Showing 3001 words to 6000 words out of 25685 words
Chapter 2 - CANJIN RAYUWA Book 2 Complete PDF Writing by k Mashi
Ta zauna bakin gado,ta kamo hannun MIMI,yata ni ce mahaifiyar khalil.da sauri, MIMI ta tashi zaune.sannu da zuwa momy.wa ya nuna miki gidan nan?ta ce, ga shi nan a falo,tare muke. da sauri MIMI ta sauko daga gadon don tabbatar wa idanunta khalil dinta ne kuwa?sabbin hawaye suka soma zubo mata.ta je ta zauna a kujerar da ke kusa da shi.cikin damuwa ya ce, dubi yadda kika rame,don ALLAH MIMI ki yi hakuri.ga momy na nan na kawo ta za ta yi magana da momy dinku ko dad. MIMI cikin kuka ta ce,ba zai saurare ku ba.don sun yi nisa da shirin aura min abbas.hajiya amina ta dafa bayan MIMI.bayan ta zauna a hannun kujerar da take,sai ta ce,kar ki damu 'yata.yaya za a yi in gan shi?MIMI ta ce bari in gwada kiran sa ko zai daga,don yanzu bai damu da daga kirana ba, Sai a kira na biyu,sannan ya daga me ya faru MIMI? abin da ya soma tambayar ta ke nan,bayan ya daga wayar.ta soma kame-kame am,am da ma wannan ne, baki ne suke son ganin ka. Hajiya amina ta amshi wayar,sannu da kokari alhaji.ya ce,yawwa,wace ce?ta ce,sunana hajiya amina daga kaduna.kuma ni ce mahaifiyar khalil saurayi MIMI,wanda take so. Haushi ya kama alhaji bishir,amma sai ya danne, ya ce,to lafiya?ta ce,na zo ne ina son ganin ka don mu yi magana a kan yaran nan. ya ce,babu bukatar wata magana domin na riga na ba da ta.yanzun haka nan da sati uku ne bikin.don ALLAH ki bawa dan naki hakuri.ta ce,amma alhaji kana sane cewa ba ta so ko?ya ce,ba damuwata ba ne,kuma ke ma ba damuwarki ba ce.ln kin zo nemawa danki aure ne, tuni ya kamata ki yi haka ba yanzu ba.yanzu kam kun makara.na gode.sai an jima.ya kashe wayar.
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (9)Ta yi shiru,ta rasa me zata ce wa yaran,ga shi sun tsare ta da idanu.ta ce,ku hakura kawai.tashi khalil mu tafi.MIMI ki bi zabin iyayenki.sai kawai ta ga sun soma kuka su duka biyu.MIMI ta riko hannunta, don ALLAH momy ku gudu da ni.ba zan iya rayuwa babu khalil ba.zan mutu,don ALLAH.momy ta ce,ba zai yiwu ba 'yar nan rufa min asiri. shi ma ya ce,momy don ALLAH mu tafi da ita. uwar ta kalle shi,lallai ba ka da hankali.ta dafa kafadar MIMI,ki yi hakuri 'yata.mu yi addua ALLAH yayi mana zabi na gari.har kasa MIMI ta biyo su da kuka,har gurin motarsu.maaikatan gidan wadanda ba su san me yake faruwa ba,sai kallon MIMI suke yi.sun fi zaton mutuwa ce aka yi gagaruma.fatansu allah ya sa ba maigidan ba ne domin gudun tarwatsewar aikinsu. Na'ima ce ta kama ta suka nufi cikin falon kasa.ta zauna ta ci gaba da kuka, na'ima tana bata hakuri. daidai lokacin lsmail ya shigo falon,don lokacin karatun sa ne da yara.ganin MIMI cikin halin da take ciki, har zai koma sai ya tambayi na'ima,lafiya dai ko?banza ta yi da shi cikin salon wulakanci.ya dan yi jim,can ya ce,baiwar ALLAH kuka bai taba zama mafita ga bawan da musiba ta auka masa ba. ldan kina da bukata zan ba ki maganin damuwa da yaye bakin ciki.kila ma ki cimma burinki.duk ba su tanka shi ba har ya fice. MIMI ta fi saa guda tana kuka har kanta ya soma ciwo.na'ima ta yi lallashi ta gaji,don haka ta kira momy nafisa ta fada mata abin da yake faruwa.momy ta yi ta kiran MIMI bata dauka ba,da yake tana kasa, wayar kuma na sama.sai da ta soma jin jiri.ta mike ta nufi saman.ta jima a kwance kafin ta ji rurinta. cikin sauri ta dauka. tunaninta khalil ne,ashe momy ce.ta dauka, muryarta can kasa,ta ce, momy'momy ta ce,na'ima ta fada min komai.lna so ki kwantar da hankalinki.na fada miki baza ki auri abbas ba.ta soma kuka,kin yi min alkawari momy?ta ce,ko rantsuwa nayi miki,ba zan yi kaffara ba.don haka nayi miki alkawari.lna dai sake fada miki,ki tsaya a kan raayinki.ta ce,shi ke nan momy.
