Showing 39001 words to 42000 words out of 49227 words

Chapter 14 - GUDUN KADDARA BOOK 1 Huguma

gilmawar walqiya,tamkar kuma gizo sultanar taga saukar mari kan fuskar maina. Tayi muguwar razanar da har sai data miqe daga saman kujerar da take zaune a kai

"Koma ki zauna,ai tunda kike nan tu es en s?curit?,bai isa yayi miki komai ba,mara gaskiya kawai,ba daka mata tsawa da hanata tona maka asiri zakayi ba,d?fendre kanka zakayi kaima indai kai me gaskiya ne,ka gaya mana a ina ka santa?" Koda yana da nufin masa bayani bayajin zai iya buda bakinsa a yanzu,domin wata irin wuta ce kai kawo tsakanin qirjinsa zuwa bakinsa,wani irin kallo yake jifan DPO din dashi da idanunsa da sukayi jazur kaman an masa kwalli da borkono.

"Wannan bashi da gaskiya,ku sakamin shi a bayan kanta" ya fada cikin bada umarni. Bai hanasu yi kasa komai ba don yasan kowanne motsi zaiyi a wannan lokacin to tabbas zai iya daukan mummunan hukunci akansu gaba daya saidai duk abinda zaya faru ya faru. Takalminsa suka karba agogonsa da wayoyinsa dukka suka kashe. Yana tsaye daga dakin yana kallon yadda suka rufe sultana suna mata sannu hade da sake dubata

"Ki rakata gida aicha" DPO din ya fada

"A'ah zan iya tafiya" ta fada da sauri tana satar kallon inda suka rufe maina

"Idan aka ganni da ku kowa ma zaisan me ya faru,banason mamana ta sani hankalinta zai tashi"

"Shikenan,ku kaita bakin layi" ya fadi yana sanya hularsa gami da miqewa.

A hanya sam batajin me suke cewa sai tunanin abinda ya faru a station din. Ranta ya danyi mata rashin dadi da kulleshin da sukayi,so tayi ace tunda Allah yasa sun rama mata mare maren da tasha a hannunsa su sakeshi hakanma kadai ya isa.

A bakin layin nasu suka ajeta ta taka har zuwa gida da qafarta. Tana shiga farfajiya ta biyu ta sami su lamira. Dukkansu sukayo kanta

"Su zinnira sukace wai yayankine ya tafi dake,sunce kaman yaa maina,amma shi kuma baya nan,ina kikaje har akayi aka gama baki wajen anata cigiyarki?" Kusan a jejjere suka dinga jefa mata tambayar

"Yaaya Samaila na raka wajen budurwarsa(wani dan aminin oncle bashar ne" itace amsar data basu kenan tana wucewa sashen bibi ba tare data tsaya jiran labaran da suka qullo zasu bata ba,don babu abinda labaransu zasu qara mata ta sani sai zallar bacin rai,tunda dai maina din da basusan da zuwansa ba ya bata mata ranar gaba daya.

"Allah ya sakamin" kawai take fadi duk sanda ta tuno burin da taci akan ranar amma ya wargaza komai

"Allah yasa ya sake musu taurin kanshi su sake lallasashi yadda ko ya dawo gida zai barmu mu sarara" ta kuma fadi sanda ta tube kayanta ta shiga wanka.

Wankanta tayi abinta ta shirya tsaf kamar ba abinda ya faru taci gaba da sabgoginta. Duk sanda ta tuna ya maina din yana kulle a station sai taji dariya tazo mata,musamman idan ta tuna zafin kansa tsananin tsaftarsa da qyanqyaminsa,yau ya zaiyi dasu?.

Ba wanda ta gayawa sai lamira yasmine da aminata

"Kuma wallahi wallahi naji zancan a bakin wani ko?,ni kadai nasan me zanyiwa mutum" ta fada tana zare fararen idanunta

"To waye ma zai fada?,can tsakaninku,amma ki sani wallahi duk ranar da yaa maina ya dawo taki ta sameki kin shiga uku,don wallahi bazai qyaleki ba" cewar aminata.

