Showing 6001 words to 9000 words out of 86229 words
wata number Dana ga ta saka 'MY HEADACHE'. Seda ya kusa tsinkewa sannan aka d'auka...
"Kina ina?" Haseena ta tambaya. A mamaki ne muryan kubra naji ya daki speakern wayan.
Kubra dake hotel tare da wani hamshak'in d'an siyasa suna aikata masha'an su ta amsa da
"Ina gidan hajja Fati. Ya akayi kun dawo ne?"
"Eh mun dawo ,Dan Allah ki dawo gida haka ,nace dai hajja Fatin nan koda yaushe kuna tare kamar cingom? To idan baki dawo Dan mu ba ,se ki dawo Dan kishiyar ki"!!
A zaton Haseena ko fad'in hakan ze tashi hankalin kubra ne ,amma amamakin ta ,dariya taji kubran nayi tare da cewa
"Cool down baby! Wacece kuma kishiya ,ban dawo Dan 'ya'ya naba, shine zan wani dawo Dan wata Abu wai kishiya? To ban gama abunda nake yi ba ,idan na gama ai zan dawo ko?
Haseena tantama take anya ma kubra taji abunda ta fad'a kuwa? Sake maimaita mata tayi
" mummy aure fa nace miki daddy ya k'ara shine kuma kike dariya?"
"Nasani ai Haseena, ba abunda bansani ba akan auren shi ,da naso in hana bama za'a kai yanzu ba ,banda lokacin su ne kawai." Cewar kubra
Haseena harta bud'e baki zata yi magana
"Mummy! " kubra ta katse ta
"Ke ni karki dame ni ,kisha fa mun kan Auta. Take care"...
Bata jira jin me Haseenan zata k'ara ce mata ba ,ta yanke kiran. Misalin k'arfe takwas na dare ,kubra tabar hotel d'in cikin shirin ta na zuwa club ,a cewar ta akwai babban casu da za'ayi a _shisha palace_ ,Wanda bata ka wani dalili daze sa tayi missing ba...
A b'angaren kubra kuwa ,abinci ta girka mai rai da lafiya iya k'warewar ta. Ta shirya komai akan dining sannan tayi dialing numbern daddy data rubuta wa _Alhaji na_, bugu d'aya biyu daddy ya d'auka. Cike da kissa kubra ke magana
" Dadddy na gama girki ,ka gaya wa su Hajiya k'arama ko"
Cike dajin dad'in yadda ta nuna damuwa da 'ya'yan shi yace
"To zan fad'a musu ,zaki gan su"
A shagwab'e tace "daddy to kai fa?"
Yace "karki damu ,ni bana jin yunwa ,idan ma ina da buk'ata Hajiya k'arama ce me girki na ,da abincin ta k'adai na saba. "
K'ara kashe murya tayi zatayi magana ,amma se jin tayi ya kashe wayan. Tsaki taja ,tare da fad'in
"Can da yawar ka. Tukunna ma ,ba'a fara wasar ba ai".
Daddy dase a lokacin yayi saving numbern khaltum, yana yanke kiran ya kira suxee dake kitchen ita da haseena suna shirya masa abinci, sheda mata yayi yadda yayi da khaltum ,tace
" to daddy zamu je insha Allah " shine amsar data bashi sannan ta yanke kiran. Haseena ce ta dube ta ,tare da cewa
"Keda waye kuma ?"
Suxee tace
"Daddy ne ,wai muje inji Anty Amarya ta gama mana abinci"
Baki haseena ta tab'e tana fad'in
"Ikon Allah. Wani iyayi ne wannan kuma? Da can kafin tazo wake dafa mana? Inace muke dafa wa kan mu?"
Suxee da dama tasan za'ayi haka tace
"Haba haseena daga abun azziki? Ina lefin ta?"
Haseena tace "kinga ni ban hanaki zuwa ba ,nidai bazani ba ,se kije keda Auta.
Auta dake tsakar kitchen d'in tana wasan ta ta karb'e da
" nima baza niba Yaya suxee "...
Suxee kad'ai taje taci abincin ta ta dawo.
Satin kubra d'aya a gidan ,hankalin ta a kwance ,tana cin gashin kanta ,babban abunda ke damun ta shine ,daddy ko so d'aya be tab'a neman ta da mu'amalar aure ba. A Daren ranar ta shirya tsaf Dan tunkarar shi , A wannen Daren ne kuma kubra ta dawo, wacce kusan tun tafiyar su daddy ,bata gidan se yau Allah yayi dawowar ta...
