Showing 6001 words to 9000 words out of 24389 words

Chapter 3 - YAR ZAMAN WANKA BOOK 2

22 Aug 2025

153

kika riƙe ni"


"Tusugunno za ka yi ba fitsari ba, ban da rainin wayo ni zaka buɗewa ido to wallahi sai dai ka saki fitsarinka a tsaye kamar saniya, dan ba zan sake ka ba, ni ma nan jigilif nake da fitsarin kayana jargaf kamar na yi iyo a ruwan maliya"

Imran ganin Inna na janyo shi ya sa ya kakkafe tana jansa yana togewa, haka ta janyoshi ta dawo dashi kusa da ita ta ce.


"Sa hannu ka taɓa yaron nan ya dawo mutum"

Idanu ya zaro ya shiga girgiza kai yana roƙonta ta sake shi.


"Ka taɓa shi na ce, ya dawo mutum yo ban sa ma lalacewa ni da nake ɗorin ɗosano ma na taɓashi bare kai"

"Inna ki min rai dan Allah"


"Ranka yana hannun Allah" Cewar Inna tana ƙara damƙe rigar Imran sai da ya gama tsurewa sosai ta ga idanunsa sun fito sai zare su yake kamar wanda ya yiwa sarki ƙarya, aikuwa ta sanya ƙafa ta danne harshen rigar Imran, ta sanya hannayenta biyu ta ɗago Hassan a siffar miciji ta ɗorawa Imran a kan cikinsa da yake data janyoshi kwantawa ya yi reran, haka ta .
ɗora masa micijin kan micijin a wajen sai tin haɓar Imran idanun Imran cikin na micijin.

Imran hatta numfashinsa kasa shaƙa ya yi duk tunaninsa ma yadda aka yi Inna ta shammacesa har ta masa riƙon da ya kasa ƙwacewa.


"Ka sanya hannu ka shafa kansa ya dawo mutum in wankesa kafin uwarsa ta fito"
Ta faɗa tana kallon idanun Imran da ke kafe cikin na micijin dan ya kasa motsa ko da yatsansa ne bare ya iya ɗauke kansa.

"Imran a mace ko a raye? Kai kamar ba namiji ba"

"Wallahi ko maza maza ne ni dole in ɗauke wuta Inna wannan in ban mutu ba ma ai kwanana ne a gaba" Cewar Imran a zuciyarsa hawaye na bin fuskarsa.


Hannu Inna ta miƙa ta ɗan taɓa micijin aikuwa ya ɗan motsa ya kaɗa jela, Imran kuka yake kawai marar sauti.


"Ba ni ka sanyawa abu a fura ba na rinƙa sawu bayi kamar mahaukaciya sabon kamu, daga na dawo wani kashin ya dawo na koma bayin har sai da na dawo na kasa zama da ɗuwaiwukana, ƙarshe sai durƙuson haihuwa na yi, bayan rabona da in yi durƙuson haihuwa tun na naƙudar uban Sadiya amma sai gashi ka sanya tarihi ya maimaita kansa"


Ganin dai ba ya motsi sai Inna ta sake zungurin micijin aikuwa micijin ya fasa kansa kamar zai sari Imran diff kake ji jikin Imran ya saki, ashe suma ya yi, hakan ya yi dai dai da shigowar Sadiya.


Wani salati Sadiya ta saki tana yin kan Imran da sauri, hannu ta sanya ta zunguri micijin aikuwa sai ya dawo mutum tare da sakin kuka ɗaukansa ta yi, ta ɗora a kafaɗa ta sanya hannu ta shiga jijjiga Imran amma shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu.


"Inna garin ya haka ta faru" Sadiya ta faɗa tana sakin kuka cikin tashin hankali. Wata harara Inna ta jefa mata, ta kalleta ta ce to uwar ƴan son miji ba mutuwa ya yi ba suma ya yi, kuma ba komai ya sumar da shi ba illa soyayyar irin ta uba da ɗa "

Banza ta yiwa Inna ta ajiye Hassan a kan gadonsa da har lokacin bai yi shiru ba ta fita da sauri ta ɗakko ruwa a kofi tana zuwa ta sheƙawa Imran, amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa, sai da ta ƙara masa ruwan sai ya sauke wata ajiyar zuciya ya buɗe idanun yana wani ƙiƙƙiftawa saboda bai gama dawo wa hayyacinsa ba, dariya Inna ta ƙyalƙyale da ita kallonta Sadiya ta yi cikin jin haushi ta ce

"Haba Inna ya haka mutum ya suma kuma kike dariya.



