Showing 1 words to 3000 words out of 19707 words
Chapter 1 - ASALINA COMPLETE Hausa Novel By completehausanovels.com.txt
ο»Ώ[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: ππππ
πππππ
*ASALI NA*
ππππ
πππππ
Na
*MARYAM ISMAIL*
πkainuwa writer's association
(Uniterd we stand & succed: our ambition is to entertain & motivate the mind of readers)
This novel Dedicated to saldefi student 2016
Bismillahi rahmanir raheem
Ya Allah yadda ka bani ikon fara novel dinnan lafiya kasa na karesa lafiya .Ameen
Page1β£
A garin katsina Alhaji Jabir ya taso haifaffen garin ne iyayensa babu laifi sunada yali yana da amini wato Alhaji Aminu sun taso tun yarinta.
Sunyi karatunsu na boko da arabi sun samu ilimi daidai kima ,bayan dawowarsu daga masters Allah yayiwa iyayen Jabir rasuwa ta hanyar hadarin mota.
Kasan cewar shi kadai suka haifa yasa ya gaji duki mai tarin yawa na daga kamfanoni gidaje .
Yakan yasa Aminu ya fara jin haushinsa saboda ya fiyeshi da komai.
A haka sukayi aure Jabir ya auri wata buzuwa mai suna Fatima.
Shiko Aminu ya auri Asma'u anan kusa dasu take kuma Allah yasa halinsu yazo daya.
Wata tara daidai su duka suka haihu inda Jabir yasa sunan mahaifinsa wato Kabir ake kiran yaron da Manab.
Aminu kuwa yasawa Dansa suna Jawad .
Amintarsu tayi karfi sosai komai tare sukeyi sun zama tamkar uwa daya uba daya duk wani sirrin Jabir Aminu ya gama saninsa,gashi beda shaki da dukiyarsa komai zai iya aekatawa a cikinta.
Shekarun su Manab 8 Fatima ta sake haihuwar santaleliyar yarinyarta kyakyawa ta karshe gata fara tas ,don duk ta fisu kyau nesa ba kusaba,ranar suna yarinya taci sunanta Saudatu suna kiranta Minad.
Minad ta taso cikin gata da soyayya da kulawa ,kowa na matukar sonta musamman Abee dinsu daya ke sonta fiye da komai nasa.
Ko kadan Minad bata da hayaniya dukda gatan data samu bae hanata samun tarbiyyah ba,wata iriyar soyayya sukewa juna ita da Manab.
Some years latter
Minad takai shekara 3 a duniya,nan mahaifinta ya sakata makaranta tare da yan uwanta.
Da sallama Abee ya shigo gida ,yayinda Minad ke zaune a chair tana game da tab din dake hannunta kirar iPhone, gashi tasha kwalliya tayi matukar kyau.
Da gudu ta taso ta fada jikin Abee tana fadin"Abee oyoyo"
Rungumeta yayi sosai a jikinsa kafin yace"sannunki da gida Maman baba".
"Yauwa Abee,muje kaci abinci na baka labarin school dinmu kaji" Minad ta fada
Tsaye Amma tayi tana binsu da kallo kafin tace"sannunku da labari a tsaye,ko tunawa damu ba'ayi balle musan ka dawo".
Dariya yayi kafin yace"ina nan da Mama na muna labartawa ne".
Da murna Manab ya iso wurin ya karbi bag din Abee tare da masa sannu da zuwa.
Minad na ganinsa ta duro ita saiya goyata dama nemansa take.
Dariya Manab yayi yadanja karan hancinta yace"see u shiyasa na buya naki donna samu nayi homework rigimammiya"
Goyata yayi suka wuce ciki suna dariya.
Gidan Alhaji Jabir gidane mai cike da farin ciki,gashi wani irin tabkeken gida ya tsaru iya tsaruwa.
M'I love u all
πππππ
πππππ
. ππ
ππππ
ππ
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: ππππ
πππππ
*ASALI NA*
ππππ
πππππ
Na
*MARYAM ISMAIL*
πkainuwa writer's association
(United we stand and succeed:our ambition is to entertain & motivate the mind of readers)
Page2β£
Bayan Abee yayi wanka ya gama cin abinci ne ya fito parlo da niyan ya huta,sallamar Alhaji Aminu ne da iyalansa ya janyo hankalinsu shida Amma,maraba da zuwa suka farayi masu suka karaso cikin fara'a da murna.
