Showing 42001 words to 45000 words out of 49227 words

Chapter 15 - GUDUN KADDARA BOOK 1 Huguma

Yana gama kaiwa qarshe shuru ya ratsa dakin,sai bibi dake sallalami tana qoqarin ture sultana daga jikinta

"Ashe fitinarki har takai haka sultana?,ki daure dan uwanki kiyi masa mummunan qazafi irin wannan?,sultana?,babanki maina yake fa?,shine yaci kashinki yaci fitsarinki fa sultana?,anya?" Bibi ta furta cikin wani fushi da bata taba kwatantashi ga sultanar ba.

Oncle umar kuwa waya ya ciro yayi kanta,saida oncle bashar ya tsaidashi da qyar

"Ka banni yau jikinta ya gaya mata,ta dauka duk cikin gidan ba'a iya dukanta ne?"

"Kada ku daketa" muryar maina da wani irin sauti ta cika falon. Waiwayawa sukayi suka dubeshi,har ya miqe tsaye ma abinsa

"Ba fyade tace zanyi mata ba?,to tabbas ta rubuta ta ajjiye NI MAINA SAI NA YI MATA FYADEN,zatasan me ake nufi da ainihin fyade"

"La'ilaha illa anta.......na shiga uku ni kubra" bibi ta fada da mugun qarfi tana zaro dukka manya idanunta waje,muryarta tana rawa

"Aliyyu,maina.....me kake fada!,maina!!" Ta qwala kiran sunansa sanda yake dab da ficewa daga falon. Bai dakata ba bare yaji me take cewa ya sanya kansa yana ficewa,ba daga falon ba daga gidanma gaba daya.

"Na shiga uku na lalace ni kubra,me yake shirin faruwa da iyalina?" Bibi ta sake fadi cikin rudewa da tashin hankali.

"Kinga bibi,kada ki wani dagi hankalinki fa"

"Kasan maina ne?,kasan duk furucin da zai furta yana nufin abinda ya fada din,kasan halinsa kaifi daya ne,kasan baya fada ya canza ko?"

"Ai bashi ya haifi kansa ba bibi" ama da sai a sannan ta samu fusgo tata nutsuwar ta fadi tana matsawa kusa da bibi din don ta taya su oncle bashar rarrashinta.

Duk yadda sukaso kwantarwa da bibi hankali ta qiya,hasalima kuka takeyi

"Ina tsoron halin maina na kafiya akan magana da cika magana idan ya fadeta,ina tsoron kada da gaske din ya lalata rayuwar marainiyar Allah"

"Ba zata faru ba bibi don Allah ki kwantar da hankalinki" ama ta sake fadi cikin nata tashin hankalin da rudanin.

Sun dauki dogon lokaci kafin su samu bibi ta tsagaita kukan,tace amma su nemo mata maina tayi magana dashi. Sam ranar maina din qin zama a gidan yayi,kamar yadda ya kama wayoyinsa duka ya kashe,bai kuma shigo gidan ba sai qarfe sha biyu saura na dare.

Yana shiga ama tana sanya qafafunta,tamkar dama tana biye dashi. A mamakance ya waiwayo yana dubanta

"Ama,bakiyi bacci ba?" Dubansa take da fuskarta a dinke tsaf

"Ta yaya kake tunanin mahaifiyar da d'anta yayi irin wannan mummunan furucin a gabanta zata iya kwanciya ta runtsa?" Tayi masa tambayar da salon da ya sanyaya masa jiki

"Zauna" ta bashi umarni kai tsaye. Bai musa ba ya koma a hankali ya zauna yana kallonta

"Aliyyu,ina dukka hankalinka da tunaninka suka tafi?,ina iliminka?,kasan illa da munin iqirarin da kayi?,ta yaya zaka dauki wuqa da kanka ka dabawa cikinka?" Ta dakata tana maida numfashi

"A gaban kowa kayi iqirari irin wannan?,inda kana da qanwa uwarku daya ubanka daya da ita wani ya fadi haka a kanta zakaji dadi?" Idanunsa ya runtse yana jin ciwon dukka kalaman a karan kansa

"Inaso ka janye wannan iqirarin,ka kuma baiwa bibi haquri,don banason ma zancan yakai kunnen mahaifinka,bana so kuma hakan ta sake faruwa ko da wasa"

"In sha Allah,kiyi haquri ama" ya fada a tausashe.

"Ya wuce,zan turo saddi da abincinka" ta fadi tana fita a dakin.

Ya jima zaune a wajen yana juya lafazin nasa,har zuwa sanda saddi ya riskeshi da karagar abincinsa cikin warmers na alfarma masu tsananin kyau kamar yadda yake kusan hakan al'adar ama ce,komai nata me kyau da tsada ne.

