Showing 9001 words to 12000 words out of 17571 words

Chapter 4 - BAMU DACE DA JUNA BA Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

2557

faruwa, Umma tayi farin ciki Jin cewa y'ar masu kud'i ce, Kaka ma tayi murna wato rabon aure ne yasa su tafiya Ashe, Nan tayi ta addu'a, ko da suka nema JAMAAL sun rasa shi, kawai suka k'yale shi domin sun San Yana buk'atar hutu.




A cikin Daren Nan Umma tayi ta aiken Yara gidajen dake kusa Dan sanarwa, Aunty JAMEELA mijin ta ya kawo ta, Nan akayi ta shigowa ana ganin Amarya, Aunty Jameela da wata ce suka shiga d'akin JAMAAL suka k'ara gyarawa duk da d'akin ko da yaushe a gyara yake, sannan aka shigar dasu d'akin, lokacin da HAJIYA SHUWERH taga d'akin sai da ta tausaya ma NIHLA sosai,Haka ma 'yar uwa'n Dad, ita dai fuskar ta na rufe Bata son ganin ma inda take.






JAMAAL ko Yana Shiga d'akin Al-Ameen ya fad'a kan katifa tare da rik'e kan shi da hannu biyu, da sauri Al-Ameen ya fara tambayar shi ko lafiya? Da k'yar cikin bak'in ciki ya sanar da shi komai!

Shi dai Al-Ameen yayi farin ciki sosai sai dai ya tausaya ma abokin nashi ganin halin da yake ciki,Haka dai yayi ta mai nasiha sosai, anan JAMAAL ya kwana da k'yar ma yayi barci.


Washegari aka shirya yin taron biki, tunda abin yazo ba shiri, gashi Kuma ranar su HAJIYA SHUWERH zasu koma, Amma Sai anyi taron da su, Lokacin da aka sanar dasu Maman RAUDAH sunyi mamaki sosai, RAUDAH kuka ta kwana tana yi Dan Allah ya jarabce ta da son JAMAAL, bak'in ciki yasa ta kasa Shiga gidan.



Da k'yar NIHLA ta tashi, Dan kwanciya tayi ta rufa da gyalen ta, sai da HAJIYA SHUWERH ta nuna mata ranta ya b'aci sannan ta yarda ta shirya cikin Swiss lace pink, tayi kyau sosai ba k'adan ba sai dai rufe fuska tayi-tayi, mutane ko sai shigowa kallon ta suke.



Anyi taro sosai inda aka ci aka Sha, sai dai Amarya tak'i fitowa Kuma tak'i yarda aga fuskar ta, Haka aka yi taro aka watse, da yamma Su HAJIYA SHUWERH sukayi Shirin tafiya, sosai sukayi ma NIHLA nasiha, tare da cewa duk Safiya taje ta gaishe da Maman mijin ta da kakan shi Kuma ta dinga kyautata musu, sannan HAJIYA SHUWERH suka yi Mata sallama ai sai lokacin taji wani irin kuka ya zo Mata, cikin rarrashin ta suka tafi,inda driver suka mai dasu.





Da missalin k'arfe 9:00pm


NIHLA dai tana kwance, yanzu har Bata iya kukan sai dai hawaye kawai dake zuba, Aunty JAMEELA ce ta shigo.


"K'anwa ta akwai abin da kike so?"

"A'a nagode Aunty"

"Toh ni Zan wuce gida, Angon ki yanzu zai shigo"

Wani irin bak'in ciki taji Wai Angon ta mtssss"Sai da safe"


"Yauwa ki kulan min da k'anni na" ta fad'a tare da fita.


Tsaki tayi a ranta cikin zafi, ba'a jima ba sai ga JAMAAL ya shigo gidan, sanye yake cikin shadda blue yayi kyau sai k'amshi yake, d'akin Umma ya Shiga ya gaishe ta, Nan ya tarar da Abba sukayi Mai nasiha sosai har jikin shi yayi sanyi, dama sai da Al-Ameen ya bashi gasashen kaza guda biyu da fresh milk Wai Yana Ango yace Haka zai Shiga d'akin Amarya ai ba zai yuwu ba shine fa ya basu Umma d'aya sannan ya nufa d'akin shi Yana tsaki a ranshi Wai yanzu d'akin ya Zama na su biyu kenan? Gaskiya shi baya son auren Nan hak'uri kawai yayi.


Shiga yayi da sallama da k'yar ta amsa Mai, d'akin ba haske sosai kawai sai ya kunna d'ayan glop d'in, da sauri ta d'ago kai ganin ko waye.