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (10)MIMI tana tsaye a windonta na falo,wanda yake kallon boys quaters da kuma lambun gidan. fararen tantabarunta take kallo masu yawa,wadanda dad ya sai mata tun shekaru da dama da ta ce tana so.hamsin ya sai mata, amma yanzu sun fi guda dubu,duk da cin su da suke yi.ta tuna ta yi kwanki rabonta da zuba musu abincinsu.sai masu aiki ke ba su.duk da kayan barci ke jikin ta,haka ta sauka. na'ima tana cewa ina zaki? ta ce,zan duba tantabaruna ne.tunda aka soma matsalolin nan ban je gurin su ba.ta kicin ta bi zuwa barandar baya,inda nan abincinsu yake.ta diba ta watsa musu.duk da ba safiya bace,yanzun lokacin da ta saba watsa musu,sai ta ga suna nan da yawa. har ta yi mamakin hakan, domin da rana suna fita. Kamar an ce waiga,sai ta hango malam lsmail yana shanya a gefensu.da alama ya wanke kananan kayansa na ciki ne.take zantukansa suka fado mata. in kina bukata zan baki maganin yaye damuwa da bakin ciki.kila ma har ki cimma burinki.lna ya san tana da wani buri? kodayake shi malami ne, kuma ta ji ana fadin malamai suna yin magani.ta tuna mina kawarta ta taba ba ta labarin cewa kishiyar mamansu ta yi wa babansu magani,sai abin da ta ce.a fili ta ce,zan nemi taimakon malamin nan, amma ta yaya zan yi masa magana? Da wannan tunanin ta hau samanta.ta jima kafin ta yanke shawarar kiran na'ima.bayan ta daga ne,ta ce,ina son ki je ki amso min lambar malam din nan mai koya mana karatu.na'ima ta dan yatsina,ba ki san ba na son zuwa boys quaters ba sam.bari in tura polina.MIMI ta ce,aa ki sa malam hamisu kawai ya amso miki ki kawo min.ta ce,ok. Na'ima ta amshi wayar MIMI da ke hannunta ta saka mata lambar lsmail,ta yi mata saving da malam.ta mika mata.MIMI ta ce,aje kawai.har na'ima za ta fita, sai kuma ta dawo.sis wai me zaki yi da lambarsa? MIMI ta kalle ta,ki je kawai. kar ki damu sai kin san dalili.tun fitar na'ima,MIMI take tufka da warwara a kan kiran malam lsmail.ln ta kira shi me zata ce masa?kuma yaya ma zai dauki zancen nata.