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[7/14, 9:39 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π
π
*_π (base on true life story)_*π
*_π INTELLIGENT WRITERS ASSOπ_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)βοΈ*
_BABI NA SHIDA_
*_____________________*
_Kubra Kai tsaye sashen ta ta nufa. Da shigar sauti ta kunna sannan ,sannan ta shiga wanka. Kwalliya ta zauna ta tsantsara Wanda ya amshi kyaky-kyawar fuskar ta, doguwar Riga ta zuba ,Wanda ya amsa sunan shi ,gashi daka gani kai kace Dan ita akayi rigar... Wani abun se mata masu diri_
_Haseena najin kid'an na tashi ,dariyar takaici tayi ,Auta ce ta tambaye ta_
"Yaya haseena waye ya kun nawa mummy hoppers d'in ta?"
Cike da takaici haseena tace
"Waye kuwa ze kunna mata? Kakar d'an k'wairo ce ta dawo da kanta ,kyaji ma fiye da haka"
Suxee dake fito wa daga toilet ,dariya maganar haseenan ya bata ,tace
"Wllh ba kida kirki haseena! Mummyn ce ma kakar d'an k'wairo? A'ah kakar Baban gida kaka dawo ne ,shine ke tashe"
"Ai tama wuce nan alqur'qn". Haseena ta bata amsa ita fuskar ta d'auke da dariya.
A tare suke je duba ta ,Kafin sukai har auta ta riga su kaiwa. Cab'e ta kubra tayi fad'in
" Auta ta takaina! Nayi kewar ki sosai." Tsuke baki auta tayi tare da cewa
"Ni bakiyi kewa na ba ,inda haka ne shine zaki yi tafiya baki je dani ba? Ni sauke nima ,mun b'ata" ...Auta ta fad'a ciki da yarinta
Murmushi kubra tayi tare da shafo gefen fuskar ta ,tace cikin sigar lallashi
"Haba Auta ,yau kuma da mummy ake fad'a? To kiyi hak'uri ,ba gashi yanzu na dawo ba? "
Sallamar su suxee ne ya katse ta. Gaishe ta sukayi a ladabce ,kafin suka samu guri suka zaune kan lallausan kushin d'in da yayi daidai da tsarin parloun.
Suxee tace "mummy da kin gaya mana zaki dawo ai da se mu gyara miki waje ,ko musa a gyara"
Wani uwar harara haseena ta banka mata tare da cewa
"Meyasa kike bin son ran mummy ne Yaya suxee? Kafin kice haka me yasa bazaki fara tambayar ta inda taje ba harna tsawon sati d'aya. Kuma da izinin wa taje , nasan tabbas daddy be Sani ba."
Alama suxee tayiwa haseena alamar ta rufe mata baki ,amma Haseena bata ji waji ba ,ta d'ora da
"Ya ga gaskiya ga rantsuwa! Idan ma bazata dawo Dan kowa ba aise ta dawo Dan mu. Tsakanin mu da mahaifiyar mu ba wani shak'uwa ko jin k'ai ,se anyi magana tace tana son mu. Yanzu ki duba fa irin abunda sakacin ta ya janyo mata ,gashi nan daddy yaje ya k'aro aure ,kuma duk akan halayen ta ne. Sati d'aya da zuwan Anty khaltum kenan. Amma bata San mummy ba mummy bata San taba ,idan ta gane irin halin da muke ciki dake wallahi ba abunda zaki siya mana se wulaqanci, Wanda b zamu lamunce ba."
Wata uwar tsawa suxee ta daka wa haseena
"Enough haseena!!!"
"Ank'i ayi enough d'in." Haseena ta maida mata a hasale ,sannan ta maida duban ta ga kubra tace
"Idan baki gyara ma inaga an kawo wacce zata gyara ki ,idan kuma ita ma d'in ba'ayi dace ba ,ina add'uan allah ya kawo me canza ki da gaggawa.
Ya kamata ki iya takun ki Dan girman Allah karki ja mana gori da gore-gore. Yanzu bamu kad'ai bane a gidan, na rok'e ki"... Haseena ta k'arasa maganan tare had'a hannayen ta biyu alamar rok'o. Tana kaiwa nan tayi ficewar ta.
Suxee da kamar taci kanta ,kallon mummy take idon ta cike da hawaye tace " mummy kindai gani ko? Kin ga abunda son zuciyar ki yake nema yaja miki ko? Duba fa ,haseena 'yar cikin ki take tsaya wa a gaban ki ta gaggaya miki maganganu marasa dad'i, duk da akan gaskiyar ta take kuma duk abunda take fad'a nasani kum kema kinsan gaskiya ne. Dan Allah mummy...
"Ke!ke!!! Malama dakata mun Dan Allah. " kubra ta katse suxee ,sannan taci gaba da cewa...
