Showing 15001 words to 18000 words out of 19707 words

Chapter 6 - ASALINA COMPLETE Hausa Novel By completehausanovels.com.txt

23 Aug 2025

189

Auran Jawad Al'amin da Sarena Samol da Nabila muh'd,akan sadaki ko waccensu dubu Dari.



Daurin auran yayi mutane har wurin 12 sannan suka soma ragewa before ya wuce coci ya karbo auran Amanar Sarena ya saka mata ring itama ta saka masa.



Anata shagali gidansu Nabila sai cashewa takeyi tana takadarci da yamma aka lullubeta cikin hijab Abba ya mata fada sosai before yai shirin daukarta.




Har gidansu Sarena Abee yaje ya karbota wurinsu Momy kuka kawai sukeyi dakyar aka rabasu ya dakkota ya kawota gidansu dake newlowcost .



Gate ne babba saika shiga kaga kofa idan ka shiga babban parlo ne da yasha ado sai part Ukku na tsakiyar ne na Jawad n right side naga Abee ya shiga da Sarena ,fada ya kara mata sannanya fito ya tafi kafin Moona ta iso gidan.




Ba jimawa da zuwansu Abba ya karaso da Nabila a kagare take su shiga ya fito ya tafi donko hijab din jikinta dukta dameta,shima fada ya mata sannan ya tafi .


Kamar jira take ta yakice hijab din ta jefar tace"Aysha Allah yasa BA's kawo shegiyar aljanar yarinyar nanba".



Tsuka Aysha taja tace"na nawa kuma ae kece amarya tun dazu Abee ya kawota".



Ihun haushi Nabila ta daka tace "wlh wannan shirin Jawad ne mugu kawai donta rigani zuwa ya tsaidamu ,to wallahi zatan tayi sallama da farin ciki tunda hartai kuskuren hada miji dani".





*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻



Luv u all
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA*





🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*





Page2⃣5⃣to2⃣6⃣







*zaman gidan jawad*





Zaman gidan Jawad zamane da kokadan bayawa Sarena dadi kowa kansa ya sani musamman yacce take hakuri da halin Nabila da irin izgilancin da take mata,tana goronta mata ita kafura ce.





Wayan dake kusa da ita yayi kara dubanta takai kareta ganin sunan Mom ya bayyana a kan screen din ya sata sakin murmushi da sauri ta dauka tana shaukin jin muryar Mom,saida suka gama gaesawa sannan tace"Sarena kizo muyi bankwana karfe 9:00am jirginmu zai tashi zuwa America ,Daddynki ya gama aekinsa zamu koma kasarmu".



Wata iriyar faduwar gaba ta iske Sarena a hankali tace"Mom zaku tafi Ku barni ni kadai".sai hawaye suka soma bin kuncinta,sallama sukayi ta kashe wayar tana tunanin ina zataga Jawad ta fada masa zataje gida,rabonta da ta saka Jawad a idonta koya kulata tun daran farkon da aka kawota gidan,text ta masa ta waya ta tashi ta fara shiri.



Yana zaune office text dinta ya shigo wayarsa kamar ya duba kamar y bari ,haka kawai ya duba koda yaga me take fada,text ya mata (ki je ae akwai driver kuma kinada mota a gidan kije inda kikaso).



Futowa tayi sanye da dogon Riga iyakarta cinya fara kal gashin kanta yasha kyara dukda ta rame amma hakan besa taki yin kyau ba,ba wata makeup a face dinta amma tayi masifar kyau ,hill shoe ta saka baki ta dauki bag dinta black colour, duba text din da yayi mata tayi,haka kawai taji zuciyarta ba dadi key ta dauka ta fice daga gidan ganin time ya tafi yasa sukayi mahada airport.




Da gudu ta bude motar ta nufi wurin su Mom ganin jirginsu na haramar tashi tun kafin ta isa wurinsu hawaye ke ambaliya a kyakyawar fuskarta,rungume Mom tayi tana fadin"Mommy narh".



Karfin hali Mom tayi tace"a'a Sarena ba kuka yanzufa kin girma,matar aurece,ba yadda za'ayi mu tafi dake, idan kin haihu saiki kaimun Baby na na rike"ta fada tana Jan kumatunta.




Kunya ta kamata ta rufe fuska ta kuma rungume Mom ,sannan ta rungumi Daddy,nan kam Mom ta kasa daurewa haka Daddy yaja Mom suka shige jirgi sukabar Sarena a wurin,tanaji tana gani jirginsu ya tashi,a jirgi Mom kuka take kamar ranta zai fita tana kuma Allah wadai da auran Jawad da Sarena tayi gashi yanzu sun rabu.



