Showing 6001 words to 9000 words out of 15413 words

Chapter 3 - MOH MAHEER

unknown   

23 Nov 2024

2493

da alama itama sallahr ta idar ta fito,




"yanzu nake shirin zuwa duba ki ai nasan halinki da shegen bacci kamar kasa"
"Eyya ammi ai na dena yanzu"
"Naji zoki zauna kici abinci dan nasan "
"yanzu saiki shashantar da cin abincin"
Batayi musu ba domin ko tanajin yunwar Dan rabonta da abinci tun jiya da daddare saboda tsabar dauki ya hanata cin abinci,matsawa inda kulolin abincin suke a jere tafa budewa,shinkafa da Miya ta zuwaba kadan kamar cin yara,sai kuma ta hada shayo me kauri sosai.



Tana cikin cin abincin ammai take fada mata nadin da za'ayi wa mudassir,cak ta tsaya na dan wani lokaci sannan ta cigaba da cin abincin ta,kamar abin bea dameta ba,Amma cikin ranta mamaki take ta yadda hakan zea yiyu,itama Ammi shirun tayi tunda taga alamar maganar tata bata samu karbuwa ba.



Da daddare ammi ta tura neman iso gurin me martaba,sanda jakadiyar taje kamar ba zea amsa ba sai kuma yace sai tazo,domin shi harmantawa yake da ita,inba ganin ta yayi ba,domin a duk lokacin da yake ganin ta wata muguwar tsanarta yake ji,itama kuma da game hakan sai ta deana shigar da kanta al_amuranshi Kuma a mamakinta bece komai ba.




Jakadiya na fada mata yace taje ta leka dakin ruwana tace mata zata dan fita, fatan dawowa lfy kawai tayi mata,amma bata tambaye ta Ina zata je ba dan tunda ta koma daki take ta jujjuya maganar nadin mudassir,amma ai ba abinda ya shafeta wannan tunanin da tayi ya saka ta watsar da batun da dauko wayar ta ta kunna ta.



Yana ganin ta ya hade rai kamar bea taba dariya ba,gaishe shi tayi cike da girmamawa,ya amsa kamar baya so,shiri ne ya ratsa palorn na wasu mintuna,
"Idan baki da abin fada ni ina da uzuri"
A jiyar zuciya ta sauke sannan tace dama akan maganar nadin mudassir ne,kowa yasan halin yaronnan Amma kum..
Katse ta yayi cike da masifa"Amma me amina nace Amma me........



from
Magic guill pen


09121810091
Whatsapp only

~MOH (MAHEER)


Mikiya writers association
'?


This page dedicated to my father>??


Typing
'?
Page 7&8



Amma me Amina tambayar ki nake kinyi min shiru, dakyar ta iya danne kukan dayake taso mata tace,
"Hakan bea dace ba Koda ba saboda bashine magajin kujerar nan ba, saboda halayyar sa"ba yadda za'ay ace me shugabantar al_umma Kuma yana bata su, maganar gaskiya ce kuma dole saina fada,baka son a fada maka gaskiya kowa ai yana kuskure amma naka ya yayi yawa,yanzu ko wani kaji Yana cewa a bawa mudassir kujerar nan sai ka yadda ballantana ma Kai da kanka kake fada,kaji tsoron Allah,kasani Allah zea tuhumeka akan mutanen da suka kasance a karkashin ka.




Zuciyar shi banda tafasa ba abinda take,yanajin yaushe amina ta rainashi haka,kodan taga yana kawar da kai daga gareta? Tabbas yasan amina ba haka take ba ko idanuwa bata yadda ta hada da shi amma shine yanzu take taga masa murya.




Amina! Amina! Amina! Wlh in kika kara furta harafi daya anan gurin zan dauki mummunan mataki a kan ki,kujera ce dai ko ta saina bashi,ai bata gidan ku bace,kuma ki fita daga harkata dan naga alamar saka min ido kikeyi,ki fita daga ido na in rufe tohm,yana gama fadin haka yaja tsaki ya wuce yana kada babbar riga,kanshi ciwo yake masa sosai sakamakon rashin sanin abinda yakamata yayi,yasan komai ta fada gaskiya amma to ya zeayi dole ne ya sauka.





