Showing 3001 words to 6000 words out of 15413 words

Chapter 2 - MOH MAHEER

unknown   

23 Nov 2024

2490

sannanu yace "park your things and leave zanyi waya da mum" and I'm leaving here end of this month are you clear?



Gyada Kai kawai tayi,tana saka kayanta tana fadin nima zan tafi immediately bayan kun tafi saboda maganar auren mu, sai anjima=?K?

Sai a lokacin ya samu nutsuwar daukar wayan.


"Hello Mumm Ina wani uziri ne shiyasa banyi picking b"
"Yarima har yanzu baka dea bin mata bako!hmm kana shirin zama sarki Amma har yanzu kaki kayi hankali,"
"Mum kafin na dawo zan deana I promise"
"Okay yaushe zaku dawo?"
"On 28 of this month"
"Kana dawowa fa za'je nemamaka auren "Rania don sarki dole sai yana da mata"
"Mum zanyi aure amma Rania ba,batai kalan matan da nake so na auraba,'yar gidan mutunci nake so, because of my children '
"Wlh baka Isa ba sai ka aure ta"
"Inna dawo zamuyi magana"
"Okay take care bye love you"



Suna gama wayan ta nufi turakar meartaba duk da bata da shamaki da sahin nasa Amma akwai abinda take so shiyasa harta aika neman iso Kuma tana fatan bukatar tata ta samu karbuwa.




Duk inda ta ratsa bayi da dogarai sai sun duka sun gaisheta wanda tsarin tane haka kuma in sun gaidatan bata kallon su bare su saka ran zata amsa,A haka har ta kara sa sashin nasa.




Kyakkyawan bafulatanin dattijo Dan kimanin shekaru 56 nagani adilin sarki kenan Abdullahi mahammad, Zaune yake akan kuje irin ta zaman mutun daya,kallo daya zakayi masa ka hango tsantsar kamala da Kuma cikar haiba da yake da ita wanda normally dama duk wani sarki yana d a wadannan abubuwan.



A kallo daya zakayi masa ka hango damuwa,da Kuma rashin kwanciyar hankali a tartare dashi,Yana ganinta ya mike tsaye da sauri ya karaso gurinta hade da kama hannuwanta "Fulani" na'am bari na kawao mk ruwa kasha inaso muyi magana,"toh yafada Yana koma inda ya taso ya zauna.





kofin ruwan dale hannun ta ta Mika masa,bayan ya sha ta dago tana kallon sa da manufofi masu yawa Amma bata bari Hakan ya bayyana ba.



A hankali ta muskuta sannan ta kamo hannun shi ta rike fin ta fara fadin,"so nake kayi murabus ka bawa "MUDASSIR" yanzu girma yazo maka zaka na Shan wahala sosai,Amma idan ka sauka zaka huta in yaso sai ka zamto masa jagora akan mulkin nashi Kuma gasu galadima duk zasu iya Dora shi a hanya,tana kara she maganar tana fatan ya amsa karyayi mata musu.




Sai dai abinda bata sani ba shine yanzu ki huta tace ya fada, bazea iya yi mata musu ba,balle sauka a mulki, dama kwana biyun nan jiyake kamar akan kaya ya zauna idai ya zauna akan karagar mulkin Kuma duk aikin Fulani maimunatu ne.




Yana ta kokarin Hana kansa yadda da bukatar ta Amma Yana jin idan beayi abinda take so ba zea iya mutuwa,a hankali yace "shikkenan Allah yasa hakanne yafi alkhairi" ameen tace cike da madaukakin farinciki.




Yanzu Koda ace asirina ta ya tuno danna zea tsaya min yaga ba'a hukunta ni ba, she cannot imagine her self as the king mother,"yaushe ne yaran zasu dawo?" ta tsinci muryar sa Yana tambayar ta, " Karshen wayan nan on 28"



Ficewa yayi ya nufi fada,gabadaya tashi sukayi alamun girmamawa a shugabannasu,bayan ya zauna da kamar minti goma ya motsa bakin shi,da karfi dogaran da suke yimasa fifita daya ya miki yace,



Mai martaba yace a buga kambu,Kuma a fara shirin tarbar sabon sarki nan da wata biyu! Ko cikakkun mintuna biyu ba'ayi ba wani kala busan sarewa ya cika masarautar gabadaya wanda yake alamta musu cewa sarki zeayi murabus amma kuma waye wanda za'a dora? Wanbai,waziri da kuma galadima cike da tsantsar mamaki suke kallon shi,Amma basu da ikon cewa komai.