Ko kusa ko alama bata taba daukar kalmar SAI NA MIKI FYADE da ya maina ya furta din zata zame mata wani abun damuwa ko barazana ba,abinda kawai yafi mata dadi da bai taba lafiyarta ba ya juya kuma yabar gidan. Ga tarin mamakinta sai gashi a sanda dare ya fara yi kalmar tana dawo mata,ta rufe idanunta ta rungume nini da kyau ta kuma nutse a blanket dinta amma sai taji maganar tana dawo mata.

A hankali labarai akan fyade suka soma dawo mata cikin kwanya. Labaran da bata taba basu muhimmanci ba cikin rayuwarta,wasu ma ta mantasu sai gasu suna dawo mata daya bayan daya. Sannu a hankali tsoro taji ya fara shigarta. Tunda take bata tabajin tsoron kwana cikin dakin ba sai a yau,tanaso ta miqe ta fice ta tafi dakin bibi amma tsoron ya hanata motsi. Qarar rufe kitchen da tanja tayi tayi mugun kada mata ciki,sai zuciyarta kawai ta bata yaa maina ne yazo zaiyi abinda yace din,abinda ya qarasa firgitata ta saki qaramin ihu hade da hawaye

"Wayyo bibi,ki taimakeni" muryarta tanja dake niyyar wucewa taji,abinda ya dawo da ita kenan,ta murza qofar dakin ta bude,sai kawai sultanan ta sake rikicewa tana boye kanta qa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????san pillow.

Kallo daya tanja tayi mata ta lura a tsorace take

"Sultana,tanja ce" ta fada tana kamo kafadarta. Jin muryar tanja din ya sanyata watsar da nini din ta miqe da hanzari tana riqe tanjar

"Ki kaini wajen bibi" ta fadi hawaye yana kwance mata saman fuskarta.

Sosai abun ya bawa tanja mamaki,me ya sanya sultana kuka da razani haka?. Hannu ta saka ta daga sultanar

"Muje na kaiki" ta fadi ba tare data tsaya tambayarta abinda ya faru ba.

Bugu biyu sukaji muryar bibi din tana cewa su shigo. Tanja ta tura qofar ta saka sultana a gaba suka shiga.

Bibi din tana zaune saman abun sallah,da alama ta jima da idarwa ta zauna ne kawai qilan tana wani tunani na daban.

Da kallo ta bisu har sultana din ta qaraso,gaban bibi ta zauna tana kwantar da kanta saman cinyarta tana hawaye. Kanta bibi ta fara shafawa a hankali

"Nazo wucewa ne naji ihunta" mummunar faduwa gaban bibi yayi, zuciyarta ta harba tana fargabar jin statement din tanja na gaba

"Da na shiga sai naga kaman a tsorace take ta qudundune a blanket shine tace na kawota gurinki"

"Shikenan jeki tanja sai da safe"

"Allah ya bamu alkhairan" ta fadi tana juyawa ta fita a dakin ta basu waje.

Shuru ne ya biyo baya na wasu mintuna a dakin,har yanzu sultana tana kwance saman cinyar bibi. Zuciyar bibi din kuma tayi nisa wajen saqe saqen abubuwa da dama na dogon zango,sai daga bisani ta sauke ajiyar ta kuma kira sunan sultana din

"Me ya baki tsoro?" Tayi mata tambayar tanason tabbatar da abinda zuciyarta ke saqa mata.

"Ba komai" ta fada a sanyaye tana sake narkewa kan cinyarta,don ko maganar ma sai taji kamar tana qara mata razani ne. Bata qara tambayarta ba itama bibi din,sai data gama addu'o'inta sannan tace

"Tashi ki hau gado ki kwanta" zare jikinta tayi ta haura gadon bibi ta rakata da kallo tana kallon laushin da jikinta yayi.

*_GUDUN ?ADDARA_*

*H U G U M A*

Page 24


Ko washegari wani irin sukuku ta tashi,babu wannan dan banzan surutun da rawar kan da take damun bibi dashi. Komai da takeyi bibi din tana ankare da ita,haka kawai ta dinga jin zuciyarta kwata kwata babu nutswa. Duk motsin da sultana tayi idanunta yana kai. Tare sukayi breakfast da sultana din abinda ba kasafai yake faruwa ba,bayan sun gama suna zaune dai a falon suna kallo,saidai kowa da abinda ke cikin jiki da zuciyarsa.

Da muryar nan tasa dake da wani irin zurfi me cakude da kwarjini yayi sallama cikin falon bibi din. Yau din yana sanye da wasu fararen hoodie and jogger pants da ratsin gray color. Fuskar nan na fidda tsananin kwarjininsa da haibarsa, qamshin turarensa me sanyin qamshi da bashi da damuwa ko kadan ya game ko ina.