Dariyar dai Inna ta cigaba da yi sai da ta yi ta ishe ta sannan ta ce.


" Barni in dara Sa'adiyya wai baki ga yadda idon Imirana ya yi ƙulu-ƙulu ba, kamar an sanya goruba a cikin kwanon sha, ji fa yadda yake kwance magashinyan ko zaune ya kasa tashi"


"Wai ma garin yaya haka ta faru Inna dan Allah ki bar dariyar nan"

"Baki lura da kyau bane Halima kalli yadda na jiƙe da fitarin tsoro da wahala, to kalli wandom mijinki ma ya saki fitsarin shi ma, amma saboda ragwanta, Imirana har suma ya yi amma ni ina tsohuwa babu abin da na yi, wai fa ɗaukan Hassan ya yi ya ɗora a kafaɗa shi ne kawai Hassan ya koma miciji a kafaɗar tasa wannan ne dalilin da ya sa ya suma kin ga kwa dole na yi dariya ni da bakina Allah ba ya tsaga min ba a hana ni walawa sai ka ce wani kututturen icce"
Cewar Inna dan bata so Sadiya ta fahimci abin da ke faruwa.

Wani takaici ne ya tokarewa Imran jin abin da Inna ta faɗa, hakan ya sanya ya fara yunkurin tashi zaune dan shi bai ma san ya yi fitsarin ba sai da ya ji ta faɗa.

"Kama shi mana Halima, bari in taimaka miki, Imran yana ji yana gani aka kamashi da Inna aka zaunar da shi dan duk jikinsa babu ƙarfi tsoro da fargaba sun yiwa gaɓɓan jikinsa katutu hakan ya sanya gaɓɓan yin sanyi.

Inna sai jera masa sannu take saboda kawai neman magana shi kuma Imran yanzu kawai idanunsa a kan Hassan yake da ke kuka gabaɗaya ji ya yi ya tsorata da yaron, Sadiya ɗaukansa ta yi, ta bashinya sha sannan Inna ta ɗaukeshi ta masa wankansa tas aka yi sa'a bai sawaya ba.


