Showing 15001 words to 17571 words out of 17571 words
gashi ta kasa ture shi, kawai sai ta fashe mai da kuka.
Cewa take"D'an iska wallahi ka k'yale ni, d'an yaro da Kai baza ka iya Dani ba"
Cikin wani irin hali yace"Zan ko Baki mamaki"
Kafin tayi magana ya had'e bakin su.
Sosai sukayi ta kokawa, Wanda sai da k'yar ya samu nasara, inda ya nuna Mata shi cikaken namiji ne๐
A Daren Nan NIHLA tasha azaba tayi *DANA SANI*(coming soon) fad'a mai cewa shi ba namiji bane, ai ko yanzu ta tabattar shi d'in namijin gaske ne, duk kukan ta Bai saurare ta ba har sai da ya maida ta cikakiyar mace,yayi farin ciki sosai samun ta a cikakiyar Budurwa wacce ta kawo budurcin ta gidan mijin ta,Haka yayi tasa Mata Albarka ko kula shi batayi ba, da kanshi ya taya ta, ta tsaftace jikin ta sannan suka kwanta barci, gaskiya a wannan Daren yaji wani irin feeling Mai k'arfi akan NIHLA.
*Budurcin ki gidan mijin ki*
*Budurcin ki gidan mijin ki, y'ar uwa ki rik'e wannan abin da hannu biyu-biyu domin kuwa ba Abu ne na Wasa ba, Mata ku kula da kanku kussan irin samareen da suke zuwa gurin ku, idan har kunsan ba da aure suke son ku ba to ku rabu dasu, ba k'aunar ku suke ba, ki rik'e budurcin ki har ki Kai shi gidan mijin ki*
*Janih one love*๐
*UMMU BASHEER CE*
[26/02 12:28 pm] Sis Ummu Bashir: ๐น *BA MU DACE DA JUNA BA*๐น
๐น
{ *Short and interesting story* }
*NA*
*UMMU BASHEER*
ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐)_
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*PAGE 45~50*
*Akwai* wata Rana da NIHLA take kwance kan katifa, zuciyar ta sai tashi yake ta rasa what's happening with her, Kawai sai ganin wani k'aton k'adangare ya fad'o daga window'n d'akin, gashi murtukeke, bak'ikirin gwanin ban tsoro, wani irin ihu Mai k'arfi tayi a gigice, lokaci d'aya cikin ta ya murd'a tsabar tsoro ganin Yana k'arasowa kusa da ita. RAUDAH da ta jefo k'adangaren tana gefe sai dariya take Dan dama burin ta, taba NIHLA tsoro.
A dai-dai lokacin ne JAMAAL ya shigo gidan da gudu ya shige d'akin, tana ganin shi ta rungume shi duk jikin ta rawa yakeyi ta tsorata sosai, tambayar ta yake mene ne da k'yar ta nuna mai k'aton k'adangaren, Direct d'auka yayi ya jefar a waje, RAUDAH dake lab'e haushi duk ya cika ta.
Dawowa yayi ya rungume ta Yana rarrashin ta, a ranar ko Zama a d'akin ta k'i, tana parlour'n Umma, a kwanakin tana son tuwon Umma, Amma ranar tana ci sai amai tayi, ga zazabi da ya rufe ta lokaci d'aya, JAMAAL duk a rud'e yake gashi tak'i yarda suje hospital, Umma ko ta lura NIHLA ciki take da shi, sai tace JAMAAL ya barta ta huta, Kuma ta sanar mai NIHLA ciki take dashi, ba K'aramin farin ciki sosai yayi ba, Yana ta ma Allah godiya, dama akwai shi da son yara, NIHLA ko kunya ne ya kamata, Umma na fita d'akin yayi saurin rungumar ta.
"I'm very Happy, Zan Zama Baba"
Dariya tayi tace"Toh Baba k'yale ni please"๐
"Allah Ina mutuwar son baby'n Nan"
"Ni ma Ina son ku duka"๐
Suman zaune yayi Jin furucin ta, "Wow my wifey dagaske kikeyi kina k'aunar mu"๐
"I mean what I said, I loved the baby"๐
Rungume ta yayi very tight cikin farin ciki.
Ni ummu basheer Ina ganin luv lokaci d'aya๐.
Cikin sati d'aya sosai yake kula da ita da ririta ta ya shagwab'a ta sosai fa, Dan komai take so sai ya samo Mata, sunje hospital an tabattar musu da ciki 2 months take d'auke dashi, sunyi farin ciki ba k'adan ba.
RAUDAH da taji NIHLA nada ciki kamar zata mutu take ji, Nan ta yanke shawaran had'uwa da JAMAAL ta fad'a mai sirrin zuciyar ta.