Idanun su ne ya had'u da na juna, Zaro ido JAMAAL yayi" ke dama kece aka aura min?"

Hararan shi tayi cikin bak'in ciki " kai wace ce KE anan?"

A fusace yace"ban sani ba, dama Ashe kece aka aura min, da nasan ke ce wallahi bazan Amince ba"

Tace"da Mai yasa ka amince? Marar kunyar yaro kawai"

Zaro ido yayi yace"ke waye yaron?"

Tsaki tayi ta juya tare da kwanciya Dan Bata jure magana Mai tsawo,

Ba k'aramin haushin ta yaji ba, Dan Haka ko kazar ma sawa kawai yayi a d'an wani k'aramin fridge, sannan ya d'auka pillow da bedsheet ya kwanta kan carpet, tana Jin lokacin da ya kashe glop sai taji tsoro Dan yau ne Rana na farko da ta tab'a kwanciya da namiji a d'aki d'aya, shima ta b'angaren shi Haka yake ji.


K'arfe 2:00 am taji motsi, farkawa tayi sai ganin JAMAAL tayi Yana sallah, tab'e baki tayi taci gaba da barcin ta.

Da asubah ya wuce massalaci, lokacin da ya dawo ya tarar da ita sai barci take, a ranshi cewa wannan kamar Bata damu da sallah ba, ruwa ya d'ebo a cup, kawai ya watsa Mata, A firgice ta tashi bala'i nace Dan ganin yanda ranta yayi bala'in b'aci abin da ba'a tab'a Mata ba kenan a rayuwar ta.

Kallon ta yayi a zuciyar shi yace ashe dai kyakyawa ce sosai Haka, Dan ranar da suka had'u ba wani kallon ta yayi sosai ba,jiya Kuma Dare ne, sai yanzu yaga Kyakyawar fuskar ta.

Mik'ewa tsaye tayi" Kai meye Haka?"

"Ba Kya sallah ne, kina ji an Kira sai wani barci kike"

Tsaki tayi"sai ka watsa min ruwa? shin ko kasan ni wace ce?"

Tsaki yayi"I don't want to know, kije kiyi sallah" ya Haye katifar tare da jan blanket, da sauri ta sauka tace"meye haka, Wai Kai baka da respect Koh?"

Bud'e fuskar shi yayi yace" ke Kar fa ki manta ni mijin ki ne, Dan Haka bana son raini"


Kamar zatayi kuka wai d'an yaron Nan ne ke fad'a mata magana gaskiya gwara SABIR sau dubu da shi, fita tayi da k'yar ta iya Shiga bayin, tayi alwala sannan ta dawo tayi sallah, tana son kwanciya amma ta kasa Dan Yana kan katifa,


Lokacin da gari ya waye taje ta gaishe da Umma, ita ko sai nan-nan take da ita, sannan taje ta gaishe da Kaka, sosai taji tana k'aunar Kaka Dan ranar tasa dariya.



Dawowa tayi d'akin tana kallon ko'ina Bata san lokacin da ta saki kuka ba, tsabar bak'in ciki Wai ita ce KE rayuwa a irin wannan gidan, sheshek'ar kukan ta ne ya tashe shi barci.


"Kina damu na fa"

Share hawayen ta tayi Nan taji motsin Umma ta kawo musu breakfast da sauri ta karb'a, sannan ta bud'e ganin kayan tea da tuwo yasa kamar zatayi amai, rufewa tayi ta aje gefe.



Wanka tayi ta shirya cikin riga da skirt brown colour. Sannan ne taga phone d'in ta, kunawa tayi, lokacin ne JAMAAL ya tashi, ko kallon ta baiyi ba ya fita d'akin.

Nan ta Kira HUDA a waya, tana kuka take fad'a mata inda take rayuwa, gaskiya ita Bata son JAMAAL ta fad'a mata ai wannan yaron ne da ta tab'a Bata labari, yanzu ace kamar ta tana rayuwa a irin gidan nan Kuma Wai Dad ya aura Mata k'aramin yaro Dan ta girma JAMAAL 2yrs ta bashi, Amma ji takeyi kamar ta bashi shekaru masu yawa,kunsan mace da son girma, gashi Kuma ta had'u da Wanda baya son raini, Dan bazai girmama ta ba. HUDA hak'uri kawai take Bata tana cewa tayi ma mahaifin ta biyayya a Haka sukayi sallama.







