Showing 3001 words to 6000 words out of 17571 words

Chapter 2 - BAMU DACE DA JUNA BA Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

2558

tolerating ba" ya bar parlour'n cikin fushi.


NIHLA fashewa tayi da kuka yayin da Mom ta rungume ta tana rarrashin ta.



Cikin kwana biyu hankalin NIHLA a tashe yake domin bata san wani irin hukunci Dad zai yanke mata ba, HUDA ce mai Mata nasiha da ban hak'uri, gashi SABIR ya nace Mata kamar maye a cewar ta.


Sanye take da English wears na gown maroon colour, tayi rolling d'in veil a kanta ga sunglass da tasa duk ya rufe rabin fuskar ta, light make-up kawai tayi, dawowan ta kenan daga aiki ta shigo gidan.




Tana Shiga parlour taji muryan mutane a parlour'n Dad, d'aga kafad'un ta tayi irin she don't care, Mom na ganin ta tace tayi lunch Dad nason ganin ta kafin Nan guests d'in shi sun tafi.



Bayan tayi lunch ne ta nufa parlour'n, ba kowa a parlour'n sai Dad, abin da ya bata mamaki shine ganin su goro da sweety, dayawa, gaishe shi tayi sannan tayi shiru.


Parlour'n ya d'auki shiru tsawon 5 minutes sannan Dad yayi gyaran murya yace"I know you'll be surprised, tunda na baki time ki fito da miji amma kin kasa to shine ni na zab'a Miki miji, D'an Aminina ALHAJI MUSTAPHA, wato SABIR, a yau ne aka sa ranar d'aurin auren ku Nan da 2 months!"



Tunda ya fara magana take zufa duk da sanyin A.C dake parlour'n, gaba d'aya ta rikice ta rasa mai za tace, she's totally out of her sense, da k'yar cikin rud'ewa tace"Dad kayi min Rai ka taimake ni, wallahi bana son SABIR"

Daka mata tsawa yayi yace"shut up, ni zaki fad'a ma Haka, in baki miji kice wai baki so, kina hauka ne after na baki chance but kin k'i kawo miji Kuma inyi Miki miji yanzu and you're telling me nonsense, tashi ki bani guri idiot kawai"


Da sauri ta bar parlour'n tana kuka, straight bedroom d'in ta, ta shiga ta rufe tare da fashewa da kuka kamar ranta zai fita.







*ASALIN NIHLA*


*NIHLA TAHIR* shine cikaken sunan ta, Kyakyawar budurwa ce y'ar kimanin shekaru ashirin da shida, 26yrs, Fara ce doguwa, tana da eyebrows masu kyau ga pink lips d'in ta gwanin ban sha'awa d'an k'arami, idanun ta farare tas.

Mahaifin ta cikaken d'an kasuwa ne, Yana zuwa k'asa-k'asa yin business, wani zuwa da yayi k'asar Misra anan ne ya had'u da RUKAYYA, mahaifiyar NIHLA, larabawa ne su, inda suka fara soyayya mai k'arfin gaske, iyayen RUKAYYA da k'yar suka yarda akayi auren da sharad'in zai dinga kawo ta, Haka Koh akayi Bayan Auren suka koma Nigeria, lokaci zuwa lokaci Yana Kai ta, sai Bayan sunyi aure da shekaru had'u Allah ya basu haihuwar y'a mace inda taci sunan NIHLA.



Kasancewar ta y'a d'aya gurin iyayen ta hakan yasa take zuba shagwab'a duk da mahaifin ta baya son yanda Mom ta shagwab'a ta, NIHLA Kyakyawar budurwa ce tayi primary and secondary School d'in ta anan Kaduna, sannan tayi University ta karanci business, Bayan ta gama Dad d'in ta ya malaka Mata d'aya daga cikin company d'in shi, ta fara aiki.



HUDA aminiyar tace tun suna secondary School har zuwa University sannan HUDA tayi aure, yanzu Haka tana da ciki, HUDA tana da kirki sosai,ita ma y'ar masu kud'i ce.



