Showing 9001 words to 12000 words out of 24389 words

Chapter 4 - YAR ZAMAN WANKA BOOK 2

22 Aug 2025

154

danke faruwa sai kawai ya miƙe tsaye. Sadiya kuwa gabaɗaya ma ta manta cewae ana taɓa Hassan ya dawo mutum gabaɗaya a ruɗe take irin yadda ta ga baƙin mata na yi kamar waɗanda aka sanya wa bakin bindiga a ƙoƙon kai.


Cikin jarumta da daddagewa Abdallah yake ƙoƙorin haɗa laɓɓan bakinsa domin ya karanto ko da addu'a ce amma tsabar tsoro da fargabar da yake ciki ya kasa ko da a magana ce, Kawai kallon ikon Allah yake wai shi ne ɗauke da ƙaton miciji haka miciji mai sanye da riga da wandon jarirai.Ganin micijin ya kafeshi da ido yana dillo harshensa mai haɗe da dafin da ke cikin bakinsa wanda idan ya sari mutane dafin ke kashe su. Dakyar sai ya iya fara magana, ya fara jero national anthem (Taken Nigeri'a) Wata dariya ce ta so ƙwacewa Imran ganin Abdallah ya daddage yana yiwa Nigeri'a kirari yana zayyano mata taken ta duk a tunaninsa addu'a yake karantowa. Inna kuwa sai dariya take abinta ta ce.

"Yau de maza sun faɗi yo soja kamar kai ga ƙiba tabarakallah kamar mai cin ƙatuwar tukunyar tuwo amma miciji ya razana ka"

dama ai karanbanin akuya yasa ta leƙa ɗakin kura, gaskiya Hassan kana birgeni yaro masomin babba ubanka ma baka bari ba da baiwarka, to yai kuma ga ubanka soja nan sai rattabo yaren nasara yake (Turanci) Har gwara ni ranar nan da na karanta alif an baki waw zal, a ce daga cikin baƙaƙen larabci suke amma shi ka ga" Ta faɗa tana dariyar. Abdallah kuwa sai gumi yake yana ta karanto taken Nigeri'a yake daga ya je ƙarshe sai ya dawo farko ya sake kamowa jikinsa sai maƙyarƙyata yake.

Ganin abin da Inna ke yi Imran ya yi ta maza ya ƙarasa gaban Abdallah ya ce.

"Miƙo shi ka huta wannan gumi kamar ka yi tsere Abdallah" Ya faɗa yana tsaye a gaban Abdallah, shi ma Imran ya faɗa ne dan kar Abdallah ya ga bai kyauta masa ba amma har ga Allah ba zai iya ɗaukan miciji ba.

"Haba Imran ta yaya zan iya ɗaga shi ma baka ganin misiji ne (miciji) To wallahi ko kunama ba zan iya ɗagawa ba bare misiji dan Allah ka ɗauke kar in mutu saboda tsoro.


"Daddyn Amira ka bashi micijin mana ya za ka bar miciji a kan ka sai ya cutar da kai" Matarsa da ke rakuɓe jikin bango tun lokacin da ta ajiye wa Sadiya Husaini a kan cinyarta.

"Ƴar jakar uba kai, wa ya faɗa miki barno gabas take, to wallahi mu nan da kike gani abin kunya gaba muka bashi ba baya ba, ashe rainin wayo ne abin naki ɗazu kika ce misiji amma yanzu gashi nan kin ce miciji ashe da hausarku a bakinku kuke rainawa mutane hankali" Cewar Inna tana dariya.

Babu wanda ya mata magana, Imran ne ya ce.


"Abdallah ya kake national anthem ne wai, duk zaman kudun ne ya sa ka manta da addu'a, Allah fa cewa ya yi Allahzina iza asabathum musibatun ƙalu innalillahi wa inna ialaihir raji'un, amma kuma kai sai kake karanta taken Nigeri'a ko Nigeri'ar ce za ta kawo maka ɗauki.

" Abdallah dai bai ce komai ba dan ba ma ya fahimtar abin da Imran ke faɗa.

"Mummy let's go home, im afraid" Cewar Amira tana neman sakin kuka.

