Showing 42001 words to 45000 words out of 138652 words
tawa , kallan matashiyar budurwar mahaifinta yayi kafun ya kira sunanta “zahra” cikin Sauri ta amsa da “na’am dady” kallan matar yayi kafun ya kalleta, “tai maka mata”, yanxun ma cikin sauri ta amsa “toh dady”, karasawa inda take tayi ganin ta na kokarin tashi zauna ne yasa ta temaka mata,tunda ta zauna bata ce komai ba sai bin yan dakin da tayi da kallo,duk abunda ya farune ya shiga dawo mata kai cikin sauri ta zabura “taheer “ shine sunan da ta fada tana kokarin sakkowa kasa, kallan ta mutuminnan yayi kafun ya dauke idanuwansa,cikin sanyin murya ya furta “kiyi hakuri kici abinci tukunna inyaso sai muyi magana “katsetsi oumma tayi tana fashewa da kuka “bazan iya ba, ina taheer dina yake , inaso na san halin da yake ciki, su wanene ku, me nake yi a nan wajan”, kallanta mutumin yayi kafun ya soma magana cikin kamilalliyar muryarsa “ kiyi hakuri ,mune wayanda muka kadeki sati biyu da suka wuce , sannan muka kawo ki asibiti sai yanxu Allah yasa kika farka”, waro idanuwa oumma tayi “sati biyu” ta fada cikin rawar murya “kuna nufin satina biyu a asibitin “gyada mata kai mutumin kawai yayi, fashewa da kuka oumma tayi “shikenan na rasashi “, ta kara fashewa da wani saban kukan, kallan ta mutuminnan yayi idan bazaki damu ba zaki iya sanar damu wacece ke , me ya fito dake cikin dare ,naji kina maganar sunan wani da alama wani makusancinki kike Nema “, girgiza kai oumma tayi har yanxu hawayen basu dena zubaba,”zan baku labari na, sannan ina rokon ku da kumayar dani inda kuka dakko ni sabida na nemo yarona”, jinjina mata kai dattijon yayi, yayinda mace da namijin suka samu waje suka zauna suma suna binta da kallo ganin yadda take kuka ,” sunana maryam ni haifaffiyar buzuwace, ‘ya’yana biyu taheer da taheera,mijina Allah yayi masa rasuwa…………..” tundaga farkon labarin ta zuwa karshe sai da oumma ta basu tare da dalilinta na fitowa waje,sosai zahra take kuka shima saurayin da aka kira da khaleed shima sai da ya goge kwalla a idanuwansa , sosai suka tausaya mata, gyaran murya mutuminnan yayi “tabbas labarinki abin a tausaya miki ne, Insha Allahu shima yaron naki zamu binciko miki shi da yar dar Allah, amma kafin nan zansa a baki sallama sai muce gidana gabaki daya in kin yadda damu, ni sunana Alhaji kabeer mai zamani, ga babban d’ana sunansa khaleed , sai autata sunanta zahra, mahaifiyarsu kuma Allah yayi mata rasuwa, ina fatan zaki amince”, shiru oumma tayi kamar me tunani ganin bata da wani zabine yasa ta amince musu ko ba komai zuciyarta ta kwanta da su”, sosai zahra dake sharan kwalla yin farin ciki har hakan ya bawa mahaifinta mamaki, ba a dau dogon lokaci ba aka rubuta musu sallama ganin wanda ya bada umarnin sallamar, cikin kankanin lokaci suka kama hanyar nasarawa G.R.A dake Garin kano.
