Showing 24001 words to 25685 words out of 25685 words
Chapter 9 - CANJIN RAYUWA Book 2 Complete PDF Writing by k Mashi
kafa ta ture.ya ce,oho dai ta yi miki amfani. ba ta kula shi ba ta kwance kudin sadakin da aka bata a gefen gyalenta,ta zuba a cikin jakar,ta dauko karamin akwaiti cikin jerin akwatunanta,ta bude akwatunan tana zabar kayan da za ta sa.yawanci kananan kaya ta diba.ta bude wata jakar ta dauki kayan ciki da na shafa,sai takalmi daya ta saka jakarta mai kudi,ta rufe.ta sauka daga kan katifar.ya ce,wai ke ko fitsari ba ki ji ne,duk sanyin nan da ake yi?ta ja tsaki,ban ga gurin da zan iya tsugunawa ba.ya ce,mu shiga cikin gidan.daga nan sai ki gai da lnnata.tunda ya ambaci fitsari,sai ta ji ya matse ta har kamar zai zuba.shiru ta yi,sai ya dauko buta,mu je in raka ki.ta dauki mayafinta ta dan yafa.suka fito zaure a share fes.don tun kafin ya shiga wanka ya share.suna shiga tsakar gida,matan gidan suna ta aikace-aikacensu.ta sa gefen mayafinta ta rufe hancinta.ya ce,ki gai da su mana.ta zabga masa harara,ta ce,nuna min toilet ni kam.ya nuna mata,ta shiga da kyar ta yi yin fitsari saboda zarni da kuma rashi inda zata tsugunna.ba ta taba ganin irin wannan ban dakin ba,don ko na kauyen su dad da ta tsani shiga yafi wannan kyau.ta fito duk ta bata kafafunta.sai da ta fito ne take ta wanke kafarta,tana zubar da miyau.cikin sauri ta bar tsakar gidan.sai da ta je soro ta sauke numfashi ta soma kuka.matan gida suka yi ta kallon kallo.fatu ta ce,salo da yayi,wai kaza ta ji shikar dare.lsmail ya ce,ku yi hakuri ba laifinta ba ne,ba ta saba da ganin haka ba.suka sa dariya,gami da shewa,to a kai ta inda ta saba,ln ji fatu. shi dai fita yayi ya bar su suna ta habaici da kananan zagi.
[01/10 10:35 pm] Abdul: (47)Ta shiga cikindakin ta dauki wayarta ta soma kiran khalil.ya ce,mun kusa ki ba ni minti talatin.gudu nake yi sosai,kin ji dear ta ce,to inda nake ne ko dakin karen gidanmu ya fi shi.ran lsmail a bace,ya ce karya kike yi.lna sake fada miki karya kike yi.ta ce,dakin karenmu akwai tayils,na fa? ya ce,dakina akwai alkurani da littattafan addini.ke nan dakina yafi naki ma,duk kyawunsa.ta sake bin dakin da kallo,tana tabe baki.ta ce,tsayawa yin musu da kai bata lokaci ne. ta sake mikewa ta zage wani zif din akwati ta ciro muhimman takardunuta,ta zage jakar da za ta tafi da ita ta zuba.ta zauna ta yi tagumi,jifa-jifa tana duba agogo,shi kuma ya kasa ya tsare ya ga inda za ta. Na'ima amarya kuwa an yi barci sama-sama a gidan abbas sai takwas ta farka ta zauna zugum a bakin gado.ta dauki wayarta ta soma kiran layin momy.momy tana dagawa ta ce,na'ima an tashi lafiya?bata jira amsa ba,ta ci gaba da cewa,da dinku jikinsa fa ya tashi kamar yadda na ce miki jiya.yanzun haka mun koma asibiti.ki fada wa maigidanki.na'ima ta ce to kawai don ta san babu damar ta yi korafi a cikin wannan halin.wanka ta shiga,ta yo alwala.ta dan fi MIMI tunda ita takan yi sallah ko da dai ba kullum ba.ta zo ta yi kwallaiya,ta bude wardrobe dinta ta ciro sabuwar jallabiya mai shegen kyau ta saka,ta yafa mayafinta irin yadda MIMI ke yi,ta fesa turarruka,ta saka lallausan silifas na zaman gida,ta nufi sama abbas.ta jima a tsaye bakin kafar tana tunanin bugawa.can dai ta daure ta murda kofar,sai ta ji ta a kulle.daga ciki ta ji an ce waye?ta dan yi shiru tare da zaro ido.a sanyaye ta ce,ni ce.a lokacin ya riga ya zo zai bude kofar ya ga ko wane ne.duk da haka bai fasa ba,sai ya bude.ganin ta sai ya bar kofar a bude.ta shiga da alama wanka ya fito don ga rigar wankan a jikinsa. a hannunsa akwai karamin tawul,yana goge kansa.ta tsuguna har kasa,ina kwana?ya bata rai ya kau da kai lafiya.ta ce,da ma momu ce ta yi min waya wai dad dina ba shi da lafiya.an mai da shi asibiti.