"Ke rufewa mutane baki kina ƴar hausawa kina magana da bakin nasara, uban leshi ma( let's) Goron uban wa (go) "Cewar Inna tana zarewa yarinyar ido, da sauri ta matsa jikin Mummynta suka maƙure a jikin bangon tare suna rarraba ido.

Miƙewa Inna ta yi cikin sanɗa, sai da ta je kusa da Imran da ya bata baya, ta shammacesa ta kama ƙasan rigarsa aikuwa yana ƙoƙarin fisge rigar amma sai da Inna ta dangwarashi ga Abdallah

. Aikuwa ya fara zazzare ido cikin tsoro ya kalli idon Inna da ta ɗaure fuska ya maida kallonsa kan Hassan sannan ya kalli Abdallah da zuwa lokacin bakinsa ne kawai ke motsi ba ma a jin abin da yake cewa.

"Yo kai Imirana haka ake, ai baƙonka annabinka, amma ka ƙyaleshi a cikin ɗimuwa, kuma da kake cewa ya kasa addu'a yana taken Nigeri'a har ƙwara wata wainar da ta wake kai fa sumewa ka yi da ka ga Hassan a kan ka, kai da kake ubansa bare kuma shi da yake abokinka"

Imran ma dai ya kasa magana dan ganinsa dab da Hassan sai ya ji ya nemi nutsuwarsa ya rasa.

"Yiiii, wayyo, a kirawo tawagar sojoji su zo da bindigo su haɗo har da igwa (Motar harbi ta sojoji) Su kawo mini ɗauki" Abdallah yake sumbatu cikin tsoron yana sakin kuka.


"Wallahi babu mai harbe Hassan kawai ku yi addu'a ya dawo halittarsa ta mutane" Cewar Inna da ke tsaye a kan su Abdallah, cikinta har murɗewa yake kan dariya.

Sadiya da tun da aka fara abin ta zabga uban tagumi hakan ya mantar da ita cewa tana taɓa Hassan ya dawo mutum, sai yanzu da Inna ta faɗa ta tuno da sauri ta tashi ta je wurin Abdallah ta taɓa Hassan aikuwa cikin sauri sai gashi ya dawo mutum tare da sakin kuka, ɗaukansa ta yi, Abdallaj da matarsa da Amira suka bi Sadiya da kallo cikin mamakin ganin tana taɓa yaron ya koma mutum.


Imran gefe ya rarrafa jikin ɗaya kujerar da matad Abdallah ta tashi ya je yana daga kan gwiwoyinsa ya kwantar da kansa a kan kujerar ya rufe idanunsa tare da sakin wata ajiyar zuciya.


Sadiya saka Hassan ta yi a nono, kafin su ankara matar Abdallah ta ja ƴarta sai ganinsu suka yi a bakin ƙofa. Shi ma Abdallah da jikinsa ya mutu murus tsabar kaɗuwar da ya yi, yunƙurin tashi ya yi, bayan wandonsa har da danshi-danshin lema wataƙila ya fara sakin fitsari ne tsabar tsoro.

"To fa yau ake yinta, lallai akwai maza, akwai mata maza, akwai muna maza kuma alamar ƙarfi dai tana ga mai ƙiba, yau dai mun tabbatar duk girman ɗan tsako ƙwai ya fishi, soja kake ko sojojo, wallahi yau dai sai matarka ta maka ruwan zafi za ka ji dama-dama saboda mutuwar da jikinka ya yi, in kunne ya ji jiki ya tsira" Cewar Inna tana kallon Abdallah da ya tashi dakyar ga nauyin jikinsa ga nauyin tsorata.


"Imran za mu wuce" Cewar Abdallah cikin sanyin murya, ya faɗa yana kallon Imra n da ya ɗora kansa a kan kujera yana sauke numfashi da ɗaɗɗaya idanunsa a rufe.

"Uhm, to,to, har za ku tafi?"

"Ya har za mu tafi baka gani abin da ya faru ne ko kai makaho ne" Abdallah ya faɗa yana ɓata rai, ga haushin Inna da yake mugun ji sai dai ya yi alƙawarin sai ya ɗau fansar wulaƙancin da ta masa yau. Haka ya juya yana shirin fita daga ɗakin Sadiya ta ce .