Duk da maganar aminata tasan gaskiya ne ta kuma ratsata amma saita murje idanunta. Dare ya fara yi tana jin bibi ta fara cigiyarsa amma tayi kunnen uwar shegu,sai ma ta nade abinta cikin blanket din da tasa tanja ta kwaso mata daga daki.

Kasa jurewa bibi tayi ta soma neman wayarsa tana fadin

"Yau kuma ina Aliyyu ya tsaya,shi da bame yawon dare ba,ba kuma wani tarin abokai gareshi ba bare nace su suka riqeshi?" Tabe baki sultana tayi tana sake cusa kanta cikin blanket

"Yau dai shalelen naku dan baqar zuciya sai kwanan magarqama" ta fada qasan zuciyarta tana lumshe idanunta hankalinta a kwance.

Tana nan a kwance ama ta aiko itama nemansa,bibi tace bata ganshi ba tunda ya fita itama nemansa take,ga dukka wayoyinsa a kashe, ba'a rufa mintuna arba'in ba ama din ta kasa daurewa ganin dare yana yin nisa ta shigo da kanta,don itama ta gaza samunsa,ta kuma tambayi su goumar ba wanda yasan ina yake.

*_GUDUN ?ADDARA_*

*H U G U M A*

PAGE 22


A hankali dare ya fara nisa ba maina ba dalilinsa,sun gwada wayarsa fiye da sau shurin masaki amma ba wani respond. Tun sunayi iya su yasu har aka saka mazan gidan iyayensa. Allah yasa aba yana gari.

Abun ya dagi hanakalin kowa saboda ba halinsa bane yin nesa da gida haka,musamman idan yana gari baya wuce sallar isha'i a waje. Sai gashi yau din har ana tunkarar biyun dare ba maina ba wayarsa ba kuma motsinsa.

Tuni sultana tayi nisa a duniyar bacci abinta,hankalinta kwance tamkar ma bata da masaniyar komai akan lamarin,koda wasa bata nuna tasan komai ba,kamar yadda su aminata suka zuba idanu suga qarshen abun. Sunsan dai qila lokacin yankewa sultana mummunan hukunci ne yazo cikin gidan.

Dukkaninsu kwanan zaune sukayi a falon bibi cikin tashin hankali. Har safiyar lahadin ba wani motsinsa ko labari,abinda ya sake tashin hankulansu

"Zaman nan bazaiyiwu ba yaaya,inaga ya kamata muyi report policestation daga can mukai cigiya gidajen radio da television,wannan shirun ba na lafiya bane" oncle umar ya fada yana miqewa

"Hakan shine zaifi dacewa,zamanmu a nan ba abinda zai maganta" oncle bashar shima ya fada

"Amma sanda ya fita bibi,baice muku zaije wani gurin ba bayan karbo dinkin?" Aba ya fadi yana duban bibi

"Nace masa dai inason nama wajen yahaya"

"Bayan can fa?bakiyi saqo ko ina ba?,don mun duba yahaya din yace yaje amma bai samu naman ba ko fita a motar baiyi ba ya juya"

"Indai haka ne to wajen yahuza nasan zaice zaije ya samomin" bibi ta fada da sauri hankalinta yana kawowa

"Shikenan,bari mu bincika can din,daga nan idan bamu samu komai ba akai saimu qarasa policestation din mu bada cigiya". Da wannan shawarar oncle bashar da oncle umar suka fice,yayin da sukaci gaba da zaman dakon jiran abinda zai faru cikin gidan. Sultana nacan kwance tana sheqa baccin safiya hankali kwance,tana jin kamar ta fidda qaya daga gidan.