Sallamar tasa tayi daidai da miqewar sultana cikin sauri daga saman cinyar bibi. Zumbur kamar wadda aka tsikarama wani kakkaifan abu saman qahon zuciyarta. Idanu ta kafeshi da shi gabanta na bada sautin bugu,shima da idanun ya kafeta,lion eyes dinsa dinnan dake azabar cika mata idanu. Kallon da a yau ya dasa mata wani mugun tsoronsa,kalamansa kuma suka sake dawo kata fes saman kai kamar yadda suka dinga yi mata kai komo a qwaqwalwa.

Yadda suka kafe juna da idanu haka bibi ta kafe maina din da ido. Gabanta nason faduwa zuciyarta na ayyana mata abubuwa da dama. Meye dalilin irin wannan kallo da yakeyi mata haka?. Zuciyarta yanzun bata da tabbas akan maina,duk wani motsi nasa a yanzun abun ta sanya masa ido ne.

Idonsa ya dauke daga kan sultana din yana qarasowa cikin falon. Ba abinda ke dawo masa a rai irin qarfin halinta da kuma taurin zuciyarta,ta yadda har ta iya kaishi ga kwana a policestation,wannan wanne irin hadari ne da ita?,a wadannan shekarun nata da duka duka idan aka kacaccalasu gida uku baifi ta tsira da shekaru qwara hudu ba?,me zai faru a nan gaba muddin dai tana da irin wannan zarrar?.

"Barka da safiya bibi" ya furta yana zama daura da ita,abinda ya sanya sultana sake kame jikinta guri guda kenan,ta kuma lanqwasa qafafunta tana maqalewa jikin bibi,har yanzu idanunta qur a kansa,tana jin kamar ma kowanne motsi idan yayi zai iya zama cutarwane a gareta. Bata sake kuma shiga matuqar tsoro ba saida bibi ta zaunar da ita a daxu bayan sallar asubahi tayi mata irin fadan da bata taba yi mata makamancinsa ba,ta kuma gaya mata meye ma'anat fyade da har zata yiwa dan uwanta mummunan qazafi da shi,illarsa da yadda yake taba rayuwar diya mace. A lokacin ta sakejin jikinta yayi mugun mutuwa,ta kuma sake jin mugun tsanar maina da tsoronsa. Banda haka duk da sanin illarsa shi da yayi din amma yaci alwashin sai yayi mata?,dama ashe shi din DAN ISKA ne bata sani ba?. Tayi furucin fyade ne saboda gani data taba yi wata jaruma tayi cikin shirin film,kuma ta samu kubuta daga hannun jarumin.

"Lafiya qalau" bibi ta amsa masa da salon amsa gaisuwar da ba irinta suka saba ba

"Tashi ki bamu guri" maina ya fadi yana maida dubansa ga sultana dake masa kallon Allah ya tsine uwar me qarya,kallon da yayi kama da kallon ban sanka ba, yau na fara ganinka

"Ki nemi hijabi ki saka" bibi ta fada tana bin sultana da kallo wadda ke sanye da wando da 'yar Short sleeve shirt wadda ta bayyana santala santalan damtsenta. Maganar ta sanya hijabin sai maina ya gaza fahimtar me ma'anarta?,da bai gane ba sai ya share batun ya dubi bibi din bayan sultanan ta iske daki

"Haquri nazo na baki akan furucina na jiya,kiyi haquri,ba kuma ina nufin hakan har raina ba,kuma ba zan sake lafazi makamancin wannan ba" idanu bibi ta gwalalo tana dubansa

"Wa?,ai tsohonka kadai nake jira ya dawo yayi mana shamaki,ni zaka yaudara aliyyu?,kaman bansan halinka ba?,kafiya taurin kai da naci akan dukkan abinda kace zakayi?,ni zaka yaudara da kalaman ban haquri?, tabdi.....bazan taba yarda ba" bibi ta fada tana kada yatsanta dan manuni.

Shuru kawai yayi yana kallonta har ta kammala,sai yadan lumshe idonsa ya bude yana dubanta,can qasan maqoshinsa yana qoqarin hadiye bacin ranshi,donshi a son ranshi banda bin umarnin ama ma bazaizo wani bata haquri ba saidai aje a haka

"Ki yarda dani,da gaske nake baki wannan haqurin bibi" ya maimaita yana kafeta da ido. Dubansa tayi cikin idanu na wasu sakanni,kamar zatayi magana sai kuma ta fasa,ta juye da rufeshi da masifar da yayi imani sultanan ya kamata ta yiwa ita amma tazo shi ta balbaleshi da ita.

