Showing 45001 words to 48000 words out of 49227 words

Chapter 16 - GUDUN KADDARA BOOK 1 Huguma

babu wulgawar masu aiki ko daya a sassan.

Da sallama ya shiga kitchen din,sallamar data sanya zuciyar sultana wani mugun bugawa,wani tsoro ya mamayeta wanda ya sanyata waiwayawa da sauri tana dubansa.

Duba biyu yayi mata ya dauke kashi yana qarasa shigowa, shigowar da ta qarawa sultana razani,ta duba hagu da dama,ba kowa a kitchen din sai su biyu rak,hasali ba motsin kowa ma a sassan sai nata da nashi,tayi wura wura kawai saita sanya gudu tana ficewa daga kitchen din. Da kallon mamaki ya bita

"Anya yarinyar bata samu motsuwar kai ba?,gudun na meye takeyi kamar wadda aka biyo?,ko wani zallar rainin wayonne?" Ya raya a ransa,sai kawai ya juya yaci gaba da takawa,takun da baiyi guda uku cikakke ba ya jiyo bibi tana doka salati,kafin kuma muryarta ta maye gurbi

"Ke!,meye hakan?,waye ya biyoki?,lafiyarki qalau?" Duka bibi ta jefa mata tambayar,tambayar da ta gaza amsa mata sai riqe bibi din kawai da tayi. Har cikin zuciyarta ita kanta tana jin yadda take gudu qwarai da gaske,bugun zuciyar da take motsawa da wani irin qarfi da batasan meye sila ba

"Matsamin ni na shiga naga wanne qaddararren abune" bibi ta fadi tana ture sultana din daga jikinta ta kuma kutsa kitchen din babu tsoro ko dis a ranta.

Cak ta tsaya saboda ganin maina da tayi a kitchen din,ita batasan ma ya shigo garin ba,dama shine ya biyo sultana din?.to me yake shirin aikata mata?, Sai ta runtse ido tana furta

"A'uzubillahi" a sarari saboda wani mummunan tunani da ya d'arsu a ranta

"Dama kaine ka biyomin yarinya?,me tayi maka?,me kuma zakayi mata?" Bibin ta fada zuciyarta tana dan bugawa.

A nutse ya waiwayo ya dubeta,cikin sakanni qalilan ya samu amsar tambayoyin da ya jima yana yiwa kansa game da kaffa kaffan bibi a kansa da yadda yarinyar ke wani guje guje. Murmushi ya subuce masa, murmushin da ya sake dada yawan fargabar bibi

"Me kuwa zanyi mata?,ko tace miki fyade nayi mata?"

"Qaniyarka aliyu" bibi ta furta tana watsa masa daquwa duk kuwa da yadda zuciyarta ke tsananta bugawa. Bai sake ce mata komai ba kamar yadda itama ta kasa ci gaba dace masa komai,saboda qafafunta sunyi nauyi kamar yadda jikinta ya sanyaya,sai kawai ta juya tana fita a dakin.

Qaramin tsaki maina din yaja,shi lamarin nasu ma sam yanzun dariya yake bashi,inda sun kwantar da hankalinsu ma sam ya fidda sha'anin sultana a ransa,duk da abun yana matuqar yi masa wani irin ciwo qasan zuciya,to amma ya ajewa ransa akwai lokacin da zai fatali da komai da kowa ya kuma gyarata koda kowa bayaso.

Tunda ta koma daki tunani iri daban daban yake bijiro mata,har ta shiga bandaki ta daura alwala ta fito duk tuntuni tayi sallar la'asar dinta sultana na maqure saman gado. Kallo daya tayi mata ta dauke kai,ai kuma shikenan,duk wani sakewa da walwala tata tayi qaura,tasan bata da wani sauran sukuni kuma.

Gefen gadonta ta zauna tana fidda numfashi. Ta soma gajiya da mugayen saqe saqen da zuciyarta keyi mata akan maina din,ta gaji da kokwanto,ta kuma gaji da bacci da ido daya,tasan kuma tunda zuciyarta ta dasa zargi akan maina ba zata taba bari ba,ba kuma zata taba bari ta huta ba.

"Gwara na kawo qarshen komai" bibi ta fada tana janyo wayarta.















