Showing 6001 words to 9000 words out of 17571 words
office, gaba d'aya yau ta kasa yin aiki, tayi zurfi a cikin tunani, abubuwa sunyi mata yawa, ga bak'in cikin had'a auren ta da SABIR da za'ayi, wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata, Kai gaskiya Ina baza ta iya yarda a had'a auren ta da SABIR ba.
Mik'ewa tayi tare da d'aukar handbag ta fita a office d'in, driver dake zaune daga can gefe ya taso da sauri Yana cewa"Madam lafiya?, Gida Zan Kai ki?"
Ko kallon shi ba tayi ba ta shige mota, ai da sauri ya Shiga suka d'auki hanyar gida, suna Isa gate man ya bud'e gate, driver ya nufa gurin parking lot yayi parking.
NIHLA fitowa tayi ta Shiga parlour, Mom dake kallon news da sauri ta fara tambayar lafiya ta dawo gida lokacin aiki?, K'arasawa NIHLA tayi jikin ta, tare da fashewa da kuka mai k'arfi.
A rikice Mom tace"Meya faru ne my daughter?, oya tell me,kinsan bana son kukan ki"
Cikin kuka tace"Mom I swear bana son SABIR, gaskiya ni bazan aure shi ba"
Mom tace"oh my God, NIHLA please kiyi hak'uri da abin da mahaifin ki yace, kinsan baya maimaita magana, but don't worry inshallah Zan k'ara mai magana"
Tace"Please Mom help me, Bana son auren Nan, na tsani SABIR, *BAMU DACE DA JUNA BA*"
Kwantar da kanta tayi a jikin Mom yayin da ita take rarrashin ta har ta hak'ura ta Shiga bedroom Dan baza ta iya aiki a ranar ba.
Around 8:00 pm in the night
Mom ce ta shigo bedroom d'in NIHLA inda ta same ta suna waya da HUDA, tana ganin ta sukayi sallama da HUDA tayi offing phone d'in.
Zama Mom tayi tace"NIHLA get ready kije ki sama SABIR a parlour yazo, and bana son Jin wani magana just ki bar komai a hannu na"
Shiru tayi yayin da Mom ta fita, night gown ne a jikin ta kawai sai ta d'auki After dress ta d'aura akai sai veil, Dan tace baza tayi mai kwaliyya ba.
Zaune ta ganshi a parlour already an kawo mai Juice and cupcakes, ba tare da tace komai ba ta zauna a d'ayan kujeran dake facing d'in shi,
Murmushi yayi yace"my Love hope kina lafiya?"
Hararan shi tayi tace"idan da bani da lafiya will you see me here?"
Murmushi yayi yace"I knew lafiyan ki k'alau ma, I'm very happy you're going to be my wife in the next one month"
Wani irin bak'in ciki ne taji kamar zatayi kuka tace"ni a matsayin matar ka? I will never be your wife so stop dreaming"
Yace"haba my wife to be kinsan da cewa Ina mutuwar k'aunar ki, ban tab'a san wata y'a mace ba kamar yanda nake k'aunar ki"
A fusace tace"Ni Kuma ban tab'a tsanan namiji ba kamar yanda na tsane ka, wallahi na tsane ka SABIR, kar kayi gigin yarda a had'a aure na da naka, Dan *BAMU DACE DA JUNA BA*"
Yace"haba meyasa kike cewa *BAMU DACE DA JUNA BA*, wait meyasa ba Kya so na?"
Tace" bana son ka saboda halayen ka na shaye-shaye da neman mata, SABIR har cikin zuciya ta nake fad'a maka Haka,why can't you understand my reasons?"
Yace"NIHLA idan har ban aure ki ba mutuwa zanyi, na rok'e ki Kar kice ba Kya so na"
A fusace ta d'auki juice wanda ke cikin cup, ta watsa mai a jikin shi! A razane ya mik'e tsaye ya rik'e rigar Wanda yake fari da hannun shi, lokaci d'aya idanun shi sukayi jajazur.
Cikin zafi tace da d'aga murya tace"I hate you SABIR, bana son auren ka, bana son ka, just live me alone, get out of my side"
A fusace ya d'auki car keys with phone d'in shi ya bar parlour'n. Yayin da NIHLA ta zauna a kujera tare da fashewa da kuka mai k'arfi, sosai tayi ta kuka har sai da kanta ya fara ciwo sannan da k'yar ta nufa bedroom d'in ta.
