Showing 18001 words to 21000 words out of 52733 words
sauran jama'a suka zagaye gadon nasa suna "sannu saifullahee"
"Brother say something mana ko maji dad'i cewar hesham ,
dariya 'yan wajen sukayi kakus yace
" heesham rabu da ja'irin yaro d'an nema tun d'azun nake masa sannu Amman ko q'ala kanzur baice ba".
dadyn deejart ya yi dariya yace
"baba kasan d'an nawa da rashin son magana shiyasa,
"dan haka kada kuga laifin sa"
Duka wajen dariya sukeyi,
gani sukayi saif d'in ya miq'a hannu ya jawo deejart ta zauna a gaban sa, ya runtse idanunsa sannan ya bud'e su,
Ya motsa bakinsa ya bud'e a hankali ya fara mata magana yanda ita kad'ai takejin miyake cewa,
yace
" aunty suwaye wad'an nan Kuma?
daga ina suka zo?"
Minene kuma rashin son magana da Wannan mutu min yace ban son yi?" nan take gaban ta yayi wata irin bugawa dammm!!!
Kardai yaya saif ya samu mntl problem??????
tuni ta miq'e tsaye jikinta na kyarma ta fita ,ba'a jimaba sai gasu itada Dr hasan da nurse q'waya 2
a bayansu ,
deejart ta cewa iyayen Nata "zasu shiga da yaya saif d'akin bincike,
nan suka tura gadon sa suka fita dashi ,
suka shiga dakin baa binda ke cikinsa sai naurorin da computers ,
kansa a kasa a wata na'urar computer dan su bincika lpiyar q'walwarsa,
ba'a da'u wani
dogon lokaci ba sai ga computer ta ta nuno hoton q'walwarsa 6aro 6aro,
doctor hasan kusan lokaci d'aya suka isa wajen computer da deejart a sukwane, dan q'ara ganewa idanuwansu gaskiar lamarin da computer ta hasko musu ,.
dai dai cikin brain d'in saif daga gefen kansa jini ne ya zurara ta cikin q'walwarsa , Wanda hakan ke nuni da cewar ya samu matsalar shafewar tunani na sanadiyyar kansa da ya bugu a hatsarin da yayi,
da q'arfi deejart tace " what "!!!
L.s of memory???!"
Innalillahee wa'inna ilaihir'rajiun"!!!!ππ»
Wata sabuwa ni deejart π,
Yaya saif Allah baka ikon cinye wannan jarabawar nan da yake maka,
Ta juyo cikin kuka ta dubi Dr hasan tace" kaga ni ko Dr? abinda nace maka Ina tunani game da abinda yaya saif yace gashi ya tabbata "!
Wlh bansan ya Zan tunkari su dady da wannan mummunan labarin ba,!!!
yanxu haka nasan suna cen suna farin cikin farkowarsa yanxu Kuma naje musu da wannan maganar?
gskia wlh bazan iya ba".
nan ta d'uqe tana cigaba da kuka mai cin rai ,
tarasa mike Mata dad'i ma a duniyar.
komi baq'insa take gani ,.
A hankali dr hasan ya zuq'unna a gabanta ya fara Mata tuni da Allah ne ya qaddarowa rayuwar sa hkn, Kuma zai yaye masa a duk sanda yaso, daman bawa bai cika cikakken musulmi face yana rungumar qaddarar sa a rayuwa ,..dole ne in kana raye zakai ta damuwa da jarabawa Kala daban daban.
" kiyi haquri deejart komi mai gushewane a rayuwa
amman fa banda ikon Allah,
A haka har ya shawo kanta ta daina kukan, sai faman ajiyar zuciya da take saukewa.
Ya ce Kuma " karki damu Nasan iyayen ki masu d'aukar q'addara ne a duk sanda tazo masu inda nagani lokacin da shi saif d'in yake a cikin halin coma,
Sun maida al'amurransu ga Allah,
sai gashi Allah ya kawo sauqin al'amarin,
Kar ki damu yanzu ni zanje na sanar dasu da kaina yanda zasu fahimta"
yana kaiwa nan ya miq'e tsaye daga zuq'unnin sa da yayi a gabanta ya fice ,
da kallo ta bi bayansa tana share q'wallan da yatsunta.