"To muna godiya ƙwarai, mumyn Amira ku gaida gida"

"Gida ya ji" Cewar Mummyn Amirar amma Abdallah da ido kawai ya bita bai ce komai ba. Imran ma miƙewa ya yi zai musu rakiya, yana kallon Inna da ta kafe su da ido shi da abokinsa tana sakin wani murmushin jin daɗi da alama wasan da ya gudana ya mata daɗi.

"To Sojojo ka gaida gida sai kuma ranar suna, kar kuma in kuma jin ko da wasa ka kira kanka Soja marmari daga nesa, in kunne ya ji jiki ya tsira, kai kuma Imirana ka dawo yanzu ka riƙe mata Hassan ta yi wankan yamma" Cewar Inna har lokacin bata tsagaita da dariya ba.


Fita suka yi suna tafiya kamar mararsa lafiya, dakyar Abdallah ya iya buɗe ƙofar motarsa ya shiga, matar ma da kanta ta buɗe suka shiga da ƴar saɓanin kullum da shi ke buɗe musu su shiga ya rufe.


"To Abdallah nagode Allah bar zumunci, ranar friday ne sunan" Cewar Imran da ke riƙe da marfin ƙofar. Shiru Abdallah ya yi bai ce komai ba.

"Sojojo, Sojojo, kai Sojojo" Cewar Inna da ta fito daga cikin gidan riƙe da ledar viva.

"Imirana tsayar da su sun yi mantuwa" Cewar Inna tana ƙarasowa.

"Ga kayanku kun manta"

"Ki mayar na babies ne da muka kawo"

"To,to,to, Allah amfana madallah, Allah sa a daɗe ana yi sai kun zo suna" Ta faɗa tana juyawa ta koma cikin gida.



Masu son a tallata musu hajarsu 09030283375
[24/03, 5:13 AM] Mom Mashkur First class: Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134


A wurin Inna ta baro su ta dawo gida riƙe da ledar, tana shigowa ta ajiye ledar ta nufi kujerar da Abdallah ya zauna ta danna da hannunta, ta ƙara taɓa inda matarsa ma ta zauna ta taɓe baki ta ce.


"Halima kin ga abin da nake faɗa miki ko? Da kin ce mutanen nan su zauna a ƙasa dan wallahi baki ji yadda kujerar ta faɗa ba gabaɗaya ta lotse dan ji na yi har katako da ƙarfen ciki ina taɓowa musamman wacce Sojojo ya zauna, dai dai ma an yi ba bashi sun kawo kaya masu tsadar gaske" Ta faɗa tana taɓe baki ta zauna a ƙasa ta shiga fito da kayan jariran na cikin ledar kaya ne masu kyau da tsada har da turmin atamfa.

"Kai, kai, kai, taɓɗi ashe dai Sojojo an iya abin arziƙi, to Allah amfana" Har lokacin Sadiya bata ce mata komai ba dan ita yanzu abin Inna yana ɗaure mata kai sosai ta gaji ma da wannan ZAMAN WANKAN gabaki ɗaya.

"Yo ko ki yi magana ko ki ƙyale, duk ɗaya dan kin ga wannan kayan da suka lodo miki kamar bashi yake dan kin ga matarsa ma tsohon ciki gareta dole idan ta haihu ke ma ki ki mata" A dai dai nan Imran da ransa ke ɓace ya shigo da sallama ciki-ciki.Amsa masa Sadiya ta yi.

"Imirana ka ga abin arziƙin da Sojojo ya kawo maka, kaima dai Imirana wallahi da karambani kake, banda karambanin akuya mai sa ta leƙa ɗakin kura, ina kai ina wannan mutumin him guda dashi, yanzu a ce ka rasa aboki sai wannan rungujejen abu kamar himilin kaya ina abokin ka Abida tun ranar da ya kawo mu shiru kake ji wai malam ya ci shirwa, amma wannan Sojojon da kuka jeru sai na gan ka abu ɗul kamar ruwan aski.

Banza ya mata ya shige bedroom dan daga Inna har Sadiyar ma haushinsu yake ji.

