Showing 93001 words to 96000 words out of 138652 words
bacci cikin kwanciyar hankali yayi kafun ya furta “ stubborn girl na kusa yin maganinki “, yana kara rungumeta a jikinsa, ba dadewa shima bacci ya daukesa, baccin da zai iya cewa tun tsawan wasu shekarun baya beyi baccin da begaji dayinsaba kamar na yau.
Kiran sallar asuba na farko ne ya farkar dashi, a hankali ya fara mutsu mutsu da idanuwansa kafun ya bude su gabaki d’aya akan kyakkyawar fuskarta ,zubawa fuskar idanuwansa yayi Kafun ya gyara mata kwanciyarta yana barin dakin. Kusan mintuna 30 da fitarsa itama ta soma mutsu mutsu kafun ta bude idanuwan gabaki d’aya, adduar tashi daga bacci tayi a bayyane ganin babu kowa a dakin yasa ta sakin ajiyar zuciya , Wanka tayi cikin simple doguwar Riga kafun ta tayar da sallar asuba , tana idarwa karatun alkurani ta yi , ta dauki kusan good 2 hours tana karatun har saida gari ya fara haske tukunna.
Turo kofar dakin da akaine yasa ta Mayar da kallanta bakin kofar, zuba masa ido tayi ganin shirgarsa ta yau sak balarabensa , jallabiya ce a jikinsa white colour sai abun nadin larabawa red colour , harya karaso wajan bata sani ba sabida yanda ta zuba masa ido , sai da ya hura mata iska kadan kafun ta sauke ajiyar zuciya, cikin kunya ta sunkuyar da kanta,kafun ta furta “ina kwana”, ba amsa mata ba sai kallanta da yayi, kara maimaita gaisuwar tata tayi ,ynxu ma be kulata ba , sun kuyar da Kai tayi kasa ya daga da kanta, bakinsu ya hade waje d’aya kusan mintuna daya kafun ya zare bakinsa “ bakyajin magana kenan ko”girgiza masa kai tayi alamun Aah , waje ya samu ya zauna , dan turo masa bakinta tayi kadan “ina kwana “, har yanxu be amsa gaisuwar tata va, sai ma a wayarsa da ya dauka , tunowa da wacce take hannunta yasa taje ta dakko ta , binta da ido kawai yayi kafun ya dauke kansa, cikin girmamawa ta miko masa wayar be amsa ba sannan be kalletaba,”ga Wanka “ ta furta a sanyaye, kallanta yayi “Menene nawa “ wayanka ta basa amsa ,”it’s your” ya furta , da wani irin shock ta kallesa, batasan lokacin data rungumeshi ba,hannu d’aya yasaka ya tallabota gudun karta fadi” dady dagaske ta wace”, gira kawai ya dage mata,kara rungumeshi tayi lokaci d’aya wani kukan ya kara wace mata, dagasken gasken yanxu kukan take me taba zuciya , very tight king ya rungumeta a kunne ya rada mata “it’s ok” kafun ya dago da ita , kallan yanda hawayen suke zuba afuskarta yayi kafun ya harareta kadan”so kuke su mahma suzo suce miki na miki wani abun kenan ko”, girgixa masa kai tayi tana goge hawayan nata “nagode sosai Allah ya kara budi”ya ji dadin adduar da tayi masa sosai cikin zuciyarsa ya amsa da amin, a fili kuwa dan tabile baki yayi “we’re friends ai no need” jinjina masa kai tayi zata mike yakara gyara mata zama akan cinyarsa,yanda ake anfani da yawar ya nuna mata komai already daman anyi settling komai na cikin wayar, murmushin fuskarta kasa boyuwa yayi sosai ta nuna jin dadinta,ganin karfe takwas ta kallesa “dady me kake so kaci” Kai tsaye ya bata amsa da “you”,wara idanuwanta tayi “toh ni taya za a da fani” bece mata komai ba yakama hannunta suka fito falon sai ynxu ta ke kallan yanda komai na dakin yake a canje,janta yayi har wajan dining ganin abunci ajjjere ne tayi serving dinsa tare da kunun aya, kince yayi saida tasa hannu ta fara basa a baki, duk loma d’aya in yayi baya sakamar mata hannun sai ya tsotseshi,abun har kunya ya fara bata, sai da tayi feeding dinshi kafun shima yasoma bata dan dole take karba,suna kammala ci falo suka zauna tana zaune kan cinyarsa kallan gashin kansa take so take ta taba amma ta kasa, kamar yasan me take tunanin ya dauki hannun nata guda daya ya dora a saman kansa,murmushi ta saki tana kara tura hannayenta cikin gashin kansa me tsananin taushi da laushi, suna zaune ahakan sukaji an turo kofar da dan karfi, zaro idanuwa tayi waje tana kokarin sauka amma ya kara riketa ajikinsa sosai yana bin amrah da tashigo masa part kai tsaye da wani rin birkitaccen kallo daya firgitata, hatta karamin ture din hannunta saida ya fadi kasa tsabar firgita.
💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖
Mss Lee 💖
💖💖GIDAN AUNTY💖💖
( a heart touching love story)
Story & written
By
Mss Lee 💖
💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖
PAID BOOK
MAI BUKATAR COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 07041879581.
BOOK 1📕
Page 53 _ 54💖
Da wani irin rikitaccen kallo ya bita dashi , hannunsa daya yasa ya rike kugun tahee da ta kasa motsi, a mugun fusace ya furta “are you mad “, jikin amrah rawa ya fara ganin yanda ya fusata , cikin rawar baki ta furta “dan Allah kayi hakuri yaya king, ca akai na kawo muku”, guntun tsaki king yaja yana dauke kansa daga kanta, wasu zafafan hawayene suka sakko mata,” clean that trash now”da sauri ta gyada masa tana furta “toh toh”, tattare kayan tayi waje daya Allah ya temaketa ma abun be bare ba dan a kulle yake sosai a cikin wata yar roba, tunda ya rike mata kugu ta kasa motsi sai ma shakuwar data kamata, mikewa tayi niyar yi ya kalleta, ganin haryanxu fuskarsa a hade take yasa ta furta “ru..ruwa zansha “, jinjina mata kai yayi yana kara rike kugun nata kafun ya kalli amrah da tayi nadamar zuwa wajan ya fi a irga,”jeki kawo ruwa yanxu”,da sauri amrah ta ajje tray din hannunta ta nufa fridge a tunaninta king ne zaisha harda daurayo cup dan ta bakantawa , sai taga sabanin hakan ,ruwan kawai ya karba ya balle murfin tare da kaishin saitin bakin tahee, a hankali take shan ruwan sai da ta sha sosai kafun ta dauke kanta,”baki iya gaisuwa ba “ ya furtawa amrah dake duke a kasa, da sauri ta furta “kayi hakuri , yaya king ina kwana”be amsa mata ba har tsawan mintuna biyu da ya shude kafun ya sake cewa “ni kadai kika gani “ da Sauri ta kara girgiza kai tana hadiye kukan da yake kokarin zuwan mata “ au… aun.. aunty ina kwana” dan kallanta tahee tayi kafun ta dauke kanta itama “lapiya Lou “ kawai tace mata,wani kululun bakin ciki ne ya kama amrah tana dannewa ne kawai dan ba yanda zatayi, cikin rawar murya ta furta “yaya king sai anjima, aunty sai anjima” mai gayyar ko motsawa beyi ba balantana tasa ran zai amsa ,kasa kasa take kallan tahee dan tasan tabbas da batayi mata sallama ba saukar mari zataji a kumatunta,Zata tafi ya tsayar da ita “wait”, yna nuna mata dinning “clean it up and ki gyara wajan”magana tahe tayi kokarin yi itama ya bita da kallansa , shiru tayi kawai tana sun kuyar da Kai,goge hawayan da suka zubo mata amrah tayi , shekara biyar kenan tunda tazo gidan bata ko daukan tsintsiya amma yau sai gashi tana bautawa wacce tafi tsana a duniya , kanta kawai take gyadawa, sai data wanke komai sannan ta gyara dinning su king na zaune a falo, kamar munafuka ta karaso inda suke tana satar kallan king “nagama” bece da ita komai ba sai dauka tahee da yayi kamar baby ya hau kan steps da ita.zubewa amrah tayi a Wajan tana sakin saban kukan da ya tsaya mata a makoshi”ni king zai wulakanta agaban wannan kaskantacciyar” birgima ta somayi akasa kamar wata yarinya jin Alamun kamar takun tafiya yasa tayi saurin barin part din bakin ciki da ta kaici fal ranta.
