Showing 3001 words to 6000 words out of 19707 words

Chapter 2 - ASALINA COMPLETE Hausa Novel By completehausanovels.com.txt

23 Aug 2025

186

aka biye maku zamu kwana bamuci abinci ba,don murnar dawowar Sarena,gashi har Furanko ya iso ma". Mother ta fada.




" wa kuma yace dashi na dawo?".Sarena ta tambaya

"Nice mana,ki tsaya Furanko yaron kirkine y'arta kinji"

Bata sake fadan komai ba,suka mike suka tafi dining area ,da sauri Furanko ya shigo gidan da murna yana fadan"welcome back home my Dear".



"Thank u ta fada ,sannan suka rungumi juna,kafin suka soma cin abincin da aka tara musu.



Furanko ya kawo mata gifts sosai duk abunda yasan tana so saida ya siya mata duk a matsayin murnar dawowarta gida.




Zaune suke a parlo suna fira anan ne Dad ke fadawa Sarena zasu koma gida Nigeria akwai wani aeki da zaiyi tsawon 2years,zasu farayin gaba suga komai ya daidaita before ta biyosu.



Wata irin tsalle ta daka da murna zataga Mona kawarta da sukayi karatu anan America tare,rungume Dad tayi tana masa godiya tunda zasuje gobe ita zatazo jibi,key din mota ta zira ta fice domin zagaya gari bag kawai ta dauka.



Nigeria



Zaune suke a desk suna duba wani Zane da sukayi aekinsa.mika Jawad yayi yace" kai Broz na gajifa ga yunwa da nakeji"


Murmushi Manab yayi yace"aekin kenan kaida ba mata ka ajiyeba sai son kaje gida kawai".


"To ae daya muke donko babu mai aure cikinmu ,balle ka fadan haka". Cewar Jawad.



" zauna nan saidai kaji ana ayyiriri Manab yayi aure"



Dariya sosai Jawad yayi kafin yace"da y'ar fura ba".


Duka Manab ya kaimasa ya goce,haka sukaitayin firarsu kwanin birgewa.




Yau tun safe Dad da Mother suka shirya don jirginsu na safene,tare da Sarena sukazo airport din har suka shiga jirgi tana daga masu hannu,hawayen idonta ta share jin wayanta na kara yasa ta laluba aljihun wandonta ta zaro Furanko ta gani ta dauka da fadin"hello"


Banji meya fadaba sai naji tace"no bana gida ma hadu anjima"kafin ta kashe wayar.



Shima Abee da safe ya shirya ya tafi airport don zaije America ya duba wani aeki zai dawo jibi.






Dad da Mother sun sauka a garin katsina a JRA kafin su iso an kyara ko ina a gidan kasancewar gidan babban gida ya tsaru iya tsaruwa ko ina sai Wanda ya gani ,a gajiye sukayi wanka,sukaci abinci,nan Mother ta soma waya da Sarena tana fada mata yanayin gidan da yarda Nigeria take.



Dariya Sarena tayi tace"na kagara nazo Nigeria Mother,kinsan ban taba zuwaba,amma hakanan naji ina matukar son kasar nasan zaiyi dadin zama,musamman idan muka hadu da Mona"





"Ki kwantar da hankalinki ba jibine tahowanki ba,ae karki damu kanki mana,ina kewarki y'arta.


Fira sukayi sosai sannan sukayi bankwana.


M'I love u all

Muhphat love



πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜

*ASALI NA*


πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜


Na
*MARYAM ISMAIL*



🌈kainuwa writer's association


United we stand and succeed: our ambition is to entertain & motivate the mind of readers.




*Ina kike Yusra Jafar wannan page din naki ne na gode da soyayyarki ga ASALI na ,(my Junior tnx ones again)*






Page6⃣





Yaune ya kama zuwan Sarena Nigeria kasar data dade tana mafarki a rayuwarta wani irin farin ciki take ciki,ta hada komai daya kasance zata bukata,jirgin safe zata bi,shiri tayi cikin wani farin wando iyakarsa gyaiwa ,pink din Riga ta saka medan siririn hannu irin na vest ,gashin kanta ta gyara ta daure da white rebom pink din tooms ta saka a kafarta kafin ta jawo akwatinta ta fito parlo.





Zaune ta samu Furanko a parlo yana jiran fitowarta,da mamaki ta karasa wurinsa tace"yaushe ka shigo ne".