A wannan Daren da k'yar barci b'arawo ya sace ta.
Cikin two weeks, NIHLA ta Shiga tashin hankali duk ta rame, Dan Mom har fad'a sukayi da Dad but yace Bata Isa ta maida shi k'aramin mutum ba aure dole ne babu fashi, shiyasa duk NIHLA ta fita hayyacin ta, ko abinci sai Mom tasa ta a gaba take cin k'adan.
B'angaren SABIR ko bai sake zuwa ba, sai dai ya wakilta abokin shi akan komai na bikin.
An kawo lefe na gani na bugawa a jarida domin ya had'u iya had'uwa, set biyu ne,har da gold da wata waya mai tsada, komai yaji a kayan Masha Allah, Mom ko duk da taji dad'in ganin kayan bare yanda take son y'ar ta, ta auri Mai kud'i to gashi ta samu, but halin da NIHLA ke ciki Yana d'aga mata hankalin ta.
Yayar Mom daga k'asar Misra tazo sunan ta HAJIYA SHUWERH, ita ma Bata ji dad'in ganin yanda NIHLA Bata son Auren ba, mussaman aka d'auko Mai gyaran jiki Wanda sati d'aya ana gyara amarya NIHLA, ga yanda HAJIYA SHUWERH ke gyaran y'ar ta da magungunan Mata Wanda daga can tazo dasu. NIHLA ko da k'yar ake fama da ita, maganin ko HAJIYA SHUWERH tasa ta a gaba take har sai ta shanye tass ko Bata son Sha kuwa, Dan HAJIYA SHUWERH ba Wasa.
Anyi Abubuwa dayawa,domin Mom da abokanan Ango su suka shirya, ranar Wednesday anyi FRUIT DAY, Thursday Mother's day, Friday akayi Arabian night, duk da k'yar NIHLA taje, Haka take ta kuka, mutane ko gani suke kukan rabuwa da iyayen ta take,basu san dawar garin ba.
Ranar Fruit day ko kaca-kaca sukayi fad'a ita da SABIR domin SABIR ya gaji da yanda take nuna mai tsana k'arara, har cewa tayi gara ta mutu da ta aure shi!.
Ranar Saturday d'aurin aure
Haka HUDA tasa ta a gaba da k'yar ta shirya cikin wani Swiss lace,dark blue, veil d'in da aka d'aura mata Kuma silver colour ne, tare da necklace and earrings and bracelet duk silver ne, anyi Mata heavy make-up duk da Bata so.
Ba k'aramin mamaki nayi ba ganin Abba(mahaifin Jamaal) da Kuma JAMAAL, sanye suke da shadda na Abba sky blue ne sai na JAMAAL white ne, ba K'aramin kyau yayi ba, k'arasawa Abba yayi gurin Dad sukayi musabaha Yana mai Allah ya Sanya alkhairi.
Bayan JAMAAL ya gaishe shi ne, Dad yake cewa"Ikon Allah yanzu wannan shine JAMAAL d'in"
Dariya Abba yayi yace"Wannan ai d'an ka ne, shiyasa nace yau tare zamu zo maka d'aurin aure da shi"
Murmushi Dad yayi yace"Allah sarki gaskiya nayi matuk'ar murna, yaro na da fatan ka sani?"
Girgiza kai JAMAAL yayi alamar A'a domin shi dai Abba cewa yayi kawai ya shirya zai raka shi gurin d'aurin aure a Kaduna,to bai san komai ba.
Nan Abba ke bada labarin abin da ke tsakanin shi da Dad a gurin lokacin mutane na sauraren su.