NIHLA ta d'auko wasu halayen mahaifiyar ta na k'in talaka, Bata son talakawa ga ta miskila ce, da k'yar aga murmushin ta bare kuma dariya, Bata son kaya irin su atamfa da shadda tafi son English wears, tafi son Riga da skirt da veil shine irin shigar ta, a rayuwar ta Bata san wahala ba, ba Wai Bata iya aiki bane A'a Bata son yi ne saboda tana da masu Mata, but sometimes ita da Mom suna yin girki,Dan NIHLA ta iya, Haka Kuma ita ke gyara bedroom d'in ta dan it's her privacy, SABIR Yana son ta amma ko k'adan ba ta son shi domin halayen shi na bin Mata da shaye-shaye, duk da kasancewar shi police, Kuma d'an masu kud'i but she doesn't loved him, Dan she hated maza masu neman mata, wannan shine dalilin da yasa Bata son shi, to gashi yanzu Dad ya had'a su ya kenan za'a k'are?.







*Back to story*

*Cigaban labarin*





NIHLA hankalin ta ba k'aramin tashi yayi ba Haka tasa Mom a gaba da kuka Wai tayi ma Dad magana ita gaskiya bata son SABIR,


Mom ko tana son y'ar ta, baza ta so bak'in cikin ta ba, Amma ba yanda zatayi Cox Dad kaifi d'aya ne baya magana biyu, Haka dai tayi ta rarrashin ta da bata hak'uri.



Shiryawa tayi ta Kira driver ya kaita gidan HUDA, tana Shiga ta fashe ma HUDA da kuka, hankalin HUDA a tashe take tambayar meke damun ta, da k'yar Bayan taci kuka ta fad'a mata!.


HUDA hankalin ta ya tashi Dan batayi tunanin Dad zai yanke hukuncin Nan ba, gashi kaifi d'aya ne Kuma aminiyar ta Bata son SABIR.


Juice ta zuba mata a cup ta mik'a mata tace"calm down Friend, everything will be okay"

Karb'a tayi Tasha k'adan ta ajiye tace"Friend Ina cikin rud'ani, I don't know what to do, please help me" wasu hawaye masu zafi suka zubo mata.


HUDA tissue paper ta mik'a mata tace"Addu'a makamin musulmai, Ina son ki dage da addu'oi, da sallan dare Allah ya zab'a Miki abin da yafi alkhairi a gare ki, Inshallah Allah Yana amsa addu'oin bayin shi"


NIHLA share hawayen ta tayi tace"I'm very happy to have friend like you, nagode sosai Kuma Inshallah Zan yi yanda Kika ce"


Tace"Yauwa my friend, yanzu dai tunda kinzo sai ki tashi ki tayani d'aura dinner" ta k'are cikin dariya.



Tace"Wai this my baby Yana Baki wahala, girkin ma yanzu da k'yar kikeyi" tayi dariya.



Kitchen suka nufa a tare suna hira kamar basu da wani damuwa, Nan sukayi pounded yam, but flour d'in shi, sannan sukayi egusi soup da yaji nama, sai mango juice da suka had'a.





Bayan sun gama su kaci tare sannan NIHLA ta Kira driver yazo ya d'auke ta, har gate HUDA ta raka ta, sai da ta Shiga mota sannan HUDA ta Shiga gida.












*Irin wa'inan k'awayen ake so masu baki shawara na gari, Allah kayi Mana tsari da mugayen k'awaye.*








*TAKU CE UMMU BASHEER UMRAH*
[26/02 12:27 pm] Sis Ummu Bashir: ๐ŸŒน *BA MU DACE DA JUNA BA*๐ŸŒน

๐ŸŒน

{ *Short and interesting story* }



*NA*

*UMMU BASHEER*


ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐Ÿ“š)_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE* *15~20*



*Assalamu Alaikum masoyana Ina mai baku hak'urin cewa Zan dakata da rubuta novel d'in DANA SANI...., Saboda wasu dalilai nawa,but Inshallah idan na gama wannan zanyi k'okari in cigaba da yin muku, Ina mai baku hak'uri massoyana,fatan alkhairi gare ku*






*Dedicated to sis Maimounath & Badeeyerh beuty queen, K'awas*



*Ina matuk'ar ji ku a raina Ina son ku kamar yanda Kuke Sona, ku sani mu d'in Aminan juna ne, Allah ya k'ara muku basira hazak'a k'warin ido tare da laushin hannu Ameen, Allah ya kare ku daga sharin mak'iyya da mahassada Ameen*