🫧🫧🫧🫧🫧
Sosai ya ci abincin yanaci yana babbata fuskarsa, yan matan falon sai faman satar kallansa suke ta kasn ido ganin ammi na zaune a falon , kallo daya yayi musu duk suka mike , kallansu ammi tayi, “sai ina kuma “ cikin sauri suka hada baki “ammi daman zamu je wajan abeey ne “ kallan ammi kawai tayi tare da girgiza kai , suna gita ta kallesa tare da hararansa “ka kyauta da ka koresu” bai ce komai ba lumshe mata idanuwa da yayi tare da mike wa cikin takunsa ya zauna akan kujerar da take ,kansa ya dora akan kafadunta yana lumshe idanuwa, murmushi tasaki tare da zura hannunta cikin lallausan gashin kansa tana masa tausa a hankali “ka rage hade fuskarta nan son , kullum inasan ganinka cikin farinciki kamar yadda nasan ka a baya banasan rashin fara’arka” ta karashe zance cikin karyewar murya , saurin mikewa yayi tare da kamo hannunta,”am sorry ammi na” daga nan bai kara cewa komai ba sai mama tsa mata hannun da yake a hankali, ganin bayasan hirarne yasa ta dakko wani zancen daban, sun dau dogon lokaci suna hirar duk da rabin hirar ammi ce keyi kafin yayi mata sallama, direct part din ummey ya nufa , be wani jima a ciki ba sabida be saba zama ba yana gaisheta ya fito daga part din tare da nufar part dinsa.
🫧🫧🫧🫧🫧
YOLA
“Aikin ku na kan gangara, baku da dogon lokaci wajan cikar ragowar burinku, watanni biyu ne sukai muku saura ku tabbata kun kawo jininsa,karkuyi saken da Jini biyu zasu hadu waje daya, kuna gab da tafka babban kuskure musamman idan Jini biyun nan suka kasance a waje daya “, a fusace take musu magana cikin bacin rai kafin ta dora “kun tabka babban kuskure kuyi kaggawar gyara abinda kuke kokarin batawa, baku da dogon lokaci kamar yadda kuka kawar da dan uwansa, shima ya zama muku dole Inba haka ba za kuyi kuka da kanku”tana kammala zan centa ta bace bat kamar bata taba wanzuwa ba. Ba Wanda bai razana da maganganun ta ba duk da kasancewar fuskokinsu a rufe yake babu alamar da za a gane mu su wanene, wani mutumine ya soma magana “tabbas yanxu ne ya kamata mu fara aiwatar da shirin mu, duniya ta muce dole mu mulki mutanan duniyar, dukiyar NAHYAN mallakinmuce dole mu karar da tsantsan su”……
Comment and share
Mss Lee 💖💖
Masu comment ina Godiya…..
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA
💖💖GIDAN AUNTY 💖💖
( a heart touching love story )
Story & written
By
Mss Lee 💖
PAID BOOK
Mea bukatar complete din gidan aunty yayimun magana ta wannan number 07041879581
BOOK 1
Free page 24 and 25 🦋
“Tabbas yanxune ya kamata mu cika kudirin mu”,cewar d’aya daga cikin su me sanye da jajayan kaya a jikinta, gabaki d’ayan su maida hankalin su sukai kan daya daga cikinsu wacce take kishingide tun d’azu bata motsaba, tashi tsaye tayi tana kurban wani dan abu cikin wani Kofi me kayatarwa,duk da ba a iya ganin ko wacece cikin kausashshiyar murya ta soma magana rai a bace “bazan taba laminta ba , ginin da na soma tunda dad’ewa babu wani hamshakin daya isa ya rushe munshi”,duk hada baki suwai wajan cewa “tabbas maganar ki gaskiya ce abar kauna “,suka gamawa suka fara surutunsu cikin wani yare kafin su had’a kofunansu waje d’aya alamaun cheers .