Acan bangaren uwar gidan me martaba kuwa tajin wannan busar tasan bawan da za'a bawa mulkin sai MUDASSIR Kuma taci alwashin bazata taba bari ayi wannan nadin ba,domin ba irinsa masarauta take bukata ba,me mulkar masarautar yana zuwa Kuma lokacine zea bayyana hakan......


***************



Bayan motar ta tsaya a tasha kowa ya fito ya kama gaban sa,a hankali yake bin tashar da suke da kallo, komai sabo ya zamto masa saboda shekarun daya dauka bea zoba,bayan ya gama kallon ko Ina yasamu ruwa yayi alwala ya samu guri yay sallah,wasu matasa ya nufa,




"Assalamualaikum" tare suka Amma sa masa,"Dan Allah inane babbar kasu ta siye da siyar anan garin"daya daga cikin su ne yace masa "sabon gari ba abinda basa siyarwa insha zaka samu abinsa kake so", godiya yayi musu sannan ya tari adaidai ya shiga ya wuce kasuwar sabon gari.





Yana sauka ya samu wani saurayi zasuyi sa'annin dashi,"Dan Allah a ina zan samu shagon haya da zan kama,ni bako ne"okay bari muyi sallah sai mu tafi na nuna maka inda nake kwana saika kama ko kuma murinka kwana tare a daki na tunda yana da girma.




Tohm shikkenan nagode sosai muje muyi sallahr,bayan sun idar suka nufi jerin shagunan da matafiya suke kamawa,dakin nashi tsaf dashi kamar ba dakin namiji ba, " gashi anan nake kwana Amma da sassafe nake fita aiki" toh shikkenan b damuwu,bayan ya ajiye kayan sa a gefen dakin yace,



"Nidai sunana Muhammad amma zaka iya kirana da maheer daga madobi nazo kuma neman arziki ne ya kawo ni" naji dadin haduwa dakai ni sunana umar daga garin Katsina,nima Kuma neman arziki nazo Allah ya bamu me amfani cewar mahir a lokacin da suka fara tafiya, daza kayadda na raka gurin wani Alaji naji yana neman yaron shago.





Farin ciki sosai ya kama maheer har kana ita gane hakan a fuskar sa,"to shikkenan ba damuwa Allah ya kaimu gobe sai muje........



Washe gari


Bayan sun dawo daga masallaci dakin suka kimtsa dukda beyi wani datti ba,karfe bawai dot suka fita zuwa shagon alhaji, saidai alhajin bashi da mutun ci ko kadan domin bayerabe na Amma dai alhamdulillah ya dauke shi saidai muyi masa fatan nasara.



Ranar dai aka fara nuna masa farashi abubuwa,a haka hae lokacin tashi yayi.saida umar yazo Sanna suka tafi, suna cikin tafiyan maheer "yace dan Allah inaso na siya waya"


"Ok bari muje shagon sai ka siya",suna tafiya suna hira har suka karaso shagon,yasiya wayar kirar techno second hand me saukin kudin,yayi registern layin,ya biyasu suka fito.Suna kara sowa Koo hutawa beayi ba ya kira num aymaan.....



From
Magic guill pen
'?



09121810091

~MOH MAHEER.


https://chat.whatsapp.com/EcY9vu9MReuI5KFHeIk57C



typing
'?
Page 5&,6


Aymaan wanda dawowar sa gida kenan yaji wayar sa na ringing,da sauri ya daga,"Assalamualaikum",
"wslm ya maheer kaine"
"Eh nine ya kuke Ina ummi "
"Gata nan dama yanzu na dawo daga gurin aiki" ya fada yana mika ma ummi wayar dan tunda taji ya ambaci maheer ta fito daga daki,
"Maheer ya kake ba wata matsala dai ko?"
"Eh komai lfy kalau "saida ya bata labarin duk abinda ya faru harma ya bawa umar wayar suka gaisa sannan ya fada mata ya samu ai a shagon kayan masarufi,nasiha takara masa akan rikon amana da gaskiya,sun dau dogon lokaci suna magana kafin sukayi sallama.