"Dama bazaki sani ba,don nace su barki ki shirya tunda murna kike zaki tafi ki barni" Furanko ya fada.




Dariya tadanyi kafin tace"kada ka dauka haka Furanko kasan inason kasancewa dakai ur my best friend u know".




Kamo hannunta yayi ya zaunar da ita,abincin da Nani ta ajiye ya dauko zai bata a baki,rike hannunsa tayi tace"I will do that ".karba tayi ta soma ci kadan tadanci da sauri ta mike kasancewar agogon hannunta data duba taga time ya tafi,bankwana tayima su Nani kafin ta shiga motar Furanko suka wuce airport.




Fitowa tayi daga motar don yanzu zasu tashi,kallonta Furanko keyi cike da tsantsar soyayya wani irin kara jin sonta yake a ransa,hura masa iskan bakinta tayi ,firgigit ya dawo daga duniyar tunanin daya afka.



" me kake tunani nixan wuce"ta fada .

Rungumarsa tayi tace"I'm going to miss u".


Karfin hali Furanko yayi yace"miss u too,ki kula da kanki sai wani lokacin"




Murmushi tayi ta shafa gefan fuskarsa kafin ta juya ta tafi.




Har jirginsu ya tashi Furanko yana wurin tsaye tunanin ya zaiyi da soyayyar Sarena yake,tun suna yara suke tare amma ya kasa fada mata yana sonta gashi hartatafi ta barshi dole yasan abunyi.






A jirgi zaune take cikin farin ciki ta rasa meye dalili,sitmate dinta ta kalla Dattijone mai kyau yasha manyan kaya bamai haske bane sosai saidai kyakyawa ne farin glass ne a idanunsa yana duba jarida,haka kawai taji mutum ya burgeta kallonsa kawai takeyi har suka iso.





Juyowa yayi zai dauki bag dinsa karama dake gefanshi da sauri ta rike tace "Bari zanyi ,zan dauka maka".




Murmushi yayi yana jin son yarinyar a jikinsa har cikin ransa yake sonta,tare da tata ta hada ta dauko suka futo,tsaye tayi cak jin wata iriyar sanyayyar iska da bata tabajin irinta ba tana ratsata har cikin kwakwalwar kanta,furzar da iskan bakinta tayi sannan tabi bayan mutumin har inda ya zauna,aje masa bag din tayi sannan tace"zan wuce Daddy ".




Wani irin yar yaji a jikinsa data kirasa da Daddy dukda hausarta bata fita sosai ya fahimci abunda take nufi" ki tsaya y'ata yaro na yazo,saimu ajeki gida".




"Na gode Daddy ,ban taba zuwa Nigeria ba,ballantana na fadi inda zanje,Driver dina ya karaso ".




Murmushi Abee yayi sannan yace" na gode Allah yayi maki albarka kinji".




Batasan me zata fada ba amma tadai San addu'a yayi mata "na gode" ta fada sannan ta juya ta tafi.




Binta yai da kallo ya fada a fili"yarinya mai kirki da musulmace dataji dadi kuwa akwai taemako".




Tafiya takeyi ta isa wurin driver dinta don ta ganesa ta hanyar waya da sukeyi ,a hankali take tafiya kanta a kasa ji tayi ta bugu da mutum luuuuuu tayi kasa zata fadi,cikin sauri Manab ya ruko hannunta yana bata hakuri.



Wani kallo ta bisa dashi don bata fahimtar abunda yake fada siririn tsaki taja ta wuce.gyada kai kawai yayi ya wuce wurin Abee.




Daukarsa yayi a mota sai faman sannu yake masa suka wuce gida.


Itama mota ta shiga suna tafiya tana bin ko ina da kallo before su karaso katsina daga kano.





"Kaga Jawad ka tashi daga wannan yamutsin abuncin da kakeyi da saika shekara kana yi sarkin bakin rai kawai,kuma kasan yau Nabila zata dawo gidan nan ,saran idan tazo ka mata wannan bakin mishkilancin da rainin wayan daka saba,kuma kasan halin innarku sarai kan Nabila babu abunda bazata iya ba.



Kawar dakai yayi gefe cikin sanyin murya yace" ae dama gulma ta kawota sai inga Uwar da zata dauka a gidan".




"Haka zaka kare sarkin bakin rai ,Allah ya shiryeka".