"Aniyarka ta bika Imirana in ƴaƴan naka kake yiwa baƙinciki dan an kawo musu kaya, wato so ka yi kuɗi ya bayar ka yi wuf da su ko?, gashi ma har yau babu sadakin gado babu dalilinsa, ka murtsuke ƴar mutane ka mata ciki ta haifa maka ƴaƴa har biyu amma har yau babu ragunan suna ga lokaci na ta tafiya, sai dai ka kawo wani ɗan nama a ƴar baƙar leda wai na me jego ne, yo wane irin me jego kawai a kawo tirkakkun raguna, ah to mun gaji da gafara sa bamu ga ƙaho ba, dan ba dani ba gaɗa a kabari in ji ƴan magana"

Babu wanda ya ce komai shi ya shige ɗaki ya kwanta yana ta jiyo Inna yana kuma tunanin abin da zai mata.

"Oh ni Ashrofa sai ka ce an aiki bawa garinsu, daga cewa za ta je gidan su ƙawarta ta dawo amma har yanzu bata dawo ba"

"Me za ta miki to idan ta dawo ɗin?"

"Haba Halima har na rasa abin da za ta min yunwa nake ji"

"To ki zubo abincin mana"

"A'a ni ba shinkafa zan ci ba so nake ta dawo ta dafa mini indo momi (indomie) Taliyar yara akwai daɗi wallahi"

Kallonta kawai Sadiya ta yi bata ce komai ba.


~DARE~

Tun da ya kwanta yake juyi a katifar, ji yake kamar ya je ya iyo waje da Inna daga ɗakin nan ya kulle, dan gabaɗaya yau ba ya jin jikinsa dai dai. Zaune yake ya zabga uban tagumi mararsa sai murɗa masa take tana neman ɗauki, haka ya dafe marar yana yin salatin annabi S.A.W Ya daɗe a haka zuwa can ya tashi ya leƙa bedroom ɗin fitilar a kashe sai dai ɗakin ba duhu sosai da yake hasken farin wata ya ɗan shigo ta gefen labule. Ba ka jin komai sai ƙaran komai a ɗakin dan Inna ko munsharin ma bata yi, hakan ya sanya ya ɗan fara lalume har ya ƙarasa wajen gadon tsaye yake yana ta nazari so yake ya gano wacce ce Inna wacce ce Sadiya dan ya lura yanzu kowacce tana iya ɗaukan bargon kowacce ta rufa haka zalika suna iya canjin wurin kwanciya saɓanin da kowacce na kwanciya a gefen da take kwanciya.Kan gadon ya hau sai da ya zauna a tsakaninsu ɗare-ɗare so yake ya gane matarsa ya shiga bargonta ya kwanta a kusa da ita ko ya samarwa kansa nutsuwa, kunne ya kai ya kara a saitin bargunan dan ya tantance na Sadiya dan gabaɗaya kowacce ta rufa ne har kanta.

Kunne ya miƙa jikin bargon Sadiya dan ya tantance ita ɗince a ciki ko kuma Inna ce a ciki. Garin kara kunne sai ya ɗan zame hannunsa ya buge na cikin bargon ashe dai Inna ce a ciki, wani uban juyi da ta yi da miƙa shi ya sanya Imran tsorata dan ya ɗauka zaune za ta tashi, idan kuwa ta gan shi a kan gadon a tsakiyarsu tabbas za a kwashi daru, da sauri ya yi wata shala sai gashi a gefen gadon wurin inda akwatuna suke, durƙusawa ya yi yana kiran sunayen Allah. Jin shiru babu motsinta sai ya ɗago kai a hankali ganin ta cigaba da barcinta sai ya lallaɓa ya fito daga ɗakin da rarrafe dan ba ya so ma ya tashi tsaye ta ji motsinsa a samu matsala.

Haka ya dawo falon wani haushi da takaici na damunsa, ga mararsa da har lokacin bata daina ciwo ba, fitilar falon ya kunna ya fita domin zuwa kicin.

"Kai da matarka halalinka amma kake raɓewa in za ka wajenta kamar wani kwarto" Cewar Imran a zuciyarsa, yana nufar kicin ya ɗakko jar kanwa ya jiƙa ya sha dan ya rage sha'awar da ke damunsa haka ya dawo ya kwanta yana jin ɓacin rai fal ransa, ya so ya shiryawa Inna wani abun cikin daren nan amma rashin nutsuwa da kuzari ba za su barshi ba haka ya haƙura ya kwanta yana cewa "In kere na yawo zabo na yawo wata rana za a haɗu.