For comments 07030865952


*TAKU CE UMMU BASHEER*
[26/02 12:28 pm] Sis Ummu Bashir: ๐ŸŒน *BA MU DACE DA JUNA BA*๐ŸŒน

๐ŸŒน

{ *Short and interesting story* }



*NA*

*UMMU BASHEER*


ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐Ÿ“š)_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE 30~35*




*DEDICATED TO REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


Mrs Hamisu taura(sisin mama (
Ummie Garkuwa
Faty Axland
Hafsat Musa(indon k'auye)
Sadnaf
Meerah
Ayshkhair
Aunty Khady
MSB
Mommy'n sultan
Sweery
Lady Fulani
First lady
Zee yabour
Mommy'n mussadiq
Fashuna
Maman Muhammed
Dee
Biebie Dee
Ummyn yusra
Rafee'at
Fk fannah


*Ina son ku irin dayawan nan, tsayawa fad'in sunayen ku zai sa mu cinye lokacin but ku sani Ina k'aunar ku sosai Allah ya k'ara zumunci da k'aunar junan mu, pure tana haskawa,*๐Ÿ˜


*Nishad'i da kike samu UMMIE GARKUWA muna matuk'ar jin dad'i sosai, gaskiya kina sani dariya sosai,wacce Bata San ki ba sai ta kusa kuka mu Kam sai dai dariya, Aunty Maryam tace Ummie Garkuwa Bomb๐Ÿ˜œ,oho ni dai ba ruwana ba ni na fad'a ba๐Ÿ˜Ž*


*UMMIE GARKUWA Ina yinki Ina jinki Ina tare dake,Ina matuk'ar son ki kamar y'ar uwa ta na jini,๐Ÿ’‹ gaskiya kina sani nishad'i sosai, heart you dearโค*





*Ban manta dake ba Aminiyar k'warai REAL MAI DAMBU CE,๐Ÿฅ— kina mak'ale a raina Ina mugun yinki, and thanks for the Dedication Allah bar zumunci*๐Ÿ˜











*JAMAAL* sanye yake cikin farin yadi Mai kyau milk colour,bai sa hula ba dan shi a rayuwar shi ya tsana hula, shigowa d'akin yayi Yana kallon yanda NIHLA tayi kyau cikin English wears, a gaskiya ta had'u fa, yace a ran shi, ko kallon shi Bata yi ba, ya samu guri ya zauna tare da had'a tea ya fara cin tuwon shi,miyar kuka,yaji dadawa da manshanu. Yana lura da yanda NIHLA ke b'ata fuskar ta, Bayan ya gama yayi brush sannan ya dawo ya taci abinci.


Hararan shi tayi" Allah ya kyauta in ci wannan abin"ta nuna tuwo tana b'ata fuskar ta.


Zaro ido yayi"ke abincin Umma'n nawa kike cema haka? Kar kici ki zauna da yunwa non of my business"


Tsaki tayi ba tace komai ba har ya fita, Around 11:15am taji wani azababben yunwa dole yasa ta had'a tea tasha ba Dan ya bata sha'awa ba.


Da Rana shinkafa da miyar dane-dage aka kawo mata ai ko Bata ci ba, har dare sannan ta tuna da nama da fresh milk ai Nan ta d'auko ta fara ci, sai Bayan sallan Isha'i JAMAAL ya dawo.



Ta shirya cikin wani night gown red colour tayi kyau, tana kwance kan bed rik'e da phone, ba k'aramin kyau tayi Mai ba, ga wani irin k'amshi Mai dad'in gaske.


Yana Shiga straight gurin ta ya nufa ya k'wace phone d'in, a fusace ta kalle shi.

D'aure fuska yayi yace"mene ne kikeyi?"

"Kai har ka Isa ka tambaye ni, why don't you have manners?"

"Ke ni sa'ar ki ne? Karki manta ni mijin ki ne"

A fusace cikin bak'in ciki tace"Allah ya kyauta d'an yaro da Kai kawai, wallahi Kai kasan *BAMU DACE DA JUNA BA*, meye zanyi da Kai"


"Ai nasan *BAMU DACE DA JUNA BA*, ni badan Abba da mahaifin ki Mai zai sa in aure ki tsohuwa dake"


"Kai nice tsohuwar?"๐Ÿ˜ฆ

"To dake mece ce In ba tsohuwa ba, ni mazanyi dake"


Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo Mata"Na tsane ka, wallahi gara ace SABIR na aura da Kai, k'aramin yaro"


Rik'o hannun ta yayi ya had'a a Bayan ta ya matse da k'arfi"wane ne k'aramin yaro, ke baki da kunya ko? Wani d'an iskan kike Kiran min?"