Miq'ewa tayi da sauri ganin yanda saif ke dafe da kansa yana bubbugawa,
da hanzarinta ta q'arasa wajen ta kama hannayen sa ta riq'e tana cewa
" kabari yaya saif kada kaji rauni ,
fizge hannayen nasa yayi yana shirin miqewa da na'urar a kansa ba'a kaiga zarewa ba,
da sauri rungumesa tsam ta mayar dashi baya suka kwanta a gadon a tare ,tana saman qirjinsa, wato
q'irjinta na saman nasa knn,
ta dannesa da breast dinta ta hanasa motsin kirki,
wato ta hanasa miq'ewar tsaye knn,
cikin sauri ta miq'a hannun ta a ,,,,,,,,
Xayynebπ€π€
ππππππ
ππππππ
*doctor deejart*
π
By
Xayynebπ€π€
*Fasaha online writer's f o w*
*Dedicated to my daughter deejart*
π
Ώ1β£7β£π΅
ππππππ
Cikin sauri ta miq'a hannun ta a kansa ta zare na'urorin sannan ta miq'e zaune,
still bai bar q'oqarin tashi ba a zaunen, Wannan karon q'yalesa tayi bata hana saba illa tagumi da tayi kawai ta tsura masa idanuwa kawai tana kallon sa.
A can cikin d'akin su kakus dr hasan ya shiga ya isa inda wata kujera take spy ya zauna,
kakus ya dubesa yace " doctor da fatan dai babu wata matsalar ga saifullahee ko?"
Dr hasan yayi d'an shiru yana jinjina maganar da zata fito bakinsa zuwa kunnen su,
sai kuma ya tuna bafa zaka iya ja da ikon Allah ba fa,
A hankali ya d'ago Kai ya dubesu yace "am alhj in ba zaku damu ba ina son zan muku wata magana amman Kafin nan kunsan dai Allah shine ke saukarwa da bawa jarabawowi Kala kala dan ya aunasa yaga shin Wannan bawan nasa zai iya da'ukar wannan kaddarar daya d'ora masa koko?
Cikin ikon Allah zakaga in har ka daure ka karbi q'addarar nan tofa Allah zai baka lada akan hakan Kuma in yaso ya yaye maka Wannan matsalar
a lokaci d'aya,
in kuwa ka bujerewa q'addarar nan da ya d'aurama to zai barka yaga zaka iya yiwa kanka maganin koko?
fatan kun fahimta da magana ta Alhj?
gaba d'aya wajen yayi tsit,!
jikin kowa yayi sanyi,
dansu a zatonsu ko saif d'in ne ma ya rasu,
dadyn saif ya juya yana kallon fuskar kowa na wajen ko q'waqqwaran motsi ba'a samu Wanda yaiba ,
tsaida idanunsa yayi ga momyn saif da hawaye keta sauko mata tana faman share su a 6oye,
shi kansa yasan duk yanda yake son saif to fa bai kai ga momyn tasa ba, dan har ciwo tayi lokacin da saif d'in yake halin rayuwa da babu.
dan shi d'aya Allah ya azurtasu da shi,
gyaran muryar kakus ne ya dawo da dadyn saif daga tunanin daya shiga.
Kakus yace
''duk munji bayananka likita, Kuma insha Allah komi zai fito daga bakinka munyi imani dukan mu masu tawakkaline da abinda Allah ya q'addaremu dashi,
dan zuciyarmu tsayayyace a kan q'addarar da ubangijinmu ya nufemu da ita a rayuwa,
dan haka in mutuwa saifullahee yayi ka fad'a mana likita insha Allah zamu karbi qaddarar mu da hannu 2 2,
Dr hasan ya girgiza Kai yace
"Alhamdulilla alhj,
Kuma naji dad'in fahimta ta da kukayi sosai,
Kuma a taq'aice dai d'anku Saifullahee ba mutuwa yayi ba, sai dai a sanadiyar hatsarin daya samu bincike ya nuna yasamu matsalar shafewar tunanin sa, amman zaku iya tafiya dashi gida za'a dinga yi masa abubuwan daya kamata ta hannun doctor deejart,
insha Allah kunayi kuna had'a masa da add'ua yana kuma karbar magungunan su da ake musu ammafani dasu,
Kuma Ku 'yan uwansa Ku kasance kusa dashi to ganinku da zai dingayi zai dawo masa da tunaninsa lpia lau, kuma insha Allah Wannan jinin daya sauka a brain nasa zai sauka ya dawo normal,
nan dai Dr hasan yayita cigaba da basu q'arfin gwiwa har suka q'ara fahimtar abin sosai Sannan ya tashi ya fita.