*_GUDUN ?ADDARA_*

*H U G U M A*

PAGE 26


Bugu biyu rak ya daga wayar,daga can bangarensa cikin matuqar girmamawa yayi mata sallama

"Wa'alaikummus salam warahmatullah,ka yini lafiya ya aiki?"

"Lafiya qalau bibi,alhmdlh,kuna lafiya?"

"Lafiya muhammat,kamar yaushe zaka dawo?"

"Gobe ma nake sanya rai bibi......wani abune ya faru?" Kai ta girgiza

"A'ah babu komai,faduwa ai tazo dai dai da zama,Allah ya dawo dakai lafiya"

"Ameen ya Allah,amma ina fatan lafiya?"

"Lafiya qalau sai alkhairi"

"To Allah ya tabbatar"

"Ameen ya Allah" basuyi doguwar magana ba jin cewa yana cikin jama'a tayi masa sallama ya ajjiye wayar.

Qatuwar ajiyar zuciya ta sake saukewa tana ajjiye wayar,sai a yanxun takejin kamar nauyin dake zuciyarta ya fara raguwa,ta hade hannayenta biyun duka ta lanqwasa waje daya tana furta

"Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammad" sai ta maida dubanta ga sultana. Ga mamakinta har bacci barawo yayi awon gaba da ita,sai ta samu kanta tana me zuba mata idanu,ba abinda take tunawa sai nafessa,shin KO TARIHI ZAI MAIMAITA KANSA?,shin hukuncinta shine dai dai ko akwai gyara?,akwai ta inda ta kuskure?.

Duk ta inda ta laluba a zuciyarta da neman amsar tambayar sai taji ta gayawa kanta da kanta dai dai tayi, addu'a ta dinga yi cikin ranta tana sake tsananta neman zabin Allah,sai ta dinga jin tabbatuwar jin cewa dai dai tayi din.


*_THE BEGINNING_*


Hira sukayi a qalla ta kusan mintuna arba'in,irin hirar dake tsakanin uwa da danta. Su biyu ne rak a falon,dai dai sanda agogo ke tafiya a hankali har zuwa sanda ya nuna qarfe tara saura na dare

"Bibi" Sir muhammat mayak'i ya furta yana gyara zamansa

"Na'am" ta amsa masa tana dubansa

"Jiya kin kirani,kuma kiran da kikamin din nasan akwai babban dalili"

"Qwarai kuwa" bibi ta fada tana gyara zamanta

"Wato akwai wani al'amari da ya faru ranar da tafiya ta kamaka safiyar juma'a,washegarin ranar da akaga maina" gyara zamanta tayi ta warware masa komai sannan tayi shuru tana dubansa. Kai kawai muhammat mayak'i yake jinjinawa

"Shi aliyyun a gabanku ya furta wannan mummunar kalmar?,ashe aliyyu bashi da hankali har yau ban sani ba?"

"Na gaya maka ya shigo ya bada haquri,to amma ni gaskiya zuciyata har yau har kwanan gobe bata nutsu ba.....muhammat duk sanda naji motsin maina a sassana sai hankalina ya tashi,duk sanda naji maina yazo gidan nan bani da sauran nutsuwa har sai ya koma. Dani da kai da dukka sauran wanda ya rage cikin gidan nan mun sani,Aliyyu bai taba furta cewa zai aikata abu be aikatashi ba,ina tsananin tsoron sharrin zuciya,ina gudun halin 'ya'yan yau,ina kaucewa faruwar mummunan abu cikin zuri'ata,ina da tsoro muhammat ina da fargaba,kuma babu abinda zai kawo mini qarshen wannan fargabar sai abu daya....."

"Idan da raina kuma ina da iko bibi,bazan taba barin mahaifiyata cikin fargaba ba,meye abinda zai faranta miki?"

"A daura auren MAINA da SULTANA,koda har yanzu akwai qudurinsa cikin zuciyarsa,koda zai aikata din zaizo da sauqi saboda ta kasance halalinsa ce ita din".

Jinjina kai kawai aba yakeyi cikin nazari,saidai tako ina maganar bibi ta gamsar dashi,shi kansa bazaiso ace diyan cikinsa ya yiwa 'yar mammodu mummunar barna ga rayuwarta har haka ba.

"Juma'ar nan me zuwa nan da kwanaki hudu zan daura aurensu bibi in sha Allah,hakan yayi miki?"