Kuka take a haka ta karasa Mota da kyar ta iya shiga mota ta nufi gida ,tana isa da gudu ta fito ta fada part dinta bakinta cike da amai ga wani irin kasala da tashin zuciya dake damunta amai ta zazzaga ba kadan ba da rairahe ta iso a bed ta fada ta rufe jikinta tana kyarmar sanyi har bacci yayi awan gaba da ita.





Tafa hannu Nabila da Hajiya sukayi kafin Hajiya ta sassauta murya tace"waya fada maku barno gabas,take saima tabar gidan kafa zage,yanzu dai ga wannan maganin ki bashi shi a abinci yaci ,dole ya tsaneta ta rika masa warin jaba yaji ko ganinta bayasonyi a gidansa kedai ki dage kiga yaci".




Ansa Nabila tayi tana boyewa a side drower tace"Allah ya barman ke Hajiya ta kin maidani mace na karbe mijina".



Haka sukaita fira marar amfani sai yamma likis Hajiya ta tafi gida.



Bancin Mama ta gama abinci ta jera a dining ,Nabila tazo ta zuba maganin kamar yadda Hajiya ta umarceta,kafin taje tayi wanka,ta shirya cikin atamfa Riga da siket Wanda dasu gwara babu duksun matseta .




Da sallama ya shiga part din Nabila da gudu ta iso wurinsa ya rungumeta yana washe baki yana kara kankameta a jikinsa yana bin wuyanta yana sinsina tare dadan lasarsa.



Zame jikin tayi tace"kaidai baka gajiya muje kayi wanka kaci abinci sannan na baka"ta fada tana kashe ido.



Wanka yayi ya shirya cikin 3kwata da vest ya feshe jikinsa da turare sannan suka iso dining suna makale da juna ,zama yayi ta zuba masa abincin jolluf rice CE da hadadden sobo ,yanaci yana wasa da ita hankalinsu kwance yaci ya koshi yana faman rirriketa.



Sarena dake lekensu ta taga wani irin bakin ciki ya ziyarci zuciyarta ga cikinta dake mata ciwo tanata tashin zuciya zafafan hawayene suka ci gaba da ambaliya a kyakyawar fuskarta da tayi jajir ta sauya launi a kasa ta zauna dishan ta kuma fashewa da kuka tana rike cikinta.







*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻



Share and comment


Luv u all
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA*




🌈kainuwa writers association

United we stand and succed: our ambition is to entatein and motivate the mind of readers




Na
Maryam Ismail
Muhphat



Page2⃣7⃣to2⃣8⃣





A ranar batayi isashen bacci ba,ga dai tsananin ciwo ga kuma kewar iyayenta uwa uba da mijinta ya juya mata baya,har safiya tayi Sarena bata kara sanin inda kanta yake ba,donko tasha amai dukta galabaita ciki ciki take numfashi.




Da misalin karfe11 na safe,Mama dukta damu tun jiya rabon data saka Sarena a idanunta amma ba halin tambaya,suko gasu a parlo sai sheka dariya suke suna fira,karaurawar dakin ta shiga kara alamar damai shigowa,yunkurawa yayi yana fadin"Manab harya karaso kenan".yana budewa kuma zatonsa ya zama gaskiya musabaha sukayi sannan ya shigo cikin gidan a parlon suka zauna,Nabila kuwa kara matsewa a jikin Jawad take ko kunyar fingilallun kayan dake jikinta batayi tana wani narkewa a jikinsa.



Wani bakin cikine ya ziyarci zuciyar Manab a kufule yace"friend ina Sarena?"


Wata faduwar gaba ta ziyarci zuciyar Jawad dandanan ya daure fuska yace"oho ka duba part dinta zaka wani dameni".



Mikewa yayi ya isa part din nata buga kofan yake amma shiru babu ko motsi kasada kawai yayi ya tura ,parlon a gyare sai zuba kamshi yake ko ina tsab,jiyo nishinta da yakeyi a hankali a hankali yasa ya kara isa kusa da bedroom nata aeko itace zaro ido yayi ,da sauri ya karasa ya tura kofar,yadda ya ganta ya masifar tada hankalinsa da sauri ya dawo main parlo yana kwalawa Jawad kira,


Yatsine fuska Jawad yayi a hankali ya furta "Menene kuma".



