Showing 12001 words to 15000 words out of 25685 words
Chapter 5 - CANJIN RAYUWA Book 2 Complete PDF Writing by k Mashi
babban falon nasu. sai ta yi sanda ta fice.da gudu ta ja mota suka tafi. Ta dubi khalil,yanzu ina muka nufa?ya ce,kaduna. don in muka ce za mu kwana a abuja,da safe za a kama mu.haka cikin dare nan suk dauko hanyar kaduna,gudu suke yi sosai. ga shi lokacin sanyi.ga MIMI ba ta son sanyi,kuma kayan jikinta irin na amare ne,ba na dumi ba.ta kudundune duk da cewa khalil ya cire t-shirt din sa ya bata ta dora a kan kayan jikinta.shi kuma ya zauna da singileti.zuciyar MIMI ta kasa natsuwa,wani gefen yana fada mata cewa ba ta kyauta ba,za ta yi nadama,ta kunyata mahaifinta.wata zuciyar kuma tana zuga ta da cewa ke ki tafi kina kan daidai.alamarin dai ga shi nan.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (15)Amma da yaje daki na musamman suka kama,sam ba ya fitowa ko kofar daki.duk abin da suke so sadau ke zuwa ya sai musu.su kuwa su momy nafisa ba su ankare ba,suna can suna ta hidimar ganin kowa ya samu abinci. a zatonsu tana can suna hotuna da kawayensu sai lokacin da na'ima ta zo tana cewa momy ina sis MIMI?ga abbas sun zo da abokansa.nan fa aka shiga neman amarya,ba ta babu dalilinta.hankula suka tashi. nan dai biki ya kare.momy nafisa kuka wi-wi.nan ta kira alhaji bishir tana fada masa cewa MIMI ta zo gida?ya ce babu wanda ya zo gidan nan.shi ma zuwansa ke nan.daidai lokacin da suke yin wayar da a ce ya waiwayo da zai ga MIMI,tunda gilashi ne ya raba falonsu da nasa. Ta ce masa,to MIMI dai an neme ta an rasa ta,ko kasa ko sama.har zuwa sha biyun dare ana ci gaba da neman ta lungu da sako, banda wayoyi da ake ta yi don ji gurin abokanen arziki. matuka hankalin alhaji ya tashi sosai.alhaji akilu ya kira shi yana jajanta masa. ya ce,amma alhaji bishir da ma yarinyar nan ba ta hakura ba?alhaji bishir ya ce,ta hakura mana.ga shi ana ta biki.sai yau a ce ta gudu?alhaji akilu ya ce,baka ganin ko yaron da suke yin soyayyar ne ya zo ya sace ta?alhaji bishir ya ce, komai zai iya faruwa.amma bari mu gani zuwa da safe.alhaji akilu ya ce,in ko ya tabbata yaron nan sace ta yayi,lallai babu abin da zai hana shi zaman gidan yari.ka ga halin da abbas yake ciki kuwa?ya ce,ko ni ma ba zan kyale iyayansa ba bare shi,tunda daga gani ba da yardarta ya sace ta ba, domin bata bar wani sako ba,ba ta dauki komai na sawarta ba.alhaji akilu ya ce,kun kira lambarta?ya ce tana ta ringing ba ta daga ba.kusan karfe dayan dare alhaji bishir ya kira hajiya sauda tana barci,ta dauka, tana fadin,alhaji lafiya?ya ce ina fa lafiya,an sace MIMI.ta diro daga kan gado.an sace MIMI kuma?ya bata labarin komai hajiya sauda ta ce,ko dai guduwa suka yi tare da saurayin nata?ya ce, bana tunanin haka,ta nuna min ta hakura.kuma sun shirya komai da mijinta, har kudi ta cire a account din ta don gyaran jiki.