har lokacin deejart na kusa da saif bata tashi ba ,
amman wannan karon hannun ta riq'e da cup tana basa ruwan Lipton masu d'an gumi 2 yanda hanjinsa zasu warware,
gani tayi ya janye kansa alamun ya q'oshi ,aje cup d'in tayi a gefe, ta yago
tissue tana goge masa gefen cikinsa inda Lipton d'in ya d'an 6arar masa,
Zama Dr hasan yayi a gefen su yana murmushi yace
" ga alama doctor deejart kina ji da brother d'in nan naki sosai gskia,
Sunkuyar da kanta tayi sannan ta d'ago ta dubesa ta d'an yi siririn murmushi tace "koba haka ba dr hasan ay patient ya cancanci kula bare shi mai irin Wannan matsalar dole sai Ana basu cikakken kulawa".
dr hasan yace "gskia ne Wannan doctor,
Naje yanzu munyi magana dasu kuma Alhamdulilla sun fahimta kamar yanda nai zato.
duban sa tayi tace
"Thanks doctor hasan amman zamu komas dashi gida in yaso acan zan dinga kulawa da shi fiye da nan ma asibitin".
" OK nima haka nace musu alhjn naku, fatanmu dai Allah kawo sauq'i,
A hankali ta furta
"Ameen"
Miqewa tayi tsaye jitayi an ruq'ota ta baya an riq'e mata hannu gadagam,
da sauri ta juyo,
saif ta gani tsaye ya zuba Mata ido tare da langwabar da kansa gefe alamun sa na nuna yana tunanin zata tafine ta barsa a wajen.
"Zan biki doctor"
a abinda ya iya fad'a knn yai shuru.
Dr hasan ta kalla taga yana musu dariya yace"kinji har ya riq'e sunan da na kiraki dashi yassn nakine , gskia patient dinnan naki yanada brain,
Murmushi tayi ta sake Juyawa dube sa tace "yaya saif Bari naje na dawo yanzun nan mana".
Maq'e kafad'ar sa yayi dan ya gane roqon'sa take ya zauna. dafe kai tayi ta ta dubi Dr hasan tace " bari mutafi gidama kawai Dr,
"OK doctor shiknn Amman ko Wannan patient d'in naki dagani zaki sha daru dashi dan ga alama bazaya yarda da kowaba sai ke,
OK koda yake kinsan duk yawancin irin masu Wannan ciwon duk Wanda ya fara ciyar dasu ko shayar dasu a lokacin da suka buq'aci hakan tofa zakiga sun riq'e Wannan mutumin a qwalwarsu vazaiyi saurin 6acewa a mind d'insu ba dan haka doctor kin samu maqale mata congrats"
Harara ta sakarwa dr hasan tace
" Uhmm zai dena kuwa ,dan ba koyaushe zai ganni a gidaba inda nanma inada patients,
Jitayi saif ya kama hannun ta ya matsa, juyowa tayi ta dubesa tace " yadai?"
jitayi yace
"patient ?"
waye haka aunty?"
Yana maganar ne kamar mai koyon ta,
Runtse idanunta tayi gam dukkansu sannan ta bud'e su ta ce
"Kaine patient"!
gani tayi ya zaro fararen idanunsa ya zubesu a nata yana binta da kallo fuska a d'aure.
gaban ta ya wani irin fad'uwa dan saitaga kallon sak irin Wanda yake musu a gida in sun 6ata masa rai !!!
A hankali ta janye idanuwan ta a nasa ta riq'o hannun sa tace "yi haq'uri to bakai bane"
Sai lokacin ya Saki fuskarsa.
Ita kuma taja hannun sa suka fice a room d'in Dr hasan na biye dasu yana murmushi a ransa yake rayawa a kwai rigima ga alamun saif kuwa....
h
Xayynebπ€π€
ππππππ
ππππππ
*doctor deejart*
π
By
Xayynebπ€π€
*Fasaha online writer's f o w*
*Dedicated to my daughter deejart*
π
Ώ1β£8β£π΅
ππππππ
Inda Dr hasan ya barsu kakus har lokacin suna nan babu Wanda ya motsa,
shigowar suce itada saif hannayen su sarq'e da na juna yasa dangin saurin miq'ewa suka yi cirko cirko suna kallon saif,
yayinda shikuma yake liq'e da Dr d'in sa.