"Naku a mene ku kuma? Rayuwa ta ko rayuwar Ku? Na hanaku kuma kuyi yadda kuke so ne? Se kune 'ya'yan ciki na zaku hanani sakata in wala? To baki isa ba, Wanda ya ajiye Ku ma yayi kad'an. Dan Allah matsa mun in wuce ,inje inyi abunda ze fish-she ni." Kubra ta fad'a kamar zata bangaje suxee. Anan tabar auta ta nufi sashen Daddy.
Mamakin wani irin hali kubra keda shi ,ya hana suxee koda taku d'aya. A ranta take cewa "wato duk cin kashin mummy akaina ya k'are ,amma Haseena idan tana yi mata fad'a ko tari. To indai hakan ze sa ta gyara zan bar ta da Haseenan taji idan da dad'i.
" Allah ya kyauta" shine abunda suxee ta furta a fili ,sannan ta kama hannun Auta suka sauko k'asa zuwa d'akin su.
Kubra tafe take Cikin takun ta na k'asaita kamar wacce bata son taka k'asa a haka ta nufi sashen daddy...
Khaltum ce zaune kan kushin d'in da ke cikin uwar d'akan daddy. Taci ado se zuba wani fitinannen k'amshi take, kai kace baza'a mutu ba.
Tana jin an shigo parloun a cewar ta ko su suxee ne ,se kawai tayi maza maza ta haye kan gado ta kwanta ,a cewar ta ko da su Suxee idan daddy ya fito ya ganta akan gado ze hak'ura ya bata lokacin ta. Bata San daddy ya wuce nan ba indai akan 'ya'yan shine. Ganin ba kowa a parlour yasa kubra ta nufi bedroom d'in shi. Knocking ta fara yi Dan ta tabbatar ko yana ciki, shiru bata ji alamar akwai mutum ba ,sake knocking tayi ,cikin tsawa khaltum tace
"Dallah wai waye ke damun mutane ne haka?"
Duk da kubra bata San muryar wacece ba ,amma tasan baze wuce gurguntaccen auren da akace mata yayi ba. Bata yi magana ba ,se sake knocking d'in d'akin data yi. A fusace khaltum ta taso tana fad'in
"Uban waye?" Tana bud'e k'ofar se jin k'arin mari kake yi
"Tassss!!!
TO MASU KARATU, DAN JIN WAYA MARI WANI A CIKIN SU ,SE KU BIYO NI A SHAFI NA GABA IDAN ALLAH YA KAIMU...
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[7/15, 2:49 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π
π
*_π (base on true life story)_*π
*_π INTELLIGENT WRITERS ASSOπ_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)βοΈ*
_BABI NA BAKWAI_
*_____________________*
_A take khaltum ta fara ganin wasu taurari na mata yawo tsabar gigitar data yi. Seda ta natsu hankalin ta ya dawo jikin ta ,sannan ta k'ara ware idanuwan ta Dan ganin me ya faru a yanzu_
_Das... Ta sauke idanuwan ta akan kubra ,dake sakar mata wani uban murmushi ,kamar ba itace ta wanke ta mari yanzu ba_
_"wow masha Allah "_ khaltum ta furta a ranta lokacin data yi tozali da kyawun kubra. " tabbas ke me kyau ce ,kin cika duk wasu qualities na mace daga waje bansani ba ko a cikin ba kamar wajen ne. Ko mak'iyan Allah yasan ke kyaky-kyawar gaske ce"... Khaltum ta saki fad'a cikin ranta.
"Bani wuri in wuce 'yan mata". Kubra ta fad'a tare da kutsa kai cikin bedroom d'in.
Da ido khaltum ke binta har ta samu wuri ta zauna akan d'aya daga cikin lallausun kushin d'in da ke d'akin. Tace
" ya kika tsaya a tsaye khaltum keda d'akin mijin ki ? Kizo ki zauna mana" ,kubra tace wa khaltum tana me nuna mata wurin zama.
Gaban khaltum ne ya shiga dukan uku-uku, lokacin da taji kubra ta kira sunan ta. Bata yi mamakin hakan ba ,dan tasan zata iya sanin sunan ta daga bakin mijin ta ko 'ya'yan ta.
Jiki ba k'wari haka ta dinga taku kamar hawainiya, har ta k'araso ta zauna. Kubra zare gilashin dake idon ta tayi ,tare da ajiye shi a gefe. Sannan tace
"Sannu da zuwa Amarya khaltum. Nasan baki sanni ba ,baki kuma tab'a gani na ba ko? Amma ai nasan dai idon ki yasan k'ima? Sunana kubra , Mata kuma uwar gidan MISBAHU." Wani irin shu'umin murmushi kubra tayi kafin taci gaba da cewa.
