Showing 1 words to 3000 words out of 25685 words
Chapter 1 - CANJIN RAYUWA Book 2 Complete PDF Writing by k Mashi
CANJIN RAYUWA
Book 2
Halima Abdullahi k Mashi
arewanovels.com.ng
(1)Ahaji bishir ya kosa ya isa gidansa don kai wannan albishir.haka nan MIMI ta kosa matuka dad din nata ya dawo don ta sanar da shi labarin masoyinta khalil.momy nafisa kuwa tana cikin damuwa,tana ta tufka da warwara a kan yadda zata hada fitina tsakanin MIMI da mahaifinta. A haka alhajin ya iso gidan,cikin doki.tun daga shigowarsa falon yake zuga kiran nafisa!nafisa ta fito cikin sauri tana cewa, "Alhaji ga ni.lafiya kake ta kira na?"ya ce,"Lafiya lau. sai alheri." Ta amshi jakar hannusa da hularsa da malum-malum. "Mu je ciki ki ji albishir!"Gabanta ya fadi. wani sabon kasuwancin ne? ya ce,"wannan duk ya wuce nan.sai da suka zauna,sannan ya ce,"Abbas, ashe MIMI yake so?"Gaban momy ya fadi. ya ci gaba da cewa, "gaskiya na yi murna sosai.burina zai cika."ta yi dan yake,ta ce,gaskiya kam, da abin zai yiwu,zaa yi murna."Ya ce,"me zai hana shi yiwuwa?daina fadin haka. Nafisa ta ce,dazun take sanar da ni cewa saurayinta zai zo daga kaduna gaishe mu. ya zaro ido yana kallon ta.ya ce, wane ne shi?wannan ba gaskiya ba ne.lnda MIMI tana da wani saurayi,nine mutum na farko da zan fara sani,domin kin san babu wani abu da take boye min.ba ta da aboki ko kawar da ta fi ni. Nafisa ta ce,haka ne, amma jiya tayi min zancen. da alamu kuma tana son sa sosai.ya daga hannun, alamun dakatarwa.sannan ya sa kai ya fita daga dakin.kai tsaye saman MIMI ya nufa.tana kwance a kan kujerarta,catin suke yi da khalil,tana ba shi labarin halin da take cikin na damuwa.shi ma duk hankalinsa ya tashi.a sama ta ji muryar dad yana cewa, uwata tashi zaune da sauri!tana fadin dad ka dawo ne?ban sani ba,ai da na sauko. Ya zauna kusa da ita.yau ina cikin farin ciki ne MIMI.burina zai cika.ya kama hannunta,kin san na dade ina addu'ar ALLAH ya kawo miki mijin da zai kula da ke ko?gabanta ya fadi,ta ce,"eh dad."ya ce,"to ga abbas dan gidan minista. mahaifinsa yake sanar da ni tsananin son da abbas din ke miki.....
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (2)Wannan lamarin ya zo a daidai da burina na hada surukunta da minista. zai kawo ci gaban kasuwancina,musamman ta fannin man fetur." Ta ce,"Dad akwai matsala.shi abbas din ai mun gama magana da shi."Ya ce,"Wace irin matsala kuma?"Ta ce,"Dad,ya zo ya ce yana so na.na fada masa ina da wanda nake so.lokaci mai tsawo muna tare da shi. dad ya kama in bar shi in koma wa abbas?"kallon ta kawai alhaji ke yi.bai fara jin haushinta ba don yana sa ran zai shawo kanta.ya ce,"Za ki iya barin sa,tunda bai nemi aurenki ba.sannan ban zaci zaki boye min komai ba.wai kina tare da saurayi tsawon lokaci ban sani ba.to ina son ki ajiye batun wani saurayi.ki natsu kin ji mamana?" Ta yi shiru,ranta bace, lndanunta sun soma kawo kwalla.ya daga fuskarta, "mene ne abin kuka?murna za ki yi.ALLAH yayi miki zabi na gari."Ta ce,cikin kuka,"Dad ba na son sa ne. ai ni khalil nake so.zai zo yau ka gan shi.lrin mijin da zuciyata take so kenan." Ya daga murya,"MIMI zo lokacin da zan ce ina son abu,ke kuma ba kya so?mun fara jayayya kenan?"Yanzu kam kuka sosai take yi"Dad ba haka bane,amma bai dace a tsananta min in so shi ba.kar ka damu zan kira abbas din in sake tuna masa cewa ba na son sa." Saukar mari ta ji fau! a fuskarta.ya ce,"ba ki isa ba!" A fusace ya nufi fita.ta rike kumatu tana kuka sosai.momy da ke labe ta sauka da gudu,jin alamun zai taho.cikin dakinta ta shiga.lallai tana cikin farin ciki.bari ta je ta kara wa wutar kananzir. Ta fito ta nufi dakin alhajin,tamkar bata san komai ba.ta yi sallama, alhajin ya amsa a ciki,yana ta zirga-zirga a cikin dakin nasa.cikin alaye ta nufe shi,"Lafiya alhaji?Me ya faru?"Ya kalle ta,"MIMI wai take nema ta tona min asiri.bakina da na uban dan nan na ce,na basu yarinyar nan,amma in zo mata da batun,ta ce,bata san zancen ba?"Nafisa ta zaro ido,tare da dafa kirji,"in ji MIMIN?"Momy nafisa ta ce,"aa wasa take yi,kana ji ko alhaji?kiyayyar mace bata wani tasiri,sai dai in ba a yi auren ba.
