Showing 15001 words to 18000 words out of 52733 words
gmail Mahmoud ya shigo , ya zauna a gefensa ya d'an kwanta a gadon ya jawo wayar saif yana duba gallery sai jin qarar message yayi a wayar ya shigo,
a saman sikrim d'in wayar ta nuno masa message d'in kamar haka,,
*message from x*
*Please zuma na, Inason in ganka yau dan Allah idanuna suna mafarkin sake son ganin kyakkyawar face dinka a Karo na 2 a rayuwata*
Iyakar sa knn rubutun.
Shi saif ma hankalin sa ya riga ya tafi ga muhimman abubuwan da yakeyi.
Baisan ma saqon ya shigo ba,.
ta6osa Mahmoud yayi yace" guy gafa wata sabuwar cika nan taimaka message.
Saida ya ida abinda yake sannan ya rufe laptop d'in ya amshi phone d'in ya duba,
Tsoki yaja baccin ya karanta message d'in ya aje wayar.
Mahmoud yace "wacece x kuma saif?
dan nidai cikin girlfriend naka ban San da ita ba.
tsoki saif ya sake yi yace "sunanta xeenat q'anwar mas'ud ce friend d'inmu duka 2 bamufi sati da had'uwa ba, lokacin naje wajen mas'ud din yasa ta kawo mana drinks,
ga yanda yake cewa a satinne ta dawo daga ingland karatu amman ta bi tawani nacemun wlh brother yanda kasan mayya haka take yarinyar nan xeenat.
gata bata da tarbiyya ko kad'an.
Tuntserewa mahmoud yayi da dariya yace " ko dai itace amaryar tamu saif kk 6oyewa?"
Had'e rai yayi yace
"Allah tsareni mahmoud da auran irinsu,
Plsss mubar mganr nan Ina son in fita yanzun ko zaka rakani ne?"
"Zuwa Ina knn saif?"
"ban sani ba mlm in zaka rakani muje kawai".
Kwanciya mahmoud yayi a gadon yace " bazan jeba jeka abinka, yau bazan fitaba dan na qudura a zuciya ta yau d'in nan zan fad'a wa doctor sonta da yaimun illa a zuciya"
ya qarshe maganar yana lumshe idanuwa tareda shafa saitin xuciyarsa da hannu.
dan haka Ina nan Ina sauraron dawowarta,
nasan bazata jima ba yau zata dawo inda yau lahadi kaga kuwa fita bata ganni ba,
Sbd ance da zafi zafi kan bugi icce brothe"r.
Tun da yafara mgnr saif gaba d'aya wuta ta d'auke masa, ya rasa cikin hankalin sa yake koko?
Wai miyasa ne ya ke damuwa da lamurran yarinyar ne?
Miyasa duk Wanda ya furta sonta a gaban sa yake jin ya tsanesa ne?"
Hakan me kenan to yake nufi?"
"Son ta yake nufi saif,"
Abinda xuciyarsa ta basa amsa knn,
Da sauri ya girgiza Kai ya na fad'in "no no no my heart na lie, bazan sota ba"
Ya Kama kansa ya danne da q'arfi yake furta hakan.
cikin sauri mahmoud ya ruq'osa yana cewa" saif mike damunka?
Wace ce ke baka so?"
A Ina take kuma ?"
In kana nufin ita xeenat d'in ay ba a so dole ko ?
plxxx ka nutsu brother kabar sa damuwa a ranka plzzz".
Saif baice masa komi ba ya d'auki keys d'in motar sa ya fita ko ganin gabansa baiyi sosai, ba abinda ke masa kuwwa a q'walwa irin abinda mahmoud yace yanzun game da deejart, wato zai fad'a Mata son ta garesa ,
mahmoud da kallo ya bisa kamar ya bisa yakeji dan ganin yanayin da yake ciki Amman sai ya fasa ya tabe baki tare da fad'in
" Allah kyauta "ya koma yai kwanciyar sa.
saif kuwa na fita mota ya fad'a ya bata wuta da qarfi ya figeta har wata q'ara kakeji ta motar, "q'uuuuuuuu,,,,,!!!
kakus na zaune a wajen shida su dady magana suke masa" ko jinsu bayyayi ma.
