Showing 21001 words to 24000 words out of 24389 words

Chapter 8 - YAR ZAMAN WANKA BOOK 2

22 Aug 2025

155

fito daga cikin motar idan ba ku yi saurin fitowa ba sai dai ku ga na maida samanta ya zama a ƙasa ƙasan kuma ya zama a sama" Da sauri suka fara fito su duka a layi kamar masu neman taimako, sai da suka fito su duka suna karkarwa Inna ta dubi ɗaya wanda ya ƙulle mata ido ya danne mata baki ganin ya yi wujiga wujiga kamar an tsamoshi a ruwa ta ce.

"Tabɗi wai kai nan wuya ce ta sa ka yi tsuru -tsuru ya wannan? Dole mana ka jigata ka ji damƙa kamar a sanyawa akuya dabaibayi, tare da datsa maka haƙori masu tsini dole ka ji jiki ai daga jin cizon ma ya wuce na bil adama ko ba haka ba?" Ta faɗa tana kallonsa kai ya shiga gyaɗawa kamar ƙadangare, ya ce

"Hakane iya aljana" Ya faɗa a fili a zuciyarsa kuma ya ce.


"Wallahi ji nake kamar hannun ba a jikina yake ba"

wannan haƙorin naki me tsini kamar mashi, ai daga ji ma ba na bil adama bane, sai dai naku aljannun"


"Ku zo nan kowa ya yi kamun kunne yau kowa sai ya faɗawa aya zaƙinta, yo ina dalili za ku mini cali-cali kamar wata gawa, haka kawai da raina ban mutu ba ku min kama -kama, ina ji ina gani, ai na muku ma da sauƙi"

Haka ta sanya su suka kama kunne tsoro kuma kamar farar kura kowa ji yake kamar ya tashi ya zura da gudu saboda tsananin tsoron ganin gashi ga aljana.

Haka Inna ta sanya su a gaba ga magriba ta kawo kai amma duk wanda ya yi wani motsi sai ta ɗaga dorinar ta zabga masa sai dai ka ji sun saki kuka kamar ɓeran daji. Babban nasu ne wanda shi ne direban da ya yi motsi sai Inna ta daddage ƙarfinta ta zabga masa dorinar har sai da ya durƙushe sannan cikin sauri ya tashi ya kama kunnensa.

"Kai dalla ka yiwa mutane shiru ragon banza da wofi, yo Allah na tuba da ƙarfinmu na aljannu na dage na dake ka ai da sai dai gyatumarka ta haifi wani, Allah na tuba jika dai jibgege amma mazaƙutar yara gareka abu kamar lagwanin fitila, in banda ma larura me zai sa ni taɓa jikinku ai ba zan iya ba ma, Allah tsari gatari da saran shuka".

A can wajen Ogansu kuwa sai jiran zuwansu yake amma shiru kake ji maye ya ci shirwa, yana shirin kiransu a waya sai wayar me gadin nan da aka ɗakko daga gidan da za sato tsohuwar nan, ta yi ƙara Ogan nasu ne ya ɗaga kiran dan dama a hannunsa wayar take, ganin an sa Hajiyar Alhaji, sai ya ɗaga aikuwa ya ji muryar tsohuwa tana cewa.

"Wai me gadi ina ka shiga ka barwa mutane get a buɗe" Cikin mamaki Ogan nasu ya cire wayar daga kunne ya kashe ta, jin maganar matar da ya sanya a kamo mamaki ma ya hanashi magana a take ya ɗaga waya ya kira wayar direban su Baaba aikuwa wayar ta shiga ringing Inna ta ɗakkota a mota ta kawo wa direban ta miƙa masa, yana ganin sunan Oga ya ɗaga da sauri Ogan ne ya fada magana


"Kuna Ina ne?" Ogan ya faɗa cikin ɓacin rai dan yana ganin sun raina masa hankali sun ce sun kamo tsohuwar a gidan amma gata tana waya.

"Oga gamu a nan dokar daji za mu ƙaraso kuma Allah bai yi...