[01/10 10:35 pm] Abdul: (48)Ya waiwayo ya kalle ta,irin kallon kashi din nan,to me zan yi masa?ln za ki je.ga ki ga hanya,amma ni bani da lokaci.kin gane?ta mike a sanyaye.har ta kai bakin kofa sai kuma ta waiwayowa,am na ce me zan dafa?ya sake waiwayowa,bana bukata. ranta ya dan sosu.ta mike ta nufi dakinta tana kuka. Bakin gado ta zauna, lallai za ta shiga matsala babba.da ma abbas bai amshe ta ba?shi ne ya amince ya aure ta don kawai yayi mata wulakanci?haka ta yi ta kuka.ko kayarwa bata yi ba har kusan karfe biyu,sai ga kannen momy,su anty rukayya.suka ce lafiya ke kuma kike kuka?anty jamila ta ce,wawiya mana,yanzu an daina wannan abin dan.kin yi daren farko a gidan miji,kiyi ta wani kuka.ta ce,ba haka bane.ta fada musu komai ta ce,ya san bai yarda ba tun farko ba sai ya ce,aa ba.sai yanzu ne zai fara yi min wulakanci?anty rukayya ta ce,ke dai sakarya ce.don wannan za ki yi kuka.ki saurare mu kiji.tunda daga ke sai shi a gidan,abu ne mai sauki ki ja raayinsa.anty jamila ta ce,ina kananan kayan nan da momy dinku ta siyo miki daga dubai?ta ce,suna cikin akwatunan da kuka zo da su.ta nuno shi,ga su can. suka je suka bude.suka ce yawwa ki gwada mu gani.ta yi ta gwadawa suna tafa mata,tare da koya mata kalolin sanya su yadda za ta ja raayinsa.ba su bar gidan ba sai da suka tabbatar da haddace duk abin da suka koya mata.ba su jima da fita ba,sai ga dangin abbas da masu aiki an kawo mata.da dattijiya da mana yarinyar dai yarinyar gwari ce,sannan ta kuko namiji.karfe tara na dare na'ima ta yi wanka sosai,ta yi gayu kamar yadda suka ce maties din ta suka ce.ta saka rigar da suka zuba mata wadda ita ce ta dace da ita a wannan dace.hannu din rigar gare ta.shi ma kulle shi aka yi kirjinta a waje.tsawo rigar bai kai guiwa ba.ta kama gashinta a tsakiyar kanta,ta yi wanka da turarurruka masu daukar hankali.ta soma rihasal din yadda za ta shiga dakin da yadda za ta tunkare shi da duk abin da suka ce ta yi.sai da ta tabbatar zata iya ta nufi saman abbas, duk da tana fargabar kar ya gwasale ta.