Be sakebi takan Ummanba ya mike ya nufi part dinsa ya zube bisa tafkeken gadonsa,kallon pic din Minad yakeyi yana sakesake arai yadaiyima picdin zuro,ga kuma murmushin da yakeyi.



Duk kwakwata dole na kyale Jawad donko na kasa gane komai yake fada.





A gajiye su Sarena ta karaso gida dake GRA da sauri ta hada iyayen nata ta rungumesu tana fadin irin missing dinsu datayi.




Cike daso da kauna da farin ciki suka tarbi y'ar tasu suna jin kaunarta.





Da gudu Nabila ta shigo gidan tana kwalawa Umma kira ,ba laifi tana da kyau saidai daka kalli farinta kasan bleecing ke aeki ya maida ita fara bata da kiba doguwa ce tayi kyau kwalliyan datayi,da gudu ta rungume Umma tana jin dadi



" keni karki karyani kinjiko ,duk murnar ne"



Tabe baki Nabila tayi tace"kinsan nayi missing dinki shiyasa nace zan dawo nan da zama fa Umma".




"To Allah ya bamu ikon rikeki da gaskiya y'ar albarka,zako muji dadi".Umma ta fada






M'I love u

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜


*ASALI NA*


πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜


Na
*MARYAM ISMAIL*


🌈kainuwa writer's association


United we sand and succed:our ambition is to entertain & motivate the mind of reader's





Page7⃣



Some days later

Sarena ta fara zama y'ar gari domin Mona na nuna mata wurare da dama a gare,magana taiwa iyayen akan cewa zata nemi aeki a companyn da Mona ke aeki,ko kadan badan ransu yasoba suka barta domin basa son bacin ranta.




Tun sassafe ta shirya cikin riga da siket ,siket din yellow colour mai roba iya karsa rabin cinyarta ,riga ta saka yellow mai hannun Vest sannan ta dauko boyfriend jaket black colour ta saka ,daure gashinta tayi ,dogon takalmi Mae tsini black colour ta saka tare da bag dinshi ,Key din motarta ta dauko tayo waje tana duba agogon hannunta .




Da sauri Mother ta tareta tace "haba bazaki break ba,kuma ki bari driver ya kaiki banason fitanki ke kadai".



" is OK Mother zanyi break anjima,kuma na soma gane gari nasan inda zanje basai kin damu dani ba".Sarena ta fada





Bude baki Mother tayi zatayi magana,da sauri Dad ya rufe mata baki yace"ki barta taje,bana son kina matsa mata".




Rungumesu tayi tare tace"bye bye"bata jira cewarsu ba ta fice daga gidan,kai tsaye wurin Motarta ta nufa kirar Vive black colour ta shiga ta fita daga tankamemen gidan.kai tsaye companyn ta nufa tasan anan zata iske Mona.




Ajiyar zuciya Mother ta sauke tace "kawai na damu da itane"



"Na sani Lissa amma karki damu ,babu abunda zai sameta" Samol ya fada yana rungume Lissa a jikinsa.





Titowa yayi sanye da black suit sai farar inner wear yayi tokin jikar laptop dinsa na a hannunsa yayi masifar kyau ga wani sihirtaccen kamshin dake fita a jikinsa,kai tsaye dianing area ya nufa,anan ya iske su Daddy ,gaeshesu yayi,cike da zumudi Nabila tace"Yaya Jawad ina kwana".



Ba yabo babu fallasa yace"qlau".zama yayi a chair yana furzar da iskan bakinsa.



"Kiyi saving dinshi kinji Daughter" Momy ta fada.



Tam ya daure fuska wani mtsssss yaja tsaki ,wani irin mugun kallo ya bita dashi ,ya tashi ya dauki bag dinsa ya fice ko bankwana.




"Uban yan bakin rai,baka daiji dadi ba". Umma ta fada.



Murmushi Daddy yayi yace" sai kunbi yaronnan a hankali domin kunfi kowa sanin halinshi ,ke kuma Nabila saikin daure kin hada da hakuri akan Yayan naki".




Yana fita kai tsaye company ya nufa office din Manab ya wuce dayake shine M.D na company, Jawad kuwa Director ,fuska daure ya shiga office din ya zauna ba tare dayace kala ba,Shima Manab bai tankashiba saida ya ida yan danne dannensa a laptop sannan yace"yadai mutumin yau na ganka a fusace".




Mtsssss tsaki yaja before yace"Momy ce mana,sai ta rika saka wannan yarinyar tanamin abu bacin sunsan bana so".