" lallai Jawad,ka kosan me kake aekatawa da iliminka zaka kashe y'ar mutane,Sarena ba lafiya sosai ko tashi bata iyayi "cewar Manab



" to mezan mata ko yarinyace karama da batasan hanyar asibiti ba,goyata kakeso nayi,nifa malan ba cewa nayi ka daman ba"Jawad ya fada.



Wani far da idanu Nabila tayi sannan tace"haba Habibi nah,ya kamata ka dubata,sannan ka kaita asibiti pls mana"



Tsaki yaja yace"Hada ke za'a tursasani wify gaskiya bazan iyaba ,aetanada hankali karki kara saka kanki a irin wannan don Allah".


Duk yadda Manab yaso Jawad yazo ya dauko Sarena fafur yaki saima ya tashi yaja Nabila suka wuce daki yace inya fita yaja masu gidan.sosai ran Manab ya baci waya ya ciro ya kira Salim ya tambaya ko yana hospital, ya amsa da eh,cikin hanzari ya koma wurinta a lokacin ko motsi batayi,babu yadda ya iya a dole ya dauketa ya fito yana gudugudu ya sakata bayan mota yaja da gudu sai hospital din salim.


Cikin gaggawa aka shiga da ita emergency a rude Manab ya rike hannun Salim yana fadin"pls Salim do ur best ,banaso Sarena ta mutu wallahi ina jinta tamkar ciki daya muka fito banaso na rasata".


Dafa kafadarsa Salim yayi ya daga masa kai ya shiga ciki.



Safa da marwa ya shigayi yana tunanin shinwai meya shiga kan Jawad wannan wanne irin cin zaline haka,yafi awa hudu a nan yana jiran Salim sannan ya futo suka wuce office.



"Wai aekin me Jawad yakeyi yakeson kashe y'ar mutane da ranta" cewar Salim.



"Hm inako zan sani tsohwan Dan iskan ya biyewa wannan y'ar iskar yarinyar ita ke juyashi fuska kamarta biri". Manab ya fada.



" to gaskiya Sarena tana bukatar kula,kagadai ya ciwan zuciyar data samu da ba'a kawota Asibiti ba at anytime zata iya rasa ranta,uwa uba ga cikin dake jikinta tana fama da laulayinsa".



Da sauri Manab ya dago kai yace"Ciki ,kuma da Cikin sa a jikinta yabarta tana wahala gaskiya Jawad ya canza ban taba tunanin zewa Sarena haka ba inka duba irin son da yake mata amma bari mu gani"
Waya ya Ciro ya fara kiransa ,harya fitar da rai akan zai dauki wayarsa sannan ya dauka ajiyar zuciya Manab yayi sannan yace"Jawad wai meke damunka kanaso ka gama da duniya lafiya kuwa?,ka sakawa yarinya ciwan zuciya har yana baraza a rayuwarta,ga Cikin daka dirka mata kuma ka barta cikin wannan halin".



"Dakata Manab tadai sakawa kanta me nake mata,nifa ko sunanta banaso kana ambatamin indai kanaso muci gaba da zama wuri daya,sannan ni tunda aka kawota so d'aya na rabeta sannan kacemin tanada Ciki,toni ban karba ba ba Cikina bane,taje ta nemi Wanda yayi mata shi" be jira ansar Manab ba ya tsinke wayarsa.



Murmushi Salim yayi yace"karka damu Manab wannan bayin kansa bane mudai muyi masa addu'a mu kula masa da matarsa har Allah ya sauketa lafiya shine kawai".




Dakin da aka kaita Manab ya shiga,Sarena yakebi da kallo tayi fari tas abunta ta kara kyau drip ne like a hannunta ,hankalinta kwance tana bacci sai fitar da numfashi takeyi.



Salim ya saka masu kula da Sarena dare da rana,bata da matsalar komai a asibitin ta murmure tayi kiba abunta,kullun Manab da Salim suna tsaye a kanta kwananta biyar aka sallameta,Manab ya dauketa ya maida ita gida yayi mata fada sosai akan tayi hakuri kuma kada ta saka damuwa a ranta.



********



Parlo ta fito dama tunda ta dawo take dakon ganin Jawad ,zaune ta samesa har kasa takai ta gaeshesa tayi masa banza.


A hankali tace"idan bakaji tausayinaba ae kodan D'anka da yake Cikina ka tausayamin my Love ".