Suna isa yahuza yana qoqarin wanke gurin sana'ar tasa. Duk da bai sansu ba amma yana ganinsu yasan cewa manyan mutane. Cikin rawar jiki yayi musu iso zuwa cikin ainihin rumfar tasa

"Akwai yaro Aliyyu dake zuwa wajenka siyan nama"

"Aliyyu?" Ya fada da dan tambaya

"Eh,maina ba" oncle bashar ya maimaita mishi

"Oh to....naji naji,jikan bibi.....aiko jiya ma yazo gurin nan siyan mata nama"

"Yauwa,madalla,abinda mukeson ji kenan dama,yaushe yabar wajen?,don tun jiya bai koma gida ba" zaro ido yahuza yayi cikin tsoro

"Bai jima ba na sallameshi,ya matsa kusa da policestation dincan yace zai dauki abun hawansa,duk da naga jama'a da dama a wajen,da alama wani case din aka kawo ko wata rigimar akeyi,don naji mutane na zancan an kama me fyade da satar mutane" yahuza ya zarce da bada bayanin da ba'a tambayeshi ba

"Akwai policestation kenan anan kusa?" Oncle umar ya tambaya. Jinjina kai yahuza yayi

"Gata can" ya furta yana musu nuni da ita". Waiwayawa sukayi dukkansu suka kalleta. Oncle umar ya fara miqewa

"To ai ta kwana gidan sauqi,inaga saimu qarasa mu bada report tunda dai bincike ya nuna daga nan guraren aka rasa kuma ina yayi"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,Allah ya bayyana,Allah ya bayyanashi" yahuza ya furta cikin madaukakin jimami,duk da yanaji a jikinsa bawai bata maina din yayi ba,yafi kyautata zaton kawai ya tafi shan iskarsa ne,tunda ta yaya sankacecen matashi majiyin qarfi irin maina din za'a iya saceshi kamar wani kaya?.

Tare suka gangara a qasa har zuwa cikin policestation din suna tattauna yadda zata kasance. Sanda suka isa gurin 'yan sanda hudu suka taras saman kanta suna hira abinsu.

"Cigiya mukazo bayarwa na yaronmu da ya bata jiya" oncle bashar ya fada yana kallon dan sandan

"To bismillah,ku zauna yallabai" ya fadi cikin girmamawa saboda kwarjinin da sukayi masa,uwa uba kuma dukka alamu sun nuna cewa su din wasu manya ne cikin nijer din.

"Kai......sanda.....zo ka taho mini da abun rubutu,oga yace wannan yaron idan aka kai azahar baice komai ba a fara tuhumarsa,don ya fuskanci girman kai aggareshi me yawa,sai an sauke mishi shi" dan sandan da ya bawa su aba masauki ya fada da qatuwar muryarsa me kauri da cika kunnuwa.

"Ya lamarin ya kasance yallabai?,inajin da kaina zan shiga na daki yaronnan yadda yakewa mutane gani gani tun jiya,yaqi bada tarho din kowa bare a nemi yan uwansa,da alama dai da gasken bashi da gaskiya"

"Ku dinga bi a hankali dai"

" Ranka ya dade?,barawon mutane kuma dan fyade za'a bi a hankali?"

"A'uzubillahi" aba ya furta yana jin laifukan sunyi girma da yawa

"Wallahi yallabai,yaro da duka duka bai wuce shekara ashirin da biyar ba amma ya iya tara manyan laifuka haka,bari ka ganshi yallabai.......kai sanda,fito da yaronnan,a sake gwada bashi abinci a waje tunda yaqi ci ata ciki kada ya mace mana ya jawo mana masifa" ya fadi yana duban hanyar guraren,sannan ya dawo da hankalinsa ga littafin statement yana qananun mitoci

"Allah ya sawwaqe,Allah ya kyauta" aba ya sake fada kawai yana sauraren statement din da oncle bashar ya fara bayarwa.