Be sauke taba sai akan gadon dakin da suka kwana, kallan ta yayi kafun ya furta “me kikeso “,juyawa tayi kamar me tunani kafun tace “kayan sa wata nake nema”, hannunsa ya miko mata ba musu ta saka nata. Fitowa sukai daga cikin dakin sai bin ko ina take da kallo ganin duk ancanza komai data sani, steps suka fara takawa a hankali,kafun ya daga ta gabaki d’ayan ta ya karasa hawa steps din da ita, bata san lokacin da bakinta ya furta wow ba tana zaro idanuwanta, yanda komai yake a tsarane ya fi burgeta ,kamar ba akasar Nigeria ba ahaka wajan ya kawatu ina kawatuwa ta yanda ko baki bazai iya fusalta kyan wajan ba,”yayi miki kyau” yanxu ma gyada masa kanta tayi, bece mata komai ba ya jata cikin white room dinsa, nan ma sakin bakintayi tana kallan dakin musamman yanda dogayen labulen suke kawanye da dakin, remote ya ya danna take a wajan tabulen ya fara bude kansa,kara zaro idanuwanta tayi kafun ta karasa wajan balcony din, ganin yanda wajan shan iskar yake da shegen kyau shima komai nashi fari ne ,kamar karta motsa a Wajan jin yanda iska ke kadata,kallan glass din da yayi wa Wajan kwawanya tayi kafun ta dan Kai hannu kamar zata tava sai kuma cikin sauri ta dauke hannunta, jiyowar da zatayi ne sukai karo dashi,sunkuyar da kanta kasa tayi cikin jin kunya sam ta manta yana wajan,hannunta daya ya kama tare da dorawa kan glass din , cikin sauri ta zame jikinta daga nasa, bece mata komai ba ya kama hannunta suka nufi wata kofa dake cikin bedroom din, babu komai a ciki sai glass na kayan sawa shake a wajan masu shegen kyau hatta fitilar wajan ta banbanta da sauran,yana dannan wani bottom gabaki d’aya wardrobe din suka bude kayansa ne shake a wajan masu matukar tsada , daga ciki kuma akwai wasu kayan matan suma masu kyau, komai na cikin Wajan na mace da namiji ne hatta kayan sawar, gefe daya ma wasu takalma ne masu shegen kyau na mace sai kuma ta kalmansa masu shegen yawa suma , komai na bukata a kwai a dakin dan lissafa su bata lokaci ne , shima dakin sosai ya mata kyau amma ganin kayan mata a cikine yasa jikin ta yin sanyi daman ta san ba santa yake ba, wasu kayan sawa ya nufa doguwar abayace purple me shegen kyau , storn din jiki sai walwali suke dauka ,kayan ya mika mata kawai tare da ficewa daga cikin dakin, kallan kayan tayi kamar bazata saba sai kuma ta saka ,kallan yanda kayan yayi mata cif cif tayi kamar an aunata musamman in tayi motsi sai storn din suma sunyi motsi dakara , gashin kanta ta gyara kafun tayi rolling din mayafi, sosai farar fatarta tafito cikin abayar da ta saka , duk da tsananin kyan da tayi murnarta koma ciki tayi dan tasan baya bawa zaiyi ba dan baya santa. Kokarin cire wa ta farayi ya shigo cikin dakin sanye da kana nan kaya farare tas dasu, gashin kansa sai faman shining suke , bin jikinta yayi da kallo kafun ya karaso inda ta ke, dago da fuskarta yayi batare da yace komai ba ya soma bata wani hot kiss a kan labba, “Kinyi kyau”ya furta ta yanda bazata jiba tagadai ya dan motsa bakinsa.