Cewa yayi, shekaru ashirin da hud'u da suka wuce matar shi wato Umma ta tashi cikin dare da nak'uda, gashi akwai matsala dole suje hospital, Haka ya rok'a wani mak'obcin su daya taimaka ya kaisu hospital, haka ko akayi ana zuwa hospital aka Shiga da Umma theater room domin haihuwar yazo da matsala,yayin da aka umarce shi da ya kawo kud'i,gashi bashi da ko sisi, Haka ya bar hospital d'in cikin dare, domin ko mak'obcin su daya kawo su bashi da kud'in yace, har safe Abba na yawon neman kud'i Amma bai samu ba, can Yana cikin tafiya a gefen titi yana tunanin halin da ya bar matar shi, Ashe bai sani ba har ya hau kan titi, wata mota ce ta buge shi, duk da Mai motar yaso tsayawa Amma sai da ya buge Abba, Nan take sai jini, mutane suka taro a gurin da sauri mai motar ya fito shida wani mutum suka d'auki Abba suka sashi a cikin mota suka nufa hospital dashi,suna zuwa aka bashi taimakon gagawa to Alhamdulillah bai ji ciwo sosai ba, sai dai ku'jewa da yayi da Kuma suman da yayi sai kan shi ya bugu Amma da sauk'i ba abin da ya samu kan, lokacin da ya farfad'o matar shi kawai ya fara tambaya,Dad shine Wanda ya buge shi,Nan ya fara kwantar Mai da hankali da fad'a mai abin da ya faru. Nan shima yace sai ya tafi yaga halin da matar shi ke ciki, daya kafe kawai sai Dad yace Bari ya kai shi, suna zuwa aka fad'a ma Abba cewa ai anyi Mata aiki an Ciro D'a namiji suka umarce shi da ya biya bills, Dad da kanshi ya biya bills d'in sannan yayi ma Abba alkhairi ya bashi kud'i masu yawa,tare da bashi number'n shi, yace ya Kira shi idan akwai wani Abu, godiya yayi ta Mai sosai Yana gode ma Allah daya had'a shi da mutumin kirki.
Haka har aka sallame Umma sannan Abba ya Kira Dad ya k'ara Mai godiya sosai, tun daga wannan lokacin suke d'an zumunci da yake ba'a gari d'aya suke ba, Dad yazo Kano wani d'aurin aure ne, shine Yana hanyar zuwa gurin Accident d'in ya faru, lokaci zuwa lokaci su kan had'u har Dad yayi ma Abba alkhairi Wanda kullum sai Abba yace shi Koh da Mai zai saka ma Dad ne? Domin alkhairin shi,
To yanzu ma mussaman Dad yasa driver da ya kai ma Abba invitation card, har Kano, ba k'aramin farin ciki yayi ba shine yace zai tafi tare da JAMAAL domin ya San shi. Wannan kenan.
Cigaba
JAMAAL sauke ajiyar zuciya yayi domin ko ya tuna wani lokacin Abba na bashi labarin, Ashe dai Shine wannan mutumin. Gurin ko sai farin ciki suke, suna cewa ai k'adan daga cikin alkhairin Dad kenan.
Da missalin k'arfe 2:00 pm
Mutane duk an hallara sai jiran Ango ake da iyayen shi Amma shiru ba ko d'aya da yazo gashi d'aurin auren 1:00pm ne za'ayi but har 2:30pm yayi Amma shiru,can dai wani Aminin Dad ya Kira mahaifin SABIR Yana tambayar shi lafiya basu iso gurin d'aurin auren ba, Nan Mahaifin SABIR ke sanar musu cewa SABIR ya fasa auren NIHLA! Domin Bata son shi! Ba k'aramin girgiza kowa yayi ba, Dad ko wani irin azababben tari ne yazo Mai Wanda sai da ya kusa d'auke Mai numfashi!
Aminin bai gaskata ba sai da ya k'ara Kiran SABIR yaji daga bakin shi, SABIR ko bai b'oye musu komai ba ya fad'a musu irin rigiman da sukeyi da NIHLA Dan Haka shi ya hak'ura domin ba zai auri macen da Bata k'aunar shi ba, da yake a handsfree Aminin Dad yasa kowa na gurin naji,Dad ko yafi kowa Shiga tashin hankali wannan wani irin tozarci ne NIHLA taja Mai, cikin mutane sai kawai ya fashe da kuka mai tsananin gaske, ba abin mamaki bane domin sun San akwai zafi, a fasa auren y'ar ka cikin mutane Bayan an shirya d'aura auren.
Share hawayen shi Dad yayi ya kalle Abba yace"Ina son idan ka yarda a d'aura auren y'a ta NIHLA da D'an ka JAMAAL!"