******
KANO
Kasantuwar akwai tazara tsakanin UMC da nasarawa hakan yasa saida suka danyi doguwar tafiya kafun su karaso Layin nasu, Kai tsaye daya daga cikin manyan gidajen dake Layin khaleed ya nufa,yayinda Alhaji kabeer yake zaune a dayan side din, zahra da oumma suna baya,tun bayan shigarta motar ta dukar dakanta kasa ,lokaci zuwa lokaci tana share hawayen da ke taran mata a ido, duk akan idon Alhaji kabeer da lokaci zuwa lokaci ya kan kalleta ta mudi bi, itama zahra nagefe ta zuba tagumi sosai take jin tausayin oumma da labarin ta, “ya kamannin taheer da taheeran suke “,tunda yan biyu ne zanzo naga kamanninsu nasan za’ayi kyawawa musamman yadda oummansu take da kyawu itama kamar wata balarabiya, tunanin da ke yi mata yawo akai kenan har su ka karaso gidan bata sani ba, horn khaleed yayi wani katan soja dake ganin gate din gidan ya bude tare da sara musu, babban gida ne Wanda ya hadu iya haduwa da kayan alatu komai na more rayuwa akwai a gidan, parking khaleed yayi a parking space,tare da futo wa ya bude wa mahaifinsa kofa,itama zahran futowa tayi har lokacin oumma kanta na sunkuye batasan an tsaya ba sai da zahra ta tabata,dago da kyawawan idanuwanta da suka sauya tayi tare da sakar wa zahra guntun murmushi,”nagode “,murmushi zahra tayi mata tare da bude mata kofar, fitowa oumma tayi tana bin katan gidan da kallo kafun ta sunkuyar da kanta ganin ta hada ido da Wanda yace mata sunansa Alhaji kabeer,murmushin manya Alhaji kabeer ya saki kafun yace “Bismillah “ya karasa da nufar inda zai sadashi da cikin gidan,”oumma Bismillah “ cewar khaleed da ke gefen ta ,saurin dago da idanuwanta tayi jin sunan da ya kirata da shi kafun ta soma tafiya cikin sanyin jiki zahra na binsu a baya, a cikin kyataccan falon gidan suka tsaya,sosai falon ya hadu iya haduwa, ba wani tarkacene aciki ba amma sosai ya hadu,kallan zahra Alhaji kabeer yayi “daughter kaita masauki ta dan huta” sosai zahra ta murmusa “to dady”kafun ta dauki magun mugun oumma ,kallan oumma tayi haryanxu da murmushin nan akan fuskarta” oumma bari na kaiki dakin da zaki hutu”,itama oumma dan murmushi ta sakarmata tana jinjina karamci irin na mutanan gidan duk da kallo daya zaka musu kasan masu arziki ne amma basu wulakanta taba.
Wani dan corridor suka mi’ka kadan ya Kawosu wasu ‘kofofi dake kallan na junansu,kofar karshe zahra ta bude mata , babban d’a kine a wajan,gadone me fadi sai wardrobe ,komai na set d’in gado a kwai a dakin brown colour , murmushi zahra ta sakar mata “oumma Bismillah “ jinjina mata kai oumma tayi , a sanyaye ta furta “nagode”.
🫧🫧🫧🫧🫧🫧
Sanye take cikin maroon d’in abaya A shape,kayan sosai ya fito da shape din jikinta, cikakken gashin kanta ya fito sosai ta gefe gefen kanta da ya kwanta,kwance take kan 3 sitter din falon ammi tana bacci cikin kwanciyar hankali, zoya ce ta shigo falon itama cikin shigar ta sa’banin tahee ita kananan kayane a jikinta bink colour Riga da wando, kanta sanye da pink din hula itama gashin go shin ta sosai ya fito, gashin d’awisun da ta zo nunawa tahee take ta faman wasa dashi harta nufa hanyar dakin taheen sai kuma ta jiyo ganin ta kwance tana bacci, saurin rufe bakinta tayi tana dariya kasa kasa kafun ta salallabo a hankali ta nufi inda taheen take, gashin d’awisun ta dauka ta somayiwa tahee tafiyar tsutsa a tafin kafarta, motsa kafan kadan tahee tayi kafun ta gyara wanciyarta, kara sa mata gashin zoya tayi nan ma motsa kafar tata tayi a hankali tana ya mutsa fuska,ganin hakan yasa zoya cigaba da sa mata d’awisun, cikin sauri tahee ta farka har dan kwalinta na zamewa, sosai zoya ta fashe da dariya ganin yadda tahee ta ‘bata fuskarta, itama tahee ganin zoya yasa ta mike da niyar kamota,sauri kaucewa zoya tayi tana dariya, ganin hakan yasa tahee binta da sauri, gudu zoya ta sa tana dariya tare da komawa bayan kujera, ganin hakan yasa