Bayan sun gaesa kafin kace me tuni masu aeki sun cika masu gaba da kayan makulashe.
Kallo Amma Jawad yayi yace"Amma ina minad ?".
Kafin Amma ta bada amsa tuni Minad ta fito da gudu tana saukowa a stairs tana fadan"ga Yaya oyoyo".
A nitse Manab ya take mata baya ya iso ya duka gaban Daddy wato Alhaji Aminu, ya shiga gaishe dasu shida Momy.
Minad kuwa kai tsaye ta makalkale Jawad tana murnar ganinsa dukda fushin da take dashi na ya daina zuwa ,hakan be hanata farin cikin ganinsa ba,dukda kankantar shekaru irin na Minad hakan besa ta kasa gane abunda take so ba,gata da masifar wayo sosai.
Bayan sun gama cin abinci ne,suka tashi zuwa dakin wasansu,su Amma kuwa suka wuce zuwa dakinta suna labartawa.
Anan ne Alhaji Aminu ya kyara zama ya tuskanci Alhaji Jabir yace"nazo ne neman wani abu wurinka ,kuma inada yakinin zan samu samoda iriyar tarayyar dake tsakaninmu".
Nan Alhaji Jabir ya tattaro duk natsuwarsa yace"ina jinka ,kuma Allah yasa zan iya yi maka".
Murmushi Alhaji Aminu yayi yace"wani abokin harkata ne yaga companyn ka na *MINAD INVESTMENT* ,yana so ka sayar masa dashi ".
Kallonsa kawai Alhaji Jabir yayi kafin yace" nasan kafi karfinsa a wurina amma kayi hakuri ba mallaki na bane ,kasan na Mamana ne na malka mata shi tuni ka bashi hakuri".
Wani kululun bakin ciki yai wa Alhaji Aminu tsaye a rai,yana tuna asarar makudan kudin da zaiyi,wata irin sabuwar tsanar Jabir ta sake darsa a zuciyarsa,amma ya daure yaci gaba da lallabashi.
Ko kadan Alhaji Jabir yaki sauya ra'a ya tsaya kan maganarsa ta farko.
Wayancewa Daddy yayi yace"to ae shi kenan saiya yakura dama jarabawa nayi,karka damu komai ya wuce".
Haka suka karashi firarsu har tsawon yinin ranar kafin suka tafi gida,inda sukayi maganan anan Abee yabarta.
2:30pm
Daddy ne keta safa da marwa a tsakiyar tankadedan dakinsa hankalinsa tashe yana tuna irin dumbin asarar da zaiyi .
Kallonsa Momy tayi tace"ae wannan ba masoyinka bane wanda zaisa kayi asarar makudai haka,kuma ka zuba masa ido kana kallonsa,bazai yiwuba kasan nayi Daddyn Jawad".
"To me zan masa,naga dai nasane kuma yace bazai sayar ba dole muyi hakuri..."
Kafin ya idasa maganarsa Momy ta dakatar dashi ta mike tsaye ta fara zagaye shi kafin tace"kada kaban kunya mana,ba haka nasan Mijina ba,a maka wannan asara kuma kace kayi hakuri, never ya kamata ka masa abunda bazai taba mantawa dakai ba ka koya masa hankali".
Lumshe ido Daddy yayi yace"me kike tunanin zan masa dazai tsaya masa arai".
Dariya tayi kafin ta daure tuska tace"badai companyn Minad bane,kuma ka manta yafi sonta da komai nasa,to kanta zaku huce Ku dauketa Ku lalata mata rayuwa Ku rabasa da ita na tsawan shekaru,ta tashi a matsayin kafura,wacce batasan ta kalli gabas ba ,Ku fitar da ita daga kasar nan,kasan babu abunda zaisashi bakinciki ,kuma yai masa taban da bazai taba goguwa ba,ya hanaku kamtanin Minad,toku Ku nisan tashi da Minad din baki daya".
Wata irin dariyar mugunta ya fashe da ita,sannan yace"gaskiya inajin dadin zama dake,dama kinga Samol zai koma,sai kawai ya tafi da ita America ".yana gama fadar haka ya fita daukar wayarsa a parlo.
Wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyar Momy ganin tasa Mijinta farin ciki ,haka ta kwanta cike da murna a ranta.