"Dallah rufe min baki, ashe ku duka, dukan iska ne, kai banda sha ka tafi ne me yasa baku ɗakko matar nan ba ka ce kun je gidan kun ɗakko ta?" Oga ya katse masa magana tare da bashi labarin wayar da suka yi da matar a wayar me gadi.

Wannan maganar da Oga ya faɗa musu a waya da yake handafree aka kunna kowa yana ji, a take suka fara maƙyarƙyata dan hakan ya tabbatar musu cewa Inna aljana ce.

Jikinsu ɓari ya shiga yi suna ta kuka tare da baiwa Inna haƙuri.

"Oga ba yin kanmu bane wallahi ashe angamo muka yi muka ɗakko aljana ka ganmu sai wahala take bamu kamar an aikota ga ƙarfin bala'i kamar raƙumi, ban da ma da kwananmu a gaba ai da sai dai wasu ba mu ba" Cewar direban a zuciyarsa a fili kuma ya ce.



"Oga iya ce muka ɗakko kuma za mu maidata gidan"

Mahaukata kawai" Ya faɗa yana jan tsaki tare da kashe waya,dan shi bai san cewa aljana suka ɗakko ba. Sai da Inna ta basu wahala sosai dan har goyo -goyo ta sanya suka rinƙa yiwa junansu.

"Da kun san ni bil adama ce na san yau kuma kashina ya bushe yo in kun min da arziƙi ku min rigijib (duka) Ku barni in ƙarasa mutuwa da kaina amma na san dai ba za ku barni a yadda na muku wasa da hankalin nan" Cewar Inna a zuciyarta.

Sai da ta gama zane su tsaf sannan ta ce

"To yanzu inaso ku maidani inda kuka ɗakkoni dan yanzu idan na ce zan ɓace guguwa ce za ta taso kuma wataƙila ta kwashe har ku a nemeku a rasa"

"Dan Allah kar ki ɓace ki taimaka mana " Suka haɗa baki wajen faɗa.

"Ina da sharaɗi"

"Muna jinki"

"Daga yau babu ku ba garkuwa da mutane ko da kuwa sauro ne "

"Ai wallahi mun tuba mu da muka yi garkuwa da aljana ai ba ma ƙara ba"

"Ba aljana ba ce Inna Azumi ce matar Malam, kishiyar Tasalla ni ma da za mu ga aljanar yanzu da sai dai a shiga ceton rai dan ƙafa mai na ci ban baki ba za a yi" Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce.

"Ku shiga mota mu tafi, ɗaya ya shiga gaba ni da ɗaya mu shiga baya ɗaya kuma ya tuƙa" Ta faɗa tana saurin shiga motar ta zauna dan tunowa ta yi da aljanin da ta gani a bayi , hakan ya sanya ta ji wani mugun tsoro dan bata manta karonsu ba. Haka suka shiga suna zazzare ido saboda tsoro Inna kuwa da ta shiga baya ta zauna a setin kujerar direban ta ɗaga ƙafafunta ta ɗora a kan wuyan direba, a haka yake tuƙin rai duk ba daɗi wuyansa ɗauke da ƙafar aljana.


Haka ake tuƙin sun yi dif kamar ruwa ya ci su suna shigowa cikin gari ana fara kiran sallar magriba, dan haka wani wurin mai saida kayan marmari Inna ta nuna musu.

"Maza ku tsaya ku cikawa sarkin aljannu leda da kayan marmari san wannan ledar da kuma sa ta faɗi lokacin da kuka kinkimeni kamar kun samu tukunya alkakinsa ne da bakilawa, to yanzu ku ramawa kura aniyarta in ba haka ba kuna komawa gidajenku za ku ga an mayar da ku dajin da muka baro yanzu, in sau dubu za ku komo nan sai an maida ku"

"Za mu siya ma" Suka faɗa suna ɗakko kuɗi kowa ya bayar aka cikawa Inna ledar viva da kayan marmari masu yawan gaske, dan cewa ma ta yi gorubar bature ta fi yawa (Apple) Haka aka ɗakko kayan nan aka sanya a mota, har ƙofar gidan da suka ɗauki Inna suka dosa za su kaita amma sai ta ce, dama ai ita aljana ce kuma ba a nan take ba, nan ta ce bangon duniya za ta je amma sai sun kaita kan bola ta nan za ta bi ta tafi, haka ta rinƙa nuna masa hanya, a haka dai suka kama hanyar gidan Sadiya sun kusa ƙarasawa sai ta ce su ajiyera a wajen wata bola saboda a nan za ta bi ta koma hanyar aljannunsu, ita kuma ta yi haka ne dan kar a a je wucewa ta ƙofar gidan Sadiya Imran ya ya ganta a motar ya tona mata asiri dan kaɗan da aikinsa.