tahee binta da gudu har dankwalin kanta ya faduwa kasa, bata damu da faduwar da yayi ba ta cigaba da bin zoya da niyar kamota ,itama zoyan ta ki bari ta kamota sai zillewa take tana mata dariya, ganin hakan yasa tahee sakin duk karfin ta ta biyo zoya da ta nufi hanyar fita da gudu gashin kanta sai faman lilo yake a bayanta, karan da tayi da abune yasata yin baya baya kamar zata fadi , batasan lokacin da ta fado kansa ba,sai daddad’an kamshin da ya cika mata hanci , da sauri ta wayo idanuwanta waje “na shiga uku ni tahee, kullum sai kinyi lefi”, saurin sunkuyar da kanta kasa tayi tare da soma wasa da yan yatsunka, dai dai ta bude baki da niyar yin magana taji an capko dogon gashin kanta me shegen sanshi da daukar ido, tanbayar da ya jefo Matane yasata zare ido “ are you a non-Muslim da zakiyi Karin gashi a kanki” ya karasa zancen nasa da sauke idanuwanka kan gashin nata, sosai sukai masa dadin a tafin hannu musamman yadda suke kyalli amma a zahiri sai kara hade fuskarsa da yayi, “ni ban kara komai ba” ta fada muryarta na rawa rawa kamar me tsoran wani abu, kara damke kan nata yayi a hannunsa da karfi,sosai taji zafin yadda ya damki gashin nata ,bata san lokacin da dora hannunta kan nasa ba tana rintse idanuwanta, hawaye ne suka fara zubo mata cikin rawar murya ta soma magana “ka..kayi hakuri”, pink lips dinta dake motsawa a hankali ya zubawa idanuwa kusan minti daya ganin tana kokarin bude idanuwan yayi sauri hankad’a ta tafadi a kasa, amaimakon yashiga cikin falon sai ya bar falon gabaki daya, bin bayansa da kallo tahee tayi tana hararar iska ,”arrogant kawai “ta fada cikin sauri kafun ta toshe bakin ta gudun kar wani yaji, mikewa tayi a hankali “ke kuma zan kamakii, sabida kisan halin kayanki shiyasa kika gudu ni kuma aka Huce akai na thank god be ganki ba”ta karasa maganar tana sakin murmushi kasa kasa tare da shafa gashin kanta “wai gashin doki”wani murmushin ta saki tunano kalamansa, lokaci d’aya kuma duk fara’ar fuskarta ta dauke tuno oumma da taheer da tayi, yau kusan sati biyu basuyi waya ba, tunanin hakan yasa ta fara tunanin yadda zata yi Waja da su wajan ammi.
4:30 ammi ce ta shigo falon bakin ta dauke da sallama , har yanxu murmushin fuskarta be ‘boyuba, kallan tahee da ke zaune ita kadai tayi, “sorry daughter na barki ke kadai “, itama murmushi tahee ta sakar mata “sannu da zuwa ammi”saida ta zauna tukun na ta amsa mata, mikewa tahee tayi da nufar kitchen bata dade ba ta fito dauke da kara min tray, lemone a ciki masu sanyi gefe guda kuma kayan fruit ne cikin wa ni dan bwol, glass cup din dake kai tahee ta dauka da niyar zuba mata kunun ayar ammi tayi saurin Girgiza mata kai “no daughter ban dade da Shan ruwana ba , bani fruit din nasha “, bata ce komai ba ta ajje cup din tare da miko mata fruit din “nagode “shine abunda tace, murmushi tahee ta sakar mata batare da ta ce komai ba , kallan ta ammi tayi sau daya kafun ta dauki banana , sai da ta kammala cin bananar kafun ta dauki wayanta, dan danne danne tayi kafun ta dora wayan a kunne ,kusan sau uku tana hakan kafun ta kalli tahee, “yau 3 days ina gwada number yaya amma bata shiga, kiyi hakuri zan kara gwada zuwa anjima sai ku gaisa nasan kinyi kewarsu “sauke ajiyar zuciya tahee tayi lokaci daya jikinta yayi sanyi dan tunda tazo ammi take kyautata mata kamar yar cikin da ta haifa, kauda maganar tayi ta hanyar sa wata jiran, sun dade suna hiran su cikin raha lokaci zuwa lokaci ammi na kara wayarta a kunne , kiran sallahn magariba ne ya tayar dasu ,ita ta nufi sama tahee Kuma ta nufi dakin ta, tun jiya take jin wani iri kamar period dinta zaizo, koda tayo alwala sai da ta duba tukunna kafun ta fito, sallahr magariba tayi bata tashi a Wajan ba har saida tayi sallahr isha bayan karatun alkuranin datayi, yau akan daddumar bacci ya dauke ta lokacin da take karatun azkar dinta.