Hamdala ummi tayi a fili,domin tun tafiyar shi take Jin gaban ta Yana dan faduwa sa'i da lokaci,Amma dai tana fatan komenene zea faru ya zamto alkhairi ne a garesu,Kuma bazata taba gajiya dayi wa dan ta addu'a b a duk inda yake domin addu'ar uwa karbabbeyace a gurin Allah (S.W.T).




To a bangaren maheer dinma haka Yana jin kamar wani abu Yana tunkaro shi amma yana fatan ko menene ya zamto alkhairi ne.



Washegari ya fara zuwa shagon alhaji Abdulbasee inda yace zea dinga biyanshi naira 20 a wata biyu beayi musu ba ya amince duk da dai kudin sunyi kadan amma kuma shi bayawan yake dubawa ba albarka kawai yake nema.


Aranar ya fara masa yaron shago Kuma alhamdulillah komai yana tafiya dai2 bisa amincewar ubangiji,Kuma kullum Yana kiran ummi a waya suna gaisawa da safe da maraice.itama tun tana jin damuwa harta fawwala Allah komai.



**************




A bangaren mubeena kuwa komai yana tafiyar musu yadda suke so dan ta fadawa muhsin babanta yace ta turo,beayi wani musu yace mata zea fadamusu.rana da mama taji wannani maganar kamar ance an bata aljanna tana ganin lokacin hutun su yazo,




Mubeena ce tsaye a gefen titi sanye ta da riga da skirt na atamafa kayan amshe ta sosai domin sun fidda tsarin halittar ta,gefen ta wata kawatace me suna jamila kayan iri daya ne ajikin su da alama saga biki suke



Wata farar motace ta faka a gabansu a hankali aka shiga sauke glass din motar,wani tsoho ne zaune a kurar driver da ganin shi kaga cikakken dan bariki, lekowa yayi yace,



"Yan mata kushigo na sauke keku ko ba tafiya zakuyi ba"
"Tafiya zamuyi amma ka tafi mun gode"
"Aah baza'a yi haka kushigo mutafi "
"Okay mun gode" suka fada kusan a tare, gaban motar ya bude sannan ya kalli mubeena yace shigo ranki ya dade,shiga tayi ta zauna tana jin kanta ya fasu dan basea an gaya mata b wannan attajirin ya fola mata




"Gimbiya Ina zan kaiku" cike da yanga da wani langwasa murya ta fada masa inda zasu,suna tafiya suna hira da jamila, mubeena kuwa tayi shiru kamar bata cikin motar,wai tayi hakanne duk dan karta bada kanta.



Suna karaso wa jamila tayi masa godiya ta shige gidan su,sannan ya tada motar suna tafiya tana yi masa kwatance har suka karaso kofar gidan su,bayan yayi parking yace,"gimbiya nifa yau nayi tsintuwa Dan gaskiya Ina ganin ki naji kin burgei inaso nayi rayuwa dake zan nuna miki soyayya irin wadda baki taba gani ba ko Jin labarinta"




Da farko dai sunana prof muttaka ni lectura ne a university din jigawa nazo hutu ne garin kano Ina da mata da yara2,zan iya sanin sunan ki,a hankali tace mubeena,"sunan ya dace dake" uhm kawai tace masa.



Haka dai yayi ta yi mata dadin baki har ta Dan sake sukayi yi hira sunkai 30 minutes a gurin kafin sukayi sallama,sannan ya amshi number dinta Kuma yace ta shirya gobe zeazo suje cin abunci a cikin gari,dazata fita rafa din 1k ya bata da kuma 500 yace ta siya kayan kwalliya,da sauri ta amshe kudin ko godiya batayi masa ba tafice.




Bayan ta yabi da kallo yadda take karkada ass kamar da gangan takeyi, tabbas wannan bazan sha wahalar shawo kanta ba, Dan shi ya samu baby 'yar da gwas da ita ya Dan jima a gurin Yana tunanin mubeena kafin ya tada motar ya tafi.