[01/10 10:35 pm] Abdul: (49)Ita kuwa MIMI kamar karfe shabiyu sai ga kiran khalil.ta daga ya ce,kina ji na?ta ce eh.ya ce,na iso.ta mike ta bude jaka lsmail suna tsane da mahmud a kofar gida suna tattaunawa a kan inda zai nemi dakin yanzun nan hamisu direba ya wuce bayan ya kawo mahmud sun yi sallama ya lsmail ya ce masa godiya,mahmud yana cewa,mu je mu samu malam.mahaifina kayi mai bayani,lna zaton akwai daki a gidansa na kofar guga amma can bayan gari ne,ba mutane sosai a gurin.gidan dai mutane biyu ne,amma daki uku ne ciki da falo.lsmail ya ce,to da ma ina da kudin nan.mahmud ya ce,ka san ma ba zai amshi kudinka ba. fatanmu allah yasa bai riga ya ba wai ba.rufe bakin mahmud ke nan,lsmail ya ce,amin...bai karasa ba,sai ga MIMI ta fito sanye da riga da wando damammu,sai dan mayafi da ta rataya shi kamar yadda take yi tana janye da dan akwatinta.da sauri ya nufo ta,ina za ki je?ta kalle shi sama da kasa,ta ja tsaki,ta tsallaka kwata.ya kalli gurin zaman yan majalisar kofar gidansu ba su fito ba rana.mahmud ya ce,bar ta mu bita a baya. haka kuwa tana tafe suna bin ta.sai ta tare dan acaba ta hau.su ma suka hau suna hangenta tana waya har zuwa garejin mota.tana tsayawa suka tsaya ta ciro kudi ta ba dan acaba,su ma haka.ta nufi wata mota.kafin su tsallaka su isa ga motar har sun tashe ta.lsmail ya shiga tashin hankali sosai.ya ce, mahmud barin ta za mu yi ta tafi?na yiwa mahaifiyarta alkawari. mahmud ya ce,zo mu dauki mai gulf din can ya bisu.sun nufi gurin sai suka ga hamisu direba ana sa masa fasinjan abuja.lsmail ya ce,aa me kuma ka tsaya yi?ya ce,lodin abuja zan yi,in dan kara na mai,ln samu na batarwa.lsmail ya ce,sauke sumu bi su MIMI,ta gudu ga su can sun dauki hanyar kaduna.
[01/10 10:35 pm] Abdul: (50)Nan da nan hamisu ya sauke su,lsmail ya shiga gaba,mahmud ya shiga baya.duk da halin da lsmail yake ciki bai hana shi ya yi wa hamisu direba nasiha ba.ya ce,hamisu tsakani da allah ban zaci kana cikin direbobi masu cin amanar iyayengidansu ba.sam bai dace ka yi lodi ba tare da izinin maigidanka ba.haramun ka ci.ai gara ka ce min in kara maka na mai.amma wannan cin amana ne.ya baka amana ne fa.ko ya san kana yi?hamisu ya ce,wai!ln alhaji ya ji ai na shiga uku. lsmail ya ce,ka gani ko?yana biyan ka hakkinka.hamisu ya ce, lnsha allah na daina.daga yanzun ba zan kara ba. Da yake hamisu gudu yake yi,sun hango su,har sun kusa zuwa daf da jun. MIMI ce ta gane motar gidansu.ta ce,ana bin mu. waccan motar gidanmu ce. nan suka kara gudu.gudun nasu yayi yawa.allah dai ya tsare...karan da suka ji shi ne ya tabbatar musu da cewa taya ce ta fashe ta su MIMI. daga inda suke suna hangen yadda motar take tuntsira gudi-gudi a kan titi.gaba dayansu suka hau salati.hamisu na cewa taya ta fashe shi. kuma ya taka burki.hankalin lsmail ya yi mugun tashi.suna isa gurin,motar tana tsayawa bayan ta tokari bishiya.suka fito suka nufi gurin.motoci suka tsaitsaya ana ta kokarin ciro su.duk jikin lsmail bari yake yi.wasu na cewa tun dana ga tukin da yaron nan yake yi na san zai yi wuya basu fadi ba. Nan zan dan huta.sai mun hadu a kashi na uku don jin shin su MIMI za su rayu?ln sun rayu,yaya zamansu zai kasance?wai na'ima ta ci nasara da ta hau saman abbas?mene ne labarin zainabu? Taku Halimarku K Mashi. sai na ji ku a 08081165107. lna jiran shawara ko korafi.