa ya fito daga akori kurar, ya zauna bisa buhun harawar da muka fara saukewa, ruwan ya kar6a ya kafa kai saida ya shanye kusan rabi sannan ya ajiye yana musu godiya, wani Abu irinna d'aukar hoto (camera) ya fiddo a cikin aljihunsa ya mik'ama mahaifina cikin yin magana da k'yar. yace_”.
“Sarkin Barga ga wannan abun, nasan zakayi mamakin miyasa Na bakashi, to banida wajen daya dace Na damk'ashi sai wajenka a kaf masarautarnan, Dan kaine hanyata mai sauk'i, akan wannan abun aka biyoni za'a kashe, shine ALLAH yabani ikon shiga motarku, dan nashigo tacikin kasuwa domin tsira da raina shine Na ganku, karka bama kowa camera d'innan sai d'an Sarki, Yarima Sameer, kokuma d'iyarsa, gimbiya Haneefa, ko matarsa uwargidansa wadda ta haifi su Yarima d'in, harda wad'annan takardunma, nasan ni tawa ta k'are Dan babu makawa saisun kasheni, Dan ALLAH ka tabbatar cikin mutane ukunnan ka bama wani, nasan yarima bashida wayon dazai fahimci minene, amma idan ka nuna masa yabama mahaifiyarsa zai bata, dukkan abinda ya faru da mai martaba yana acikin wannan Camera d'in, ni zan koma, Dan banason wani ya fahimci nama shigo masarautar nan balle har asan Na gana daku”.
“duk yanda mahaifana sukaso tsaida mutuminnan sun gaza, dan ya tabbatar mana dolene yabar masarautar a lokacin, saboda akwai munafukan da sukasan abinda yafaru da Mai martaba. Sai dai kuma abinda bamu saniba shine, Ashe dukkan abinda ya faru akan idon waziri ne, dan haka a wannan dare yabiyo sahun abinda mutumin yabada, mahaifana Na barci ya tashesu akan su bashi, sukace basusan mi zasu bashiba, shine ya kashe mahaifiyarmu wai dan baba yaji tsoro yabashi, dukda baba ya razana hakan baisa ya bashiba, ya yarda d'in gwamma a kasheshi shima da dai yabada , daga k'arshe shima ya kasheshi, k'arar da mahaifina yayi sai dukkan dokuna suma suka d'au haniniya. Hakanne ya sakani farkawa a rud'e Na fito daga d'akina, ina sako k'afata a d'akin mahaifana, Waziri Na cakama baba k'arfe a mak'oshi,, babana ya rik'e mak'ogwaronsa da hannu, yaringa min nuni da d'ayan hannun alamar Na gudu karnayi magana kuma, Na fahimci haka saboda ni baba yabama ajiyar abin d'aukar hoton da takardun, inhar iyayena zasu iya jurar mutuwa akan su bashi ni mezai hana na bi umarnin baba na gudu da abun, ko takan iyalaina banbiba na gudu ta hanya mafi sirri dana Sani, lokacin dana fito zan gudu waziri ya farga dani, hakanne ya sakashi biyo bayana, ganin bazai cinmini ba saiya saka dogarai masu tsaron k'ofa akan su bini wai na kashe iyayena zan gudu. Na rasa Inda zan dosa da wad'annan kaya saboda na tabbata ana bina a baya, saboda mun had'a ido da waziri, na shiga cikin jeji sosai, dan a wancan lokacin gari bai gama dunk'ulewa waje d'ayaba irin haka, Masarautar gagara badau ba tsakkiyar gari takeba kamar yanzu, dabarar hawa bishiyace tazomin dan haka na hau itaciyar wani Kalgo dake kusada k'oramar da mukan raka Yarima hutawa, har dogarannan da waziri ya saka su biyoni suka iso wajen domin nemana, ALLAH bai basu ikon ganinaba, saima suka wuce ni, lokacin sanyine sannan, nasha sanyi dan na wahala, sosai na fita hayyacina, abin mamaki da asubahi sainaji hayaniya a kusa dani, ido na bud'e da k'yar saboda tsantsar jigatar da nayi da muku-mukun sanyin wannan lokacin, wannan bawan ALLAHn nagani tare da Wanda yazo masarauta ya bamu abin d'aukar hoto (ya nuna baba Rabilu), hakanne ya sakani jin dad'i na sakko a nufin maida masa abinsa, nakuma sanar masa dalilin abin d'aukar hoton an kashemin iyayena, sai dai ina sakkowa wasu mutane na isowa wajen a mota guda biyu, yunk'urin guduwa mukayi mu duka ukun dukda su saima lokacin suka farga da ni a wajen, sun sami damar kama Wanda ya bama mahaifana abin d'aukar hoton, saboda kamar yaji ciwo a k'afa bazai iya guduwa ba, shine ya ringa fad'a mana mu gudu karmu sake mu basu abinnan. Iya k'arfinmu muka ringa gudu a lokacin Ranka ya dad'e, nashiga tashin hankali ganin rana tsaka masifa tazo ta haye mini ba tare dana san farkonta ba, gashi na rasa iyayena, na baro iyalina da k'anwata, bansan halin da suke cikiba, na samu damar shiga wani k'auye, Anan ne nasamu taimakon wani tsoho makaho, dan shine yabani mafaka ta tsawon shekaru 4, makahon tsohonnan yana zaune ne da matarsa amma ita tana gani, lokacin da jama'ar gari suka farga dani a gidan sai sukaje suka sanarma mai unguwar yankin, shikuma ya sanarma dagaci, har gida akazo aka tafi dani wani babban k'auyen dake kusa dasu inda dagacin yake akamin tambayoyi nida tsohonnan makaho, koda aka tambayi baba makaho saiya sanar musu ni d'an y'ar uwarsane, nazo ne na koyi sana'a na koma garinmu, dagaci yarigada ya yarda da baba makaho shiyyasa ya amince, aka kuma barni nacigaba da zama a k'auyen, tundaga wannan lokacin nasamu saken zama k'auyen gamji, ban sake waiwayar masarauta ba har tsawon shekaru hud'un nan. Saida ALLAH yayma baba makaho rasuwa sannan, matarsa gudun kar naci gadonsa shine tace yakamata na koma gida hakanan, ban mata musuba na had'o y'an kayana da abinda na samu a k'auyen da wad'annan takardu da abin d'aukar hoto nabaro k'auyen ina kuka saboda sabo. Sai dai abinda ban saniba Ashe anata bibiyata har lokacin, tun a hanyata ta shigowa gari wasu mutane suka farmin, na zubda komai nawa amma banda akwatin dana zubo abin d'aukar hoto d'innan da takarda, a cikin wannan gudu sai Ubangiji ya had'ani da wani bawan ALLAH akan besfa, ya bigeni, naji mummunan ciwo dan alamomin fitar rai sun bayyana agareni, cikin magana da k'yar, na mik'a masa akwatin ina rok'onsa dan ALLAH ya kar6i akwatinnan, ya Isar da shi masarauta amma yarima Sameer ko gimbiya Haneefa zai bamawa, ko mahaifiyarsu, bayansu karya bama kowa, idan bai samu damar badawa a yanzuba yabari sainan gaba inhar Yarima Sameer yay girman mallakar hankalinsa, zai iya kwatama kansa y'anci saiya bashi, na rok'esa karya ci amanata dan ALLAH, na aminta da shine shiyyasa na bashi....., da Sauri ya amsamin da insha ALLAH bazaici amanataba dan shima yana aikin jaridane, iya abinda naji kenan Daganan na suma a wajen, ban sake sanin

Join Our Groups

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login