Tunda ya tafi ya barta take kuka sai da tayi har ta godewa Allah sannan ta tashi ta fice,tana shiga sashin ta ta sallami duka masuyi mata hidima duk Dan karsu gane tana cikin damuwa,dakin ta ta wuce tana kullawa da kwancewa tabbas da'a ce ya saurareta da ta fasa abinda tayi niyya,Amma halin yanzu tana jin muddin tana da rai mudassir bazea taba zama sarki ba.





Bawai Dan ta tsane shi ba,aah kawai dai be cancantaba bashi da qualities din da za'a bashi ragamar kula da al_umma.tana wannan tunanin rumana ta shigo,far'a ta kirkira ta sakama fuskar ta duk dan kar ta gane tana cikin damuwa,hira suke cike da burgewa,tana bata labarin Egypt wani tayi dariya wani kuma ta girgiza kai,kaso 30 daga cikin damuwarta taji ya ragu,





Suna haka har akayi sallahr isha,bayan sunyi sallar ne,rumana take cewa,
"Ammi wai Ina Farida ne tunda muka dawo ban gantaba"
"Uhm sai ynx kika tuna da ita,tana gidan adda na aiketa sai gobe zata dawo"
"Eyya ammi dama kin bari n dawo sai muje tare,nima gobe zani wallahi",
"To Allah ya kaimu goben lfy"
Ameen summer ameen.


Sai bayan sallar asar sannan ya tafi gurin Fulani maimunatu,yana zuwa tace
"Dama yanzu nake shirin kara aikawa a kiraka"
"Gani nazo ai" ya fada dai dai lokacin da yake zama.
"Son ba ruwanka da bayi na fada maka sarki kake shirin zama ka dauke idon ka daga kansu duk abinda zakayi kabari kayi a wajen masarauta kuma ba tare an San asalinka ba"
"Toh"kawai yace mata.
"Sati biyu masu zuwa za'je nema maka aure n Rania"
"Mum ni bana sonta she's not my type"
Haka tayita lallashin sa har saida ya amince da auren,ammafa a cikin ransa ya sha alwashin indai har akayi auren sai ta nemi saki da kanta.



Suna gama magana ya fita,itama tashi tayi ta wuce gurin me martaba don su tattauna akan batun auren,a dai2 lokacin da ta kara sa kunnuwanta suka jiyo mata maganga nun Fulani ameenatu,idanun ta har rufe wa sukeyi saboda tsarba bakin ciki,(niko nace tunma ba'a hana nadin b kenan=??).



Tun bayan barin warta gurin ba abinda take banda tunani kan ya zatayi da fulani ameetanu, tabbas barin fulani babbar nakasa zea zanyo mata gashi koda na kan dutse yayi mata aiki akanta baya jima yake lalacewa,wannan karon da kissa zata ci galaba akan ta.




Dole ne ta koya mata hankali ta yadda ba zata kara shiga sabgartaba,"kodan taga ita bata da da namiji, shiyasa take min ciki"zuciyarta ta fada mata haka,haka dai tai ta kullawa tana kwancewa daga karshe ta shirya ziyartar na kan dutse gobe da asubah.



****************



Abangaren maheer kuwa abubuwa sun fara zafi domin a rana daya beafo yay cikin dubu 50 ahankali kuma yanata kara raguwa,da farko komai normal Yana ciniki sosai,dan alhaji Abdulbasee har yana cewa baze taba rabuwa da shi.



A yanzun ma bawai yayi magana bane aah kawai dai shi ne ya fara damuwa duk da yasan kasuwa wataran a samu wataran Kuma akasin haka.



Yayin da kwana ki suke ta tafiya komai kuma na harkar shagon su Yana kara zafi don min yanzu abin yayi kamari sosai danta kai har ya fita ya dawo beafo yayi cinikin dubu 20 b.kuma kullum yana waya dasu ummi amma bea taba fada mata ba.




Alhaji Abdulbasee fara tunanin kodai maheer yana debar masu kudi ne,amma kuma yayi binki cike yaga babu wani abu me kama da haka,sai kuma ya koma tunanin kodai abokan kasuwan cin sane sukayi masa haka Dan sunga yana samu.





A halin yanzu sosai maheer yake damuwa da lamarin domin abin yafi karfin a kira shi da yanayin kasuwa,yau tunda suka dawo daga masallaci shida umar yake tunani,duban shi umar yay yace "abokina wai me yake damunka ne naga kwana biyu duk ka canja?"
Kamar ya fasa masa damuwar sai kuma kawai yace masa gajiyar kasuwace kawai.