Tsawa ya daka mata wacce tasa ta firgicewa lokaci daya tana kyarma.sannan yace" karki kara kirana My love ,Cikin Jikinki ba nawa bane,kije ki nemi Uban danki karuwa kawai,kuma daga yau kin daina zaman banza a gidannan duk wani aeki ke zaki rika yinsa bance ki zauna ki hutaba ,inko naga akasin haka zaki gane kuranki,wannan kadan daga hukuncin Cikin shegen da kika kawomin ne"kafa yasa ya halbeta harta fadi ya wucewarsa.




*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻



Gaisuwata a gareki kawar alkairi masoyiyar Asali na,Khadija Haruna Abdulkadir alkairin Allah yakai maki inayinki irin sosai dinnan.





Share and comment


Muhphat luv
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA*




🌈kainuwa writer's association


United we stand and succed:our ambition is to entertain & motivate the mind of reader's




Na
Maryam Ismail
Muhphat



Page2⃣9⃣to3⃣0⃣




Wani irin kuka ke shirin kubuce mata,da sauri ta toshe bakinta ,sai wasu zafafan hawaye da suka kwaranyo daga idanuwanta ,bakin ciki cike da zuciyarta ,kallon Jawad kawai take harya bacewa ganinta,kasa mikewa tayi daga inda take saida Mama ta kamata sannan dishi dishi ta soma gani a haka tabi bango zuwa dakinta a kan chair ta kifa kanta ta fashe da kuka.




Nabila kuwa duk abunda yake faruwa tana ta window tana lekensu ganin tahowar Jawad yasa tad'anyi baya ,yana shigowa suka rungumi juna kallonta kawai yake ,sannan ya hada bakinta da nashi ya soma tsotsa kamar ya samu sweet daga nan wasa ya sauya,na jawo kafafuna nayi waje😀




*AMERICA*



Zaune take a chair iskar garin na ratsata ,yanayin yayi dadi ga Wanda yake kwanciyar hankali,hango fuskarta nayi idanuwanta rufe suke cikin bakin glass tayi kyau sosai ,saidai hawayen dakebin gefan fuskarta kallo daya zaka mata ka tabbatar tana cikin tashin hankali sosai .



A hankali Mr Samol ya karaso gareta kamata yayi yana goge mata hawaye yace"meke damunki wify".



Bakin Lissa na rawa ta furta"Sarena ,inason y'ata anya banyi kuskuren barinta a Nigeria ba,gashi inata kiran wayarta bana samu".



Murmushi kad'an yayi yace"ki daina damuwa,kinsan mijinta na sonta sosai zai kula da ita,kuma muma zamuje ganinta kada ki damu"
Da kalamai masu dadi ya shawo kan Lissa harta daina kuka ta dauki tunani irin nashi.




Some months later.



Cikin Sarena ya shiga wata na tara a kowanne yanayi zata iya haihu,bayan hanyoyin da su Hajiya sukabi wurin kasheta ita da cikin Amma basuyi nasara ba,hakan ya basu dama suka maisheda Sarena cikakkiyar baiwa a gidan,ko kadan idan bakayi mata mugun saniba bazaka taba ganeta ba tayi baki, ta rame, ta fita daga hayyacin ta koma kazama don a sati so daya take wanka,ga wasu kaya da basu da maraba da tsunma su take sakawa,daki daya suka bata a part din masu aeki wata guntuwar tabarma CE shinfide a dakin sai gefe kullin kayanta na sakawa,rayuwa kenan.




Zaune take a gefan tabarmarta kanta a gwaiwarta hawayene kebin fuskarta daduk ta koje .



Banko kofar dakin Nabila tayi tana yan harare harare tare da toshe hancinta ,wankin dake hannunta ta watsa a jikin Sarena tace "ke dallah tashi ki wankemun kayannan sannan ki wankemun Mota zan fita".


D'ago kanta tayi tanabin fuskar Nabila data gama konewa da mayukan kara fari na kanti" tace haba,wai bakya tausayina kiji yadda nake amma ko'a jikinki kamar kema ba y'a mace ba".



Saurin dakatar da ita Nabila tayi sannan ta kwashe da dariyar mugunta tace"tausayi aeni ban sanshi a kanki ba,na tsaneki yadda na tsani mutuwa ta,dama nace zan sakaki kukan wuya tunda har kikayi kuskuren had'a hanya da abunda nikeso".



Mikewa Sarena tayi sannan tace"tir da irin wannan rayuwa taki,sai naji ke keyi nikejin kunya shin baki girmama addininku ,kobashi ya basu damar auran mace fiye da d'aya ba,amma ke kike jayayya,kodayake ae addinin ba kama jikinki yayi ba"
Dukawa tayi ta kwashe kayan wanki tana tafiya da kyar ta soma wankin kayan tanajin kunar rai a tattare da ita.