A dai dai bolar suka tsaya, wanda ke zaune a mai zaman banza ya fito da sauri ya buɗewa Inna ƙofa ta fito aka miƙo mata ledarta shaƙe da kayan marmari.


"Gashi iya" Ya faɗa yana durƙusa gwiwoyinsa a ƙasa.

"Ku ajiye a nan sarkin aljannu zai sa dogaransa aljannu su zo su ɗauka" Cewar Inna a fili a zuciyarta kuwa cewa ta yi.

"Yo Ina dalili zan hau bola da abun da zan ci"

Ajiyewar ya yi, gabaɗaya suna jin tsoro Inna kuwa dosar bolar ta yi tana addu'a a zuciyarta dan kar ta je ta yi gamo da magribar nan. Suna ƙoƙarin jan motar suka ga Inna ta fara wata girgiza da sauri ya ja motar suka bar layin a sukwane.

Sai da suka yi tafiya me nisa suka tsaya kowa ya kama gabansa dan sun ce sun bar garkuwa da mutane daga yau, sbd angamo da aljanar da suka yi yau, shi ma Ogan bayanin da suka masa a waya bayan barinsu wajen Inna ya sanya an maida me gadin kuma sun fasa ɗakko tsohuwar da suka yi niyya dan suna ganin kamar idan za su ɗakko ta aljana za ta iya rikiɗa su ɗauki aljanar a maimakon matar dan haka shi ma barin garkuwa da mutanen ya yi ya koma ya kama sana'a.


Inna kuwa tana ganin gilmawar motarsu ta gefen ido, sai ta ɗan dakata, sai da ta tabbatar sun tafi sanna ta baro kan bolar da sauri ta suri ledar kayan marmarinta, tana ta waiwaye tana cewa

"Ja'irai ƴan iskan ƙarya yo me na manta gashi na samu kayan marmarina ko banza ai na ƙwaci kaina, da yanzu ina can wataƙila ma wani daga cikinsu ya far mini tsakar dare tsofai-tsofai da ni, ya je ma ya goga mini cuta mai karya garkuwar jiki" Ta faɗa tana shigewa gidan Sadiya, sai da ta sanya ƙafarta a cikin gidan tsoron aljanin gidan da ya tsorata ta rannan ya faɗo mata, tana fatan kar dai yana jin yadda ta yaudari samarin nan, ya zo da dare ya tambayeta dalili.

"Assalamu alaikum, gafaranku dai masu gida" Cewar Inna lokacin da ta shigo gidan amma gidan shiru kamar ma babu kowa.

"Ikon Allah kun ji ina Halimar take ta barni ina ta faman rafka sallama" Ta faɗa tana shigowa tsakiyar falon amma babu kowa sai su Hassan da ke kwance kan gadajensu suna bacci.

"To ko dai bayi ta shiga, kenan Asharofa har ta tafi gida, to ai shikenan" Ta faɗa har lokacin ledar kayan marmarinta na riƙe a hannunta.

Imran da tun sallamar Inna ta farko ya jiyo ta amma Sadiya bata ji muryar Inna ba, hakan ya sanya ya riƙe hannun Sadiya da ke shirin fita ya hanata ta fita kuma ya yi hakan ne saboda ya yiwa Inna abin da za ta kunyata. Sadiya kuma da yake ta ga yana ta ƙuncin rai sai ta kasa tafiya ta dakata, tsaye suke a tsakiyar bedroom ɗin, ya riƙe hannunta babu wani abu da ya ce kuma bai mata komai ba duk da tana ɗan tsoron yanayin nasa dan ta san shi bai iya riƙe kansa ita kuma jego take babu damar yin hakan.

