Showing 18001 words to 19707 words out of 19707 words

Chapter 7 - ASALINA COMPLETE Hausa Novel By completehausanovels.com.txt

23 Aug 2025

190

of reader's





Page3⃣1⃣to3⃣2⃣





Cike da kisisina Nabila ta mike ta nufi dakin Jawad tana zuwa kai tsaye ta tura kofa,ta shige ciki ,kan sallaya ta hangosa,gabanta yayi wata mumunar faduwa tuni kyarma ke shirin kwace mata,daurewa tayi ta karasa garesa zata kwanta a jikinshi,wata iriyar tsawa ya daka mata Wanda yasa sora kadan ta zubo fitsari.



Binta yayi da mugun kallo sannan yace"uban waye tsaranki da zakizo ki kwanta a kaina,kuma daga yau karki kuma shigomin daki babu sallama tashi ki fita ki bani wuri Jaka kawai".




Kallonsa kawai take tana hawaye a zuciyarta tana fadin na shiga ukku ni Nabila ya akai haka ta faru,mikewa tayi ta fice da gudu tana isa daki waya tayi saurin dauka tana kiran number din hajiya,bugu daya ta dauka baki na kyarma take fadin"Hajiya na shiga ukku na,Yaya Jawad ,duk abunda nayi masa Hajiya ya warware sallah fa yakeyi yanzu kumani yake kora daga dakinsa tsantsar tsanata tananan kwance a zuciyarsa"kuka ya kwace mata.



"Rufe bakinki kinji,daina damun kanki bazamu gaji da bannatar da miliyoyi ba akan farin cikinki,kije kiyi aeki akan wannan mayyar kafurar yarinyar,ki fita harkar Jawad ni kuma zanje wurin malam karki damu"
Da irin wannan maganganun gurbatattu Hajiya ta kwantarwa Nabila hankali harta Dan daidaita sannan sukayi sallama.




Fitowa tayi don duba ajiyarta kamar yadda ta saba ,ganin an tone wurin batasan lokacin data kurma uban ihuba,tare da zaro ido ta dafe kai,ba damar tayi tambaya a gane da saka hannunta a abun da suka gani wurin,rai bace ta juyo zuwa part dinta.



Duk abunda takeyi akan idanun Mama da Sarena take yinsa suna kallonta ta window,numfasa Mama tayi tace"Allah ya shiryi mai hali irin naki,ke kuma Allah ya juyo da hankalin mijinki a wurinki".



Murmushi kawai Sarena tayi tace a gurbatacciyar hausarta"na gode,Amma ni kasarmu zan koma Mama ,na fasa auran dashi".




Ko kadan Jawad bayajin karfin jikinsa kwance yake rufda ciki hankalinsa tashe,abubuwa da yawa sunata dawo masa akai,ji yayi daga kwance kamar ana juyashi ga tashin zuciya,da gudu ya fada toilet ya soma kwarara amai,bakinkirin dashi ga wari,ya dade yana yinsa,kamar fitar wani abu take a lokacin yajishi ya koma sawat har wani karfi yakeji a jikinsa,wanka yayi ya fito ya shirya cikin kananan kaya,ya feshe jikinsa da turaruka masu dadin kamshi yayi matukar kyau cikin wando black da riga red ,wayarsa ya dauko ya soma kiran layin wayan Manab.




Shiko Manab zaune yake gaban Ammi sunata fira akan matsalar Jawad din tana fada Masa anjima zasuje gidan ita da Ummansu suga meke faruwa.



Karar wayarsa yasa yakai dubansa garesa cike da mamaki ya furta Jawad,dauka yayi a sanyaye jin muryar Jawad a sanyaye yasashi sakin ajiyar zuciya yace"friend ya kake".



"Nrml kana ina ,zanzo yanzu" Jawad ya fada.


Murmushi Manab yayi yace"Angon Nabila da wuri haka,ina gida".


Wani irin tsaki Jawad ya saki sannan yace"banza kawai ,dallah ka daina fadamun haka"be jira amsa ba ya kashe wayarsa ya dauki key din motarsa yayi waje.




Gefe take tsaye ita da Mama ya fito hankalinsa bekai Kansu ba,Mama zata gaeshesa Sarena ta rufe mata baki ,kallonsa kawai takeyi yayinda wasu zafafan hawaye kebin kuncinta.harya ja Mota ya fita akan idanuwanta.