Dariya Manab yayi yace "to minene a ciki ba kanwarka bace sarkin son girma".



" kaga kaima karka batamin rai malan"Jawad ya fada a fusace.


"Iz OK,yanzu ba wannan ba,yau sabuwar ma'aikaciyarmu zata fara aeki ,a America tayi karatu result dinta yayi kyau komai da muke bukata tana dashi,don haka itace ,assistant Director, mataimakiyarka,tunda dama a kujeran ba kowa".




" ba damuwa"kawai ya fada ya fice ya nufi office dinsa.




A parking space tayi parking sannan ta Ciro waya ta kira Mona ba jima ta karaso suka shiga ciki,office din Manab suka shiga,kallonta kawai yake yanason tuno inda ya taba ganin face dinta amma ya kasa itama haka,sharewa yayi ya ida mata abunda zaimata ya turata office dinta.zata fara aeki daga ranar.godiya sukayi suka futo,Mona kam wucewa tayi office dinta itama.





Tsayawa tayi a bakin office din nasu sannan tayi knocking, "yes come in" ya fada.




A nutse ta fara taku zuwa cikin office din ta isa kusa da table dinsa,tun daga kan santaleliyar kyakyawar kafarta ya soma kallonta har zuwa kyakyawar fuskarta wani irin dummmm yaji a kirjinsa lokacin da suka hada ido da ita,itama hakan taji ya faru da ita,daurewa tayi tace"Morning sir,nice sabuwar office mate dinka da zamu fara aeki tare".





Dan murmushi yayi da gefan baki yace"your welcome".



Hannu ta mika masa tace"thank u,I'm Sarena Samol nice to meet u".




Shima hannun ya bata suka gaesa yace"I'm Jawad Al-Ameen,nice to meet u too"


Wani irin yar yaji lokacin da hannunwansu suka hadu,wurin table din daya nuna mata ta nufa ta zauna,tasowa yayi ya Dan nununa mata aekin dake garesu da yarda suke aekin,godiya ta masa ta soma aekin.




M'I love u all
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜



*ASALI NA*


πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜



Na
*MARYAM ISMAIL*



🌈kainuwa writer's association



United we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers




*IT UR DAY YAYA HAYAT*


*when a year is dead,a year is born,when poverty dimishes,riches overflows,when sadness is gone ,happinesses is all that u have so as u have achieved from the past..happy birthday! Yaya hayat ones again.*




Page9⃣






Suna isowa asibitin da gudu aka iso da gadon daukar mararsa lafiya,aka dorashi a sama aka soma turashi zuwa emergency da gudu Sarena ta juya zata bisu riko hannunta Manab yayi ya jawota,jikinsa ta fada tana kuka mai tsima zuciya,rarrashinta ya somayi yana bata hakuri yace"kiyi hakuri dama yanayin haka cos yana da ciwan zuciya ,kada ki damu zaiji sauki".





Share hawayen idonta tayi tace"ciwan zuciya,me kuma ke damunsa meya rasa haka".




Shiru Manab yayi yana kallonta ya kasa fada mata komai,tunani yakeyi da yanzu Minad takai kamar haka ko ,kuma da yanzu suna tare,ji yayi hawaye na neman zubo masa yayi sauri ya kauda kai gefe dai dan fitowar Salim suka wuce office, anan akabar Sarena tanata saka da warwara a ranta.






Gaesawa sukayi da Salim sanan yace"yanzu kuma me akayi masa,ciwansafa yana kara gaba fa".




Murmushin yake Manab yayi yace"look at u kaima kasan damuwar ae basai an masa komai bama yana tashi".





Dafe kai Salim yayi yace"wallahi Manab i don't want to lose my friend, ya kamata I yanzu mu fallafawa Allah lamarinsa domin shikadai yasan inda Minad take kuma shizai kareta".




"Haka ne friend buh kasan yanda Jawad da Minad suka taso,abun yafi karfinmu saidai mu tayasa da addu'a,bari na kirawo su Umma".




Lokacin aka fito da Jawad a bed yanata sharar baccinsa daki aka canza masa,da sauri Sarena ta shiga dakin tana kallonsa cike da fargaba da tsoro,addu'an ya tashi kawai takeyi wayanta ne ya soma ringing tana duba taga Mom ,dauka tayi jin tana kiranta emergency yasa ta sauke wayar a kunne ta juya tana duban Manab dake bayanta.