A daddafe ya karasa cikon wata daya alhaji Abdulbasee ya sallame shi bayan ya bashi dubu 25, tabbas ranar ya yayi bakin ciki saidai yasan komai Allah ne meyi, Koda umar ya tambaye shi dalilin rabuwar su haka kawai yace masa alhajin ya samu Dan yayar sane shiyasaa.



washe gari bayan ya tashi yaje gurin masu p.o.s sukayiwa aymaan transfer din 10k yace su siyi abinda basu dashi sauran kuma ya hada su da kudin daya zo dasu wanda kadan ya raba a ciki su.




Bayan ya dawo ya bazama kasuwa nema wani aikin domin zama haka ba nashi bane, tunda ya fita bea dawo ba sai bayan magrib kuma bea samu wani aikin,gaba daya a gajiye ya dawo,dan yau ko hirar da suka saba danyi da umar basuyi ba.




Ya kai sati daya Yana neman wani aikin amma bea samu ba,da yaga haka kawai sai ya fara dako a cikin kasuwa,kuma bayan shi duk wani aikin karfi yanayi muddin za'a biyashi.



Wata rana ya dauki kayan wani mutumi zuwa wani shago,bayan ya ajieyi kayan harya zuya me shagon ya kirashi yace
"Kana da wani aikin da kakeyi me bayan wannan"?
Cike da nutsuwa yace"aah bani dashi, amma dai Ina nema".
"Zaka iya yin yaron shago"?
"Eh insha Allah zan iya"
"Okay kaje gobe ka dawo sai ka fara aikin".
"Nago sosai maheer ya fada yanaficewa daga shagon.



**************




Duniya sabuwa ta samu a gidan su mubeena,Dan kuwa prof muttaka hidima kawai yake mata kamar besan za fin kudi ba,Kuma har yanzu bea taba nuna mata wani halayya mara kyau ba.




Mushin ma sun ajiye shi agefe Dan suna ganin prof ya fishi komai,kum shina baya damun kanshi Dan dama ba son tsakani da Allah yake mata ba,sune suka shi yasota,daya kara mata maganar turo iyayen shi ma haka tace ya bari ba yanzu ba.




Zaune suke a tsakar gidan su cin abinci me rai da lfy,sunayi suna lissafin kudin da prof ya kashe mata tun daga farkon haduwar su,abin kunyar ma harda malam musa din (baban mubeena) da Kuma kannen ta.





"Gaskiya profesa dinnan yana da sakin hannu sosai kodai dashi za'ayi",
"Uhm mama sai yanda ta kama dai"
"Gaskiya aunty mubeena karki rabu da ya muhsin yana da kirki sosai kuma gashi kyakkyawa"fadin kara mar kanwarta da alama dai duk ta fisu hankali.
"Kedalla yiwa mutane shir,dama me kika sani a rayuwar,yanzu ba kyau ake nema ba inda mutum zea huta" mama ce ta fadi haka cike da masifa kamar tana magana da wata cikakkiyar budurwa.





Suna nan zaune har lokacin sallah la'asar yayi amma ba wanda ya tashi a cikin su,warya mubeena ce tayi ringing wadda prof ya siya mata kirar iphone Xs_max,da sauri ta amsa tana shigewa daki.



"Hello baby na"
"Uhm ykk"
"Ba lafiya ba"
"Meyasa meka "kewanki nake gaskiya yanzu zan taho na ganki kishirya yanzu kinji"
"Tohm sai kazo"ta fadi haka cike da farin Dan ko ba komai in yazo zea bata kudi,Dan ita bata ki kullum ma yazo ba.




Bayan kamar awa daya ya kara kiranta yace mata ya karaso,mayafi kawai ta dauka Dan dama ta riga ta gama shiryawa,sanye take da atamfa dinkin pitted gown,kayan ya kayan ya kamata sosai.




Tana fitowa tace wa mama prof yana jiran ta a waje fatan dawowa lfy tayi mata,tana fitowa ta ganshi a cikin mota,tana ganin motar taji zuciyar ta kara melting akan shi,tana son mota musamman irin masu tsada dinnan.