Karfe 6:10am na safe tahee ta farka sabida ciwon maran da ta soma , sosai kafarta ta dama take mata ciwo, ban daki ta shiga domin gyara jikin ta ganin har yanxu period din be zo bane yasata yin sallah, kafarta sai faman ciwo take , asabe ce ta kwankwasa kofar daman shigo tahee ta bata sai faman yatsina fuska take, breakfast ta kawo mata yau ko hirar da suke batai ba bayan ta amsa tayi kwanciyar ta , fita asabe tayi bayan ta mata sallama tana mamakin ta, ganin ta fitane yasa tahee mikewa tare da nufar abincin, kadan tashi ta tashi aguje ta nufi ban daki, duk abunda taci saida ta amayo dashi, jikinta sosai yake mata ciwo, wanka tayi da kyar tare da saka dogon hijabi Sabida sanyin da ta keji,ko da ta fito falo bata tarar da kowa ba , ganin hakan yasa itama bata zauna ba ta nufi part din dada, tunda ta doshi hanyar zuciyar ta ke tsinkewa bata san dalilin hakan ba, ta dora kafar da niyar shiga kenan taji kukan ammi” BA’ASAN INDA SUKE BA ,DAGA ITA HAR TAHEER DIN ANNE MESU AN RASA ABUNKURE “ kalaman da suka shiga kunnanta kenan, bata san lokacin da ta kwalla kara da karfin gaske ba , kafarta da ke step na biyar ya gurde ta fado kasa Tim kanta ya bugu da jikin step din, sosai Jini ya barke mata akasan ta , kanta da ya buguma sosai yake zubar da jini , da gudun gaske sukayo kanta , tun lokacin da ta saki karar nan, ganin tahee Baje a kasan yasa hankulansu kara tashi kowa fatan da yake Allah yasa bataji me ake tattaunawa ba, wani saban kuka ammi ta saki, kaka ma ganin halin da tahee take yasata sakin nata kukan “shikenan ta faru ta kare”abunda dada ke fadan fada kenan , ummey da abeey sukai dauriyar dagowa, ganin yadda jikinta yasaki ne yasa dada sakin wani kukan” wai ina sadaukine ba bokan turai bane yazo ya dubamana amanar Allah”kallan abey dada tayi cikin fada fada ta soma magana me kuke jirane ku kira sadauki ya dubata duk kunbi kun tsare ta da itanuwa “ ta kara zancen nata da kallon su uncle salim da suka karaso suda iyalansu, sosai hankalin yan gidan ya tashi, “amma dada me zea hana a tafi asibiti kawai tunda nasan ba za a rasa king acan va” kwallar da ta zubo mata ta share maza zayed dauketa mu tafi asibitin kuma sai ku biyo bayan mu “da Sauri ammi ta mike ganin harsun nufi mota, baya ummey tashiga sai dada da tahee dake tsakiyarsu ba alamun rai , yayin da gaban motan kuma dr zayed ne da kansa zai tuka motar ammi na gefan sa, da gudun gaske suka bar gidan ganin haka yasa motoci biyu na sojoji bin bayansu, suma sauran yan gidan shiga mota sukai da bin bayansu sojoji ne take musu, aunty kawai aka bari datace ta zata taso amrah sai su taho tare, ba Wanda yace mata kala har suka taho asibitin.
Koda su dada suka shigo asibitin da gudu sojojin nan suka zagayesu kowa duk Wanda yazo wucewa sai ya kallesu, kara dialing number king abey yayi akaro na ba adadi, yanxu ma kara kiran yayi not rechable Daidai lokacin da wasu manyan likitocin asibitin suka karaso da gadon daukar mara lapiya , inda take abeey ya nuna musu, daya daga cikin doctor dinne ya