M'I love u all
πππππ
πππππ
ππ
ππππ
ππ
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: ππππ
πππππ
*ASALI NA*
ππππ
πππππ
Na
*MARYAM ISMAIL*
πkainuwa writer's association
United we stand and succed:our ambition is to entertain & motivate the mind of readers.
Page3β£
Daddy kuwa yana fitowa parlor ya dauki wayarsa ya kirawo Mr samol kuma ya amince zai dauketa subar kasar,sannan ya kuma kiran amintattun yaransa ya fada masu mai yake buka,ya kuma ja kunnensu akan kada a samu matsala kuma ya zama dole su kawo masa Minad duk rintsi.haka Daddy ya kwana cike da farin ciki dajin dadi.
7:10am
Nani din Minad ta futo rike da ita sanye cikin uniform, sunyi masifar karbar jikinta siket din iyakarsa gwaiwa red sai farar riga da kwalliyan red a jiki ,gyaran gashi aka mata sai y'ar karamar hula a kanta red.
Daga stairs suka sauko iske Abee tayi yana karatun jarida idonsa sanye da white glasses, sai Amma da Manab a dining table Manab na break fast,shima yayi shirin school da irin colour din Jikin Minad,saidai shi ya saka suit red da ratsin White students din little angle kenan.
Cikin sauri ta isa ga Abee ta rungumesa tace"Good morning Abee".
"Morning My Dear,maza aje ayi break fast kada kuyi latti".
Gyada kai tayi ta wuce ta gaeshe da Amma da Yayanta Manab,nan fa aka soma rigima da ita ita bazatayi break ba,da kyar Abee ya lallabata yasa tadanci Irish potatoes da stew din egg.
Cike da girmamawa Nani ta shigo tace"Hajiya driver din ya shirya kada suyi latti".
" OK suna zuwa yanzu"Amma ta fada.
Har sun kusa fita Minad ta dawo tayi hugging Abee da Amma a tare kafin tace"I'm going to miss u".
Dariya sukayi kafin Abee yace"Allah yayi maki albarka ayi karatu sosai saikin dawo"
Ta tsaya surutu Nani ta sab'eta tana fadin"sai kinsa kun makara ko".
Dariya suka fita sunayi,girgiza kai Amma tayi tace"inasan Minad na kasancewa da Nani ,tana matukar farin ciki suna son junansu".
"Ae gaskiya Jamila tayi tana kula da Mamana sosai". Haka suketa dan fira jefi jefi.
Dai dai wannan lokacin ne yaran Alhaji Aminu suka takewa Motar su Minad baya,har suka shiga cikin makaranta,su kuma sukayi parking suna tsara yadda za'ai su dauketa.
1:30pm
Jazi ya shiga cikin little angle yana zagayawa donko an tashi yaran kanana dake primary, nan yai sa'ar hango Minad na dososhi a nutse,murmushi yayi da yaga ta iso dap dashi ,nan ya zubar da kudin dake hannunsa ya juya ya soma tafiya sannu sannu.
Dafe kai Minad tayi time din data iso wurin kudin tace" oh my God kuji wancan Yayan ya yarda kudinsa ,maybe ma bashi da wasu".ganin zai bace mata yasa ta dauki kudin ta bisa da gudu tana kiran"Yaya,Yaya".
Lokacin data iso gate ba gateman yadan zaga bandaki hakan ya bata damar fita ,tsaye ta hangesa ta isa gunsa da sauri tace"Yayana kana neman kudinka ne ko?".
Daga mata kai yayi alamar eh ,kafin tace"gasu ka zubar dasu a cikin school dinmu ka rika kula da kudi kaji ko suna da mahimmanci a rayuwarka"
Da sauri ya ruko hannunta yace"na gode"
"Ka godewa Allah ,bani na taemako kawai nayi".
Da murmushi ta juya wani abu Jazi yai saurin shaka mata a hanci ,ba jimawa ta lankwabe zata fadi,saurin daukarta yayi ya fada da ita mota inda su Tiger suke da sauri suka fizgi motar suka bar wurin.
A kuma daidai lokacin Driver dinta ya shigo wurin ya shiga don daukarta,duk fadin Makarantar aka duba babu Minad ,Manab dayaji labari da sauri ya fito idanuwansa sunyi jawur ,a nanne y'ar ajinsu ke fadar taga fitarta waje,wasa wasa har wurin 3:00pm babu alamun Minad a school din,a dole aka sanar da Abee dinta.