Kakus ne yace afara shirye shiryen tafiya gida kawai.
ay ko nan da nan su mahmoud suka fara d'aukar abinda ya kamata su d'auka suka fita waje suna shiga motocinsu,
zuwa lokacin momyn saif har ta gaji da son ruq'o hannayen d'an nata yana gocewa,
dan gani yake rabasa da Dr d'in sa zatayi,
iyayen na lura da hakan sai dai kawai su girgixa kansu.
haka dr hasan ya misu rakiya har suka shisshiga motocinsu suka tafi,
gaba d'ayan su kakus ya umarcesu dasu tafi shahinsa zai yi magana dasu.
bayan duk an hallara waje d'aya anyi tsit Ana sauraran bayanin kakus a lokacin deejart na kusa da momyn saif sai mamanya dake kusa da momyn saif d'in itama sai patient d'in nata dake 6arin damanta uwa ya shige jikin ta tsabar qwalailaita irinta saif haka take furtawa a ranta, dn har d'an zakud'awa take intaga shigewar tai yawa amman dukda haka saiya biyota, idanuwa suka had'a da Mahmoud Ashe yana Lura da hakan gani tayi ya sakar Mata murmushi tare da girgiza Kai alamun tabar gujewa saif d'in,
Sunnar da kanta q'asa tayi ita kanta tasan inda a cikin nutsuwar sa yake ba zaiyi mata Wannan shisshigewar ba,
amma fa a tunaninta.
Kakus ya fara magana da cewa
"Alhamdulilla ala kullihalin,
'Yan uwa na da 'yayana da kuma jikokina,
Maq'asudin taraku a nan dan in q'ara nausar daku mu godewa Allah a kowane irin hali,
rayuwar mu d'in nan dai gaba d'aya Allah ya tsaro mana ita tun kan a haifeka duk a abinda zai samu bawa yana cikin kundin rsyuwar sa a rubuce.
Wato Kai mai arxiq'i ne ko maras shi?
Kai shiryayyene ko batacce?
kai rayayyene ko matacce?
Kai mai lafia ne ko maras ita?
Zaka rayu cikin dad'i ko cikin wuya?
Kai d'an wuta ne ko d'an aljanna?
dadai sauran abubuwan,
to Kunga babu wanda yasan Wannan amsoshin sai ubangiji Allah mahaliccinmu buwayi gagara misali,
to cikin hakanne ta faru ga saifullahee,
yayi mummunan hatsari kuma sai gashi yasamu lpia baccin har mun kusan fidda rai gashi,
sai kuma lokacin da muke murnar samuwar lpiar tasa wata sabuwar qaddara daga cikin qaddarorin uban giji daya rubuto masa ta sake samunsa ta shafewar tunani,
to da hakane nike jan hankullanku daku yi haquri ku iyayensa da 'yan uwa a dinga add'ua koda yaushe dan ita add'ua tana matuqar kaiwa ga gaci, to alhamdulilla abinda yasa na ce muzo nan knn Kuma na gabatar muku dan haka kowa ya tashi yaje yayi abinda ke gabansa na sallame sa.
Nan dangi suka ce insha Allah zasu sanya saif a kowce salla tasu cikin add'ua akan Allah ya kawo masa sauqi za'edan.
Kakus qwarai yaji dadin hkn anan take yaita kissafowa Wanda zai kaisu aikin hajji a Wannan shekarar dukda yasan bakasawa sukayiba saidai kawai yana burin yaga yanawa dangi da 'ya'ya da jama'ar Annabi bauta da dukiyar sa.
nan sukayi godia suka tashi ,.
Baba barsu shine babba a dangin kakus dan sunxo ma tanga a shekaru ya isa wajen kakus yace " Alhj Abdul samad malaman islamiyoyinnan da makarantr Allo da ka kaiwa sadaq'ar buhunnan hatsi da shinkafa sunzo godia lokacin kana asibiti wajen saifullahee,
sun ban saq'o na d'in bin godia da add'uar samun lpiar kowa da gamawa duniya lpia.
Kakus yace masha Allah Allah shine abin godia,.
Ina Mahmoud da akram da sauran matasan?
duk sukace
"gamu kakus"
Yace yawwa kuje Kusa wad'an nan shaddojin da atanfofin a motocinku ku Kai gidan marayu da sansanin 'yan gudun hijira a matsayin sadaq'a
dukkansu suka amsa da
"tho kakus"
Suqa miq'e suka fita suka nufi s.t - room d'in inda kayan suke.
Akram da hesham tunanin su d'aya sukeyi a ransu suke cewa "da fa saif na lpia lau da shine jagoran tafia duk in za'a kai sadaq'a wani waje.
Allah sarki brother Allah baka lpia,,,,
A can cikin falo anata daga da saif ya saki deejart ta shiga ciki ya q'iya, sadda dadynsa ya zare masa idanuwa ya d'aure fuska sannan ya saki hannunta a sanyaye ya zauna wajen ya gama kai da q'afafu.
momyn saif d'in ce kakus ya umarceta data jasa su tafi cikin gida.