Kakus kuwa ya dage da fad'in kiransa da
"Kai saifu ,saifu, lafiyarka kuwa? wannan tada mota haka kamar dai marar hankali?!
Ina saif bai sanma da kakus a wajen ba, tuni ya fice a estate d'in.
Kwalta ya hau yanata faman sharara gudu a mota shi kansa baisan inda hankalin sa yake ba ma Sam sam.
sai cewa yake "mahmoud why?!
Mahmoud karkayi mun haka plzzzzz mahmoud",kaifa d'an uwanane na jini.
kan ya ankara yaji
Garammmm!!!!
Motarsa ta yi arangama da wata qatuwar tirela tuni ta hantsila gefe, motar tasa tahau yin q'undubala tana juyin waina a saman titi,
Tuni motocin dake wucewa kan titin suka dinga Jan burki suka furfuto suna kallon ikon Allah.
Dan har zuwa lokacin motar tasa taq'i tsayawa,
da sauri suka q'arasa ganin motar ta tsaya cak.
daq'yar suka zaliq'osa a motar, kansa da jikinsa sunyi face -face da jini tuni numfashin sa ya tsaya cak ya mimmiqe a wajen.!
Xayynebπ€π€
ππππππ
ππππππ
*doctor deejart*
π
By
Xayynebπ€π€
*Fasaha online writer's f o w*
πjin jinar ban girma a gareku kainuwa writers, gida na gari,
mutane na qwarai, duk group din ya had'a.
Allah dai yabar zumunci a tsakaniπ€ππ
*Dedicated to my daughter deejart*
π
Ώ1β£4β£π΅
ππππππ
A can gida kuwa hankalin iyayen nasa yaq'i kwanciya ganin yanda yabar gida hankalin sa a gushe.
kakus ne ya umarce su da subi bayansa suga inda ya nufa, mafarin knn suka take masa baya a cikin motar su suma.
Amman da yake gudu ba d'aya ba shiyasa saif d'in yai musu rata har yayi accident d'in basu isoba wajen,
sai baccin mutane sun fiddo sa a motar ne suma suka iso wajen a gigice,
ganin yanda motar tasa ta lallanqwashe a gefen titi,
"dagani ba tantama wannan motar saif ce"
cewar dadyn deejart,
dadyn saif kuwa wato alhj Abdul Hakim bai tsaya cewa komiba ya isa inda mutane sukaiwa wajen zobe ya dinga tutture mutanen yana kutsawa ciki.
jikinsa gaba d'aya tsuma da kyarma yake yi lokacin da yayi tozali da d'an nasa kwance cikin jini rai hannun Allah.
da sauri ya isa ya durq'ushe gaban d'an nasa ya kifa kansa a jikinsa,.
Wani irin kuka yakeyi Wanda ya karyarwa da mutanen wajen zuciya suma, rungume sa yayi yana fad'in "saifullahi dan Allah kar ka tafi ka barmu kasan Kai kad'ai ne d'ana.
dadyn deejart ma hawaye kawai ke ambaliya a fiskarsa dan babu Wanda zai kalli saif a lokacin yace yana da rai a jikinsa,
da qyar ya shawo kan dadyn saif yayi shiru mutane suka kakkama saif suka sanyasa a motar su dadyn suka musu fatan samun lpiar sa.
Kai tsaye special care health hospital suka nifa, wato inda deejart ke aiki knn.