Kalaman oncle bashar ne suka maqale masa a maqoshi sanda ake shigowa da maina gurin

"Uban waye ya kawo mana yaro ya daure mana shi?,uban me yayi?" Oncle bashar ya fada cikin matuqar zafi da zafin zuciya yana duban dan sandan da wani irin kallo da ya sanyashi yasha jinin jikinsa

"Ah......yallabai ai shine barawon mutanen kuma dan fyaden"

"Rufemin baki shashasha!" Oncle umar gwanin zuciya ya fada da wata mahaukaciyar tsawa

"Ku kwance masa hannu ku bashi takalmansa"

"Yallabai...... yallabai bari a kira DPO"

"Kayi hauka ne?!" Oncle umar ya sake fadi a fusace,fusatar data tabbatarwa da dan sandan lallai akwai abinda oncle umar din ya taka

"Omar......yi a hankali mana,a hukuma kake fa" aba da ya dafa kafadarsa ya fadi cikin tausasawa,kasancewarsa mutum me nisan zangon daukar zafi

"To 'yar gidan uban waye zai yiwa fyaden?,uban waye kuma ya sata?,wanan da alama baisan FAMILYN MAYAK'I ba" Oncle umar ya sake maimaitawa a fusace yana duban aba

"Ka bari dai ayi komai a nutse......yallabi ku kira DPO din"

"Okay sir" dan sanda da jinin jikinsa ya kusa daskarewa tunda aka furta mayak'i family ya fadi da rawar jiki yana saluting aba,don sai a sannan hankalinsa ya dauko masa hoton fuskar waye aba din.

Har dan sandan yaje ya musu iso wajen dpo ya dawo maina baice komai ba sai kansa dake qasa,duk kuwa da tambayoyin da oncle umar keta jero masa

"Ka gani ko yaya?,baya magana fa,Allah muddin wani abu ya sameshi dasu da wanda ya kawoshi nan din sai ya raina kanshi"

"Muje dai Omar " aba ya fadi yana sanyasu a gaba.

Aba din yana shiga DPO din ya miqe cikin mamaki

"Barka da zuwa yallabai,yau kaine da kanka a office dina?,bismillanku" murmushi kawai aba din yayi,yaja kujerar ya zauna sannan su oncle bashar suka zauna,banda maina dake a tsaye bashi da ko alaman tsaiwa,don bai qaunar dogon zama sam cikin office din mutumin,shi daya yasan me yakeji a zuciyarsa,shi kansa din ma bazai iya tantancewa ba. Bayason kallon fuskar mutumin sam,saboda tana tuna masa da mummunar lafazin da suka jefeshi da shi shida sultana,tana tuna tozarcin da yayi masa irin wanda ba'a taba masa irinsa ba tunda ama ta kawoshi duniya

"Kada dai ace wannan yaronka ne?" Dpoya fada yana nuna maina

"Eh yarona ne,nazo kawo cigiyarsa kuma muka sameshi a nan"

"Subhanallahi" tiryan tiryan ya gaya musu yadda komai ya faru,sannan ya dora da cewa

"Yaqi bayani ne yaqi fadin komai,ko kare kansa wallahi yaqi yayi,bansan ba mara laifi bane tunda baiyi yunqurin bawa kansa kariya ba"

"Amma yarinyar wace a ina kuma take?"

"Bansani ba tunda baiyi bayani ba amma dai ga unguwarsu ga kuma hotonta mun ajjiye report saboda gaba" ya fada yana miqa musu wani file

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,sultana ce,'yaruwarsa ce ai,'ya take a wajensa" oncle bashar ya fadi,yayin da aba da kuma oncle umar suka bushe a wajen suka kasa cewa komai.

Shuru dakin ya dauka na wasu sakanni,a nutse aba ya daga kai ya dubeshi

"Meye ya hada haka da ita?,a ina ka daukota?" Sai a sannan yadan motsa kadan daga tsaiwar da yayi kamar an dasa itacen bishiya,rayukan 'yan maza ne a dugunzume ainun. Dpo din ya fahimci muddin yana wajen bazaiyi magana ba,su dinma sun fahimci hakan,saboda haka oncle bashar yace

"Maganar nan ta gida ce yaaya"

"Gaskiya dai" DPO ya fadi. Dukkansu cikin mamaki da juya lamarin suke dukka su ukun,har zuwa sanda DPo da kansa ya rufe case din,ya kuma tattara musu dukkan wani document da ya shafi case din suka fice da shi.