"Ni gaskiya pounded yam nake son ci" NIHLA ta fad'a Haka cikin shagwab'a da k'ara kwanciya kan jikin JAMAAL.
"Duk abin da baby na ke so shi Zaki ci,oya Bari in je gurin Aunty Jameela in samo miki"
Kissing d'in forehead d'in ta yayi, ya Mata bye.
Fitowa yayi k'ofar gida kawai sai yaci karo da RAUDAH da zata shigo.
"Yauwa Yaya na dama Kai nazo nema"
"Ok ya akayi,Ina sauri ne Aunty'n ki na jira na"
Wani irin bak'in ciki taji,sai ta daure tace"dama ...Ina...son in ... fad'a ma.."
Katse ta yayi ta hanyar cewa"come-on ki fad'a min mene ne kin tsaya kina in Ina"
Daurewa kawai tayi tace"Yaya na jima da birne wani sirri a cikin zuciya na, nayi k'okarin ganin cire abin a raina Amma hakan yak'i yuwuwa, Na jima da kamuwa da ciwon so, Yaya ko kasan wa nake so?"
"A'a, wane ne?"
"Kai ne nake so"
A firgice ya kalle ta, "kin San me kike cewa?"
"Eh Kai ne nake so, Yaya Ina k'aunar ka, wallahi Zan iya mutuwa idan baka aure ni ba, Na jima Ina jinyar son ka, ka taimake ni ka so ni"
Gaba d'aya ya rasa Mai zaice Dan baiyi tunanin abin da zata fad'a kenan ba, gaskiya shi ya d'auke ta ne a matsayin K'anwar shi ba zai iya auren ta ba, kuma idan yace Yana son ta yayi k'arya.
"RAUDAH da farko dai Zan Baki hak'uri gaskiya na d'auke ki ne a matsayin K'anwa na, idan naje Zan aure ki to tabbas na Yaudare ki Dan ko k'adan bana k'aunar ki a zuciya na sai dai Ina Miki son y'ar uwa ta, kiyi hak'uri ki samu wani mijin kiyi aure, Kinga Ina son NIHLA Mata ta, bani da sha'awan k'ara aure, Mata d'aya ta ishe ni a rayuwa Dan Allah kiyi hak'uri Kuma zanyi Miki addu'a Allah ya Baki miji na gari"
Wani irin kuka ne ya taho Mata da k'yar ta iya dannewa, tace"ba komai Yaya, tunda har baka so na,to wallahi na hak'ura domin Ina son auren namijin da yake so na, nagode sosai" Nan ta shige gidan su, shi Kuma ya nufa gidan Aunty Jameela Yana mamakin RAUDAH, shi a gaskiya ma RAUDAH Bata cikin irin matan da yake so, Bata da shape Mai kyau gashi Bata son aiki, tana da k'azanta, gaskiya ba zai iya auren ta ba, bare yanzu NIHLA ita ce farin cikin shi.
Har ta fara barci taji dawowan shi, A hankali ya k'arasa gurin ta "baby I'm sorry har kin Fara barci Koh?"
"Uhm nidai please ka bani sakwaran Nan in ci har mafarkin shi nake"๐
"Hoo baby har dreaming kike,oya zo inyi feeding d'in ki"
A kan cinyar shi ta zauna ya dinga Bata har ta k'oshi Tasha ruwa sannan ya rufe ta da blanket sukayi barci.
Saura sati d'aya JAMAAL ya tafi Canada, sosai yake mak'ale Mata Dan baya son rabuwa da ita, Kullum cikin kula da ita yake,yayin da take Jin wani irin mugun son shi a zuciyar ta, har mamaki take yanda take k'aunar shi.
Tana kwance kan kujera dake parlour'n Umma taji wata murya Wanda har abada baza ta manta ba, Muryan Mom take ji.
Mom ce ta shigo gidan cikin yatsina fuska take k'are ma gidan kallo, Umma ganin Babbar mace yasa tayi tunanin ko Y'ar uwa'n NIHLA ne Dan sune masu kud'i, cewa tayi"Hajiya barka da zuwa ga guri ki zauna"
Tsaki mom tayi "ke yanzu nayi Miki kama da wacce zata zauna anan?, Ina y'a ta take?"
A wannan lokacin ne NIHLA taji muryan Mom da gudu ta fito.
Umma tace"wace ce y'ar ki baiwar Allah?"
NIHLA na ganin Mom ta rungume ta cikin wani irin tsananin farin ciki, hawaye Mom tayi tana cewa"My daughter I can't believe you're leaving here"
Cikin hawaye tace"I really missed you Mom"
Umma tace"NIHLA mahaifiyar ki ce?"