Tun daga zaure take fadin mama mama,da sauri mama dake cikin dan kitchen dinsu ta fito tana cewa lfy,batayi magana ba illa kudin data daga tana karkada mata, da sauri mama tace,





"Lallai na iya haihuwa, a ina kika samo wannan kudin haka ko muhsin dinne ya baki?"
"Aah mama" labarin prof muttaka ta fara bata Kuma ta fada mata har ma yace ta shirya suje cin abinci gobe,guda mama tayi cike da tsantsar farin ciki tana ganin kamar tafi kowa sa'a...



***************



A bangaren bayin masarauta kuwa tunda sukaji labarin dawowar prince MUDASSIR iyaye suke cike da fargaba domin kowa yasan halin shi na bata 'yan mata,wanda saboda wannan halin nashi ne yasaka a tura shi karatu Egypt shida kanwar me suna jalila sa da kuma 'yar fulani animatu
Ummu_rumana.


Yayin da wasu suke cike da tsananin farin cikin dawowar tasa,saboda su samu shiga a gurin sa.Musamman 'yan mata marasa kamau kai.




A can bangaren Fulani maimunatu kuwa tana baro sashin me martaba,ta fara tunani kar mukarravan fada su canja masa ra'ayi,ko kuma suki aminta da wanda za'a dora duba da halaiyar sa.



Wannan tunanin tayi yasaka ta dauko wayar ta a kira boka na kan duste kan ya rufe mata bakin kowa na fada,bayan ta gama wayar kanwarta ta kira (maman Rania) sun dade suna tsara yadda bikin nadin sarautar zea kasance.




A cikin masarauta kuwa an cigaba da shirye shiryen dawowa yarima mudassir saidai komai suke yi jikin su a sanyaye yake saboda taraddadi da tsoron dawowar tasa,




A bangaren Fulani ameetanu ma dai shirye take da dakarta da wannan nadin da za'ayi wanda bea yi dai_dai da tsarin masu mulkar masarautar ba,da shirinta wanda ita kadai ta barwa kanta sani sai kuma amintaccan sarki.




Bayan sati daya


Yau laraba wanda Kuma yayi dai2 da saura kwana daya dawowar su unmu_rumana,sosai ake gyare gyare a cikin masarautar kamar lokacin nadin ne yazo,duk wanda yaga wannan shirin to zea tabbabr da cewa 'ya'yan gata ne zasu dawo.



Fulani maimunatu kuwa sai shirye shirye take na tarbar 'ya'yan ta, a bangare daya Kuma tana cike da tsananin farin ciki na danta zea zama sarki,a halin yanzu ji take ba wanda bazata kawar ba muddin yayi wa danta shamaki daga hawa kujerar,




Rana bata karya


Karfe 12 na rana jirgin su yay landing,bayan shudewar kusan mintuna goma sannan kofar jirgin ta bude perssengers suka fara fito wa.




ummu_rumana itace a gaba,sanye take da red Dubai abaya tayi mata kyau sosai she very innocent,kyakkyawa ce ajin karshe domin hasken ta har daukan ido yake.komai nata very perpect,tana da tsaho Amma ba can ba,tana da kirar jiki masha Allah komai yaji.



sai jalila itama fara sai dai tana karawa dana bature,sanye take da riga da wando sai kuma ta dora wata rigar budaddiya, tana da kiba sosai, saidai kana gani kasan kayan bature ne suka saka ta kibar (supplement).



Sai Kuma mudassir a karshe tabbas shi din kyakkyawa ne domin ya hada komai saidai kyan Dan miciji gareshi,sanye yake cikin kufta da wanda irin asalin kayan sarauta kayan sun amshe sosai masha Allah,a hankali yake bin ko ina da kallo ya dade rabon shi da kasar Dan tunda ya tafi bea dawo ba shekara 5 kenan.



Tun fitowar su airport din ya ciki da busar sarewa,suna kara sowa aka bude musu motocin biyu na tsakiya suka shiga,suka bar airport din.



Tarba ta musamman suka tarar dan harda me martaba aka fito tarbar su,tunda suka fito yake bin ummu_rumana da wani mayataccen kallo wanda take jin shi ha cikin kashin ta amma tayi burus dashi.