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (3)Ku tsai da rana. kafin ta kammala makaranta ku daura musu aure.bikin kwa yi in ta gama karatun."Ya ce,"Kina ganin hakan zai yiwu?"ta ce, sosai kuwa.ldan ta san cewa da akwai igiyar wani a kanta,dole ta rabu da kowa.ya ce,"Ke ma kin kawo shawara.amma zan so ki je ki dan kara bata shawara. ko don gatan da na nuna mata,ya kamata ta yi min biyayya."momy ta ce bari in je.amma kafin in tafi, za a hada maka ruwan wankan ne,ko abincin za ka fara ci?"Ya ce bana bukatar ko daya.ya zauna bakin gado,"bari in kira sauda,ko zan samu natsuwa."ranta ya dan sosu,amma ta danne. bari to in je gurin MIMI din.ka ce da ita ina gai da ta." Kuka sosai ta samu MIMI tana yi.don haka ta shiga lallashinta da cewa ta yi shiru,su yi magana.ta zo ne don sama mata mafita. bayan MIMI ta share hawayenta ne,momy nafisa ta ce,ki ce masa ya turo iyayensa,shi khalil din. kila in alhaji ya ga magabatansa sun zo ya hakura. cikin disasshiyar murya ta ce,momy bana fada miki ba karatu yake yi?lyayensa,yanzu baza su saurare shi da batun aure ba.da ma mun bar shi a kan sai mun gama karatu ne.momy nafisa ta yi shiru tana tunanin mafita.MIMI ta kama mata hannun,don ALLAH momy ki fada min yaya zan yi? Ta rungumo ta,kwantar da hankalin ki MIMI.wannan karamin abu ne,kuma kin san dad dinki yana son duk abin da kike so.shawarar da zan baki ita ce,ki tsaya a kan raayinki na cewa khalil ki ke so.zai hakura. amma in kika bi raayinsa,ba za ki ji dadin zaman auren wanda ba ki so ba. MIMI ta ce,to ni bana son dad ya ce ban ji maganarsa ba.ta ce,kar ki damu da haka.yanzun nan daga dakinsa nake.ya ce in ya ga kin dage zai hakura. MIMI ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce, shi kenan zan tsaya a kan raayina.momy nafisa ta ce,duk runtsi ki ce baki son abbas.MIMI ta ce, "shi kenan." Alhaji kam, hajiya sauda ya kira yana labarta mata komai daya faru,tun daga burinsa har zuwa yanzu.ya ce,ina son ki kira ta ki yi mata fada,ta bar batun wani yaro.......
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (4)Ta tsaya ga wanda ni na zaba mata. hajiya sauda ta ce,alhaji ba zan shiga zancenku ba,kai da lelenka.abu daya kawai nake ganin zan iya.shi ne zan kira ta in bata shawara. ya ce ban gane ba zaki shiga zancenmu ba. ta ce alhaji ke nan.yanzu ne da ta kwabe muku ka san da ni?lna uwarta mai son ta wadda aka canza mata da ni,saboda ni ina takura mata ta yi abin da ya kamata?shawara kawai zan ba ta ta yi maka biyayya,amma ba wai in takura mata ba.ldan ta ki yarda,sai ka yi mata abin da take so,kamar yadda ka sabar mata tun tana karama.shiru ya yi,ya kasa magana.sai kuma ya kashe wayar. momy nafisa ta same shi cikin damuwa, yana ta tattauna maganganun hajiya sauda a cikin zuciyarsa.ta zauna kusa da shi.alhaji nayi maga da MIMI.ya kalle ta cikin sauri,ta amince? "MIMI ta ki sam alhaji.kuka take ta yi.da na tsananta mata da lallashi,da nuna mata cewa ta yi maka biyayya, sai ta ce min don na ga bani na haife ta ba.ln dani na haife ta ba zan so a