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (11)Kuma yaya ma zai dauki zancen nata? wanan tunanin shi ne ya dauke ta har zuwa karfe takwas din dare,wanda har lokacin ba ta tsai da matsaya ba. Sallamar mahaifinta ne ya zaburar da ita cewa an bude kofar.ta waiwayo,ta dube shi.kwanaki kusan hudu ba ta sa shi a ido ba, domin yana fushi da ita. cikin in-ina ta amsa sallamar, ta dinga kallon sa cike da kewa.ya zauna kusa da ita.cikin sigar lallashi ya ce,uwata ta kaina.ta dube shi,dad na yi kewarka.don ALLAH ka yi hakuri a kan abin da na yi. ya ce,kar ki damu.kina ji na MIMI,ki tashi ki je ga abbas can ya zo don ku tsara irin shagalin bikin da kuke so lokacin bikinku,ku zabi kasashen da za ku tafi shakatawa. MIMI ta yi shiru tana tunani,kamar ta amince,sai kuma ta tuno zance momy nafisa da ta ce duk runtsi ta tsaya a kan raayinta.don haka sai ta ce,dad don ALLAH ka taimake ni. wallahi dad ba na son shi. ya ce,"what?! lna cewa mun gama wannan maganar.ya rike kansa yana tunanin yadda zai bullo mata.can ya saki ya dube ta cikin lalama.MIMI ki yi nazari da kyau.tunda kika fito cikin mahaifiyarki nake dawainiya da ke.na fifita ki cikin 'ya'yana.na yi miki dukkan gata.MIMI zan tambaye ki,na taba neman wani abu gurinki? ta ce,dad,ni ba ni da komai da za ka nema.ni ma da kai nake takama. ya ce,to yau ina neman alfarmarki,ki taimake ni ki min biyayya,ki auri abbas.ta ga kamar zai sauko ya runsuna mata.sai ta yi sauri ta ce,na amince dad.ta soma kuka wi-wi.ya rungume ta.na gode 'yata. ni da ma na san irin son da kike mini ba za ki ba ni kunya ba.daina kuka.ki share hawayenki.ki je ku yi magana.ln kun gama,ni ma ina son mu yi magana da ke.za mu je store din wani abokina ki zabi kalolin gadon da kike so.gidanki dakunan barci shida ne; gaba dayansu zan zuba miki gadaje na alfarma 'yan dubai da chaina da lndiya. zan nuna miki wata mota da na yiwo miki oda.ba ta karaso ba.amma hotonta yana cikin laptop dina don ki yi yawon amarci in kun dawo....
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (12)Shakatawa tashi maza ki je kin ji MIMI. MIMI ta mike cikin kasala ta nufi dakinta.mayafi kawai ta dauko,suka jera da mahaifinta har kofar falon baki ya raka ta.sai da ta shiga sannan ya dawo. Ta zauna kujeri biyu tsakaninta da abbas.ya mike ya dawo wadda suke daf da juna ya zauna. sabon kuka ta soma.abbas ya ce,haba MIMI,wai ta ina ALLAH ya rage ni ne da kike ta ki na har haka?ta dago ta dube shi,"Ya rage ka ta soyayyata.abbas don ALLAH ka taimaka min ka rabu da ni.khalil kadai nake so.ya tausasa murya,MIMI ki ba ni dama ni ma in nuna miki kalar tawa soyayyar. na yi miki alkawarin zan koya miki sona har sai kin manta cewa an taba halittar wani da namiji a doran duniya in ba ni ba. Ta ci gaba da kukanta.ya ci gaba da fadin,gobe karfe goma zan zo mu fita.ki fada ma kawarki amina, zan zo da abokaina don mu duba guraren da za mu yi shagalinmu.me da me kike son mu yi?ni dai ina son dinner. Ta ja tsaki,don ALLAH ka bar ni,ka shiga tsakani na da mahaifina.ya ce,kin kasa yi masa biyayya ne MIMI?me zai sa ba zaki yi wa mahaifinki sakayyar son da yayi miki ba?ta mike,zan je in kwanta,kaina ciwo yake.ya ce,ba ki ba ni amsa ba.MIMI ta ce,ba ni da amsar da zan ba ka.amma ka sani in ka matsa cewa sai ka aure ni,nadama da dana sani sune karshen lamarin. shi ma ya mike, ban damu da su ba MIMI, saboda ban taba sanin su ba.kada ki manta gobe karfe goma za mu zo. fatana za mu same ki da kawarki.suka fito a jere.ta ce,ban taba ganin mutum mai son kai irin ka ba.ya ce, ban taba ganin mara tausayi irin ki ba.ko barci fa bana yi.amma ban damu sosai ba,da kin zama a gefena,zan rama duk barcin da na ci bashi.tsaki ta ja,har yanzu ban taba hasashen hakan ba.ko cikin mafarki aurenmu ba zai kasance ba,na yi ma kaina alkawari.daidai lokacin suka iso babba falon,ya runsuna ya yi wa dad bankwana tare da sanar da shi cewa gobe za su fita don duba guraren da ya dace su yi bikinsu.dad ya ce ba damuwa,sai ka zo.ya kalli MIMI wadda ke shirin...