*Heart you my Sis & K'awas*โค










*KANO STATE*


*JAMAAL* na gani sanye cikin riga navy blue and white jeans yayi kyau sosai, sai murmushi yake lokacin da yaga fitowan RAUDAH, ita ko hararan shi tayi tace"kayi dariyan mugunta da kyau tunda ka buge ni"


Gyara tsayuwa yayi yace"ai that's why nazo baki hak'uri, Cox nasan nayi laifi I deserve anything"

B'ata fuskar ta tayi tace"Bayan yau na iya hada amma sai da ka buge ni"


Yace"surutun ki yayi yawa da y'an aji, ki daina kula su idan sunayi"

Tace"ba wani Nan sai na fad'a ma Umma na" Nan ta shige cikin gidan su da sauri, bin Bayan ta yayi.



Tana Shiga ta fara fad'a ma Umma ai yau ya buge ta a islamiyya,Dan tayi surutu kawai, Umma ko fad'a tayi Mai, shi Koh sai hak'uri yake bayarwa.





Shin wane ne JAMAAL?



*JAMAAL* Kyakyawan saurayi ne yaro d'an kimanin shekaru ashirin da hud'u 24, sunan mahaifin shi Malam IBRAHIM, mutum ne Mai kirki da son addini, ya kasance talaka ne, Yana da Mata MARYAM (Umma) suna da Yara guda biyu, *JAMEELA* daga ita sai JAMAAL, iyayen su sun basu tarbiyya Mai kyau, Aunty JAMEELA, a yanzu haka tayi aure harda yara biyu *IMAN da AMAN*, mijin da take aure Yana da d'an rufin asiri Haka Kuma tana da kirki, tana son K'anin ta JAMAAL shima yana son Aunty'n shi, Yana da son yara Sosai, shiyasa Koda yaushe Yana mak'ale dasu Iman da Aman, mahaifiyar su tana da kirki ga tsafta da iya girki, sannan akwai ta da son kud'i Dan indai kina da kud'i to shikenan zaku k'ula da ita.




JAMAAL Yana matuk'ar ji da mahaifiyar shi, shiyasa yake Kiran ta da Umma na, baya son ganin tana aiki, Yana kula da ita, Kuma baya son b'acin ran ta, Yana son farin cikin ta, duk da basu da hali sosai Amma suna cin abinci mai kyau, wani lokacin da nama ko kifi, sai dai Umma tafi yin tuwo, JAMAAL Yana da Kaka, wato mahaifiyar Abba mahaifin shi, anan gidan take zaune, akwai ta da ban dariya, sau dayawa tafi Zama a d'aki, a cewar ta Kar ta damu surukar nata, Dan zaman mutunci suke, sai dai Kaka ta rik'e girman ta, Bata cika shigar harkar ta ba, sai idan ana tare da jikokin ne.



Gidan su Yana da d'an kyau duk da kasancewar na k'asa ne, akwai tsakar gida babba,da bishiyoyi guda biyu Wanda ke bada iska, Akwai Parlour da bedroom biyu, Wanda nasu Umma ne, sannan Kitchen a waje,daga can gefe, Ban d'aki ne, da na wanka sai daga can gefe d'akin Kaka ce, sannan ta d'ayan gefen an gaba da na Umma shine na JAMAAL, babban d'aki ne sosai, an shimfid'a carpet blue, sai babban katifa, Wanda akayi shimfid'ar Bedsheet blue da blanket blue, sai wardrobe da gurin sa takalma, da labulaye(Curtains), Suma duk blue ne, sai TV stand Wanda akwai K'aramin plasma, sai decoder na Go TV, d'akin kullum cikin k'amshi yake, ga tsafta, duk da d'akin ba'a zuba dukiya ba,Amma fa ya had'u sosai.




JAMAAL yayi primary and secondary School d'in shi inda ya nufa University na B.U.K, duk da taimakon Aunty'n shi Jameela, kasancewar Allah ya bashi k'wakwalwa Yana da k'okari sosai gashi yanzu har ya gama, inda ya karanci, Building and engineering, sai dai lokacin da ya gama bai samu aiki ba, Dan yanzu aiki sai mutum nada hanya, to gashi Nan dai Yana zaman jiran aiki, sai dai Yana koyarwa a islamiyya saboda Yana da ilimin addini,ya sauke Al-QUR'AN tun Yana da shekaru goma sha shida, yasan litafan addini, dan haka sai Yana koyarwa a wani islamiyya cikin unguwar su, ana Kuma biyan shi albashi.