"Inaso ki iya ,takun ki ,kar kiyi tunanin kinzo Dan ki mallaki gida na ne. Bari kiji ,auren ki ma da banso ba da kawo yanzu ya zama tarihi. Nasan duk wani shiri da kuke yi keda mahaifiyar ki ,zuwan Ku gurin malamin Jibiya ,irin kashe kud'in da kuka yi kafin kuka dace a naku, da irin abubuwan daya Baku na ganin kinzo kin juya mun gida, ke hatta yawon malamai da kuka yi kafin Ku dace duk a tafin hannu na yake." Dariyar gefen baki kubra tayi taci gaba da cewa
"Wai ke Amarya ko? Sati d'aya kenan baki San miji ba be sanki ba. Wannan auren soyayya ne ko auren had'i ? To wannan duk yana cikin tsarin kubra. Bayan ke ma akwai wacce ko ince masu zuwa, ina nufin aure ze k'ara. Saboda haka ki iya takun ki ,ni bakya gaba na ,idan kuwa kika ce zaki shigo gona ta ,shakka babu zaki zama tarihi a doron k'asa. Nice kubra, _gidan Misbahu_ gida na ne, wannan kuma yanki na ne, inaso ki rik'e wannan."
Har ta mik'e ,se kuma ta koma ta zauna tare da cewa
"Am! Nace marin Dana miki ,karki d'auka ko Neman magana nazo yi, ke bakiyi matsayin da zan yi dake ba,hasalima kamar yadda na gaya miki bakya gaba na ,kuma karkiyi k'ok'arin shiga gona ta, ki tsaya a matsayin ki ,azziki dai kika zo dangwala ko? To u're highly wlcm. Na miki ne saboda gobe kisan yadda zakiyi magana da manya. Bana tunanin ni da yanki ne sena nemi izinin shiga. Me Abu ne da abun shi maganin akwab'e shi.
Sannan maganan Amarci,,, Nina hana komai ya wakana a tsakanin ki ,saboda inaso ki d'an San koni wacece da kuma abunda zan iya aikatawa,,, amma yanzu Dana shigo na ganki se kuma kika bani tausayi ,saboda haka zan baki dama ,amma fa yau inason kisani duk wani shirin ki baze yi tasiri ba ,sedai ko zuwa gobe zan duba ingani ,idan kuma kina ganin kamar ba haka ba ,zaki iya jarabawa kika idan hak'arki zata cimma ruwa..."
Fitowar daddy daga toilet ne yasa kubra tsagaitawa ,nufo shi tayi tare da rumgume shi tana fad'in
"Nayi kewar ka sosai daddy"
Shima daddy rumgume ta yayi cikin murnar ganin ta ,tare da cewa
"Nima haka my wife"
Janye ta daddy yayi daga jikin shi tare da cewa
"My wife kiyi hak'uri ,nayi miki wani lefi ,nima badan inaso ba"
Murmushin jin dad'i kubra tayi tare da
nuna khaltum alamar akan wannan kake magana?
Gyad'a mata kai yayi alamar eh. Bud'e baki daddy yayi zeyi magana kubra ta had'e bakin su waje d'aya, cikin k'warewa da salo take tsotsar bakin shi, a hankali ta zare bakin ta daga nashi tare da masa magana k'asa-k'asa kamar me rad'a
"Daddy indai wannan ne karka damu, na Riga nasan komai akai" maida duban ta tayi inda khaltum ke daskare a zaune, kai kace an dasa karas ,,ko motsin kirki bata yi ,murmushin mugunta tayi mata ,sannan ta maida duban ta ga daddy tace
"Inaga ka fara kimanta mata daga gobe ,bance kuma ya wuce iyaka ba".
Godia daddy ya mata ,sannan ta nufi inda khaltum ke zaune, hugging d'in ta tayi ,tare da bubbuga bayan ta ,tana cewa
" Asha amarci lafiya! Ina fatar zuwa yanzu kin gane kuyanga ko da an 'yanta ta bata isa ta kamo matsayin takalmin ban d'akin uwar gijiyar taba? Saboda haka ki kula"...
Seda safe tayi musu sannan ta wuce abunta tana kwasar dariyar da ita kad'ai tasan ma'anar sa...
Kusan ranar khaltum baccin bak'in ciki tayi ,Dan a iya gajeren tunanin ba kubra bata kai haka ba ,se yanzu take gasgata lallai ita d'in hatsabibiyar gaske ce. Tayi iya bakin k'ok'arin ta na ganin daddy ya kusance ta a wannan Daren sakamakon wani maganin mallaka data matsa, amma ina abun ya faskara ,a Dole ta hak'ura ta k'yale shi badan taso ba. Allah Allah take kawai gari ya waye ta kira mahaifiyar ta Hajiya khairi ,ta sanar mata komai... Dan iya tsorata khaltum ta tsorata da kubra, maganganun data gaya mata su kad'ai ke mata reto a dodon kunne...
_Washe gari_...
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[7/16, 4:56 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π