Duk abubuwan da akeyi hankalin shi baya gurin Yana kanta,
"My son tunanin me kakeyi haka"
Sosa sumar kansa yayi kafin yace"sorry dad"barka da wannan lokaci mun sameku lfy"?
"Lfy kalau, masha Allah ka kara girma sosai kamar b kai ba yanzu kuma sai aure ko"?
"Eh dad insha Allah,bari naje na huta kafin anjima.
Tohm b damuwa.


Dogarawa ne suka saka shi a tsakiya,tafiya yake cike da izza, fuskar nan tashi ya daure ta tamau,kamar ba bashi ne yaga gama magana da ladabi ba, wani hadadden part suka shiga wanda yake matsayin nashi,tun a bakin kofa dogarawan suka dakata domin a tsarin shi namiji baya shigar masa part sai dai bayi mata sune suke masa komai,hatta da hada ruwan wanka.




Palorn yabi da kallo komai tsaf yake kamar b wanda ya tafi ya bari ba dan komai na sashin an canza shi,Yana tafiya yana Dan kalle kalle harya ya karaso bedroom din shi, dakin yasha ado kamar na mata komai na cikin shi blue =ؙ? ne.



Jagwaba y??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a zauna akan gado,yana da feelings sosai akan rumana,Amma yasan ko giyar wake yasha bezea iya kusantarta a zahiri ba,wani bangare yace masa "to ka aure ta mana" no I can't marry her she's not my type.



Yana sane da ita ko magana bata yi masa sai da dalili me karfi,to ta wace hanya zeabi ya cika muradin sa kanta?ya bata lokaci me tsawo yana sakawa da kwance wa, knocking din da akayi ne yasaka shi dawowa daga dunyar tunanin daya fada.




Saida akayi sau uku kafin ya bada izinin shigowa,wata baiwa ce tashigo tana kwarkwa irin ta 'yan bariki dinnan,dogawa yayi Yana kallon ta da alamar tambaya fuskar a hade,"dama fulani ce tace in zo in duba idan kashirya tana neman ka" sai da yadau kusan mintun biyar sannan yace "ina zuwa yanzu".



Harta zuwa zata tafi taji yace"kee kinji nace ki tafi ne" da sauri tace
"Aah ranka ya dade"
"Jeki hada min ruwan wanka"
Ko karasa maganar beaya ta wuce zuciyanta cike da farin ciki, bayan ta gama tazo ta fada masa,shiru yadanyi yana kallon ta takasan ido,kamar baya son magana yace"anjima ki dawo bayan isah zan saki aiki.
"Toh tace masa,saida yace ta tafi sannan ta zuya ta wuce.




A bangaren mai martaba kuwa ganin mudassir dayayi yasaka yaji hankalin shi ya kwanta sosai da bashi mulkin dan aganin shi yayi hankali,ba kamar daba,lokaci yayi da zea huta tsohon shekarun dayayi dama akwai dalilin zaman nashi Amma abin mamaki ya manta dalilin yanzu dai burin shi kawai ya sauka ya bawa wani koma waye.




*************


"Rumana ki tashi ki shiga ki watsa ruwa kizo kici abinci",
"Ammi kin gaji dani ko?"
"Aah ya za'ayi na gaji dake naga tunda muka shigo kike nanike dani kamar zan gudu"
"Tohm Ammi yanzu zan tashi fa"
Dakyar rumana ta tashi ta shige cikin dakin ta masha Allah nace domin ganin haduwar dakin,kayan dakin light Pink ne da blue black,dakin ya tsaru sosai.




Kan madaidai cin gadon ta fada tana zuyi,wani farin ciki take ciki wanda ta jima bataji irin shi ba,yau gata a gida a gidan ma kuma kusa da mahaifiyarta, alhamdulillah kawai take fada,da sauri kuma ta mike ta hau cire kayan jikin ta shiga bathroom,bata wani dade sosai ba ta fito.



Gaban mudubin ta wanda yake cike da kayan shafa na gyara fata ta matsa ta fara shafa mayukan kamar bata so,Sharp Sharp ta shirya cikin riga d wando marasa nauyi sanna tayi sallahn azahaar sannan ta fito palor,anan ta samu Ammi a zaune

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login