"Wayyo hannu na, ka sake ni"

K'ara matse hannun yayi yace"ni ba sa'an ki bane, bana son rashin kunya"

Sakin hannun yayi ai ko hararan shi ta dingayi a ranta cewa take Ashe d'an yaron Nan nada k'arfi? Ni ko nace oho Zaki sani Nan gaba๐Ÿ˜‚





Bayan sati biyu


Cikin sati biyun nan NIHLA ta fuskanci canjin rayuwa sosai Dan ba kamar da data ke gidan su ba, abinci ba irin Wanda take ci ba,Haka ruwa ma, ga inda take rayuwa gaskiya bata son irin rayuwar Nan, Abu d'aya ke Mata dad'i shine idan taje gurin Kaka suna hira, tunda Umma ta lura NIHLA Bata iya cin abincin su, sai tana sa JAMAAL ya siyo Mata irin su take away ko baya so sai ya siya dole, ko ruwa Swan water Umma ke sashi siyowa, Tunda NIHLA ta Gane Umma na son ta sai taji dad'i har tana k'okarin cin abincin duk da sau dayawa idan taci sai zuciyar ta yayi ta tashi kamar zatayi amai, Dan Bata Saba ba, B'angaren ta da JAMAAL ko, kowa na harkar gaban shi Amma duk ranar da wani Abu ya had'a su to zata gaya Mai bak'aken maganganu, shi Kuma ya nuna Mata bai son raini shine gaba da ita, ya matse hannun ta, Kuma hakan ba zai hana ta k'ara Mai rashin kunya ba, kullum cikin waya suke da HUDA tana cewa tayi ma mijin ta biyayya sai tayi banza da ita, sunyi waya da Mom inda take kuka tana fad'a mata irin rayuwar da takeyi Dan Haka Mom tace zatayi tunani ta samo musu solutions Dan Bata son Y'ar ta tayi rayuwar talauci.


Wata Rana RAUDAH ta shigo gidan kawai sai taci karo da NIHLA a tsakar gida,ba k'aramin tashin hankali ta Shiga ba ganin NIHLA kyakyawa har sai da ta tambaye Umma wace ce shine take fad'a mata matar JAMAAL ce, ta rud'e sosai inda ta koma gida sai kuka take tana bak'in cikin yanda NIHLA ta fita komai, tasan dole JAMAAL yaso NIHLA Kuma dole suyi rayuwar aure Wanda RAUDAH ke bak'in cikin hakan, ni ko nace ai matar shi๐Ÿ˜’



NIHLA na kwance kan katifa tasa three quarter da K'aramin top tana Shan iska kasancewar ana zafi sosai gashi ta Saba da A.C Nan ko sai celling fan, JAMAAL ne ya shigo dawowan shi kenan daga masalaci sallan Isha'i, kusan suman tsaye yayi da ya ganta.


K'arasowa yayi kusa da ita ai bai san lokacin da ya kwanta kan katifar ba tare da rungume ta, a firgice ta juyo sai ganin JAMAAL tayi, ture shi tayi tace"Kai wani irin iskanci ne Haka?"

Lokacin da idanun shi suka Kai kan breast d'in ta duk sai ya rikice, habawa ai bai san lokacin da ya had'a bakin su ba Yana Mata wani irin kisses, tunda suke a rayuwar su basu tab'a Shiga irin yanayin Nan ba, NIHLA jikin ta rawa ya fara, gaba d'aya ta manta a wani duniyar suke, nace duniyar luv๐Ÿ˜‚


Da k'yar ta iya ture shi, tana goge bakin ta da hannu, shi ko sai sauke ajiyar zuciya yake.

"Yanzu d'an yaro da Kai ka iya iskanci?"

"K'adan ma Kika gani"๐Ÿ˜‰

"D'an iska kawai nafi k'arfin ka, da zaka wani had'a baki na da naka,shin ko ka manta ko ni wace ce?"

Tsaki yayi yace"wace ce ke Bayan Mata ta, look nine nafi k'arfin ki, Dan ni saurayi ne ba tsoho ba" ya mik'e ya bar gurin Yana lashe lips d'in shi gaskiya kiss yayi idan har Haka yake da dad'i. Yake fad'a a ran shi.