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (14)Dayan dare suka shigo garin kaduna.sadau abokinsa shi ne ya kawo shawarar su shiga cikin wata unguwa su nemi otal,kar su kama na bakin hanya.ta titin kagoro suka shiga,inda suka sami wani otal suka kama.MIMI ta ce su kama mata dakinta daban khalil ya ce,dear za ki iya kwana ke kadai?ta ce,eh mana kar ka damu.ta yae,shi ke nan. daki biyu suka kama a sama.khalil ya kalli sadau bayan sun kwanta,abokina ina kake ganin ya dace mu je?sadau ya ce,gobe ku shiga motar sakkwato ko zamfara.ba za a yi tunanin za ku je can ba.khalil ya ce,ni da lagos na so mu tafi,mu boye kamar na sati daya.sadau ya ce,kai banza ne.wane sati daya.ai in ni kai sai na dinke yarinyar za mu fito. yadda dole za a aura min ita.khalil ya tashi zaune,ban gane ba.sadau ya ce,ina nufin,yayi kwatance da hannunsa da cikinsa.khalil ya ce allah ya sawwake.ba ni da niyyar in cutar da MIMI zan barin mu yi halastaccen aure da ita. sadau ya ce,ka ji matsalarka.a shawarwarin da na baka,wacce ce aka samu matsala?na ce ka sai da gwal din mom dinka,mun sai da na ce ka dauke ta ku gudu.ba ga shi ka yi nasara ba?khalil ya ce,ban dauke ta da niyyar aikata wani abu ba,sai don in fid da ta daga auren wani na.kai dai naka da safe ka kai mu garejin mota mu tafi.kai kuma koma gidanku mun gode. MIMI kuwa ta kasa barci, sai juyi take yi.wayarta tana,silent,amma tana kallon kira.da wani ya yanke,wani zai shigo da farko ta ki dubawa,amma daga baya sai ta duba.kiran dad dinta ne da momy nafisa har da su na'ima. kuka take ta tayi tare da tausayin mahaifinta.ji take kamar ta daga ta ce su zo su dauke ta,kuma ta amince za ta auri wanda suke so.amma sai shaidaniyar zuciyarta ta kangare,ta kuma hana ta aiwatar da hakan.da zazzabi ta farka tare da ciwon kai mai tsanani,don haka sai batun tafiya ya fasu.sun fita suka sayo mata doguwar riga da hijabi ta saka,suka dauke ta zuwa asibitin biba.gado likita ya bata,don tana cikin damuwa.hankalin khalil ya kara tashi, tsoron sa kar wanda ya san shi ya gan shi burinsa su bar kaduna,
[01/10 10:34 pm] Abdul: (16)Ba ta dauki komai ba. hajiya sauda ta ce,allah ya kyauta.amma a zuciyarta tafi yarda cewa MIMI kudi ta diba suka gudu.ta ce to yanzu wane mataki ka dauka?ya ce,mun sanar da yan sanda,gobe za mu je kaduna gidan iyayensa. hajiya sauda ta ce,to ku kuwa hada da addua. bayan sun yi sallama da kansa ya taka gefen masu masu aiki ya kwankwasa kofar dakin lsma'il ya yi sallama ya amsa,don lokacin yana ta juyi cikin damuwar rashin masoyiyarsa zainabu.jin muryar alhaji ya bude kofar cikin fargaba.ya ce.alhaji lafiya?ya ce baka ji abin da yake faruwa bane?lsma'il ya ce,ban ji ba alhaji.a zatosa ma barayi ne suka shigo gidan.alhaji ya ce mu shiga daga ciki.a tsakiyar dakin suka yi cirko-cirko. alhaji ya ce,malam lsmail a gurin shagalin biki aka sace MIMI.aka sace MIMI?lsma'il ya maimaita.alhaji abbas ya ce,na zo gurin ka ne ina son a taya mu da addua kafin gobe in samu malamina saboda ya duba min inda suka boye ta.lsmail ya ce,allah ya kyauta,ya kuma bayyana ta sai dai alhaji baka tunanin ko sun gudu ne? alhji ya ce,bana tsammani, tunda bata bar wata alama da za ta nuna hakan ba.ba ta dauki kaya ba.lsmail ya ce haka ne.shi ke nan insha allah zan taya da addua. ikon allah a gabana suka hau mota alhaji da zasu tafi. to ni dama muna yin isha'i,na yi shafa'i nake shiga in kwanta da wuri saboda ina tashi cikin dare. alhaji ya ce,to bari mu je mu yi sauraro.lsma'il ya ce allah ya jishe mu alheri. bayan fitar alhaji,lsmail yayi ta mamakin MIMI.tabbas sun