Haka dai aka gyara falon kowa ya gyara jikinsa kafin Ashrof ta zo ta gyagygyara gidan duka, Imran kuwa ya ƙufuli Inna a ransa sosai.


```DA YAMMA```

Ƴan barka na ta shigowa ƴan unguwa da kuma dangin Mama da kuma abokan arziƙi, Mama da Hajiya Amina tun da suka yi la'asar suka tafi gida, Imran kuma ya fita ba ya nan, Inna da ta fito za ta je kicin, Imran ta gani ya shigo daga waje waya a kunnansa yana magana bakin nan a washe kamar gonar auduga sai sakin fara'a yake. Kallonsa Inna ta yi, ta wuce abinta, lokacin da ta dawo sai ta same shi yana cewa Sadiya.

"Yanzun nan ya iyo min waya wallahi ya ce suna hanya za su zo shi da matarsa barka "


"Ikon Allah to yaushe suka zo garin" Cewar Sadiya tana washe baki ita ma.

"Kin san ai yanzu an maido da shi Kano da aiki yana barek ɗin cikin garin nan" Cewar Imran.

"Allah sarki ka ce yau muna da manyan baƙi gaskiya yaushe rabon su da Kanon ma baki ɗaya sun yi zaman su a lagos abin su"


"Wallahi kuwa"

"Bari na duba ko sun zo" Ya faɗa yana juyawa ya fice. Inna ce ta taɓe baki ta kalli Sadiya ta ce.


"Wai Halima in ce dai gwabna ne zai zo gidan nan?"

"Gwabna kuma Inna"

"Yo in ba gwabna ba waye zai zo da kuka ta rarraba haƙwara a tsakaninku sai dariya kuke na ɗauka ai sai gwabna zai zo dan zai raba kuɗi ma ai a yi dariya"


"Kai ke kuwa Inna to abokinsa ne da ya tafi aikin soja, a Lagos yake aiki shekara da shekaru ma yana can tun kan mu haɗu da Abban twins yake aikin soja"

"Soja??? Inna ta tambaya.

Kafin Sadiya ta bata amsa sai jin sallama suka yi, cikin muryar da Hausa bata wadaceta ba an ce

"Assalamu alekum" Mata da mijin suka haɗa baki wurin faɗa. Idanu Inna ta zaro ta kalli Sadiya da ta amsa sallamar ta ce

"Wai Sadiya inyamuraine amma dan daga ji babu hausa a harshensu" Ta faɗa cikin raɗa-raɗa. Kafin Sadiya ta ce wani abu sun shigo tare da Imran, miji ne da matarsa da tsohon ciki sai ƴarsa ƴar kimanin shekaru biyar. Wani ƙato ne baƙi kamar ya shafa shuni.

"Tabɗi danƙari iko sai lillahi, mutum kamar buhun gero, tamkar dusa yake ci"......Cewar Inna da ta zabura ta tashi tsaye ganin girman mutumin.


Masu son a tallata musu hajarsu
09030283375
[24/03, 5:13 AM] Mom Mashkur First class: ```Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

DAN ALLAH KAR WACCE TA SAYI LITTAFINA DAN TA FITAR MINI,IDAN DAN KI FITAR ZA KI SIYA KI RIƘE KUƊINKI BANA BUƘATA.```


1️⃣3️⃣ ➡️1️⃣4️⃣


Tsayawa baƙin suka yi cak jin furucin Inna Imran kuwa ji ya yi tamkar ƙasa ta tsage ya shige saboda tsabar kunyar da ya ji ta baibayeshi. Sadiya tamkar ta saki kuka dan takaici, ji ta yi dama ta ce Inna ta shige cikin ɗaki in baƙin sun tafi ta fito. Dakyar Sadiya ta ƙwaƙulo dariyar yaƙe ta ce.

"Bismillah ku zauna mana, sannunku da zuwa"

"Eh, eh, eh ku zazzauna mana" Cewar Imran shi ma cikin inda-inda.

Zauna wa suka yi jikin matar sanyi ƙalaw sai wani haɗe rai take tana hararar Inna tamkar dai ita ta yiwa ba'ar.

"Ku da kuke cewa su zauna daga matar har mijin babu na ɗauka, yanzu tsakani da Allah mutumin nan ya zauna a kujerarki Halima, sai dai a sayi sabuwa inda hali in kuma babu hali sai dai a jefar, dan babu kafintan da zai iya gyara kujerar nan, ko a duniya masu girman mutumin nan basu da yawa" Ta faɗa tana daga tsaye.

Sadiya kuwa sai sigina take yiwa Inna da ido tana ta nuna mata ta yi shiru kar fa ta kunyata su.