Nabila ganin ba kowa da gudu ta shiga dakinsu Sarena ganin kwanon abincinta a gefan katifarta da alama shizataci ,cikin sauri ta warwaro kullun maganin ta zuba ta motse abinci ta rufe,ta fito da sauri ta koma part dinta.



Kallon Sarena Mama tayi, tace"har yanzu kina son mijinki,amma kuma kince zaki rabu dashi".



Goge hawaye Sarena tayi tace"ina sonsa,Amma bazan zauna dashi ba,baya sona"


"Kinga kada kiyi kuka,kinga kinada ciki banaso kina damuwa,muje kici abincinki kada yayi sanyi kinji y'ata".



Kai tsaye dakinsu suka shiga ,zaunar da ita tayi ta jawo kwanon ta mika mata ta dauka spoon ta bata,ta wuce waje don ida aekace aekacenta.ita kuma ta soma cin abincin.





Jawad yana isa gida ya gaeshe da Ammi,sannan yake fadawa Manab mike faruwa kuma shi yanzu besan yazaiyi da Sarena ba harta saurareshi,sannan ya roki Ammi dasuje gidan,wucewa sukayi suka dauki Umma,suka wuce gidan Jawad.





Sarena kam ta cinye abinci tsab,kai tsaye taji cikinta ya soma juyowa kamar zai fito kai tsaye jini ya soma bin kafarta wani azababban ciwan ciki ya taso mata,Mama ta soma kwala ma kira,Amma bazata jitaba kasancewar tana kasa,a hankali ta soma rairafe tayo hanyar waje.




Da Sallama su Jawad suka shigo main parlor din,Mama ce kadai gaesawa sukaci gaba dayi sannan Ammi tace"ina Sarenan takene".



" tana ciki abinci takeci bari na kirata"kafin Mama ta rufe baki,suka hango Sarena tana fito da rairafe a hankali ta dafa kofa ta mike bakinta na rawa tana so ta furta sunan Mama.




A razane Ammi ta dago tana kallon cinyarta dake dauke da wani bakin tabo a jiki ,bakinta ta kyarma ta fada da karfi"Minad".



A razane kowa kebinta da kallo suna maimaita sunan data fada Minad.



Cikin Sarena ya kuma murda mata ta saki wani razanan ihu ta tafi zata fadi,dukansu sukayi kanta,kafin kowa ya isa gareta Ammi harta isa ta riketa,tana kuka tana fadin"Ku taimaka mun kada Minad dina ta mutu don Allah",tuni Sarena ta some a hannun Ammi,Nabila na gefe tana kallonsu .



Cikin sauri Manab ya fizgeta yayi mota da ita,da gudu suka rufa masa baya.




Comment
Share
Like





Muhphat luv
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA*



🌈kainuwa writer's association


United we stand and succed:our ambition is to entertain & motivate the mind of reader's



Na
Maryam Ismail
Muhphat


Godiya gareku masoya TABON D'A NAMIJI,ina bada hakuri na jina shiru kwana biyu da kuka jini naji dadi sosai wasu sun kirani,wasu sunman text,insha Allah ranar Sunday zaku rika jina kullun Alhmdllh yanzu shine gabana.





πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š
Last page
πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š


Sadaukarwa ga kainuwa writers Allah ya kara hada kanmu.






Mota Manab ya shiga suka rufa masa baya,kowa da abunda yake fada sabanin Jawad da tunda aka ambaci Minad ya rasa gane komai yanaso yasan tayaya Sarena zata koma Minad dinsa wannan wanne irin rudadden Asali ne a tattare da ita.


Da kyarma Manab yake kiran Salim yana fada masa ga Sarena ba lafiya su taimaka mata,kai tsaye Emergency suka shiga da ita yayinda kowa ke safa da marwa a wurin suna jiran saka mako.





Su Mr Samol kuwa yaune jirginsu ya sauka Nigeria saboda rigimar Lissa kullun kuka take tace wai tayi mafarki Sarena na cikin damuwa da kunci hakan ya tilasta masu tahowa don duk jiya basu rintsaba,kai tsaye gidan Jawad suka nufa nan Mama ke sanar musu Sarena na asibiti,tun kafin su isa Asibitin Lissa ke kuka suna isa ko parking basuyi ba ta bude murfin mota ta fito tana tambayar sisters din wurin,a rude suka isa da ita wurin hakan yayi daidai da turowar da akayiwa Sarena a Bed an fito da ita daga Emergency zuwa wani dakin na daban,wani irin ihun kuka Lissa ta saki lokacin data gama bin jikin Sarena da kallo duktayi baki ta lalace kwatakwata batayi kama da Sarenar data bari ba,kai tsaye Jawad ta nufa tana dukansa tana fada masa mugayan kalamai da nuna masa irin tsanar data masa,dakyar Mr Samol ya riketa ta fada jikinsa tana fadin"I will never forgive u inhar Sarena ta mutu,kaima ka jera sunanka a matsayin matacce I promise u this".