"Eh Umma itace,Mom ga mahaifiyar JAMAAL"
Umma tace"Ah maraba lale bissmillah shigo daga ciki"
Tab'e baki mom tayi tace"ban zo Dan in zauna ba nazo d'aukar y'a ta ce"
Gaba d'ayan su a rikice suka kalle ta, lokacin Kuma yayi dai-dai da shigowan JAMAAL gidan yaji wannan kalmar daya firgita shi.
Umma tace"A'a Hajiya ba za'ayi Haka ba"
A fusace Mom tace"Dole ne in d'auki y'a ta yau Dan wallahi baza tayi irin wannan rayuwar na talauci ba, y'a ta tafi k'arfin ku"
Da sauri NIHLA ta rik'e hannun ta taja ta zuwa d'akin ta.
JAMAAL ne ya k'araso gurin Umma "Umma na ki taimake ni kar ki Bari a raba ni da Mata ta, wallahi Ina k'aunar ta"
Cikin kwantar Mai da hankali tace"karka damu ba abin da zai faru sai alkhairi"
Daga inda suke suna jiyo maganar su Mom, inda NIHLA ke cewa"Mom ya akayi Kika san Nan?"
"Daughter dole in bincike inda kike, tabbas mahaifin ki baiyi Mana adalci ba da har ya raba mu, ya hana in zo inda kike, da k'yar na samu Aunty Shuwerh ta bani address d'in inda kike,Dan kullum cikin yin mata waya nake Ina rok'on ta har taji tausayi na, Dan Haka dama nace Zan shirya plan, yanzu Zan tafi dake Misra Dan har nayi Mana visa, kije ki zauna gurin Ummie na, har sai nasa ya Baki takardan sakin ki"
Gaba d'aya ta tsorata da Jin furucin Mom, Haka ma su JAMAAL.
"A'a Mom kiyi hak'uri bazan iya binki ba, Ina son yin ma Dad biyayya a karo na biyu"
"What do you mean NIHLA,nazo ne fa Dan tafiya dake"
"Kiyi hak'uri Ina son Zama, Ina son miji na"
A rud'e tace"are you out of your sense NIHLA,do you know what you're saying?, Ko kin manta ke wace ce?,kece fa NIHLA TAHIR , kyakyawa Mai ji da kanta, kud'i da dukiya kina dashi, kina da company inda kike aiki, driver ke kaiki duk inda zaki, Shin duk kin manta ko ke wace ce a lokacin but look at you now, duk kin rame kinyi duhu, kalla kayan jikin ki, kalla fuskar ki, NIHLA what's wrong with you, kefa Kika ce Baki son auren, what happened?"
Cikin hawaye tace"mom I knew all that, na tuna ko ni wace ce Earlier,but now everything has changed, Mom yanzu ba nice NIHLA da Kika sani ada ba, Ni yanzu Mai kud'i da talaka basu ne a gaba na ba, duk Allah ne yayi su, tabbas Ada nayi kuskure da nake nuna jiji da Kai da nuna Isa, Mom ni yanzu Ina k'aunar miji na bazan iya rabuwa da shi ba, kiyi hak'uri kawai ki tafi"
"Anya ba suyi Miki asiri ba kuwa, Anya kece y'a ta NIHLA da na sani kuwa?I don't think so, NIHLA ki dawo cikin sense d'in ki, kisan me kikeyi"
"Mom Ina cikin hayyaci na nasan me nakeyi, Ina son miji na bazan iya rayuwa Babu shi ba, Kuma Ina d'auke da ciki"
A firgice tace"Ciki? Kina nufin ciki kike da shi NIHLA, da wannan yaron d'an talakawa?"
Cikin kuka tace"Mom please I'm sorry but just go, bazan iya binki ba"
A fusace tace"Yau nasan matsayina a gunki, daga yau Ina son ki d'auka na mutu, Baki da iyaye a duniya kiyi rayuwar ki keda talakawan da Kika zab'a" tana fad'in haka tayi waje.
Da sauri NIHLA tabi bayan ta tana cewa"Mom please wait, karki ce Haka"
Mom ko kallon su Umma batayi ba ta fita waje inda driver ke jiran ta, NIHLA ce ta bita da sauri Nan JAMAAL yabi Bayan ta Yana Kiran ta.
Shiga mota tayi yayin da NIHLA ke knocking d'in glass d'in window tana Kiran sunan Mom, ita Koh kawar da Kai tayi yayin da driver ya ja motar a guje, da gudu JAMAAL yayi saurin rungumar NIHLA saura k'adan motar ta ja da ita.
Kuka ta fashe mai da shi, Shiga da ita cikin gida yayi Yana rarrashin ta.
Haka Kaka wacce dawowan ta d'aga unguwa kenan, da Umma sai Bata hak'uri suke, Kuma yanzu JAMAAL ya tabatta da NIHLA tana k'aunar shi.
Har dare tana kuka shi Kuma Yana aikin rarrashin ta har ta hak'ura.