Lokacin da suka isa hospital d'in ne dadyn deejart d'in cikin kyarmar hannu ya zaro wayarsa ya kirata yace tazo dan gasu nan sunzo da emergency patient a waje.
ba jimawa sai gata da sauri ta nufo gunsu.
ta q'araso wajen Norse na biye da ita Jaye da gadon d'aukar patient,
cewa take
" plzzzz dady waye ba lpia a gida?"!!
Kasa bata amsa sukayi dukkansu.
Illa bud'e mata bayan motar da sukayi suka fiddo sa suka d'ora a gadon daukar marasa lpia.
Zaro idanuwan ta tayi waje Lokacin da tayi arba da yaya saif,
a yanayin da yake kuwa ba q'aramin gigicewa tayi ba,.
hawayen tausayin sa suka Fara 6ata mata fuskarta..
Share hawayen tayi ba q'aramin daurewa tayi ba data umarci nurse d'in su turo gadon sukaisa room ,.
su dady dole suka tsaya a nan waje add'ua kawai sukeyi Allah basa lpia.
A ciki kuwa deejart ta duq'ufa wajen goge masa jinin jikinsa daya bata komi na jikinsa, baccin ta xare masa rigar shirt d'in jikinsa.
Ta umarci nurse dasu miq'o Mata towel,
nan ta Fara gogewa sannan tafara basa taimakon gaggawa ta hanyar sa masa na'urori a jikinsa
Sannan ta Fara dubasa,..
"Wayyo ni ni deejart na shiga 3 na"!!!!!
Ta fad'i hakan da q'arfi tare da duq'ar da kanta gefen gadon hawaye masu d'umi nabin fuskarta.
Miq'ewa tayi ta umarci nurse d'in da su fita kawai,
Itama bayansu ta bi ta q'arasa wajen su dady tace cikin rawar murya
"dady kuzo mu shiga ciki Ku gansa, da sauri suka nufi d'akin kuwa.
gaban gadon suka ja birki suna tambayar ta ko ya far fad'o kuwa?''
Cikin muryar kuka tace "dady sai abinda Allah yayi dai kawai,!"
dan yaya saif ya shiga *COMA*,
Farfa d'owarsa sai abinda Allah yayi,!
Ta d'oro in Allah ya temaka ma iya ganin ya farko yanzu!, ko anjima!,ko gobe!, ko jibi!, ko wannan satin!, ko wannan watan!, ko wannan shekarar,,,!!!
Ta qamaimai dai ba mai cewa ga ranar.
Amman insha Allah dady zan q'oqarta kan naga komi ya tafi normal".!!!
tana kaiwa nan ta fice da gudu ta shige office d'inta tana share qwalla.
Iyayen nasa kuwa innalillahee wa Inna ilaihirraji'una sukeja hnkalinsu a tashe
Xayynebπ€π€
ππππππ
ππππππ
*doctor deejart*
π
By
Xayynebπ€π€
*Fasaha online writer's f o w*
*Dedicated to my daughter deejart*
π
Ώ1β£5β£π΅
ππππππ
Add'uar da suke yine nutsuwa ta saukar musu,
gaba d'aya suka miq'a al'amurran su ga sarkin.
Dadyn saif ya dubi dadyn deejart yace
"Ya kamata mu sanar wa family halin da ake ciki yanzun, musamman ma kakus,"
Hakane yaya Amman Bari muje gidan gaba d'aya inda deejart na nan zata basa kulawa".
Shigowar ta room d'in ne yasa shi cewa
"Yawwa 'yata zamuje gida yanzu mudawo ga d'an uwanki nan ki kula dashi to".
da q'yar ta amsa da
" to dady"
bayan fitar su ne ta zauna a gefen gadon da yake tana kallon sa , miq'ewa tayi ta had'a wasu bandej ta sake d'aura masa a saman kansa,
tare da masa wasu allurai masu sinadarin magunguna a ciki,
Tanayi hawaye na suroro mata sbd matsa-nancin tausayin yaya saif da yake d'awainiya da ita,
dawowa tayi ta kifa kanta a q'irjinsa tana kuka mai girgiza jiki,
Jin anturo q'ofa za'a shigo ne yasa tayi saurin miq'ewa a jikinsa tana kallon q'ofar dan ganin waye zai
shigo.
doctor hasan ne ya shigo ya na fad'in
"Doctor deejart ance an kawo brother naki ba lpia inji sister rahma,?.
da q'yar ta samu ta daidaita nutsuwarta tace " hakane doctor hasan ,
Amman wlh ya shiga coma"!!,
da sauri yace "subhanalla,!!