yi mata auren dole ba.ya ce haka ta fada?kenan tana da daurin gindin mahaifiyar tata?domin da na kira ta a kan ta yi mata fada,ce min ta yi ita shawara zata iya ba ta, ba fada ba. Momy nafisa,cikin jin dadi ta ce,amma hajiya sauda ba ta kyauta ma kanta ba.ta yaya za ta hana 'yarka ta yi maka biyayya?"ya ce,shi ne abin mamakin amma zan gwada musu su duka cewa ba su isa ba."ta ce, "abin da ya kamata kenan da ma ku zauna kai da minista ku sa lokacin auren sati uku ko hudu,ku daura kawai,ka wuce gurin kamar yadda na fada maka.ya ce, gobe za mu tattauna da shi.amma MIMI ba ta isa ta ja min asara ba.ta lelo ta koma min kenan. lta kuwa hajiya sauda, wadda ba ta san komai ba, sai da alhaji ya fada mata, amma ita ma yanzun laifin ya shafe ta,ta kira MIMI. can kasa-kasa ta ji muryar MIMI ta amsa sallamar hajiyar.hajiya ta ce"ba ki da lafiya ne?"MIMI ta soma kuka,dad ne wai sai na auri dan minista,kuma ni bana son sa."Hajiya sauda ta ce,ni dai in na isa in fada miki ki ji,to ki bi zancen mahaifinki,
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (5)Ki auri wanda yake so.yanzu ke wannan ba abin kunyarki bane,saura 'yan uwanki su ji kina takaddama da ubanku? mutumin da ya nuna miki gata,ya yi miki duk abin da ki ke so,ya nesanta ki da duk wani abu da zai bata miki rai.MIMI na zaci ko wuta babanki ya hura ya ce,ki shiga,za ki shiga ba tare da kin tsaya dogon nazari ba.ashe ba kya yi masa son da yake yi miki. ki yi tunani sosai,kuma ki yi abin da ya dace.shawarata kenan."Ba tare da ta ji uzurin MIMIN ba ta kashe wayar. Alhaji lawal ya kawo sadakin zainabu dubu dari kamar yadda lnnarta ta fada musu.kuma an kawo akwatuna,an kuma sa ranar bikin sati biyu.zainabu na ta kuka kuma har gidan su mahmood ta je ta fada masa,ta kuma bukaci ya bata wayar don ALLAH,ta kira lsmail.ya ce mata ai kawai taje tabi maganar iyayenta.lsmail ba abinda zai iya tunda an rigaya an yi mata miji.shi ba ya so ma lsmail din yaji zance ma haka ta tafi ba tare da ta cika burinta ba.lsmail kuma duk kwanakin sai yayi ta fama da muggan mafarkai marasa kai.ln ya kira mahmud,sai ya ce masa kowa lafiya.tun kwanaki da yayi waya da zainabu, mahmud bai sake hada su ba.ln ya ce masa don ALLAH ya je gun ta za su yi waya,sai ya ce masa ba lokaci.daga karshe har ya ji haushi,ya ce,na daina cewa ka kai mata wayarka.da na dawo zan sai mata in huta. mahmud ya ce,ka taimake ni,don ba a son raina nake zuwa ba.lsmail ya kashe wayarsa cikin takaici. kusan kwanaki uku,in lsmail ya shiga gidan don koyar da MIMI,har lokaci ya cika bata fitowa,don haka sai ya kuduri niyyar yau in alhaji ya dawo zai sanar da shi. haka kuwa bayan sun yi sallar isha.sai ya sanar da alhajin.alhaji ya ce zai yi mata magana.ln ma bata fito ba kar ka damu.ka ci gaba da koyar da kannenta. lsmail ya ce shi ke nan.alhaji ya ce in ta fito kuma,to don ALLAH ka dinga yi mata nasiha.ka ji ko?lsmail ya ce,insha ALLAH. momy nafisa ita da naima sun kulle kansu a dakin momy tana sanar da na'imar yaddaa tsarin da ta yi yake tafiya yadda take so.