Kallonsu Salim yayi yace muje Office,Manab da Jawad sai Mr Samol suka bisa nan ya masu bayanin gubar da aka bata,amma Allah ya taimaka sunkaita asibiti da sauri gubar batayi tasiri a jikinta ba Alhmdllh ita da abunda ke cikinta suna cikin koshin lafiya.


Wata sanyayyar Ajiyar zuciya Jawad ya saki yana godewa Allah ,sannan suka fito,a dakin da aka kai Sarena suka shiga har Daddy da Abba sun iso rigima na neman ta balle tsakanin Ammi da Lissa.



Cikin kuka Ammi tace "wannan tabon na cinyarta akwaishi tsakiyar bayanta,kuma Ku duba wannan Minad ce,".


Nanfa ido ya soma raina fata ana bude bayan Sarena saiga tabo ya bayyana.


Matsowa dab da ita Ammi tayi tace" ki tashi Minad,yauga mahaifiyarki a gabanki tana cike da kewarki da soyayyarki dama ban taba sakawa raina kin mutu ba,ina matukar sonki nasan zaki dawo gareni"


Wani irin nishi Sarena tayi a hankali ta bude idanuwanta da suka lumshe ta fara bin kowa na dakin da kallo baki na rawa take mikawa Momy hannu tana fadin"Momy na,ki tafi dani banason nan ".




Matsowa kusa da ita Momy tayi ta dafata tace" share hawayenki gatanki ya dawo Mind ki kalli wannan itace Mahaifiyarki bani ba ki bude kunne ki saurareni".




Lissa bata jira neman Shawar mijinta ba ta fadi komai ke faruwa da tun ranar da suka dauki Sarena har kawo yau,gaban Ammi taje tace"kiyi hakuri bama da zabin daya wuce wannan,komun dawo da ita,zasu iya cutar da ita kumani Soyayyar ta ta shiga raina, amma kuyi hakuri".



Kowa na dakin hankalinsa tashe yake masu kuka nayi ,Abba ko da Umma sunyi sufa sharaf suna faman kamekame,ananme kuma Mama ta shigo dakin ta kalli Nabila da Hajiya kai tsaye ta mika video din dake hannunta kowa ya kalli duk abunda ke faruwa,ganin ba sarki sai Allah yasa Nabila saluda tana Neman afuwa da fadin abubuwan dake faruwa.




Da sauri Abba da Hajiya sukayi waje kankice me suka shige Mota suka fita da gudu be kallon ina yakeyi da mota horn wata babbar Mota ke masu, basuji ba kafin motarsu Daddy ta iso motarnan ta murjesu tas jikinsu yabi kwalta dakyar aka tattarasu aka sallacesu zuwa kabarinsu,tashin hankali da sauyin yanayi yasa Sarena shiga labour room bata shirya ba ta haifo yaranta yan Maza guda biyu masu masifar kama da Jawad sosai .




Nabila kuwa kai tsaye ciwo ya sakota gaba ta kamu da HIV ga wasu kuraje da takeyi suna fitar da ruwa mai wari duka jikinta ta rame tayi baki ta lalace,a cikin mabaratan asibiti suke zama,



Umma ko ta dade da saluda,ta zauna tana istigfari ta koma ga Allah,sosai Ammi ke tausaya mata kullun cikin sadaka da ibada take.



Alhmdllh Sarena ta koma Minad a ranar sunan yayanta suka karbi musulunci ita da Daddy da Momynta,yaranta kuma sukaci sunan Abba da Daddy suna kiransu da Ashman da Ashwan,Mama ke kula dasu.



Some years later




Farin ciki ya dawo wa family dinsu,hankali kwance tuni Minad tayi sauka,yaranta sunyi wayau sosai Alhmdllh sun zama yan uwa dasu Mr Samol, soyayya tsakanin Jawad da Minad ta kara karfi hankalinsu kwance duk wani damuwa ta yaye masu Minad tayi kyau tayi fari yar gata a wurin iyayen ta da yayanta ga kuma mijinta rayuwata hankalinsu kwance.



Godiya ga sarki Allah daya nunamin karshen wannan littafi.





Muhphat luv

5
6
7
Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login