"Ke ƙyaleni ni fa ƴar gaskiya ce wallahi, in zaka faɗi faɗi gaskiya komai taka ja maka ka biya, babu munafurci, yo ina zan yi munafurci Malam da yake faɗa mana cewa munafuki yana ƙasan kafuri a cikin wuta, a ce kafuri wutarsa bata kai ta munafuki ba a zafi kin ga kuwa ai abin ba ƙarami bane, kuma wannan ƙifƙifta idon ma ki daina Sa'adiyya dan wallahi babu kyau, yafice da ƙyafuce, ke kuma da kike hararata wallahi ni ban san harara ba sai ido ya faɗi kuma me kike ci na baka na zuba indai ni ce ina dawo wa kan ki" Cewar Inna tana kallon baƙuwar.


Babu wanda ya yi magana, Imran kuwa yanzu lamarin tsohuwar nan ya fara bashi tsoro dan yana tsoron ya tanka ko ya mata wani abu ta masa ramuwar gayya ta fi ta gayya. Sojan kuwa kallon kan sa yake ta yi yana so ya tabbatar cewa wandonsa na sojoji ne a jikinsa ko kuwa dai tsohuwar bata lura da wandon ba ko dai ita bata cikin masu tsoron sojoji, dan tun da yake a duniya ba a taɓa ci masa fuska irin haka ba duk da tsohuwa ce yana ganin da girma amma ai ba hauka take ba daga shigowarsu za ta fara musu wulaƙanci har da saurin miƙewa tsaye shi duk tunaninsa ma sara masa za ta yi ko kuma girmamawa ce ta sa ta yi hakan amma sai ya ga saɓanin hakan.

"Abdallah ina wuninku" Sadiya da take son datse maganar ta faɗa ƴar dariyar yake.

"Lefiya lo, Sediya, ya kake ya ya kuma babies?" Shi ma sojan ya amsa cikin gurɓatacciyar hausar sa dan gabaɗaya zaman kudu ya daƙusar masa da hausar.

"Lefiya lo, to wallahi gwara ma ka ce lefe irin wanda ake yiwa amarya, yanzu fa aka kira ka da Abdallah haba ina dalili kana bahaushe ɗan bahaushe menene kuma lefiya, haka kawai kuna arar yaren inyamurai kuna ɓata mana yaren hausa" Cewar Inna tana komawa ta zauna. Babu wanda ya kulata amma Abdallah ji yake kamar ya shaƙe Inna dan da ace a hanya ne ta musu hakan sai ya mata hukunci. Ita matarsa ma ta kasa cewa komai wace irin tsohuwa ce wa wannan, ransu in ya yi dubu ya ɓaci da abin da Inna take, Imran kuwa kansa a sunkuye yake yana jin a ransa da a ce Inna daga ɓangarensa take a yau ɗin nan sai ta bar masa gidansa dan ba zai iya da wannan abin kunyar ba.

Abdallah kuwa tun da Inna dama ta ce zai lotsa kujera da ya zauna ma sai bai saki jikinsa ba ɗan ɗosanawa kawai ya yi dan shi bai taɓa zaton har ƙibarsa ta kai ya yiwa kujera illa lokaci guda ba.

Gaisawa dai suka shiga yi da tambayar bayan rabuwa, Abdallah yana jin daɗin ganin twins da ke kwance kan gadajensu sai addu'a yake a ransa Allah sa matarsa ta haifa masa dan tsohon ciki gare ta.

"Zo yaki nan ƴar yarinya" Cewar Inna tana miƙawa yarinyar da suka zo da ita hannu, da yake yarinyar bata jin hausa dan iyayen basa mata sai bata fahimci me Innar ta ce ba ta dai ga tana miƙo mata hannu, matar Abdallahn ita ta sanya hannu ta dafe yarinyar dan bata so ta je wurin Inna aikuwa Inna ta kalleta ta taɓe baki tare da sakin dariya, sai da ta yi dariya sosai sannan ta ce.

"Wai bakya so ta zo wurina, haba ke kuwa baiwar Allah ki ji da halin da kike ciki mana yadda kike da tsohon cikin nan amma bakya gani ji kike ɗaya kike da kowa shi yasa kika ɗauki wani uban jambaki kika lafta a leɓe to wallahi baki ganki ba yadda kika san akuya ta ci dusa, haka ya miki danɓarɓar babu kyan gani, hodar ma ta miki busu-busu ita da ban fuskarki da ban"