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (13)Ya kalli MIMI wadda ke shirin yin samanta ya ce,ki taka masa mana zuwa gurin mota.ba ta yi gardama ba, suka fita. Ya dube ta, nawa kika sa in auren ya kasance?ta ce,in har auren nan ya kasance,na yi maka alkawarin halaka kaina.ya waigo ya dube ta,ni kuma nayi miki alkawarin hana hakan faruwa.sannan zan yi kokarin ganin mun samu 'yan biyu a haihuwarmu ta farko.rasa me za ta ce ta yi,sai ta ja tsaki,ta koma ciki tana jin shi yana cewa,mu kwana lafiya. Dad ya ce,zo uwata zo ki ji.ya bude laptop dinsa ya dinga nuna mata kalolin kayan kicin din da momy nafisa ta siya ta turo masa ya gani.ya ce,suna da kyau, sun yi miki?cikin kosawa ta ce,eh.ya nuna mata motarta.motar ta ja hankalinta don ta shekara mai zuwa ce,amma ga shi an sai mata cikin wannan shekarar.ya ce,bari ki ga fa irin gadaje da abokina ya turo min.su ma sai kin zaba. Ta kalle su,ta kalli dad, sun yi yawa.ya ce kar ki damu uwata.zan yi miki duk abin da kike so.zan kashe ko nawa ne gurin auren nan ba tare da jin cewa na yi asara ba.ribar mai daya in aka bani kwangilarsa,zan ribanya dukkan kudin da na kashe. MIMI ta mike.zan sha magani dad,zan kwanta ne. ya ce,to je ki kwanta.ya fada miki za ku fita karfe goma ko?ta ce,eh.ya ce,to sai ku je har da na'ima.ta ce,to.A sama MIMI ke ta nazarin abubuwa.zuciyarta ta fi aminta cewa ta bi umurnin mahaifinta.dubi duk daular da yake shirya mata. gaskiya bai kamata ta bari a ji su ba.ita da mahaifinta.hakuri shi ne kurum mafitarta.za ta huce haushinta a kan abbas ne kurum,wanda ya dage cewa sai ya aure ta. Har ta kwanta da nufin barci,sai agogonta ya buga sha daya.kallon agogon ya zo daidai da ringin din wayarta.khalil ne.gabanta ya fadi.shi da take tunanin shafe babinsa,amma ba ta iya share shi,don haka ta daga.cikin sanyin murya ta ce,dear,ina ka shiga na kasa samun ka a waya?ya ce,na yi kokarin na hakura da ke ne,shi ya sa na kashe wayata,sai na ga ashe ba zan iya ba.zan mutu MIMI.don ALLAH ki fada min yaya za mu yi."