"Allah ya albarkaci rayuwarka muhammat, ubangiji yadda kake farantamin yaci gaba da faranta maka kai da sauran 'yan uwanka"

"Ameen ya Allah"

"Amma kuma hamdiyya fa?,ina gudun kada tarihi ya maimaita kansa" qanqanin tsaki yaja

"Kada ki sanyata a sahun qalubale bibi,wancan dinma RABO NE YA RANTSE shi ya kawo komai".

Duk da ba shakka ko shayin hamdiyya ama yakeyi ba,amma haka ya dinga juya yadda zai gabatar mata da zancan,a haka har lokacin kwamciya bacci yayi,ta kawo masa tea din da duk dare saita dafa masa yasha yake kwanciya,tunda jajayen sawaye kawo yau ba tana nan da wannan dabi'a tata bata canza ba

"Allah yayi miki albarka,amma zauna zamuyi magana" ya fadi yana karbar tea din daga hannunta sannan ya kurba kadan yana ajjiyewa saman bedside drawer.

Zaman tayi idanunta bisa kansa tanason jin abinda ya sanya ya dakatar da ita a irin wannan lokacin da yace mata a matuqar gajiye yake,hutawa kawai yakeso yayi sosai

"Kin qagauta kiji meye ko?" Ya tambayeta cikin zolaya,sai ta saki murmushi tana kauda kai gefe. Tana da zafi a wasu al'amuran,ba a komai takan sanya baki ba,tana kuma da kawaici saidai a wasu abubuwan kuma bata da haquri sam ko daukan ganganci ko ba dai dai ba

"Inaso idan Allah ya kaimu juma'ar nan na daurawa danki aure" ya fada cikin halin ko in kula,kuma hankalinsa kwance kamar ba wani batu bane me muhimmanci.

A mamakance ta juyo tana dubansa,kanta yana daurewa tam

"Dana kuma?,wanne dan nawa?"

"Kina da wani shaqiqin d'anne sama da Aliyyu maina?" Ya tambayeta idanunsa cikin nata

"Maina kuma!?" Ta jefa masa tambayar ranta yana motsuwa cikin zallar shakka da mamaki

"Eh mana,amma fa kada kice zaki wani daga hankalinki,ba wani aure bane da za'a yiwa shagali ba,sultana ce kawai zan daura masa aure da ita shikenan suci gaba da rayuwarsu,sauran lamarin kuma mun barwa Allah ikonshi".

Batasan takai tsaye ba sai da taji qafafunta suna taka qasa,tamkar wadda aka daurewa jijiyon jikinta gaba daya haka taji. Aba ya daga kai ya bita da kallon yadda ta miqe din a razane

"Ko a yanzunma bai isa aure ba kaman yadda kika yi akan nafessa mahaifiyar ta?" Motsa bakinta tayi,akwai maganganu masu yawa a ciki amma sai ya sake datsar hanzarinta

"Kayi GUDUN K'ADDARA iya iyawarka,amma ka sani matuqar tana rubuce cikin littafin KADDARARKA to sai ta iskoka.......shawara daya zan baki,koda wasa kada kice zaki kwatanta abinda kika kwatanta a baya,domin qarshen wannan karon kece ba zaiyiwa kyau ba......an zana a cikin zanen qaddarar sultana maina ne yafi dacewa a daura mata aure dashi a yanzun,bansan gaba ba,bansan kuma me gaban zata haifar ba" ys qarashe jawabin yana jan blanket zuwa qafafunsa.

Kamar wadda aka dasa haka taci gaba da tsaiwa a wajen,ta gaza furta komai saboda wani bahagon yanayi data kasa tantance launinsa dake kai kawo a zuciyarta SO KO K'I?,MURNA KO BAQINCIKI?,oho itama bata sani ba......abu daya dai ta riga ta sanyawa ranta,ta yaya zata so abinda tasan wani irin ZARGE ne me wuyar kwantuwa?,sultana fa?,kaf yaran gidan a rasa waye za'a bashi sai sultana?, sultanar da tun ba'a diga samuwarta a mahaifiyar mahaifiyarta ba ta nesanta tsakanin maina da mahaifiyartata?,ta hana UWA yanzu kuma 'YA zata maye wannan gurbin na UWAR?,ta yaya hakan zata faru?.