A rude ya shigo makarantar yana goge gumi nan aka fada masa duk abunda ya faru a take ya Ciro waya ya shaidawa police abunda ke faruwa suka bazu don fara bincike a kanta.
Kamar sunsan haka zata faru kai tsaye airport suka wuce da Minad anan suka samu su Alhaji Aminu ,kai tsaye suka mika Minad hannun Lisa wato matar Mr samol,hannu biyu ta karbeta kasancewar bata taba haihuwa ba gata da son yara.
Kallo Mr Samol Alhaji Aminu yayi yace" gata nan amana kada ka ruguza mana plan please,kada Ku dawo har nan da tsawon shekaru masu dama".
Murmushi Mr Samol yayi ya fada a gurbatacciyar hausarsa"baka da damuwa zanyi hakan".
Bankwana sukayi suka shiga jirginsu dazai tashi yanzu zuwa America, Alhaji Aminu na tsaye har jirgin ya tashi sannan ya juya zai tafi karar wayarsa ta tsayar dashi nan yaga amininnasa ne ya dauka tare da sallama.
"Kazo Minad ta bata har yanzu ba labarinta" Abee ya fada.
"Subuhanallah sai kace wasu kaya,bazai taba yiwuwa ba,ganinan zuwa school din"
Bai jira ansa ba ya kashe wayar tare da bushewa da dariyan mugunta sannan ya nufi school din.
Lokacin daya isa school din bala'i ya shigayi anata rarrashinsa amma Sam ya tubure yaki saurarawa yana fadan laifin makarantar ne da suka barta ta fita.
Da kyar Abee ya lallabashi suka koma gida.
A parlo suka samu Amma zaune kallo ta bisu dasu ganin kowa fuskarsa cike da muwa sannan ta fara tambayar ko lafiya.
Murmushi Abee yayi yace"dole mu dauki kaddara Amma,Allah shi yasan me take nufi da hakan".
"Wait Dr wani ne ya mutu ko yaya ina Minad ?".
"Sai hakuri Amma ,Minad ta bata tun dazu ba'a sameta ba". Alhaji Aminu ya fada.
Da sauri Amma ta mike hawaye suka gangaro mata a fuska tace"never duk inda y'ata ta shiga dole a fito da ita bazan taba lamunta ba"
Tana karashe magana jiri ya soma dibarta basu ankara ba sai ganinta sukayi kasa a sume.
M'I love u
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: ππππ
πππππ
*ASALI NA*
ππππ
πππππ
Na
*MARYAM ISMAIL*
πkainuwa writer's association
United we stand and succeed:our ambition is to entertain & motivate the mind of readers.
Page4β£
Da sauri sukayi kanta Manab ya dauko glass cup da ruwan sanyi yana zuba mata yana fadan "Amma na ki tashi don Allah".
A hankali ta soma bude ido tana binsu da kallo,sosai ta rike Abee tana kuka lokacin da ta tuna abunda ke faruwa.
" yanzu kana nufin Minad ta tafi ta barmu?,wanne irin bakin ciki ne wannan me ta aekatawa wani".
"Kiyi hakuri kaddara ce ta kama haka idan Minad rabanmu ce zata dawo garemu,kuma kinga yan sanda na bincike akan lamarin" Alhaji Aminu ya fada.
Nan dai sukaita ta bata baki harta hakura ta rungumi kaddarar data iso garesu.
Wasawasa abun yaci tura duk inda ake tunanin Minad ba'a sameta ba har sun hakura sun fallafawa Allah al-amarinsa suna addu'ar samun zabin alkairi dukda damuwa na damunsu.
Rike da plate din abinci Momy ta fito kai tsaye dakin Jawad ta nufa ,can jikin bango kusa da bed ta gansa ya hada kai da gwaiwa,a hankali ta dafasa tace"Mike damunka Jawad ka duba yadda ka koma,baka cin abinci kullun sai damuwa".
Hawayen idonsa ya goge yace"Momy yanzu mun rasa Minad kenan?,gaskiya Wanda ya dauketa bashi da imani,kuma na ganesa sai munyi shara'a don bazan taba yafe masa ba".