"Sa'adiyya ba dai baccin magriba kike yi ba" Cewar Inna tana dosowa bedroom ɗin da ƙarfin gwiwarta, Imran da ya ji takun tahowarta ɗakin ya yi saurin janyo Sadiya jikinsa ya rungumeta, hakan ya yi dai dai da bankaɗa labulen da Inna ta yi.
Ledar kayan marmarin ta saki ta faɗi ƙasa, ta fara rafka salati, tana tafa hannuwa kamar wanda ta ga mazinata turmi da taɓarya. Sadiya da ta ji maganar Inna ta shiga ƙoƙarin raba jikinta da na Imran, aikuwa Imran ya riƙe ta ƙam ya ƙi sakinta dan yanzu yake so ya ga yadda tsohuwar nan mai tsuru-tsurutun tsiya za ta yi, dan shegen shishshiginta da zalama ne ya sanya ta zo masa wani ZAMAN WANKA dole ya nuna mata bashi da kunya ko ta tattara komatsanta ta bar masa gida ta haƙura da ZAMAN WANKAN.

"Imirana, kai Imirana, wai Imirana ba magana nake maka ba" Cewar Inna a fili a zuciyarta kuma ta ce.

"Wannan an yi taƙadarin yaro wataƙila ma ba ya cikin hayyacinsa, sai na yi da gaske zai ƙyale ƴar mutane yo ban da jaraba ma yarinya tana jego amma ba zai ƙyaleta ba"

Sadiya duk kunya ta kama ta sai kiciniyar ƙwace kanta take, amma Imran ya ƙi bata haɗin kai nema ma yake ya haɗe bakinsu amma sai kauda kai take"

"Na shigesu ni Azumi me idanuna ke gani, Imirana riƙe da Sa'adiyya ko shamaki babu a tsakaninsu, yanzu ba za ka saka ta ba Imirana ko dan kunya ta ma ai ka saketa, amma ka runƙunƙume yarinyar da jego take ɗanye sharaf, ai abin da kunya yin tsirara a gaban uban miji" Inna ta faɗa kamar ta saki ihu dan jin nauyin yadda ta gan su, gashi kunya duk ta kamata amma tsegumi da kuma son ganin ƙwaƙwaf dan kar a yi katoɓara ya hanata tafiya daga ɗakin.

Imran kuwa jin yadda Inna duk ta rikice sai ya sanya hannunsa ɗaya ya riƙe ƙugunta ɗayan kuma ya kai wajen ƙirjinta a ransa yana cewa

"Ai tun da gane -gane gareki wallahi sai kin ga abin da ya fi ƙarfin ganinki, wa ya ce miki ana shiga tsakanin ma'aurata?" Ya faɗa a ransa.

" Na shigesu ni ɗiyar me daddawa jiƙar me barkono yau ina ganin abu , yo Imirana banda fallasa auren bashi ya za a yi ka rungumi me jego, tabbas shi yasa ba a baiwa kura ajiyar nama nima da gangan ne na fita na barku a gidan in ban da tsautsayi zagin mahaifi ai dama ba a bar mutum kamar Imirana ba da mace a cikin gida, yo me nema a duhu ne ya samu a sarari" Ta faɗa tana ɗan tako ƙafarta ta matso cikin ɗakin, dan so take ta san yadda za ta yi ta ƙwaci Sadiya kar a yi abin kunya.

Har lokacin nan da Inna ke ta karaɗi Imran ko niyyar sakin Sadiya be yi ba so yake ya ga iya gudun ruwan Inna za ta fice ta basu wuri ko kuma za ta cigaba da tsayuwa kamar an dasa ta har sai ta ga abin da zai turewa buzu naɗi.