JAMAAL Kyakyawan saurayi ne sosai kamar yanda nace muku, sai dai Sam Mata basa gaban shi domin yace soyayya ai shirme ne, wasting of times ne, y'an Mata dayawa suna son shi sai dai baya basu fuska ko k'adan Dan tsoron tunkarar shi suke, duk da Yana da fara'a Amma ba kowa yake sakin ma fuska ba, sai iyayen shi da Kuma Wanda ya sani sosai. Yana da aboki Wanda tare sukayi karatun su daga secondary har University, shima dai bai samu aiki ba, sunan shi *Al-Ameen* Yana da kirki halayen su yazo d'aya da JAMAAL sai dai shi Al-Ameen Yana da son y'an Mata kullum cikin soyayya yake da canza y'an Mata, sai dai fa baya neman mata iya ka kawai yayi soyayya dasu kwana biyu ya canza wata, Yana da yayye maza su uku shine na hud'u.







RAUDAH Kyakyawa ce ba laifi black beauty ce, sai dai ko kwata Bata kai NIHLA kyau ba, ita kad'ai ce gurin iyayen ta, RAUDAH akwai surutun tsiya, wani lokacin rashin kunya, gidan su na kusa da nasu JAMAAL ne, su mak'obta ne, kullum tana cikin Shiga gidan su JAMAAL, sun shak'u sosai da JAMAAL, iyayen ma sun San da Haka, RAUDAH Bata son karatu a rayuwar ta da k'yar tayi j.s.s 3, yanzu shekarar ta goma sha Tara 19yrs, islamiyya ma Bata son zuwa, shiyasa JAMAAL ke dukan ta acan.










*Wannan kenan*



*Cigaban labarin*






"Come-on NIHLA ki daure ki shirya muje tare ko Zaki ji sauk'in abin da ke damun ki" Mom ce ke fad'a ma NIHLA Haka.



NIHLA dake kwance cikin blanket ta fito da kanta tace"Mom just go, save journey"


Tace"No My daughter tare zamu je bikin Nan, two days kawai zamuyi fa, kinsan HAJIYA AMINA tana son ki, kuma tace in zo Mata dake"


Zama tayi tace"okay Mom but kinsan ni bana son Shiga cikin mutane especially Kuma biki, kawai dai zanje ne"Nan ta mik'e tsaye ta fara shirya kayan ta cikin wani traveling bag pink and blue Mai kyau, sannan ta Shiga toilet tayi wanka,Bayan ta fito tasa wani Arabian gown peach colour tayi rolling d'in veil a kanta, light make-up tayi sannan tasa hill shoe white da handbag shima white.



Fitowa tayi parlour janye da Traveling bag, Mom ma ta gama shirin ta har ta fito, driver ne ya shigo ya kwashi kayan zuwa mota, inda Suma suka shiga cikin motar driver ya d'auki hanyar Kano.











Around 5:00pm suka Isa Kano, cikin wani Had'ad'en gida Mai shegen kyau motar ta Shiga, driver yayi parking gurin parking lot, da sauri wata Mata ta fito ita da wasu y'an Mata su biyu.



Welcoming d'in su sukayi yayin da suka shiga cikin gidan, abubuwan motsa Baki aka Shiga kawo musu, NIHLA ko Danna waya kawai take Cox ita fa Bata son Shiga mutane, ni ko nace ko kallon abin da aka kawo Bata yi ba, da kin ganta Kinga masu kud'i.




Nan Y'an matan Nan suka Kai ta bedroom d'in su, sai b'ata fuska take Cox tana ganin bedroom d'in yayi Mata local, duk da ko ya had'u, toilet d'in su da k'yar ta iya Shiga, Dan k'yama take ji, Dan ita daga gidan su sai na HUDA take sakewa, Bayan ta fito ma abincin k'adan taci ta kwanta.










HAJIYA AMINA K'awar Mom ce, ita tana zaune ne a Kano,tana da Yara Mata, to shine d'ayan zatayi aure shine tayi inviting d'in Mom da NIHLA.