" don't worry, Ummansa tana zuwa yanzu zaki iya tafiya,kiji kiran da ake maki,hannu tasa ta janye gashinkanta zuwa baya,ta duka ta sumbanji Jawad a goshi"tace,fatan samun lafiya,kawai na damu dakai, I will be going"ta fadawa Manab





"Ga car key dina kije da ita".



" no am ok zan dauki mota naje company na dauki tawa"bata jira mezaice ba ta fice daga dakin da sauri tana duba Jakarta,ashhhhh naji ta fada tana dafe gefen kanta yayinda Nabila itama taja baya rike dakai tace"ke dabbar inace bakya ganine ko hanyan ance ta tsohoce kafura kawai".




Juyar dakai Sarena tayi ta duka ta dauki wayanta tabi ta gefanta ta wuce,da sauri Nabila ke shirin binta Umma ta riko mata hannu tace"kiyi hakuri muje muga yayanki".





"Umma harta isa wacece ita,aena rike face dinta zamu hadu wata ran" Nabila ta fada tana kumfar baki.




Sarena kau taje company ta dauki Motarta tuna maganganun Nabila a kanta ya tilasta mata ta yanke hukunci dole ta samu Wanda zai koya mata Hausa sosai ko biyansa zatayi,da wannan tunanin ta isa gida.




Tana shigowa parlo ta saki Jakarta a chair ta dauki glass cup mai dauke da ruwan sanyi ta kurba,da sauri Lissa ta nufo ta kamata tace"ke Sarena meke damunki naga kin damu da yawa haka?".





Murmushi Sarena tayi tace"a'a Mom kada ki damu ba komai bane ,kawai na gaji ne"






"Ki samu kiyi wanka ki huta kinsan na damu dake sosai" kama hannunta tayi suka shiga dakin Sarena,taimaka mata tayi ta cire kaya ,saida ta tabbatar ta shiga toilet sannan ta baro dakin,kai tsaye kitchen ta nufa wutin Nani kas tasa ta hadawa y'arta abinci takai mata daki.






Tana fitowa wanka taci karo da abinci a table ,tsane jikinta tayi sannan ta saka vest da karamin sikat rabin cinya ta feshe jikinta da turare ko bra bata saka ba,sama sama taci abincin sannan ta kwanta a bed tana tunanin Jawad da haka har bacci ya kwasheta.






Su Umma kam suna shiga sukayi kan Jawad ,Umma ta soma shafa masa fuska,a hankali ya fara bude idonsa yana binsu da kallo harya isa kan Manab"ina Sarena?".abunda ya fada kenan.





Murmushi Manab yayi yace"ta samu emergency call ne taje gida wurin Mamanta,kada ka damu tana lafiya"





Sai a sannan ya kalli Umma yace"sannu da zuwa".


Murtuke fuska tayi tace"ae nasa baka ganniba,tunda saida ka gama tambayar wacce ta fini".




"Kiyi hakuri " kawai ya fada.Nabila ta soma masa ya jiki cikiciki ya ansa kafin yace"nifa mu koma gida bazanyi zaman hospital ba,ina Salim din yake".




A dole suka sallamesa a ranar badon sunso ba saidon kafewarsa don tunda ya fada sunsan zai iya tafiyarsa gida ne.




Bayan wani lokaci Jawad ya warke tas yau tun sassafe yake shiri zai koma office as everyday wankan suit yayi white colour da inner black yayi masifar kyau sosai kaman ba shiba fitowa yayi yadanyi break ya kama hanyan company, parking yayi ya fito yana takun kasaita kai tsaye office dinsu ya nufa a kofa sukayi karo da Sarena tsaye sukayi suna kallon juna,sanye take da White wando har kasa sai black riga mai Dan karamin hannu gashinta a gyare yake ta zubosa har gadon bayanta yanata sheki plat shoe ne kafarta baki tayi kyau sosai sai zuba kamshi takeyi,kallon juna sukeyi kamar a yau suka fara ganin juna.



Wai Allah kuyi hakuri da wannan






M'i love u all


Ur comments is needed shizaisa mu zage my gane kuna so mitayi maku typing ba ji ba gani




πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜


*ASALI NA*


πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜



Na
*MARYAM ISMAIL*



🌈kainuwa writer's association


United we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers.





Page8⃣






Cikin sauki Sarena ta gane komai da company ke bukata da aekinta ,ba laifi sun saba da Jawad yana sakan mata fuska

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login