A can deejart ta samu ta shiga toilet tayi wanka ta shirya cikin kaya marasa nauyi ta fito falo ta iske ammy na jera abinci a dng table,
Ata baya ta rungume ta ta kwantar da kanta a bayanta ta lumshe idanuwa tace
" momy i am feeling hungry βΉ"
Juyowa momyn tayi tace "to deejart ay gashi nn na gama girki zauna kici,
ta langwabar da kanta knn zata fara shagwaba su basma suka shigo falon,
waje suka zauna a kujerun dake kan dng suka Fara bud'e kulokin abincin jawaher tace
" woww momy badai iya girkiba,
Basma ta ce "ay shiyasa kikaga kullum nake liqe da ita a kiching Ina daukar cos,
momy tace to sarakan surutu yanxu dai maza aci abinci Nina shiga zanyi salla"
bayan tafiyar momy ne deejart taja kujera ta zauna sai hararar miemie take tace " kekuma daga zuwa mlm kin ba mgn kin wani fad'a wa cin abinci uwa mai sickness want food"π
Ko saura ranta miemie bataiba tacigaba da cin abincin ta tana fad'in "ay indai kan cooking d'in momy ne kiceman ma abinda yafi haka"
Basma tace "hyyyy guys ansu lilla mana a gama cin abinci tukun,
Jawaher ta na faman matse dariya tace khazalika haq'qun ya ustaziyya basma"
harara basma ta sakar Mata sauran kuwa dariya suke musu a haka suka ci abincin,
bayan sun gamane jawaher ta ce" wlh baqaramun tausayawa yaya saif naiba q'warai sisters,!
Basma tace Uhmm wlh kuwa sis ciwo daga Wannan sai Wannan, Kai ALLAH yai mana maganin abin yakuma basa lpia, ameen suka amsa dukkansu,
Miemie tace yanzu ma daga wajen sa muke ganosa yanacen mynsa na fama dashi yaci abinci amman yaq'i"
"What a pity!"
deejart ta furta tare da dafe kai tayi saurin duban agogon hannunta taga lokacin shan maganin sa yayi da sauri ta miq'e tsaye tace "sisters zanje na basa maganinsa ko zaku zo muje tare ne?"
Jawaher tace
"no,
jeki kawai in kin dawo kya iskemu a wajen kakus.
"OK sai na dawo"
ahaka ta fice tabarsu suna ida q'arasa gyara wajen da sukaci abincin.
A can shashen momynsa ta shiga da sakkamarta hannunta d'auke da tiren magani ta q'arasa zama kusa da momyn saif tace
"Momy Ina yayan yake?"
momy tace " yawwa deejart qwamma da kikazo kingan sa can d'akin sa ya shige bayan nayi nayi dashi yaci abinci yaq'iya wlh sam ,
Harsu Mahmoud da suka dawo suka shigo tanan sunyi iya yinsu yaq'i ci,
nidai kaina na kaisa dakinsa ko Allah zaisa yatuno wani abu har yaci abincin Amman saif yaq'i ya, shiyasa inagafa rabakun da akayi d'azun ne yasa shi yin Wannan kumbure kumburen, dan Allah ga abincin sa can a flask ki d'auka kije d'akin da kanki kiga kozai karba daga wajenki zama da yunwa ay bazai yuwuba"
"to momy dama magaungunan sa nazo bashi bari in Kai masa abincin in yaso saiya sha maganin".
yaww deejart kina mana qoqari ay Allah miki za6i dai na q'warai"
Sunkuyar da kanta tayi a kunyace ta isa wajen abincin ta d'auka ta nufi d'akin saif d'in dashi.
Tana isa tasa q'afa ta tura q'yauren d'akin sbd kayan dake hannunta, q'ofar ya bud'e ta shiga ta mayar ta rufe.
a gefen gadon sa ta hangesa yayi zaune ya tsurawa tafin hnnunsa idanuwa kamar mai Neman wani abin a ciki.
zama tayi a gefensa bayan ta aje kayan q'asa kusa dasu Wizen 5 na marece ne a lokacin data kakki watch d'in ta.
A hankali ya dire Mata fararen idanuwan sa a fuskarta Yana kallonta,
Yanayin kallon nasa dayake Mata na tuhumane,
Tasan qilan dan ta gudu d'azun ta barsa shiyasa.
gani tayi ya matsa daga wajen sosai alamun fushi yk,.
ya kwantar da kansa a bedsheet dake saman gadon sa ,.
Murmushi tayi ta had'a