"Yau na tabbatar da waye kai Imirana, dan tabbas gani ya kori ji, ni kaɗai na san abin da ya faru da ni a fitar nan tawa daga gidan nan, kuma ni na san abin da hannu na ya damƙa (Al'aura) ya Allah kai ka san karatun kurma Allah ka tsare min idanuna da gani na daga abin da zai ɗaga min hankali, yo banda ƙaddara ma ni da ba na ƙaunar ganin mazaƙuta in ba ta Malam ba, me ya kaini na taɓa mazaƙutar maza har uku da hannuna, ji nake kamar na sa wuƙa na gundule hannun nan nawa da ya taɓa al'aurar da ba halalinsa ba" Cewar Inna tana sakin kuka, dan gabaɗaya sai ta ji birnin ta fita a ranta yau ta haɗu da maza da abin da ta musu kaɗai ne ya ƙwace ta gashi kuma yanzu ta dawo gida ta tarar da wata katoɓarar.

Imran kuwa furucin Inna ya sanya dariya ta kusa ƙwace masa, amma haka ya daure ya cigaba da ƙoƙarin kai hannunsa wajen ƙirjin Sadiya ita kuma tana ƙoƙarin bige hannunsa.

"Amma wannan yaro an yi me wankekken ido, bayan ƙwaƙumarta da ka yi babu shamaki tsakaninku, hallaw na shanunta kake so ka damƙo, to wallahi dai ka bi duniya a sannu a gaban idona baka jin kunya kake waɗan nan abubuwa kamar wanda uwarsa ta ce jeka ka ganiz shi yasa ashe ko zamana baka ƙauna a gidan na kafi so a barka ka ci karenka ba babbaka, ai dama idan ka ji makaho yana cewa a yi wasan jifa to tabbas ya taka dutse"

Imran juya Sadiya ya yi yake neman kwantar da ita a kan gado.

"Halima wai duk a gaban idona fa ake sarrafa ki kamar wata injin kaɗin taliya, amma kin kasa kataɓus ki ƙwaci kan ki so kike sai sheɗan ya masa linzami ya haike miki da ɗanyen jegon, wallahi ki kiyayi biyewa ɗa namiji Sa'adiyya ina rabaki da kiwon kyalle kina kyalle ta haihu, , ni nan yanzu na ƙwaci kaina daga hannun maza ƙartai uku, bayan haka harda yaudarar kayan marmari amma ke a hannun namiji ɗaya kin kaya ƙwato kan ki kin barsa sai waricinsa yake a kan ki, sai ka ce wata matar shige, ai matar shige bata daraja amma ke kuwa da ba matar shige ba kya biye masa"

Ganin Imran ya kwantar da Sadiya a kan gado Inna ta saki ihu me haɗe da kuka.

"Dan Allah Imirana na roƙeka dan darajar iyayenka ka rabu da yarinyar nan, kar amana ta ci ni, duk wacce taje ZAMAN WANKA tamkar an damƙa mata amanar me jego ne a hannunta, so kake ka je ka sa ƴar mutane ta yi ciki da goyo, ka farke mata ɗinki a shiga uku, bayan ɗinki bakwai Amina uwarka ta faɗa min an mata a mafitar ɗa (HQ) Sai ka ce wata ƙwarya amma kake neman maida hannun agogo baya, dama duk abin da aka yi da jaki sai ya ci kara, kuma ai dama abin kirki bai gaji kare ba, in ya yi ma dukansa ake"


"I luv u baby) Cewar Imran cikin wata murya da ya yi da gangan.

"Ƙarya yake miki wallahi yaudara ce kawai irin ta maza, duk da ban san fassarar abin da ya faɗa ba, amma na san magana ce me daɗi dan na ga a kan gado ya yi maganar kin san kuwa maza kalamansu basa tashi sai suna neman biyan buƙata to a nan za ki ji kalaman soyayya har da na siyarwa"

"Ina sonki masoyiya" Cewar Imran shi ma yana ƙoƙarin hayewa gadon, sai da ya hau gadon ya kife a kan Sadiya ɗare-ɗare, kicinyar tashi Sadiya ta shiga yi amma ya hanata.

"Lahaula wala ƙuwata illah billahi aliyal azim, Imirana kan ruwan cikinta za ta hau a gabana" Inna ta faɗa tana sauri ta yi taku ɗaya biyu sai gata a gaban gadon a sukwane, aikuwa ta shiga kiran Imran da ƙarfi tana cewa.


"Imirana kai, kai Imirana tasata (Ɗaga ta) tasa ƴar mutane, wallahi ban bari ka yi wannan aikin da na sani,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login