Ba wanda suka yiwa bayanin inda suka samoshi,saidai oncle umar daketa banbamin fada kaman zai ari baki,daga qarshe kuma

"Zataci qaniyarta sultana wannan karon" har yanxun maina din bai cewa kowa uffan ba,don bayajin bakinsa zai budu har wasu kalamai su iya fita.

Jikinsa dukka radadin cizon da sauro ya kwana yana masa a jiya,uwa uba tsabar tsantsami ya sanya yake masa qaiqayi jikin nasa,don haka ya hada ruwa me zafi yayi wanka bayan ya watsa kayan jikinsa a dustbin,duk tsadarsu bayajin zai iya sake amfani dasu.

Shi daya suka bari a shiyyar tashi,don yace yanason ya kwanta ya huta,ko abinci da ama tayi masa tayi cewa yayi baici ya qoshi. Da gaske bayajin abincin zaibi ta maqoshinsa,da bibi ma ta aiko dashi sawa yayi aka maida mata,ya rufe qofofinsa ya kwanta yana fatar yayi baccin da bai samu yi ba a daren jiya.

Bayan ya kwanta din labari ne yasha banban. Duk inda ya runtse idanunsa ya juya ba abinda idanu da kunnuwansa ke jiye masa sai kalmar SATONI YAYI,FYADE ZAIYIMIN.

"la haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem" ya dinga maimaitawa. Futucin yaqi barin kunnuwansa......Ga tarin mamakin sai yaji wata siririyar qwalla na fito masa ta gefen idonsa guda daya.

Hannu ya sanya ya shafosu yana kalla,shi kam iya tsahon wayonsa da girmansa ya mance yaushe ne lokaci na qarshe da ya ga hawaye cikin idanunsa haka. Duk da ya karbi horo na sajoji masu matuqar wahala da azaba,amma basu taba sakashi dar ba bare damuwa har akai ga qwalla,sai gashi yau furucin sultana ya karya zuciyarsa har haka?.

Haka ya wuni ya kwana,saida tursasawar ama yaci abinci zuwa dare

"Wai ina ka bace?,me sameka da wannan mummunar damuwar take bayyana kan fuskarka?" Ta tsareshi da tambar tana kallon fuskarsa. Har ama din tayi ta gama itama bata samu amsa ba hakanan ta haqura tunda ta samu yaci abincin.

Sultana kuwa tunda taji yaa maina ya dawo gida ta koma tamkar kazar da aka jefa da wuqa,wato kenan tasan wa'adin kwanakin rayuwarta a duniya qididdigaggu ne. Dukka saita tsargi kanta,ta rasa dukkan wani sukuni da walwala,ta yiwa kanta iyaka da kuma shamaki iya dakinta kadai.

Tayi tsammanin games dinta da su nini zasu debe mata kewa,amma kowanne sai taji baya yi mata dadi,idan ta dauko game din sai taji batayi mata ba saita watsar,idan ta dauko nini din ta rungumeta kaman yadda takeyi a baya sai taji ta isheta itama saita ajjiye ta koma ta kwanta. Haka ta dinga juyi kafin daga bisani aminata da lamira suka leqo suna mata dariya tare da sake gaya mata tabbas ya maina fa ya dawo

"To sai me?, mala'ika ne shi?,yayita dawowa,nidai ko banza ai an rama min marina" ta qarashe fada tana murguda baki sannan ta juyar da fuskarta zuwa bango abinta.

**_GUDUN ?ADDARA_*

*H U G U M A*

Page 23



W A S H E G A R I*


Idan ka hango yadda ta takure a quryar bango ta kuma cukuikuye cinyoyin Bibi saika dauka mala'ikan daukan rai ne daura da ita. Idanunta sunyi tsilli tsilli sanda maina ke maimaita yadda komai ya faru da wata iriyar saryayyar murya. Dukkansu suna wajen banda aba da tafiya ta kamashi niamy da sassafen. Idanunshi basu kan kowa saboda suna cike ne da wasu al'amura da shi kansa baisan iyakarsu da nauyinsu ba. A karon farko da yaji yarinyar ta fice masa fit daga kanshi gaba daya.

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login