*WASHE GARI*


Kamar kullum yau ma haka Inna ta haɗa ruwa sai dai cikin ikon Allah har ta wanki Hassan ta gama amma bai sawaya ba, haka ta shirya su tsaf.

*DA YAMMA*

Suna zaune a falo Ashrof, Sadiya da kuma Inna Imran ya fita ba ya nan, sallama ake yi a Ashrof ta amsa da ta leƙa sai ta ga Abid ne.

"Ya Abid ina wuni" Lafiya ƙalaw Ashrof ya mama ina Hajiya Inna?"

"Mama tana gida Inna kuma tana ciki in nemanta kake"

"Kamar kuwa kin sani saboda ita na zo, ki ce tana nan ana shan ZAMAN WANKA"

"Eh" Cewar Ashrof tana ƴar dariya.

Tare suka shigo Inna na ganin Abid ta fara murna tana cewa

"Lale da Abida sannu da zuwa"

Shi ma dariyar ya yi ya zauna yana gaishe da Inna suka gaisa da Sadiyar.Ya tambayi kwanan yaran nan aka bashi amsa da lafiya ƙalaw.

"Wallahi abubuwa ne suka ɗan sha kaina ban samu na dawo ba, na ga yaran ba"


"To wane gani kuma kai da muka dawo da kai daga asibiti da su" Cewar Sadiya tana ɗan murmushi.

"Haba Sadiya ke me yasa kike haka ne ni wai, ai in kin ji an ce za a ga mutum ba wai gani na ido ba ake nufi. Baki ga ƴan siyasa ba ko masu kuɗi idan ƴan maula suka je wurinsu sai su ce zan ganka zuwa gobe, to ai suna nufin za su sallami mutum da wani abun shi ne hausar" Cewar Inna tana kallon Sadiya, Sadiya kwa da Ashrof kunya ce ta rufe su ai hakan kamar roƙo ne. Wani yatsina fuska Sadiya ta yi take yiwa Inna kallon irin me yasa haka.

"Kai ka ji ni da mata, yo sai ka ce wani wanda na yi saɓo, kawai dan yarinta ta sa kun kasa gane inda maganar Abida ta dosa na warware muku zare da abawa sai ki rinƙa zare min ido kamar dai ke ce uwata mai daddawa"


"Rabu da ita Inna ai gaskiya kika faɗa kuma ni ma dama irin ganin da na zo na musu kenan" Cewar Abid yana dariyar maganganun Inna sosai ya so ya dawo amm abubuwa suka masa yawa amma da tuni ya dawo ko dan ya ci dariya.Ya kuma ga irin zaman da ake tsakaninta da abokin nasa dan Imran ya ƙi bashi labarin komai kuma ya san tabbas akwai wata a ƙasa dan babu yadda za a yi a zauna lafiya tsakanin Imran da Inna.

"Ga wannan Inna naki ne wannan kuma na jarirai" Ya faɗa yana miƙa mata manyan ledoji guda biyu, ɗaya kayan jarirai ne da less mai shegen kyau na Sadiya, sai kuma ɗayar atamfa ce da goron cikin farar leda.

"Ayyiriri, taɓɗi yau ake yinta ai shi sa jiya nake tambayarka a wajen Imirana , nagode Allah saka da alkairi, ya buɗa maka, wallahi Abida ka fiye min Imirana sau dubu ka ga Imirana ko goron murtala (Ashirin) Bai taɓa siyo wa ya kawo min ba bare turmin zane" Cewar Inna tana sakin goɗa tana ɗaɗɗaga atamfar.


"La ba komai Inna in ba a kyautatawa tsofaffi ba wa za a yiwa"

"Kai dai da ka san hakan amma Imirana mai ya sani yaron nan banda ƙafafa da nuna shi mai gida ne"

"Imran ko Inna"

"Shi mana, bari ma na baka labarinsa, amma sai na fara baka daga farko ranar da na kwana ban yi bacci ba"


"Baki yi bacci ba fa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login