Wadannan dama tarin wasu tambayoyin su ta dinga yiwa kanta ita qwallin qwal cikin dakinta. Batasan da waye zata tattauna wannan maganar me uban nauyi da tarin sarqaqiya ba,abun tana jinsa kamar a cikin mafarki ne kawai bawai a gaske ba,SULTANA?,MAINA?,to waye ya qulla?,......amsar dai daya ce,ta tabbatar bibi ce,da basu cimma nasara ba wancan karon shine a yanxun suka shammaceta?. Gwara nafessa sau malala gashin tinkiya NAFESSA tafi sultana nagarta nesa ba kusa ba,sultana din ALBASA CE wadda sam batayi halin ruwa ba,nafessa bata da wani aibu gabanta da bayan halayenta kaf,banda wani dalili guda biyu rak,bataga abun gufu ga nafessa ba,amma kuma sultana fa?,aibubbuka da abubuwan gudu gasunam birjik basu da iyaka

"Karki matsantawa kanki da yawa,ina kikaga hadi tsakanin maina da sultana?,ko hankali ya bada haka?,barsu suyi iyakar iyawarsu,idan suka sheqa suka samu babu qwaya zasu warware da kansu" hajiya dezatou tace da ita.

Daren gaba daya bata samu wani isashen bacci ba. Da safe da maina ya shigo suna breakfast kallonsa kawai takeyi tasan baisan abinda ke shirin faruwa cikin gidan ba,amma taji aba din yace idan ya kammala ya sameshi a baya ta gurin swimming na gidan,ta tabbatar zancan zaiyi masa.


*_TOFA MASU KARATU,AKWAI TARIN TURKA TURKA CIKIN LABARINNAN_*

"_akwai BAZATA masu yawan gaske_*

*_inason na jaku zuwa wata kyakkyawar gaba da zata zame mana tamkar tsani ko shimfida na labarin da zamu samu bigire me kyau bayan sallah da zamu dora_*

*_SHIN MAINA ZAI YARDA?_*

"_SULTANA FA?_*

*_IDAN HAR HAKAN YA YIWU ME ZAI BIYO BAYA?_*

*_AKWAI WATA MURDADDIYAR QADDARA CIKIN LABARIN,WADDA KE ZAMOWA TAMKAR WATA GUGUWA DAKE WAJIGA ZUKATANSU DA ZUKATAN MUTANE DA DAMA_*

*_AKWAI TARIN KUKA/NADAMA/SADAUKARWA/BA ZATA DA QARFIN DA QADDARA KE DA ITA CIKIN RAYUWAR KOWANNE BAWA_*

_INA SAKA RAN GOBE NA BAKU SHAFUKAN DA ZASU ZAME MANA MURFI NA LABARIN IN SHA ALLAH,MURFIN DA ZAI RUFEMU HAR ZUWA BAYAN WATAN AZUMI_


HUGUMA CE =?Q?=?Q?

*_GUDUN ?ADDARA_*

*H U G U M A*

Page 27



Kamar yadda aba ya buqata,maina bai gusa daga gidan ba har sai da ya sameshi cikin balcony dinsa dake bada kyakkyawar iska tatacciya. Yana tsaye sanye da kaftan abaya me sulbi wadda yadinta ke fadin irin kudi da tsadarta. Hannunsa duke da daya daga cikin jaridun qasar nijer din yana dubawa ta cikin eye glasses din da ya yiwa kyakkyawar fuskarsa kyau,fuskar da har yanzu kyanta bai gushe ba,kyawun kuma dake bayyana adadin sharafin samartakar da aka sha a shekarun quruciya.

"Zauna maina" ya fadi yana daga tsayen ba tare da ya zauna ba yana nuna masa kujera. Komawa yayi da baya ya zauna,yayin da aba ya ajjiye jaridar hannun nasa saman wani dan table,ya kuma goye hannayensa a qirjinsa yana duban idanun maina

"Kasan me yasa na kiraka?" Kai ya girgiza a hankali,sai aba ya saki hannayensa yana gyara tsaiwarsa

"Ranar juma'ar nan me zuwa zan daura maka aure kai da sultana,nace bari na baka labari kafin kaji a wani guri gwara kaji a bakina........don banason duk wani bore ko wani motsi na rashin amincewa,to kawai nake da buqatar ji daga bakinka" yakai qarshen zancansa yana qoqarin bude ruwan gora don yasha.