Ƙwallah ce kawai ta kawo a idon matar, dan tana ganin Inna ta gama da ita yadda ta tsaya ta ɓata lokaci a gaban mudubi tana kwalliya amma tsohuwar nan ta ce mata wai janbaki kamar akuya ta ci dusa, duk da dai tana jin ana cewa idan mace me ciki ta tsufa komai ma ta yi bata kyau saboda yadda wasu mata ciki ke maida su. Dama dakyar ma ta samu kayan da suka shigeta duk wanda ya sanya rigar bata shiga zanen ma sai ta ga ya ƙi ɗauruwa. Mijin ne ya yi saurin kallonta yana mata alamar da ta yi haƙuri dan ba ya so su nunawa Imran sun ji haushin abin da aka musu saboda kar ya ji babu daɗi haka ta haƙura ta zauna amma ranta in ya yi dubu ya ɓaci.

"Yanzu dan Allah Halima kalli kan yarinyar can, sun jamɓara mata gashin doki a kanta kamar tsohuwar ƴar bori babu kyan gani wai su nan cinyewa ce ni wallahi ban ga ba abin so a gashin doki" Cewar Inna hankali kwance dan ita gani take dai dai take yi kuma gaskiya take faɗa.


Shiru dai ba wanda ya sake tankawa, sai ƙaran TV kawai kake ji da aka kamo tashar namun daji, matarce kallon ya ɗan ɗauke mata hankali, wani miciji da aka nuno ta gani ta ce "Daddyn Amira ji wani misiji (mijici) ka san ina son misiji " Ta faɗa hankalinta a kan TV kalla kawai ya yi bai ce komai ba dan gabaɗaya ransa a dagule yake.

Imran ne ya ce "Sadiya miƙo musu yaran mana, tun a waya Abdallah yake cewa yana son twins" Cewar Imran yana sakin dariyar yaƙe wacce bata kai ciki ba.

"Allah ya baku ƴan baiwa duka biyu mu ga ƙaryar inyamuranci" Cewar Inna tana hasaso yadda za su yi da zama da yara duka biyu masu baiwar sawaya zuwa micizai.

Tashi Sadiya ta yi ta ɗakko Husaini za ta baiwa mijin, ganin hakan Inna ta yi karaf ta ce

"Ki baiwa matar tasa mana shi sai a bashi Hassan ɗin kin ga sai su riƙe biyu a tare ko sa musu goshi" Cewar Inna tana ɗan washe baki dan ta hango diramar da za a yi saboda ganin Hassan yana miƙa ta san kwa daf yake da sawaya zuwa miciji, za ta ga ƙaryar soja. Sadiya da bata fahimci manufar Inna ba ta miƙawa matar Abdallah Husaini, ta dawo ta ɗauki Hassan da bata lura yana miƙa ba ta baiwa Abdallah shi. Sai yaba kyan yaran suke suna fatan su ma su haifi ƴan biyu.Ƴar tasu ce take ta dariya tana son a bata Hassan amma uban ya hanata yana mata magana Inna da ba sanin me suke cewa ta yi ba sai baki ta taɓe dan yarinyar bata jin hausa sai turanci.

"Za ka yi yaren nasara da kyau wallahi daga lokacin da ka ganka riƙe dumu-dumu da miciji.


"Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta yi dariya kawai tana ta kallonsu, ana jimawa sai kuwa Hasaan ya fara rikiɗa yana sawaya, babu wanda ya lura, sai da ya gama zama miciji sannan ne fa Abdallah ya zaro idanu ƴar tasa kuma sai ta matsa ta yi wurin inda Inna da Sadiya suke zaune, cikin jin tsoro, matar ma a sukwane ta tashi daga mazauninta tana zare ido ta yi wajen su Sadiya, Abdallah kuwa bakinsa ya kasa haɗa ko da kalma ɗaya ne sai zazzare ido yake ya kalli Hassan sai ya ɗago ya bi mutanen falon da kallo, jikinsa a take ya shiga mazari sai karkarwa yake . Imran kuwa tsaye ya miƙe yana so ya tallafawa baƙon nasa y karɓi Hassan ɗin dan ya ga alama ana jimawa Abdallah suman zaune zai yi saboda irin yadda fuskarsan ta bayyana tsoro muraran amma ya kasa ko da yunƙuri ne.


"Ashsha yau ake yinta wallahi a gidan nan, ga soja ga miciji ashe dai sojoji ma suna da tsoro" Inna ta faɗa tana dariya tana kallon Abdallah ba komai ke bata dariya ba irin yadda abokan biyu suke rarraba ido kamar mararsa gaskiya, shi kansa Imran kamar dai yau ya fara ganin Hassan ya zama miciji yadda yake ciccira ido kamar ka ce kulle ya ce cass dan dama a kusa da ƙofar fita daga falon yake a kan kujera amma ganin abin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login