Tsaki tayi ta d'auki brush d'in ta taje waje Wai a dole zata goge kiss d'in da yayi mata๐Ÿ˜†


JAMAAL ko Yana fitowa waje ya had'u da Al-Ameen, shaking hands sukayi, a kunne JAMAAL yace ma Al-Ameen"Kai Aure fa yayi a rayuwa"

Dariya Al-Ameen yayi yace"Kai friend kace kaje duniyar ma'aurata ka dawo?"๐Ÿ˜‚


"Ban je ba tukun amma na kusa"๐Ÿ˜‰

"Gaskiya Nima ina son yin auren Nan inji Wai me ake ji ne"

"Kai nifa sai dai in San auren but bana son ta"


"Come-on ka daina cewa Haka, Kar wata Rana kazo kana min kukan love d'in da kake Mata"


"Mtssss Kai banza ne wani lokacin, Allah ya kyauta inyi kuka akan love, never"


Haka dai sukayi hira k'adan sannan sukayi sallama, lokacin da ya Shiga gida already ya samu har tayi barci, kasancewar rigar da tasa k'arami ne har ana ganin breast d'in ta, kwanciya yayi kusa da ita sai k'are Mata kallo yake, gaskiya duk yanda yake tunanin NIHLA ta wuce Nan, she's very beautiful, Haka ya kwanta kusa da ita har asubah.


Gyara kwanciya tazo yi, kawai taji ta jikin mutum, ihu ta saki da sauri ya had'e bakin su Yana tsotsan lips d'in ta,sai zaro ido take cikin tsoro dan ba haske sosai, Haka yayi ta romancing d'in ta, lokacin da ya Kai lips d'in shi kan nipples d'in ta ai duk sai ya birkice, ita kanta a rud'e take sosai. Knocking d'in k'ofar da akayi ne ya dawo dasu hayyacin su, dan dama kullum Abba Yana tashin JAMAAL Dan kar yayi late.


Cikin sanyin jiki yake sanar da Abba cewa ya tashi, ko da yaje massalaci ya dawo k'ara mak'ale NIHLA yayi, already dama tayi sallah ta koma barci.


Sai da safe ta bud'e ido taga JAMAAL ya wani rungume ta kamar irin za'a gudu da ita d'in Nan, da k'arfi ta buge shi, bud'e ido yayi cikin Jin barci yace"oh baby I'm feeling sleepy"

Ture shi tayi tace"are you out of your sense, Kai meyasa baka da kunya ne, ni sa'ar ka ce"

"I'm your husband fa,so you should respect me"

Tsaki tayi ta tashi, ta nufa bayi Dan yin wanka,Cox already akwai hot water a flask.


Har ta cire kayan ta ta d'aura bathrobe d'in ta tana son yin brush, kawai sai taga wani k'aton kenkeso, wani irin ihu tayi ta fito a guje.


Umma dasu JAMAAL duk sun fito, ai Bata San lokacin da ta rik'e hannun JAMAAL ba tana pointing d'in bayin.

Umma tace"lafiya mene ne?"

"Wayyo Allah na cockroach ne"

Dariya JAMAAL ya k'yalk'ale dashi.

Kaka tace"oh ni Jumai mene ne Haka Kuma?"

Umma tace"Wai mene ne ka tsaya kana wani dariya?"

"Wai tsoron kenkeso takeyi"๐Ÿ˜‚

Tafa hannaye Kaka tayi tace"yau naji shirmen banza yo ba sai ka kashe mata shi ba ka tsaya kana dariya"


"Kaka ita ta kashe Mana"๐Ÿ˜

Umma tace"yi hak'uri d'an albarka, je ka kashe shi"

Shiga bayi yayi but bai ga komai ba sai cewa yake kawai dai NIHLA ta cika tsoro ne ba komai, ita ko sai murgud'a Baki take tsabar haushi.


Dole ta Shiga bayin tayi wanka but a tsorace take fa๐Ÿ˜‚











*Janih one love*๐Ÿ’˜











*UMMU BASHEER CE*
[26/02 12:28 pm] Sis Ummu Bashir: ๐ŸŒน *BA MU DACE DA JUNA BA*๐ŸŒน

๐ŸŒน

{ *Short and interesting story* }



*NA*

*UMMU BASHEER*


ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐Ÿ“š)_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE 40~45*



*DEDICATED TO UMMI AISHA*


*Aunty Aisha wannan shafin naki ne gaba d'ayan shi, thanks for your love and care,Ina mugun yinki a raina, Allah ya k'ara Miki basira da hazak'a k'warin ido tare da laushin hannu a cikin litafin ki na ALWASHI.....!*๐Ÿ’


*Kamar yanda nace Miki ga naki page d'in*๐Ÿ˜




*UMMIE GARKUWA BOMB*๐Ÿ˜Ž๐Ÿ’‹





*Yinin* ranar NIHLA tayi shine a d'aki cikin jin kunyar fitowa Dan tana tsoron kar su Umma su gane, shi ko gogan naku sai wani ririta ta yake Yana tambayar meke damun

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login