gudu ne,tunda ta fada masa cewa sun samu mafita,ya kira layinta,yayi ta ringing har ya tsinke.haka yayi ta kira har ya gaji.alhji kam yana tafe yana tunanin maganar lsmail haka sauda ta ce ko sun gudu ne.shi ma gashi ya ce hakan.momy nafisa ya samu ta zabga ta tagumi bakin gadonsa.ya dafa ta,kar ki damu nafisa za a gan ta.ni damuwata ma da sauda ta ce ko dai guduwa suka yi haka ma malaminta ya fada min yanzu.sai dai ina shakku don na san MIMI baza ta guje ni ba ta bi wani sakarai.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (17)Momy nafisa ta ce,haba ba za ta gudu ba.don ta tabbatar da ya zai yi in gudun ta yi,sai ta ce,ko ta gudu ma,ai dole ta dawo.ya ce,me kika?ya mike cikin tashin hankali,ya ce kuskure mafi girma da MIMI za tayi shi ne ta guje ni.kin ji na rantse miki,in MIMI guduwa ta yi ta kunyata ni,to ni kuma sai na yi mata abin da ba za ta manta da ni ba wannan alkawarina ne. tunda asubahi momy nafisa ta shiga dakin na'ima ta ce,tashi ki ji,ga fa dama ta samu.na'ima ta gyagije daga barci.ta ce wannan gudun na MIMI yayi matukar zuwa mana a daidai.yanzun abu daya ya rage mana.shi ne dad dinku ya san cewa tana sane ta bar gida.na'ima ta ce,in ya sani mene ne?nan momy ta sanar da ita alwashin da ya ci,ta ce,kuma tabbas MIMI ba sace ta aka yi ba. ga shi na yi ta kiran ta bata daga ba.amma zan ci gaba da kira.ln ta daga zan sa ta fada wa alhaji cewa ta gudu ne.safiyar ranar lsmail yana masallaci zaune,alhaji ya fito zai fita.ya nufe shi ya gai da shi cikin girmamawa.ya dada jajanta masa.alhaji yayi godiya.lsmail ya ce,sai dai jiya na yi mantuwa.sai bayan ka tafi na tuna.alhaji ya ce,ta me?ya ce,alhaji duba haramun ne a musulunci.akwai inda yake zama shirka ma.wato mutum ya fita daga musuluci.alhaji ya ce, istihara ce ai za a yi malam lsma'l ya ce,alhji ai istihara kai ne zaka yi da kanka,ba wani ne zai yi maka ba, kamar yadda wasu malaman suke cewa don su ci kudinku.alhaji ya ce, shi ke nan.ana jira na.ln na dawo zamu yi maganar. bayan ya koma daki ne ya ga kiran hajiya sauda. nan take ya kira ta.cikin girmamawa.ya gaishe ta,ya jajanta mata abin da ya faru.ta ce,lsma'il na kira ne ina son a taya ni da adduar allah ya tsare yarinyar nan, don ina zaton guduwa ta yi tare da yaro nan.lsmil ya ce,ina yi hajiya ni mana fi zaton sun gudu ne.ta ce,ina amfanin gatan da ya nuna mata.ai da ma kuskure ne mutum ya gina dansa a kan cewa duk abin da yake so sai ya samu.gara ka nuna wa yaro cewa akwai kuma kaddara.amma sam ita ba ta san wannan ba.duk abin da take so zai mata.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (18)To yaya yanzu ba za ta turbure ya bata wanda take so ba?lsmail ya ce, haka ne.a ransa ya ce da ma hausawa sun ce,ka sa danka kuka kafin yasa ka a fili ya ce,allah zai saukaka mana lamarin da yardarsa. hajiya sauda ta ce,allah ya sa.abbas kuwa shi ma cikin tashin hankali yake.a nasa zaton an sace ta ne,tunda ya ga gab da bikin ta saki jiki.da alamu ta yarda za ta aure shi.cikin mutunci ta amshi kudin gyara jikin da ya kai mata.ranar da aka yi family night sun yi ta hotuna tare.a ce an sace ta.ko dai masu yin garkuwa da dan adam ne?alhaji akilu ya ce kar ka damu.ln ma sune zamu ba da ko nawa ne don su sake