Cikin sati d'ayan Nan suna wani irin soyayya ne Mai zafin gaske domin wani irin shak'uwa sukayi da junan su. A yau ne JAMAAL zai tafi, NIHLA sai kuka take, Har airport driver ya Kai JAMAAL inda su NIHLA,Umma,Kaka da Abba suka raka shi.
Jirgin su ya tashi zuwa k'asar Canadaโ
Yayin da ya tafi cike da k'aunar matar shi NIHLA,Haka ita ma suka juya gida cike da k'aunar mijin ta da kewar shi.
******************************
NIHLA cikin ta ya tsufa, haihuwa yau ko gobe, sosai Umma ke kula da ita, Haka Kaka ma, kullum cikin waya suke da JAMAAL, Yana Jin lafiyan baby'n shi. Ta b'angaren JAMAAL ma ya maida hankali sosai kan karatu ya gama ya dawo Dan ganin matar shi, y'an Mata dayawa na son shi amma basa samun ko kallon kirki, Dan Burin shi karatu. Yayi watsi dasu.
Ranar wata Friday ne NIHLA ta tashi da nak'uda tun abun Yana Mata k'adan-kad'an har yayi yawa, Umma ta Gane, ba tare da b'ata lokaci ba aka nufa hospital da ita, Dan dama JAMAAL Yana karatu Yana wani aikin ne acan Kuma Yana turo musu da kud'i, duk siyayan kayan baby ma shi yayi acan sai ya turo musu.
Cikin awa d'aya Allah ya sauke ta lafiya inda ta haifa yaro namiji Mai kama da mahaifin shi JAMAAL sak, carbon copy kenan inji ni Ummu Basheer.
Anyi taron suna inda yaro yaci sunan mahaifin NIHLA,suna Kiran shi da HANIF, yaro ne Kyakyawa, Haka NIHLA tayi wankan jego Mai kyau domin sosai Umma ta tsaya Mata, ta Zama kamar mahaifiyar ta, Haka HUDA na yawon zuwa. RAUDAH ko ta gaji ta hak'ura ta fito da miji tayi aure.
NIHLA ta cigaba da zuwa makarantar islamiyya sosai ta dage har ta sauke Al-QUR'AN, gashi ta k'ara kyau sosai, Dan ko suna cin abinci Mai kyau sannan Kuma ga tsafta, Koda yaushe JAMAAL cikin turo musu kaya yake har iyayen nashi ma, yanzu suna rayuwa cike da ban sha'awa.
"""""""""'''''''""""""""""""""""'''''''''''"""""""""""""""""
*Bayan shekaru Uku*
*After three years*
A yau ne ake ta Shirin dawowan JAMAAL daga Abroad, NIHLA ce na gani, Masha Allah nace, domin ba k'aramin kyau tayi ba gashi ta dawo yarinya k'arama baza ku tab'a Gane Tana da shekaru ba, wani Kyakyawan yaro ne d'an kimanin shekaru biyu yaje gurin Umma.
Dariya Umma tayi tace"Wato HANIF baka son wanka Koh"
Cikin maganar shi da Bai iya ba yace"Ci b'oye ni, ka Mommy ci gani"
NIHLA ce ta k'araso gurin "Let's go and bath,ai na gan ka"
Mak'e kafad'a yayi yace"A'a ban sho"
"Daddy'n ka zai dawo kazo ayi wanka kaji miji na Mai kawo cefane"cewar Umma cikin Wasa.
Da k'yar dai NIHLA ta d'auke shi tayi mai wanka, ta shirya shi cikin riga blue Mai check da ratsin white,sai white jeans, ta gyara Mai gashin shi Wanda yake kwance kamar na larabawa.
Abinci kala-kala ta shirya ma mijin nata, ga natural drink na fruit da ta had'a, gashi dama a shirye take domin ta gyara kanta sosai gurin Aunty Jameela. Fatar ta yayi smooth ga wani irin sihirtacen k'amshi Mai dad'in gaske da takeyi. Ko'ina na gidan kamar Koda yaushe k'al-k'al yake.
KANO STATE AIRPORT
Sanu a hankali yake saukowa daga stairs na jirgin, Kyakyawan saurayi ne kamar bature Haka yake cikin suit black,ga sunglass da yasa, a hankali ya shak'i k'amshin k'asar shi Nigeria, JAMAAL kenan Wanda dawowan shi kenan daga k'asar waje, Yana cike da Burin had'uwa da Matar shi da yaron shi tare da Family'n shi.
Wani driver ne yazo ya d'auke shi tare da mutumin Nan da yayi Mai komai na tafiya, inda suka gaisa, sannan suka nufa unguwar su JAMAAL.
*Janih one love*๐
*UMMU BASHEER CE*
*For comments only 07030865952*