Kama hannunta yayi da kanshi ya fara nuna mata ko ina na cikin part din musamman wajan kucciyar sa da sukaje, wani irin farinciki da shauki ne ya kamata , duk maganar da zatayi itama kucciyar sai ta kwaikwayeta,bata san lokacin da ta ke dariya ba , be hanata ba saida ta gaji dan kanta kafun ya kaita dakin gym dinsa, nan sai bin wajan take da kallo kamar a mafarki, wajan swimming fool dinsa ya kaita ,kinshiga tayi wai batasan fadawa ruwa, murmushi kawai yayi ya kama hannunta da gyar tahee ta shiga wajan tana makale a bayansa take bun ko ina da kallo, gabaki daya 3rd floor da 2nd floor sai da suka zagashi, ita kadai sai faman sakin murmushi take. Tare suka sakko down stairs hannunsu sarke da na juna, kallanta yayi kafun ya rada mata “ am going out now “, cikin dan jin kunya ta furta “A dawo lapiya ,Allah ya bada abinda aka je nema”lumshe idanuwansa yayi sabida yanda yaji dadin adduar,gefen fuskarsa ya nuna mata alamar ta sumbaceshi, dan ware idanuwanta tayi akansa, shima kwaikwayr yanda tayi yayi ,kafun ya kara nuna mata , girgiza masa kai tayi alamun bazata iya ba, gyada Mata Kai yayi kamar ya hakura sai kuma ya janyota jikinsa”tunda bazaki iya ba , ni I can do it”, kokarin kwace kanta tayi ya kara matseta ta yanda bazata iya kwacewa ba,knocking din kofar akai tayi saurin kallansa ,”ana knocking” , hakan yayi ai sai su kalli yanda zanyi miki kiss din ai,dan turo masa baki tayi tare da marairaicewa, “dan Allah ka sakeni “, lumshe mata idanu yayi,”dan Allah “ ta kara karye masa murya a shagwabe , yanda tayi sai ya burgeshi kamar karta dena,wani knocking din aka sakeyi, batare da ya ankara ba ta sumbaceshi a kumatu, kasa motsiyayi sabida yanda kiss din tazo masa a bazata, da mugun sauri ta kwace kanta tagudu upstairs tana dariya kasa kasa. Kwafa kawai yayi yana bin stair case din da kallo kafun ya bude door din, zaki ne tsaye a bakin door din , yana ganin king cikin girmamawa ya gaishe shi kafin ya mika masa wasu file , jinjina masa kai king yayi yana karban files din amaimakon ya koma ciki sai ya fita shima .