Har tayi ta gama bai sake ce mata kanzil ba,sai data sauke sannan yace

"A bani breakfast"

"Yau bamuyi da kai ba"

"Nasan hanyar kitchen" ya fada yana miqewa hadi da gyara zaman rigar jikinsa ya soma takawa

"Kaga,nifa yanxu ina da diya mace da nake raino nan sashen,ba kowanne lokaci ya kamata ma ka dinga shigomin ba,ko zaka shigo ma ka dinga neman izini saboda mu kintsa" cak ya dakata da tafiyar,ya waiwayo yana duban bibi din yana jin maganar nayi masa banbarakwai.

Wata irin dariya mara sauti ce ta subuce masa,sai kawai ya cije lips dinsa yana kada kai. Wai dukka akan sultana take gaya masa haka?,sultana ce wai har za'a kira budurwa?,sultanar da tasan hanyar club tasan hanyar hotel wai yanxu ita akewa kaffa kaffa?,bama haka ba.....shi tasa lalacewar ma ta rasa ina zata qare sai akan wannan qaramar halittar?,ya baro manyan mata da komai yaji a hostel,suna kiransu ma free of charge,matan abzinawa,shuwa da fulani masu shegen kyau da baijin duk kyau irin na sultana zata bude musu idanu tunda nata bai riski 'yammatanci ba,su basu tsone masa idanu ba sai sultana?.

Har zai biyewa bibi din sai yaga ma bashi da lokaci,ya sanya kai kawai ya wuce kitchen din abinsa.

Har ya cinye asabar da lahadinsa baima sake haduwa da sultanan ba. Litinin da sassafe ama ta sakashi a gaba akan ya koma. To shi dinma dama ranar yayi niyyar komawar,don haka ya tattara ya nasa ya nasa ya koma din.

Kamar jira sultana din takeyi dama ya tafi sai ta warware ta koma halayyarta. Sau tari idan ama na veranda dinta tana hangenta ta farfajiyar gidan tana wani iya shegen saidai kawai taja tsaki

"Allah ya shirya". Tana hangen abubuwa da yawa da yarinyar ke dashi wanda sauran sa'aninta a gidan basu dashi. Amma mugun gata da saken da ake bata a gidan ya hana komai ma tasiri.

Bata sake shiga taitayinta ba sai ranar da ya sake zuwa hutun kwanaki uku. Shi zam baima wani lura da yadda take mugun gudunsa da d'ari d'ari da shi ba sai a wannan zuwan da yayi,d'ai d'arin da shi baima fahimci akan meye takeyi ba.

A hankali bibi ta fahimci komai,rashin sakewar sultana din a duk sanda akace yau maina ya sauka a gidan,abunda ya dinga taba ranta kenan,ta dinga jin babu dadi. Hakanan zuciya ta dinga yi mata saqe saqe kala daban daban cikin ranta. Kwata kwata itama bibi din sai ta dinga rasa nutsuwarta idan yana nan din,a hankali itama sultanan saita daina kwana dakinta duk sanda maina yake gari,idan kaga ta koma dakinta to baya nan ne ya koma makaranta.


*********K'arfe hudu na yammacin ranar,ranar da gidan ya kasance akwai qarancin jama'a,saboda kusan duka yaran gidan sun wuce islamiyya idan ka dauke sultana dake kitchen din bibi a dai dai lokacin. Oat takeson sha amma kuma tanja bata kusa,ita kuma baya ga tanja din bata yarda kowa ma yayi mata komai a gidan sai bibi. Bibi a lokacin bacci take,ita kuma ta matsu da tasha din,abinda ya sanya ta shiga kitchen din kenan ta dinga hada kwabarta.

A qalla babban gwangwanin oat da qatuwar gwangwanin madara ta kusa juyewa cikin bowl,ta kammala tayi tsaye riqe da qugunta tana tunanin yadda zata tafasa ruwan zafi. Tana dari dari saboda tana tsoron wuta,tana kuma iya tuna yadda ruwan zafi ke mugun tururi duk sanda tanja ta saukeshi daga saman gas.

Bacci yayi me nauyi a yau din,saboda muguwar gajiyar dake jikinsa sakamakon training da sukayi duka wancan satin babu hutu,wannan dalilin ya sanya yana samun interval na kwanaki a wannan satin yayo gida,yasan a nan dinne kawai zai huta sosai,kanshi yayi fresh yadda ya kamata,babu me takura masa,koma bayan hostel da ba lallai su sultan su barshi ya huta ba su da gayyar abokansu.

Dispenser dinshi babu ruwa ciki,don haka ya zura jallabiyyarsa me sulbi 'yar marocco ya sauko ya fito daga dakin.

Tun azahar yasan ama bata nan,don tana da taro na musamman a qungiyarta data bude don taimakawa mata iyayen marayu da zauwara,wannan dalilin ya sanyashi wucewa kai tsaye sassan bibi.

A falo yayi sallama,tunda yaji shuru yasan bacci ne ya sace bibi din,sai kawai ya wuce kai tsaye ya kutsa zuwa kitchen yana mamakin yadda yau sam

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login