Babu Wanda basu razana ba a gurin, bare kuma JAMAAL suman zaune yayi! Cikin rud'ewa da tashin hankali Abba yace"JAMAAL ai yaro ne k'arami, Amma babu abin da zaka nema daga guri na in k'i amincewa"
Dad yace"sai dai idan zaka k'i amincewa, Amma tunda Naga yaron ka naji ya kwanta min a rai naji k'aunar shi lokaci d'aya, Ina rok'on ka, daka share min hawaye na,domin sani cikin farin ciki yanzu"
Gaba d'aya mutanen gurin suka Fara ba Abba hak'uri da ya amince, Abba ko a zuciyar shi cewa yake ya Zama dole ya amince domin Dad ya taimake shi lokacin da yake tsananin buk'atar taimako, sannan ya rasa da Mai zai saka Mai, to yau ga ranar sakayar yazo, shine ya amince bare kuma yanda manyan mutanen gurin ke faman rok'on shi da bashi hak'uri, Nan take yace"wallahi na amince! Ni na ba JAMAAL Auren y'ar ka NIHLA!"
Gaba d'aya gurin akayi kabbara, Dad wani irin farin ciki ne ya ziyarce shi, yayin da JAMAAL kalaman mahaifin shi suka girgiza shi!
Dad ya kalle JAMAAL yace"D'a na ka amince zaka aura y'a ta NIHLA!"
Wani irin zufa ne yaji ta ko'ina,a zuciyar shi Yana tuna halarcin Dad gare su, bare kuma yanda yake babban mutum har yace shi ya aura y'ar shi Kuma yak'i, lokaci d'aya yaji k'warjinin Dad Nan cikin rawar murya yace"Na amince!"
Habawa ai Nan akayi farin ciki, ba tare da b'ata lokaci ba aka d'aura auren *JAMAAL IBRAHIM da NIHLA TAHIR* akan sadaki mafi daraja Naira dubu Ashirin, Wanda Nan take wani mutum ya biya ma JAMAAL yace shima d'an shine.
Mutane sun shaida wannan d'aurin auren, Masha Allah Nima na shaida, Haka nasan Fan's sun shaida.
*Akwai cakwakiya fa*๐๐ป
*TAKU CE UMMU BASHEER*
[26/02 12:28 pm] Sis Ummu Bashir: ๐น *BA MU DACE DA JUNA BA*๐น
๐น
{ *Short and interesting story* }
*NA*
*UMMU BASHEER*
ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐)_
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*PAGE *25~30*
*SAMAREEN BANA*
*Na Rahmat muh'd Rufa'i Nalele (Aunty luv)*๐
*Congratulations Aunty Rahmat Nalele Ina taya ki murnan Kamala litafinki da kikayi lafiya, Allah ya k'ara basira hazak'a k'warin ido tare da laushin hannu Ameen, more grace to your shining elbows, keep the fire burning,*
๐น. ๐น. ๐น. ๐น.
*Ina son ki, Ina jin ki, Ina Bayan ki Ina tare da ke a Koda yaushe,one love keeps us together, ja muje tawan naki ba irin nasu bane, ke d'in ta daban ce Naga yayi gaba na baya sai labari, kin nishad'antar Kuma kin ilimantar damu a cikin litafin ki na SAMAREEN BANA, tsayawa fad'in tsaruwan litafin ba zai fad'u ba a Baki, Amma kinyi bala'in k'okari sosai sister, fatan mu shine Allah ya raba ki da mahassada da mak'iyya, Ameen*
*Kai ku bani guri in d'an taka rawa*๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป *SAMAREEN BANA litafi ne da ya d'auki kusan shekara d'aya ana rubuta shi, karku Bari a baku labari ku nema ku karanta, Amma matan aure kad'ai๐, domin Aunty Rahmat tace Bata yarda kina budurwa ko bazawara ko saurayi ko bazawari, su karanta Mata litafi ba, Nima dai na k'ara fad'a, na matan aure ne irin mu๐ Banda su O'o ehe๐*
*Wayyo hausawa sunce laifin dad'i k'arewa, muna missing d'in SAMAREEN BANA sai mun jiki a sabon litafin ki Mai sunna LIKITAN ZUCIYA, duk da dai kin lasa Mana Zuma a baki๐sai mun jiki*๐๐ป
*Dad* ne ya shigo cikin gidan tare da nufan parlour'n shi, Mom na Ganin shi tayi saurin bin Bayan shi Dan taji kamar mutane na fad'in Wai SABIR ya fasa auren, Nan ta fara tambayar shi ko lafiya ya ake ciki?.