**** kan gadon ta ta fada tana sakin dariya kasa kasa, ita kadai tasan yan da take san bawan Allahn nan dan ya galadima ta komai arayuwa, ya kula da ita alokacin da take bukatar kulawa, ya zauna da ita alokacin da bata san wacece ita ba, indai ba butuluce itaba be kamata ta butulce masa ba , Ada tayi alkawari bazata taba nuna masa tana sansaba ,yanxun ma Hakane amma tayi alkawarin kula dashi iya iyawarta. Wani murmushine ya subuce mata musamman yanda ta hango face dinshi dazu bayn ta gudu, so take taje ta gaishe dasu ammey amma tasan hakan ba me yuwa bace kuma bata da number ammeyn balantana ta kira ta, wayar da ya bata ta dakko tana kare mata kallo, babbar wayace meshegen tsada dukda bazata iya kiyasta kudin taba. Snap tashiga ita kadai ta dinga daukar selfie, da Wanda tayi tana murmushi da Wanda take turo bakinta,da ka karshe ma gyalan tacire gashinn kanta y zubo, sosai tayi snap din ta, duk ciki babu na banza dan bakaramun kyau hotunan sukayi ba. Shaf shaf ta kara tsaf tace dakin , ta fito ta kara gyra floor 2 duk da yanda ya kasance kalkal dashi. Kamar ta gyara masa saman sai kuma taji tsoran hawa , hakura tayi da gyarawar Daidai zata sakko down stair ta hango wata yar karamar white farar takarda,dan karamin tsaki ta saki a fili ta furta “Allah ya shiryeni “ tana daukar paper har zata saka a trash bin dan karami dake wajan sai ta fasa tare da bude ta , Rubutun da tagani ne yasata jefar da takardar zuciyrta na tsananin bugu, kara kallan paper din tayi da kyau tana karanta ta , bata gasgata abunda yake ciki ba ta dan goge idanuwanta , d same kallarce a jiki” KILL YOUR HUSBAND” shine dai still a jikin paper din sai wani dan karamin zare ja da ya fado, a matukar rude taja baya in bata manta ba ta taba ganin zaren wata mata ta jefo mata tana dariya a cikin baccinta,yanxu ma kuma ta sake ganin zaren, Bismillah tayi ta dauke zaren tare da paper harzata yardar sai kuma ta fasa ,cikin dakinta ta koma , wani dan karamin locker da ba kowane zai kula da itaba tasaka paper da zaran a cikin tare da kullewa , har yanxu bata dena mamakin paper data gani ba musamman Rubutun ciki “KILL YOUR HUSBAND” ta kara nanata kalmar, tunani take so tayi Akan paper amma komai ya tsaya mata, ganin kanta na kokarin ciwo ne yasata ajje tunanin a gefe daya ta sakko down stairs din adai adai lokacin dasu zoya suke shigowa parlorn ita da su ihsan.da gudu zoya ta rungumeta ,itama rungumetan tayi ajikinta tana sakin mata dariya , kallan su ihsan tayi da suke shigo da trays a hannunsu, “bismalla “ta furta musu binta da kallo sumayya tayi dan batayi tsammanin jin haka daga gareta ba, zama kowannansu yayi kafun ta gaishesu tana sakin murmushi, suma gaishe tan sukai dan kwata kwata basu kawo tana da saukin kai hakaba , tunanin me zata kawo musu tayi kai tsaye tanufi kitchen , wasu manya robobine masu shen kyau da girma a gefe, dan bubbudesu tayi taga garane cike a ciki, Baban trays ta dakko ta zuzzuba musu aciki tundaga kan dublan, cincin , har abunda bata sani ba saida ta zuba musu ta kawo musu, still saidata koma ta dakko musu lemo da ruwa data gani shake a fridge, binta kawai suke da kallan, tana zama ta sakar ta sakar musu murmushinta da baya boyuwa”bismilla ku”, suma martanin murmushin suka mayar mata ,
sumayyace ta furta “mungode “, yaya fa” firdausi ta dan tanbaya,cikin dan jin nauyinsu ta furta “ya dan fita” , daga nan babu Wanda ya kara cewa komai sai zoya dake faman hira da tahee cikin wasa itama taheen tana bata amsa , su ihsan sai binsu da kallo suke dan sosai suke mamakin shakuwarsu,basu dade ba suka tashi zasu tafi kamar zatayi kuka,dan ko bakomai sun debe mata kyewa,kitchen ta koma tadakko wasu designers back masu kyau ta juye musu garan da ta zubo musu,kallan zoya tayi “amma zaki zauna ko”, zaro funny eyes dinta zoya tayi ,ummey nace karna zauna akwai islamiyya yau ,amma zan dawo gobe muyi game”, Tom shikenan kizo da wuri kinji,Jini jina mata kai tayi har bakin kofar falon ta rakosu tare da mika musu bags kin,suma cikin girmamawa suka karba ko ba komai ta karramasu,”ku gaishe da mutanan gidan “ta fada tana sakin musu murmushi, suma martanin murmushi sukai mata kafun su bar part din, ganin ana kiran sallah yasa ta koma sama tayi sallanta, bataci abincin da aka kawo ba sai gyara su da tayi a dinning