ta. Alhaji bishir ya sanar da duk masu kofofin sadarwa don neman ta,ko in ce cigiyarta.da kamfanin layin MTN aka gane cewa tana kaduna,don haka can suka dosa.kwamishinan yan sanda na kaduna shi ne ya kira mahaifin khalil ya sanar da shi cewa ga iyayen yarinyar da dansa ya gudu da ita sun zo.bai yi kasa a guiwa ba ya iso gidan kwamishinan,sun tattauna da mahaifin khalil,ya ba su hakuri,tare da tabbatar musu cewa dansa khalil ya gudu tare da yarsu.ya fada wa kwamishina cewa in ya zo a kama shi kamun barawo don ya dauke sarkar mahaifiyarsa. Daidai lokacin MIMI ta daga wayar momy nafisa, bayan momy ta tura mata message cewa ta daga su yi magana,ta san dai tana tare da ita a kan komai, bayan khalil ya karanta,sai ya ce,MIMI momy nafisa ce, ki daga wayarta.na san za ta taimaka mana.ta tashi zaune ana yi mata karin ruwa.ta daga.cikin sauri momy nafisa ta ce, MIMI kuna ina ne yanzu?ta ce momy yaya dad?wane hali yake ciki?ta ce,dad dinki yana cikin matsananciyar damuwa.yana tunanin ko an kashe ki ne,ko an sace ki.kuma sun ce za su daura aurenki gobe,ko gawarki aka gani dai abbas ne mijinki.don haka ki rubuto masa text cewa kin gudu ne,don ba ki son abbas.ke ba za ki dawo ba har sai ya amice zai baki khalil.kin ji ko,ki yi haka yanzu.na san zai ce ki dawo.cikin kuka MIMI ta ce,ni fa na soma yin nadama momy.zan hakura ne kawai in auri abbas.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (19)Wallahi ina jin tausayin dad dina.momy nafisa ta ce,aa ki yi abin da nace. 'yan gidan su abbas din ma da suke ta zagin ki,wai kin bi namiji.wa ya san abin da za kuje ku yi?MIMI tana kuka tace shi ke nan zan yi momy.ta ce,yanzu nan za ki yi,MIMI tana kuka tace to Suna cikin yin musabaha don yin sallama message din MIMI ya shiga wayar dad dinsu.bai yi kasa a guiwa ba,ya bude ya soma karantawa kamar haka: Ka yafe ni dad in na bata maka.na yi kokari in yi maka biyayya,amma na kasa.ba na jin zan iya zama da abbas a matsayin mijina.zan dawo gida,in ka amince zaka bani wanda nake so.ya dago ya kalli alhaji lsa,wanda dashi suka zo kaduna,ya ce,ka gani ko? karbi ka karanta.ka gani guduwa suka yi ba sace ta yayi ba.ni kuma zan nuna mata cewa ta yi mummunan kuskure. Da kyar alhaji bishir ya kai cikin gida saboda ciwon kai.amma kafin ya kai tsakiyar falo,tuni ya zube kasa.sabon alamari ke nan wanda yata da hankalin mutan gidan.nan da nan aka yi asibiti da shi.ya farfado,inda aka tabbatar masa jininsa ya hau sosai. an gano yana da ciwon sugar.cikin abin da bai fi minti talatin ba,dukkan iyalansa sun samu labari kuka sosai hajiya sauda ta yi domin ta san MIMI ce silar komai. karfe sha daya momy nafisa ta kira na'ima ta ce,ga lokacinki fa yayi daga yanzu zuwa da safe.na'ima ta ce,shi kenan momy ya farka ne?ta ce,eh in ya farka yana tambaya ta wai ga shi gobe daurin aure.bai san yadda zai yi ba.na dai lallaba shi.ki shirya zan fita in sa hamisu direba ya dauko ki,don shi ya kawo su kawunku da suka zo biki.tana fitowa ta leka ta ce ma hamisu ya je ya dauko na'ima.alhaji lsa ya ce ta yi me da daren nan? momy nafisa ta ce,kuka take yi sosai.kuma ta ce tana da magana da shi,cikin kuka na'ima ta shigo dakin momy ta rungume ta,yi shiru mana.ai jikin da sauki. kalle shi har ya farka. Ta isa gurin sa,dad ta kama hannunsa.dad kar ka damu ni na amince in har abbas yana so na.gobe a daura auren da ni.wallahi dad bana son in rasa ka.ya yunkura zai tashi.