Jawad kam ya zama saniyar ware banda Hajiya da Nabila babu mai rabarsa su kadai ke morarsa harta Manab da Salim sun rabu dashi donko kadan bazasu iya daukar halayyarsa ta yanzu ba ko sallah bata damesa ba ,saidai daga gefe suna masa addu'a





Zagaye kawai Umma take tsakar d'aki abun duniya ya dameta ace d'anta na cikinta ko kadan yanzu be damu da itaba yau kusan wata biyu bata sakashi a idonta ba,bazai yiwuba dole tasan abunyi gaskiya ,dole Jawad ya dawo gareta.



Da sallama Momyn Manab ta shigo gidan cike da fara'a mata meson mutane,cikin mutunci Umma ta taryeta suna murnar yaushe gamo,part din Ummu suka shiga a bed suka zauna



A hankali cike da nazari Momy tace"wai meke damunki ?,kika wani fita hayyacinki".



"Ba dole ba,yaufa wata biyu banga Jawad ba,kuma yana cikin garin nan ,an rabani dashi ko ta waya baya iya kirana gaba daya ya koma bashiba" cewar Umma.



Murmushin takaici Momy tayi tace"haka nikejin labari donkoni ya daina zuwa wurina,ya kuma rabu dasu Manab, dama idan na gansa yake d'an debeman kewar *MINAD* to nima ya gujeni,ki tashi ki kama addu'a babu abunda yafi karfin Allah d'anki ze dawo gareki.


Haka Momy tayita bata shawa ta gari,sannan suka rabu akan cewa zasuje gidan jibi.



Flowers duksun cika gidan and'an jima ba'a gyara wuriba,me kyara aka kirawo yazo yayi masu aski,a lokacin kuma Nabila ta fita zuwa wurin bokanta akan ya kashe mata Sarena tunda hartayi bakin maida mata magana.




Askin yake Mama da Sarena suna Sharar flowers din dake zubewa a kasa,sauri Sarena tayi ta dago a firgice har cikin kwalwarta abun ya ratsata ga wani irin mumunar faduwar gaba,a hankali ta dago kafarta daga tudun data taka.

Riketa Mama tayi sannan tace Bari na tona wurin naga menene a ciki,tsab Mama ta tone ramun,wani irin ihu suka rigaji yana fita faga ramin, hannunta na kyarma ta kwaso kayan dake ciki,layune iri iri ,ga katon abu gunki sak sai wani gashi,ga kuma rigar Sarena data Jawad an dauresu wuri daya.



Duk abunda ke cikin layun saida Mama ta karantasu tasan makarar asiri bata nunawa kowa ba facce Sarena ,wuta ta hada ta konesu kurmus tare dayin addu'o'i har suka cinye sannan tasa ruwa ta wanke tokar tas.




Bacci yake tare da mafarki,hannu taketa miko mashi daga cikin bakin ramun da take,tana kuka tana fadin ka tai makeni,zuwa yayi cetonta ya mika mata hannu sai aka janyeta kasa,ga jarirai har biyu sai binsa suke suna kuka,suna kiransa da Abba.
Firgigita ya farka yayi zufa sharkaf a hankali ya furta *MINAD* ina kika shiga kika barni ,zumbur ya mike jikinsa ko kadan ba kwari ga jiri yana gani,tunani yakeyi yaushe rabon da yayi sallah Alwala ya dauro ya soma jero salloli.




Nabila kuwa bokanta ya tabbatar mata saiya sadu da ita maniyinsu shine mahadar gubar kisan Sarena,bako musu ta bishi suka shige bukkarsa suka soma masha'arsu dukda warin da bokan yakeyi haka ta daure har sukayi ya samu maniyyin ya hada maganin a kwalba ya bata tare da sharadin ta tabbatar Sarena tasha wannan maganin cikin ruwa ko abinci.cike da farin ciki ta dawo gida hankalinta bekai kan wurin ajiyarta ba ,ta wuce part dinta tayi wanka don tsabtace jikinta bayan ta gama take shedawa Hajiya yadda sukayi.



Umma kuwa ko kadan taki bacci yanzu ko ta fara saluda zaune take a sallaya tanata yiwa danta addu'o'i,addu'ar uwa akan danta.


Typing ba dadi kuyi hakuri da wannan pls



Comment
Share
Like



Muhphat luv
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA*



Na
Maryam Ismail
Muhphat




🌈kainuwa writer's association


United we stand and succed:our ambition is to entertain & motivate the mind

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login