Wani yarrrr maina yaji tun daga saman kansa har yatsun qafarsa

"Sultana 'yata aba?" Ya jefa masa tambayar cikin wata murya me cike da sanyi

"Yar nafessa dai da mamuda ko?" Ya maida masa amsa kai tsaye,sai kawai maina din ya sadda kansa qasa.

Bayajin komai akan hakan,shi kawai abunne yaji ya masa banbarakwai. Dukka shirin bibi ne wannan ya tabbatar,saboda ya gama karantar takunta fes,wai ita a lallai tsoronsa take kada ya bata mata jika. Tuna hakan da yayi ya kusa sanya dariya ma subuce masa,wannan auren ai kawai wahal da kansu su aba zasuyi,baiga ma abun tada jijiyar wuya ko daga hankali ba,ya fahimci auren fakewa ko auren jingina bibi keso ayi saboda tsabar bata sadaki da batawa mutane lokaci,shi da zai wuce makaranta ma ranar alhamis kuma sai an sake ganinsa?. Wannan tunanin ya sanyashi miqewa yana fadin

"Allah ya sanya alkhairi" kawai a gajarce. Da ameen aba ya bishi,dama baya sanya ran maina din zai wani kawo matsala me yawa,ta inda ya zaci ma zai iya taurarewa saboda sabanin fahimtar da ya shiga tsakaninsa da yarinyar da qaqqarfar rashin jituwa.

Yana saukowa ama na tararsa,tun daga qafar bene na qarshe

"Me yace maka?,kaji abinda ya ballo kuma?" Tayi maganar fuskarta kwance da muguwar damuwa da rudani. Hannunta dukka biyun ya kama a nutse ya isa da ita saman kujeru ya zaunar da ita

"Zauna don Allah ama ki daina damun kanki,wannan wani game ne kawai da bibi ta shiryashi,kada ki daukeshi wani abu me muhimmanci don Allah,ranar alhamis ma ni zan koma makaranta" ganin bai daukaki al'amarin ba shima sai taji hankalinta yadan kwanta,ta sakawa ranta salama kadan,saidai kuma abun yana damunta qasan zuciya. Wai a rasa kaf gidan da waye za'a masa wannan gantalallen daurin auren sai sultananan?,yarinyar da ta gallabi kowa?,ko su kuwa basa iya controlling nata?. Saita ajiye doguwar ajiyar zuciya tana mamakin yadda suka dauko al'amarin da bazasu iya warwareshi ba,don ko ita ina bata hango wata mafita ba sai sake dagula komai.

Shirin komawa makaranta abinsa yaci gaba dayi hankalinsa kwance,don shi a wajensa wannan abun dai dai yake da buga wasanni,koma meye suka shirya oho,shidai ko meye ma a yanzun baida lokacinsa bashi kuma da plan dinsa sam sam.

Sultana kam sanda bibi ke gaya mata wai za'a daura mata aure da maina ranar juma'a maida bibi tayi kaman wata nini dinta da take wasa da ita,ta dinga qyalqyala dariya harda buga qafa,su aminata dake zaune da yasmine sai suka fita hankali ma,su kansu kallonta suke saboda yadda ta maida lamarin wani abun wasa

"Nice matar maina" ta fadi tana wani lanqwashe murya,sai kuma ta saka dariya

"Allah ya sawwaqe,tabdijan,ni kuwa me zanyi da wannan mutumin?,dan iskan me cewa zaiyiwa mutane fyade?" Duka bibi ta kaiwa bakin sultana,ta tsani jin wannan kalmar daga bakinta,tadan sameta kuwa amma baiyi yawan da za'a zuzutashi ba,ai kuwa ta bare baki ta saki kuka

"Na sake jin kin furta wannna kalmar a bakinki fasa bakin zanyi sosai,ba irin wannan shafar mai ba". Kuka tuburan ta zauna tana ma bibi,tun bibi din na shareta har kukan ya fara damunta,tanja tayi lallashi tayi lallashi har ta gaji,sai suka fahimci mafaka take nema saboda dama ranar Monday za'a karbo result na exams dinsu,tanja ta gama fahimtar kome,batayi abun arziqi bane shi yasa takeson ta fake da wannan.

A dole bayan bibin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login