Cikn motar suka shiga suka fara hira,
"Meye matsayin karatun ki" ya zefo mata tambayar
Saida tai fari da idon ta Sannan tace masa "nagama secondary school amma ban Dora ba"
"Okay idan kika samu dama zaki dora kenan"
"Ehmn"
"Tohm shikkenan nan ki fara shiri nan da kwana ki goma zaki fara school ya fada yana miko mata wasu takaddu, a makarantar da nake lecturing,na gama miki komai kawai tafiya ce tarage"
"Saboda tsabar farin ciki bata san lokacin da ta ruko hannun shiba, "boo dan Allah da gaske ko wasa"
"Na taba miki irin wannan wasan"
"Da saurin tace aah"
"Wani sabon farin ciki ne ya kara kamata yanzu itace zata cigaba da karatu,abinda ta dade da fidda rai, dama masu iya magana kance rabon ajali".




Haka dai sukayi ta exchanging love words,kamar karsu rabu ji take dama su dauwa ma haka tabbas ta gama mata komai, yanzu bata Jin akwai abinda zea tambaya bata bashiwba ko menene kuwa.



Shi kuwa prof muttaka yayi hakanne kawai Dan ya samu ya cimma manufarsa a kanta shiyasa ya shirya komar da ita kusa dashi yadda bata gata sai shi,yaji dadin yadda take masa komai zata iya yi dan shi,haka dai sukayi sallama ya tafi akan jibi zeazo ya kaita shopping na makaranta.





Tana shiga ta fara bawa mama labarin prof ya samo mata mkrnt,duk yadda sukayi ta kwashe ta bata labari, Sannan ta bata kudi har rafa biyu shima ya bata ne don tayi shirye shirye,duk wannan abinda ke faruwa basu kawo da wata manufa yake yi ba, idon su yariga ya gama rufewa.





Malam musa ma da aka fada masa,haka ce Allah ya kiyaye,tunda bashi zeyi dawainiyar makarantar ba shi ba abinda ya dame shi.
"To yanzu inkin tafi ya zamuyi da abinci kinsan dai niba wata kwakkawrar sana'a ce dani ba",ai ko dai hakane mama ta fada tana zare idanuwa.
"Karku damu kafin na tafi zan siya na ajiye,Kuma zan siya muku waya,duk abinda babu sai ku kirani",
"To koke fa yanzu naji magana" fadin m_musa".



***************



A bangaren su ummi ma dai komai lafiya kalau,Dan kudin da maheer ya tura musu ta samu taja jari ma siyar da kayan yara kuma alhamdulillah san'ar ta karbe ta dam tana samu sosai.




Sai dai kullum tana cike da fargaba Dan har zuwa yanzu tana yawan Jin faduwar gaba,wadda bata san dalilin taba,kullum bata da kwanciyar hankali indai twins suka fita(imaan da aymaan) har sai sun dawo, ga wasu Kuma mugayen mafarkai da take, shiyasa har rama tayi,Amma dai bata taba gazawa dayi musu addu'a ba.




Zaune suke ita da imaan suna jiran aymaan ya dawo ya kira musu maheer Dan kwana biyu ba sufiya yin waya sosai,wani lokacin ma saidai insu su kirashi kamar dai yanzu.



Sallamar sace ya saka gaba daya suka daga kai suna kallon sa,a daya bangaren ummi ya zauna ya fara loda katin a cikin wayar,bayan ya gama ya fara kiran lambar maheer amma bata shiga,yayi masa yakai kira goma amma bata shiga.



Ganin duk sun shiga damuwa yasak ummi danne tata damuwar ta fara kwantar musu da hankali, har saida taga sun saki ransu sannan suka dauko abinci suka fara ci,suna cikin cin abinci wayar tayi kara ganin lambar maheer dinci yasa ya daga smda sauri amma mai mamakon muryar maheer sai yaji wani yana cewa,
"kaine kanin me wannan wayar"?
Dama.......



"Me zakuce game da iyaye masu halin irin halin iyayen mubeena"



"Da Kuma 'yan mata masu hali irin nata"

From
Magic guill pen
'?



09121810091
Whatsapp only

MOH MAHEER


https://chat.whatsapp.com/EcY9vu9MReuI5KFHeIk57C



Mikiya writers association
'?