[01/10 9:45 pm] Abdul: ya soma kuka.
itama kukan ta soma yi.
sai kuma ta tuna da batun malam Isma'il. da sauri ta CE, yauwa Khalil zanyi wa malam din nan magana, ko zai bamu magani.
ya ce AI ba irin shine masu yin maga ni ba.
ta ce bari kaji abin da ya CE min...
nan ta fada masa yadda sukayi.
ya CE, OK, ki kirashi yanzu.
sai dai ina so ki Sani ba mu da ishashen lokaci, sabo da kullum kwanakin aurenki kara matsowa yake.
ta CE, to bari in kira shi.
zan fada maka duk yadda m kayi.
ba tare da wani dogon nazari ba, mm ta soma kiran Layin Isma'il.
ya gama shafa'i da wururi kenan, yana kwance kan doguwar dar dumar, duk hankalin shi ya koma katsina, gani yake kamar akwai abin da mahamud yake boye masa.
yana ganin cikin satin nan zai koma gida...karshen wata yayi mashi nisa, duk da saura kwanaki takwas watan ya kare...
Ringing din wayar Sa ne ya katse masa tunani.
cikin sauri ya duba, bai San lambar ba, amma yadda yaga numbobin ya San cewa na musan man ne.
ya daga tare da sallama, yar siririyar murya CE, ta amsa da helo! ya sake yin sallama, ta CE, ni ce mm.
ya CE, baki amsa sallamata ba..."
[01/10 9:45 pm] Abdul: Wanda ya kasance ba ya qmsa sallama wajibi ne a cikin addini.
cikin kosawa ta amsa, sanan Tace, kasan dalilin kiranka..?
ya CE, a a...Tace, ka CE, zaka bani maganin bakin ciki da, yaye damuwa.
sanan kace, zan iya cimma buri na.
Isma'il yayi dan murmushi, amkar yana gaban ta, sanan ya CE, kwarai kuwa...ta CE, to don Allah ka tai maka min ina cikin damuwa, mahaifi nane .yace, dakata!
ba sai naji damuwar ki ba, ko abin da kike ciki ba, sanan zan taimaka maki.
ta ce , nasani malam.
INA so be kawai in fada maka, kila zaka tausaya min cikin gaggawa..
ya CE, Allah ne me taimako.
tun da kin zabi ki fada min, INA sauraron ki.." ta CE, dady nane zai yi Mun auren dole...INA kuma da Wanda nake so.
wlh mlm ni dashi Muna cikin wani hali.
shine muke son mafita.
Isma'il yace, mafita dai ita CE komawa ga Allah. Zaki: ya tashi cikin dare..?...ta CE, zan iya ko mai mlm don in cin ma buri na.
ya CE ki tashi karfe ukun dare kiyi alwala, kiyi sallah raka'a biyu ko sama da haka.
[01/10 9:45 pm] Abdul: ki fada wa Allah da muwarki.
in sha Allahu Allah zai yaye maki halin da kike ciki.
sanan ki yawaita zikirin Allah da karatun Alkur'ani mai girma.
ba wai sai can cincikin Alkur'ani ba, ko kanan surorine kiyi ta karanta su, Zaki sami waraka.
Mimi dai shiru, tayi, yana magana ita tana kuwa tana tunanin ta daban...to, shi wanan malamin da yake cewa tayi sallah, baya ganin cewa da ba ta damu da yin sallah ba, yanzu da matsala ya sameta, sai kuma ta wai wayi sallar...?...tam kar ya shiga zuciyar, ta, ya CE, kar ki dubi yawan zunubin ki, matsawar kika t ba, Allah zai yafe maki kurakuran ki sanan, yana da kyau kiyi adu'ar istihara, wato Neman zabin Allah kafin kikyi zabin mahaifin ki.
ta CE, to malam AI ni ban iya ba...duk abin da ka CE min inyi din nan bansan ta inda zan fara ba...
ya CE, in kin amince sai in koya maki yadda zakiyi.
ta CE, to, amma ka bari zan kiraka.
Khalil, ta kira, ta fada masa ko mai.."
[01/10 9:45 pm] Abdul: ki fada wa Allah da muwarki.
in sha Allahu Allah zai yaye maki halin da kike ciki.
sanan ki yawaita zikirin Allah da karatun Alkur'ani mai girma.
ba wai sai