Allah kyauta doctor, matsowa kusa da gadon yayi yace
"amman miyasa mesa ne hakan?
"accident ne doctor,
"Assha!!
Doctor Deejart sannu insha Allah zai samu lpia,
kifara masa wannan checking din da Mr Johnson ya koyar daku,
wato irin Wanda akewa wanda suka shiga step d'in nan na coma insha Allah zakiga ya farfad'o soon doctor"
"to doctor insha Allah i will it thanks"
bayan fitar doctor hasan 'yan gidansu suka Fara shigowa,
ganin halinda saif yake ciki tuni suka Fara zubda masa q'walla har saida kakus ya tsawatas sann suka lafa.
sun jima a asibitin kusan magrib sannan suka Fara komawa gida.
su shahed ne kawai dasu basma sai maman saif da kakus d'in da iyayensu maza ne sukai saura Amman dangin du sun tafi sbd dare.
Kakus lazumi kawai yake yana tofawa saif addu'oe dan har kuka yai masa a 6oye dan ganin dayai masa ba q'ara min firgita yayi ba shima.
Sai dadyn saif d'in-ne ke salla yayin da mahaifin deejart ke gefen gadon saif a zaune ya zubawa saif d'in ido gwanin tausayi.
bakajin komi sai tashin shessheqar kukan su jawaher.
Kakus yace "yaran nan bazaku daina kukan nan haka ba?
Tun zuwan kufa kukeyinsa haka? shi da ba cewa akai muku ya mutu ba? bare kuzo ku tusasa gaba kuna masa kuka?
add'ua ya kamata kuyi masa a halin da yake ciki yanzu dan ita yafi buq'ata gunku bawai ku sanyasa a tsakiya kuna masa kuka ba,
Ya juya ya dubi deejart datai tagumi tana sauke ajiyar zuciya alamun taci kuka har ta q'oshi.
Girgiza Kai kakus yayi ya dubi akram yace" ka d'aukesu ka mayar gida haka nan dare yayi",
"To kakus Kai ba yanzu zaka tafo bane?
"A'a akram sai su dadynku zasu tafi sannan zamu tafo tare, yanzu ka mayar dasu gida."
badan sun soba su jawaher suka bisu suka tafi,
kakus ya dubesu dukkansu yace " maganar kwana wajen safa ?"
Cikin disasshiyar murya deejart tace
"A'a kakus , anan hospital d'in bassa buq'atar masu jinya amman inda Ina asibitin Zan dunga kula dashi inta kama ma zan kwana wajen sa zan kwana,
Ku kwantar da hankalin ku insha Allah yaya saif bazai jimaba a wannan halin.
nan iyayen suka shiga samata albarka.
sun jima sai kusan 12 na dare sannan suka Fara shirin tafiya,
deejart tace ita a nan zata kwana dan tanada dutyn dare"
a haka suka tafi.
ta dawo d'akin ta kwanta a wani gado dake kusa dashi,
Ta tsura masa ido sai kuma tayi zumbut ta miq'e tsaye ta isa wajen sa ta leq'a fiskarsa taga tamfar ta kirasa ya amsa, wasu hawayen ne masu zafi suka zuraro Mata,
ta sunkuya ta sum6aci kumatunsa cikin hawayen take fad'in
" xaka warware yaya saif da yardan Allah ".
itace bata kwanta ba sai da tayi salla ta roq'i Allah akan ya dafa mata.