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (20)Momy ta rike shi.ya jingina,ya kama hannuwan na'ima,da gaske kina son abbas?ta ce,ni ban san so ba dad.amma zan koye shi a gidan abbas.zan so shi in ya zama miji gare ni.alhaji bishir ya rumgume ta.na gode yata.allah yayi miki albarka.ya kalli momy ta ce,na ji.allah yayi miki albarka.kar ka damu,ka kira alhaji akilu din.bai san ma akwai matsalar bai san kana asibiti ba.ln ya zo sai ku tattauna.ya ce,haka ne. ke ma din allah yai miki albarka.momy nafisa ta ce, amin.ya ce,leka ki kira min alhaji lsa. nan suka shigo,ya sanar da su abin da naima ta ce,suka yi ta sa mata albarka alhaji ya ce,to kowa ya koma gida,insha allah,biki babu fashi.momy ta ce,alhamdulillahi ga shi da ma yan biki sun cika gidan,yan masari da yan malumfashi.hajiya binta da ma bata taho ba,tana shirin zuwa ta ji labarin batar amaryar,don haka ta dakata.yanzu kuma sai ga labarin ciwon alhajin don haka dole gobe sai abuja. A daren,alhaji bishir ya sanar da alhaji akilu komai. da yake kowannensu ba damuwar 'ya'yan bane,su dai hada surukuntar ne kawai don cimma burinsu.ba tare da neman shawarar abbas ba,ya amince da auren na'ima sai da asubahi bayan sun dawo sallah yake sanar da abbas din canjin da aka samu.nan take abbas ya ce, shi sam bai so na'ima alhaji akilu ya ce,ba damuwata ka so ta ba.ln aure ya dauru burina ya cika.ka aure ta in ya so daga baya ka auri wadda kake so.abbas ya ce,MIMI nake so.ln kuma ina auren kanwarta yaya zan yi in aure ta?ya kawo iyaka wuya,cikin fada yake cewa,kai ma za ka yi min irin abin da 'yar alhaji bishir ta yi masa ne?to bari ka ji. ba zan dauki rainin wayo ba.kawai kayi abin da nace. dukkan su ai mata ne.abin da waccan ke dashi,ma tana dashi.yanzu an daina auren soyayya,sai auren me zan samu.ka gane?na fada maka nasarar da zan samu ta hulda da alhaji bishir so kake sai ka ja min asara ne?abbas ya ce,shi ke nan dady,na yarda har da hawaye ya bar gurin.a dakinsa kuwa yaci kuka sosai domin ya kallafa rai a kan MIMI.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (22)Ba ki zo bada 'yata ta bata,amma da jin an ce mijinki babu lafiya,kin debo yara kun taho.sauda ta ce, shi ne dole na,yarki,ai ba dole na ba ce.suka gaisa ta ce,ina muktar?hajiya sauda ta ce,mun yi ta jiran sa bai karaso ba.na ce mu tafi,ya zo.sauda ta isa gurin mijinta ta zauna daf da shi.ya kama hannunta.har kin zo? ta ce,jiya ban yi barci sosai ba,amma yadda na ga jikin naka,alhamdulillah.ya ce, ashe ina da ciwon sugar ne.kwanaki kina ce min duk na rame.sugar?sauda ta tambaye shi.ya ce,tabbas har ya soma yi min yawa. yanzu dai likita ya dora ni kan magani da dokoki da kuma abincikan da zan kiyaye.hawaye suka zubo a idon sauda.ya dafa ta,aa kar ki yi kuka sauda,insha allah zan warware,ta ce, allah ya baka lafiya.ya ce, amin.ya kalli abba,ina takwarana?abba ya ce, suna gida.za su zo da mamansa.alhji ya ce,madallah,allah yayi maku albarka.kun ji abin da MIMI ta yi min ko?ya dinga kallon su da dai-dai,ya dan sunkuyar da kai.na