"A'a Jawad ka daina fadan haka,Ku mata addu'a zaifi "
Nan ta lallabashi yadanci abinci,har bacci ya saceshi ,nan ta soma tunanin yadda zata bullowa lamarin Jawad.
America
Tunda su Samol suka isa America Minad ke masu kuka a kaita Abee,wani irin son yarinyar ya darsu a zuciyar Lissa tana matukar son Minad tana bata kulawa musamman daya kasance basu taba haihuwa ba.
Yanayin kulan da suke da ita yasa cikin kankanin lokaci Minad ta mance wacece ita, minene ASALIN TA,tuni sunanta ya tashi daga Minad ta koma tana ansa suna *SARENA* kwata kwata kamanninta duka sun rikede,tana zaune cikin gata da kula da soyayya taban mamaki komai take bukata shi take yi ,musamman Samol da yake yana da kudi sosai,tuni ya riketa kamar y'ardaya haifa,ya sakata makaranta mai kyau gata ta koyi riko da addini sosai bata wasa da addinsu.
*SOME YEAR'S LATER*
πππππππ
Cike filin makarantar yake duk inda ka juya zakaga dalibbai da kayan bautar kasa(N Y S C).ko wanne cike yake da farin ciki,da iyayen zagaye da wurin.
Wata doguwar kyakyawar yarinya na hango fara tas gashinta har tsakiyar baya yasha gyara fuskarta babu wasu tarkacen makeup a jiki kayan bautar kasane jikinta tayi tokkin da farar green din na daure ga kugunta rike take da sateficate dinta da gudunta ta iso wurin iyayen nata ta rungume wani dattijo Dan gayu dashi tace"I miss u Dad"
Sannan ta rungume matar dake gefanta tace"Mother I made it".
Dariyar farin ciki sukayi suka rungume juna tare,suna kukan farin ciki.pic sukaci gaba da dauka kafin suka taho gida cike da farin ciki dajin dadin da soyayyar juna.
Nigeria
Yanzu kam alhamdullih Amma ta daina damuwa ta boye abun a ranta, ta rungumi kaddarar da Allah ya dora mata.
Jawad da Manab a kamfanin Abee suke aeki sun karanci Architecture sun zama manyan samari kyawawa saidai Jawad black beauty he ba fariba sosai ,zumuncinsu sai karuwa yake bacci kawai ke rabasu.
Haka zalika ga iyayensu ma suna gudanar da rayuwarsu cikin jin dadi da soyayyar juna,yayinda Daddy da Mommy suka zama masu fuska biyu .
M'I love u all
Muhphat love
ππππππππ
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: ππππ
πππππ
*ASALI NA*
ππππ
πππππ
Na
*MARYAM ISMAIL*
πkainuwa writer's association
United we stand and succeed: our ambition is to entertain & motivate the mind of readers
Page5β£
Da karasowar su Sarena gida da murna ta fada a chair tana fadin"I miss u home".
"Ke nasan kin gaji ko,kizo kiyi wanka ki huta mana" Mother ta fada tana kamota.
Tayata tayi ta cire kaya tare da daura dan karamin towel a jikinta before ta shiga toilet ,tuni Mother ta fitar mata da kayan da zata saka kafin ta fita,gidan ya kauraye da kamshin girkegirke kala kala da sukayi don tarbar Sarena.
A hankali ta zuro kyakyawar kafarta daga toilet zuwa cikin tankameman dakinta daya hada komai ya kawatu,karamin towel ne a hannunta tana goge gashin kanta dake jike da ruwa,bakin mirrow ta tsaya ta shafa mai tare da powder jikinta ta feshe da turere kafin ta dauko kayan da Mother ta fitar mata,wando ne iyakarsa rabin cinyarta kalar brown sai riga marar nauyi fara iyakarta kugu,gashin kanta ta shafe damai ta sakesa har gadan bayanta ,fashion silifas ta saka kafin ta kara gyara yar siririyar sarkar zinarin dake zanan kuroz a wuyanta sannan ta fito parlo.
Zaune ta samu su Dad suna jiran ta fito suci abinci,da murmushi ta karasa tace"kuyi hakuri na barku kunata jirana ba".
"Kinga zo nan y'ata ,ba wani damuwa ae wannan ranarki ce" Dad ya fada.
Kusa dashi ta zauna ta dora kanta a kafadarsa tace"ina sonka Dad".
"Idan