Sai wajen 3 tasamu ta kwanta barci.
A haka dai suka kwashe tsawon wata d'aya a hospital.
Iyayensa sun rarraba sadaq'a masallatai da islamiyyu akan tayasu da add'ua kan Allah ya bawa d'ansu lpia.
A haka suka sake kwashe wata 2 a asibitin.
Deejart bata gajiyawa da yin duk wani abu da zai dawo da lpiar sa
yau takama juma'a bayan an taso masallaci d'akin cike da 'yan uwa da iyaye sunzo ganin saif , sun jima sannan suka tafi,
dadyn saif ya dubi kakus yace " baba da na yanke shawaran mizai Hana bazamu fidda saif waje ba?"
Kakus ya dubesa rai a d'an 6ace yace
"ban amince ba Abdul Hakim , lpia dai ta Allah ne, kuma ko a Ina kk in Allah ya q'addari warkewar ka tofa ba mahani,
dan haka muci gaba da add'ua Allah zai dubemu insha Allah koda yaushe ne, sbd add'ua makamun mumini ce,kuma deejart tana aikinta a kansa a kullum batare da gajiyawar taba yarinyar kirki,"
Shiru dadyn saif yayi a ransa yake fad'in" baba duk da yana d'an boko akwai tawali'u da son fifita addininsa akan na boko,
ba kamar yanda wasu masu hannu da shunin sukeba. komin q'anqntar ciwo sai kaga sun kwashi iyalinsu a tafi q'asar waje a kai dan duba lafiyarsu, su ko tunanin na q'asa dasu basayi
( talakawa)bare su taimaka musu, Kansu suka sani kawai.talakawa
sune wad'an da idan ciwon ya kamasu nn suke haq'ura da asibitocinsu har Allah ya kawo musu iyaka ,kuma sun yarda Allah ne mai bada lpia ga Wanda komin wajenda yake maqasqanci kuwa, kuma ya Hana masu fiddawar lfiar, sai kaga yanda aka fidda mutum q'asar wajen haka za'a maidosa ba biyan buq'ata ,
Allah knn buwayi gagara misali. Mutane
kamar basuda alqibla sbd tsabar yarda da d'abiar yahudu.Alhalin su bazasu daura yardarsu a knmuba musulmai,
Wata q'ara ce tayi saurin dawo da hankullansu wajen,
nau'rorin da ke jikin saif,
su ne suke yin wannan q'arar mai sauri,
Yayinda suke sake kawo wasu irin dogayen danjoji nan da nan suka nufi wajen da yake kwancen,
deejart ta latse wajen da sauri cikin murna dan indai wannan danjojin suka bayyana a mai ciwon tofa yayi free ne cikin yardar Allah,
da sauri ta jona wata na'urar a daidai xuciyarsa tana d'an gogawa ko minti 3 batayi ba da farawa sukaga idannuwan saif na d'agowa suna warewa a hankali 2 har ya bud'esu tangaram,
tuni ya fara miq'a yana sakin atishiwa sama da goma a lokaci d'aya, tare da da shaqquwa alamun yana buq'atar ruwa,
wani tsallen murna deejart tayi ta rungumesa gagam tana hawaye,
su kakus kuwa Allahu Akbar sarki gagara buwayi alhamdulilla suke ta ambato cike da farin ciki,.
lallai add'ua takobin mumunice maganin kowace matsala a rayuwa ,,gashi haqurinsu da karbar q'addarar su ta kaisu ga gaci ..
Runfa sukayi masa cike da tsananin murna kowa sannu saif yake fad'a". shidai Nasa idanune ya gaza furta komi sai binsu da kallo yake kamar bai San suba kuma.
A hankali saif ya janye deejart a jikinsa yana q'oqarin miq'ewa zaune.
da sauri ta sanya hannun ta a q'irjinsa ta,,,,,,
Xayynebπ€π€
ππππππ
ππππππ
*doctor deejart*
π
By
Xayynebπ€π€
*Fasaha online writer's f o w*
Afuwan dears,,,,!!!