Typing
'?
Page 9&10




A can bangaren maheer kuwa lolacin da suke ta kiranshi ya yarda wayar ne a shagon nan da aka dauke shi aiki Kuma me shagon bea lura ba harsai daya tafi,shine ya kira number aymaan dayaga yayi saving da my bro,Kuma network ya hanasu magana.




Koda ya bar shagon ba shagon kwannan su ya wuce ba,cikin kasuwa kara shiga don yin wani aikin ya Dan samu kudi kuma alhamdulillah ya samu fiye da zato ma.




Bea tashi lura da ba wayar b harsai da ya koma yayi wanka,ya zauna zea kira su ummi Amma kuma bea ganta ba,ya dan dudduba Amma bea ganta ba,
"Me kake nema ne"? Fadin umar wanda yake zaune yana ciin abinci.
"Wayata ce ban gani ba,da alama ma ba da ita na dawo ba"
"Gaskiya dai Amma ga wayata kira takan kaji".



Karbar wayar yayi ya kira number sa kuma cikin sa'a tashiga,tana ta ringing kamar ba za,a daga ba sai kuma aka daga.



Daga bangaren aka yi sallama,
"Wslm, Dan Allah malam wayata ce wannan na yarda itaene acikin kasuwa"
"Ohh maheer kaine,nine wanda na dauke ka aiki dazu,sai bayan ka tafi na lura da wayar taka",saida suka kara gaisawa cike da mutunta juna,sannan yace,
"Ko zaka zo ka karba yanzu?"
"Aah ba komai gobe in Allah ya kaimu na karba",daga haka sukayi sallama.




Washe gari.

Kamar yadda suka saba tun da suka tashi da asbah basu koma bacci ba suka shiga kimtsa dakin,karfe 7 dai2 suka fice kowa ya tafi gurin nashi aikin.



Lokacin daya karasa ya tarar har an dade da bude shagon dan har customers sun fara zuwa,an Dan nuna masa abubuwa wanda bea sani sakamakon wannan shagon kayan sabulai da man shafawa suke siyar dawa.



Sai gurin 12 sannan alhaji Ibrahim yazo,bayan sun gaisa da duk yaran shagon nashi,sannan ya kira maheer ya fada masa aikin da zea dinga yi na hada list din duk wani abu daya shigo ko kuma ya fita daga shagon (a turance sai nice book keeping).




Sun Dan jima suna Yana masa bayani,sai bayan sun gama ne kuma ya bashi wayar sa,dama kamar jira yake Yana bashi ya kira layin aymaan.




Suna zaune jugum jugum tun jiya basu kara walwalaba suka ji waya na ringing, da sauri imaan datafi kusa da wayar ta daga,
"Assalmualaikum aymaan"
"Wslm yaya imaan ce,Ina kashiga tun jiya bama samun ka?",
"Wayar ce ta fadi"
Aymaan ne ya kwace wayar shima ya fara masa tambayo irin na imaan.



Sai da duk suka gama sannan suka kaiwa ummi wayar,dan tunda taji imaan ta ambaci maheer hankalinta ya kwanta.



"Assalmualaikum ummi Ina wuni"
"Wslm maheer lafiya kalau, ya aiki"
"Alhamdulillah"
"Ina ka ajiye wayar ka tun jiya ba'a samu"
Nan dai ya bata labarin abinda ya faru,sun dade suna magana,Yana tambayar ta komai lafiya tace lafiya kalau,
"Maheer yaushe zaka dawo?"
"Ummi nan da wata biyu insha Allah"
"To Allah ya kaimu" daga haka sukayi sallama.




"Assalamualaikum"amsa mata sallamar ummi tayi, wai inji maman mu tace wai kina saida tamfa? Kice mata eh za'a kawo zuwa jibi, tohm yarinyar tace kawai ta tafi,"gaskiya ummi kisa ya aymaan dai yaje ya karo miki kayan a idan yaya yake kinga ko kwana daya sai yayi ya dawo ko" fadin imaan dake zaune a kan kujera,"eh hakan ma yayi kinga ana yawan tamabyar atamfofin", bari in ya dawo sai muyi magana shima yayan naku zan fada masa naji me zeace.




Yau dai maheer yasha aiki sosai saboda rashin sabo,gashi kuma aikin nasa me zirga_zirga ne sosai,kuma suna ciniki

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login