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (6)Ta ce an kusa zuwa gurin kar ki damu. na'ima yanzu fa har hajiya sauda,alhaji haushin ta yake ji.ya zaci ita ce ke zuga MIMI.shekaran jiya MIMIN ke fada min wai hajiyar saudar ta ce lallai ta bi zabin alhaji.na ce mata MIMI kin san dai sai dai mahaifiyarki ta gwada min ta haife ki,amma ba ta kai ni son ki ba ko?MIMI ta ce eh.na ce to ki yi duk abin da na ce,lta kin ga bata yi boko ba,ba lallai ta san 'yancin kanta ba,bare naki. MIMI ta ce haka ne.nan da nan na zuge ta.sai da na goge dan tunanin da ta soma yi na danganar da uwar ta sa ta yi."Na'ima ta ce momy ai na ji dadi.yanzu dad ya fi kula mu a kanta.momi ta ce shegiya ba,ni ma na dan ji tsai,a yi nan dad dina,a yi can dad dina,ta kwaikwayi muryar MIMIN,suka kwashe da dariya.na'ima ta ce,to ba ki ganin dad zai iya daura musu auren,ni kuma fa? tunda kin ce masa kawai su sa rana.momy ta ce,ina so ne a yi mai yiwuwa ne a gama.shi ya sa nake son a sa rana.ke dai duk abin da na ce ki yi,to ki yi kokari ki aikata.na'ima ta ce,"an gama." Alhaji akilu da alhaji bishir suna zaune cikin ofishin alhaji bishir din,su zabi haduwa a nan ne don su tattauna batun auren yaransu.alhaji bishir ya ce,ka san ja'irar yarinyar nan wai ina fada mata sai take neman yi min gardama."haba dai?!"in ji alhaji akilu.alhaji bishir ya ce,"ALLAH kuwa.amma na san duk iyayi ne na yaran nan."alhaji akilu ya ce,ka san mata ba mamaki tana zaton mu ne muka hada su,ba shi ne ya gan ta ya ce yana so ba.ka bar ta kawai.da zaran an yi kiyayyar mace bata dorewa.sai dai in ba ta samu kula ba. Cikin jin dadi,alhaji bishir ya ce na gode daka fahimci hakan.yanzu wane lokaci kake ganin za musa? alhaji akilu ya ce kar mu ja abin;mu yi mu wuce gurin. ni ma haja na gani,in ji alhaji bishir.mafi sauki mu saka sati uku ko hudu.alhaji akilu ya ce,mu bar shi hudun.don naji mata suna cewa za a fita dubai ko chaina hado kayan auren.shi kuma angon ya soma gyaran gidan nan nawa na asokoro.
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (7)Alhaji bishir ya ce, ka fasa sai da shi ke nan? ya ce,ba dole in fasa ba, tunda abbas ya dage gidan yake so?gidan yayi masa girma,amma shi wai tsarin gidan yayi masa.alhaji bishir ya ce,to a bar masa. ALLAH ya sa hakan ya fi alheri.alhaji akilu ya ce. amina.zan turo waliyyan nasa,kanina da alhaji sa'idu abokina za su zo.alhaji bishir ya ce,babu matsala. ni ma zan yi wa nawa kanin da kuma alhaji kabiru magana.yaushe ne za su zo?alhaji akilu ya ce cikin satin nan.za dai muyi waya. bayan sun gama tsarinsu ne suka koma batun kasuwancinsu. Abu kamar wasa,zance ya soma nuna,don an kawo sadaki.kuma momy nafisa da wata kawarta sun shaki kudi gurin alhaji sun nufi dubai siyayyar kayan kicin, ta zage kuma tana ta zabar masu kyau da tsada,domin tana fatan su rikide su zama na na'ima. Tafiyarsu da kwana biyu,sai ga khalil da mahaifiyarsa har gidan su MIMI.yadda abin ya faru kuwa,hajiya amina ta ga danta ya shiga damuwa da tashin hankali ta rasa gane kansa,sai ta tsare shi a daki don ya fada mata damuwarsa.ta yi ta lallashin sa da nuna masa cewa,ita ce ta fi dacewa da ta san matsalasa,kuma ta magance masa,in har za ta iya.jin haka ya sa shi koro mata komai.ba ta yi kasa a guiwa ba ta sanar da mahaifansa wanda hankalinsa yake kan siyasa. nunawa yayi wannan ba damuwarsa ba ce damuwarsa kawai khalil ya yi karatu ba tare da zabin da ya wuce bai wa dan nata hakuri,gami da shawarar tsayawa kan karatunsa.amma cikin kwanakin sai ga yaro kwance warwas,ba ci ba sha,duk ya fita hayyacinsa. ba arziki ta taso shi zuwa abujan don rokon a bar masoyan su ci gaba da soyayyarsu har zuwa lokacin da za su hattama karatunsu,sai a daura musu aure. na'ima da ke falo ita ce ta amshi bakuncin nasu. suka gaisa.ta ce,kun zo gurin momy ce?ga shi ba ta nan.hajiya amina ta ce, mahaifinku fa?na'ima ta ce, yanzun nan ya fita.khalil ya ce MIMI fa?na'ima ta ce tana samanta;in kira ta ne? hajiya amina ta ce,eh.kudundune take cikin bargo.yau tun safe zazzabi ke jikinta.
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (8)Na'ima ta yi sallama,ta shiga ta sami MIMI.baki aka yi.sun ce in kira ki.ta ce daga ina?ki ce su hawo,ba zan iya sauka ba.na'ima ta raka su har falon MIMI,ta ce,sis ga su nan.MIMI ta yunkura za ta tashi,ta kasa.ta ce,tambaye su na'ima,daga ina?ba zan iya tashi ba.na'ima ta tambaye su.sai ko hajiya amina ta mike mu je kawai,in yi mata bayani.