Na mnta nasa wata uku instead insa sati 3 a shigarsa coma ,,
Fatan kun fahimta.
*Dedicated to my daughter deejart*
π
Ώ1β£6β£π΅
ππππππ
#da sauri ta sanya hannun ta a q'irjinsa ta komar dashi ya kwanta tace"yaya saif sannu kabari ka q'ara samun sauqin jikinka kuzarinka ya dawo sannan,nan ta sanya abin awo ta auna lafiyar sa ta d'an Lura yana da buqatar qarin ruwa nan da nan ta hada tareda allurai a cikin drp d'in dan saboda q'arfin jikinsa ya ida dawo wa normal,
Bayan ruwan sun gama shiga ne har lokacin idanunsa na kanta,
itama ta d'an d'ago ta dubesa tace
"ina zuwa yaya saif"
da sauri ta juya ta shiga toilet ta fito da brush da kwanon silba ta taymaka masa ya goge bakin sa ta hanyar riq'e masa hannu da tayi,
baccin ta maida kayan ta isa wajen wani deep frzr ta d'auko swan water na roba tare da cup ta dawo ta zauna a gefen gadon ta zuba ruwan ta fara d'ago kansa da hannunta tana basa ruwan a haka har ya q'oshi sannan ta janye,
Komawa yayi ya kwanta tare da lumshe idanuwa.
Doctor hasan ne ya turo q'ofar ya shigo cikin mamaki ya q'araso gaban gadon inda su kakus suka zagaye saif cike da farin ciki.
gaisawa doctor yayi dasu sannan ya matsa kusa da saif yana fad'in "alhamdulilla deejart congrats patient namu ya samu lpia"
Murmushi kawai take faman yi tace me too thanks doctor hasan kaima ay ka taimaka ba kad'an ba".
Yace "bakomi ay doctor zaman taren knn ay,
da kyautatawa yafi"
kakus yace
"hakane kuwa kudai Allah saka muku da alheri likitoci,
dan kuna q'oqari ba kad'an ba haqqun".
"Ameeen baba cewar su dady".
Doctor hasan bai jima ba ya fita.
deejart takai dubanta ga saif taga still idanunsa a rufe suke yana faman sauke ajiyar zuciya ,.
Kakus ya matso wajen saif d'in sosai yayin da dadyn sa ke riq'e da hannunsa cike da farin ciki yana kallon fuskar d'an nasa.
Shikuma dadyn deejart ya fita waje yana fad'awa family farkowar saifullyace da yayi yanzu.
Kakus na isa wajen ya shafa kansa yace " saifu abin ba magana kuma?
Munata magana kayi shuru?
ko jikin ne kuma ?"
a hankali saif ya bud'e idanunsa ya saukeso a na kakus kallonsa kawai yakeyi yaq'i furta komi,
deejar ta miq'e ta isa dai dai fuskarsa tasa tafin hannunta tana jujjuya masa a gaban fuskarsa gani tayi ya dawo da kalkonsa a zoben yatsarta ya miq'a hannunsa ya kamo hannun yana q'oqarin zare zoben azurfan hannun ta,
janye hannun tayi ta zuq'unna tace "mikakeso yanzu kaci a kawo maka?
saida ya d'an kalleta na 'yan seconds sannan ya kauda Kai gefe nan ma yaq'i furta komi,
jin an banko q'ofa da sauri an shigo yasa gaba d'aya sukabi wajen da kallo, mahmoud ne gaba sai su akram saisu basma DA zugar 'yan uwa anxo ganin saif,
Mahmoud ya riga kowa isa wajen sa ya rungume sa cikin tsananin farin ciki yace " Alhamdulilla saif ,! .
Sannu ya jikin ?
Akram da