Ranar mother's day


NIHLA Kam kwanciya tayi a gida tace baza ta je ba, Cox Bata son hayaniyar mutane duk an watse an bar ta ita kad'ai, lokacin da ta gaji da kwanciya ta mik'e ta shirya cikin wani material na Mother's day d'in, doguwar Riga ce, milk and golen colour, style d'in yayi kyau shiyasa tasa, tayi rolling d'in veil na kayan a kanta,wow tayi kyau sosai milk handbag da hill shoe tasa sannan tasa sunglass, ga heavy make-up da tayi, phone d'in ta, ta d'auka ta Kira driver ya kaita Restaurant ta d'an Sha Ice cream.




Suna cikin tafiya a hanya sai wata yarinya ta shigo ta gaban su saura k'adan driver ya buge ta, NIHLA kuma yanda ya taka burkin ne ya tsorata ta, parking yayi yayin da NIHLA ta fito cikin motar a fusace ta nufa yarinyan Dan a ganin ta laifin yarinyan ce da sunyi accident.



Tana zuwa ta d'aga hannu da niyar Marin yarinyan, cak taji an rik'e mata hannu, d'ago da Kai tayi cikin bala'in mamakin wani Mai gangancin ne wannan?.


Idanun su ne ya had'u da na juna, fusge hannun ta tayi cikin zafi. Shin ko kunsan wane ne? JAMAAL ne Wanda ke zaune yazo wucewa shida Al-Ameen, duk abin da ya faru sun gani,Kuma sun San laifin driver ne shiyasa JAMAAL yayi saurin rik'e mata hannu Dan kar ta Mari yarinyan.





Kallon ta yayi yace"Kar kiyi kuskuren Marin yarinyan nan domin laifin ku ne"


A fusace ta nuna shi daga sama zuwa k'asa tace"and who are you to talk to me like that? Kuma har kayi gigin rik'e min hannu?"


Gyara tsayuwa JAMAAL yayi yace"ni mutum ne Mai son adalci, Kuma ni mutum ne da bana d'aukar rashin gaskiya,domin kin San laifin ku ne"



Tunda take a rayuwar ta ba'a tab'a fad'a mata irin wannan bak'ar maganar ba sai wannan d'an yaron Wanda she's very sure ta girme shi, tace"you don't have manners, kaje gida a baka tarbiyya, I don't have your time little boy"tana fad'in haka ta shige mota driver yaja suka bar gurin.






JAMAAL ko wani irin bak'in ciki ne ya kama shi Jin abin da tace, a fusace yace"wallahi da kin tsaya sai na nuna Miki rashin tarbiyya"


Al-Ameen yace"Kai kazo mu bar gurin Nan, Dan wallahi k'ila ma y'ar wata babba ce a k'asar Nan"




Tsaki yayi yace"Kai wani irin matsoracin namiji ne? Idan y'ar wani ne then so what? Da ta tsaya sai na koya mata hankali tunda ita Bata da shi"


Al-Ameen ne ya jashi Yana bashi hak'uri su tafi, Shi ko zuciyar shi tafarfasa kawai yake tsabar bak'in cikin maganar NIHLA.






NIHLA ko ice cream d'in da Bata Sha ba kenan domin bak'in cikin abin da d'an K'aramin yaron Nan ya fad'a mata, lokacin da su Amarya suka dawo Mother's day sai zuba Mata surutu suke, komai ba tace ba,daga k'arshe barin gurin tayi, waya sukayi da HUDA tana Bata labarin abin da ya faru, ita ko hak'uri take Bata Cox tasan an tab'o aminiyar ta.





Washegari Bayan an d'aura aure NIHLA da Mom suka koma Kaduna,yayin da NIHLA still tana bak'in cikin abin da ya faru tsakanin ta da JAMAAL.

















*TAKU CE UMMU BASHEER*
[26/02 12:28 pm] Sis Ummu Bashir: ๐ŸŒน *BA MU DACE DA JUNA BA*๐ŸŒน

๐ŸŒน

{ *Short and interesting story* }



*NA*

*UMMU BASHEER*


ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐Ÿ“š)_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE* *20~25*




*Sister AYUSHERT MUH'D, nagode sosai da Dedication, Naji dad'i ba k'adan ba, yanda kikayi min Sadaukarwa na page d'in KAINUWA, gaskiya I'm very happy Allah ya k'ara zumunci, Allah yasa ki gama novel d'in ki lafiya kamar yanda Kika Fara lafiya, sosai nake Jin ki a raina, ke d'in ta daban ce, Thanks a lot*๐Ÿ•Š

๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š







*NIHLA* zaune take a

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login