Ba tare da b'ata lokaci ba ya sanar da ita komai da ya faru! Ba k'aramin razana tayi ba, domin da ayi auren NIHLA da yaron da yace ai gara SABIR sau dubu a cewar ta, a fusace ta fara magana Tana cewa ai ba zai yuwu ba NIHLA ta aura d'an talakawa,sai dai a kwance auren, Dad ran shi ya matuk'ar b'aci, yace ko Bata Isa ba Kuma yanzu ba sai anjima ba za'a tafi da NIHLA Kano, Kuma babu shi ba ita! Ya cire ta a rayuwar shi!.
Ba k'aramin tashin hankali Mom ta Shiga ba, a fusace ya mik'e ya Isa bedroom d'in NIHLA inda wasu 'Yan uwa'n suke ciki, Yana Shiga yace"Burin ki ya cika na ganin Baki aura SABIR ba, kin wulak'anta ni, kin tozarta ni cikin d'umbin mutane, na had'a ki da miji kin k'i min biyayya sai da Kika sa ya fasa auren"
Jin an fasa auren yasa NIHLA Jin dad'i sai dai maganar da yayi yanzu ya birkita Mata k'wakwalwa, inda yace"To Allah ya taimake ni inda ya bani Wanda zai share min hawaye na, an d'aura auren ki da JAMAAL!Kuma yanzu za'a wuce dake, Ina son daga yanzu ki d'auka Baki da iyaye! Kuma ni bani da wata 'YA!"
Ba NIHLA kad'ai ba gaba d'aya kowa na gurin sun girgiza da maganar shi, Nan ya umarce HAJIYA SHUWERH da 'Yar uwa'n shi da su shirya ta zasu wuce Kano yanzu, Kuma yace Kar Wanda yaje, sai su biyu, sannan Kuma NIHLA Kar ta d'auki komai nata sai Kaya.
Mom ce ta bishi tace ita Sam bata yarda ba, ko kulata bai yi ba, NIHLA kuka kawai take yayin da zuciyarta ke Mata wani irin azababben ciwo, HAJIYA SHUWERH sun shirya Mata kayan ta, HUDA sai kuka take tana rarrashin NIHLA.
Dad sai cewa yake suyi sauri za'a tafi, duk matan gurin sun tausaya ma NIHLA wannan wani irin aure ne Haka? HUDA ce tayi saurin saka Mata phone d'in ta a akwati, NIHLA rungume Mom tayi tana kuka, da k'yar aka raba su, Har parlour'n Dad aka Kai ta, tana Shiga ta rik'e k'afar Dad "Dan Allah ka yafemin, wallahi Na amince da SABIR, bana son auren Nan, kayi min Rai Dad, wallahi bana son shi"
Wani gigitacen Mari ya Kai Mata sai da jini ya fito ta gefen lips d'in ta, "har ni zaki fad'a ma haka,?to kije kiyi rayuwar da nasan ba Kya so yanzu ne zakiyi hankali kisan duniya, ki d'auka cewa Baki da kowa a duniya sai inda Zaki" Nan ya umarce su da su jata, tana kuka sosai Haka aka sa ta a mota, su HAJIYA SHUWERH suka shiga.
Motoci biyu ne su Abba suna d'ayan motar, zuciyar JAMAAL ko tafasa kawai yake tsabar bak'in ciki, Haka NIHLA tayi ta kuka a hanya, HAJIYA SHUWERH ke faman rarrashin ta da yin Mata nasiha.
Da missalin k'arfe 8:00pm
Suka Isa cikin Kano State, Abba ne yayi ta ma driver kwatance har suka Isa k'ofar gidan su, sannan motocin sukayi parking, mutanen unguwa sai kallon motocin suke, Dan unguwar 'yan k'auye ne, Da sauri JAMAAL ya fita motan, direct gidan su Al-Ameen ya nufa.
Abba ne ya Shiga gidan Yana sanar da Umma ga bak'i nan, Shigowa sukayi yayin da fuskar NIHLA ke rufe cikin gyale, da k'yar take tafiya.
Shiga sukayi har d'akin Umma, Nan tasa aka kawo musu ruwa, Abba ya aika aka siyo musu nama dasu juices aka ajiye musu, sannan ya Kira Umma d'akin Kaka ya sanar dasu komai dake