Showing 3001 words to 6000 words out of 86229 words
masa ,sannan ta sake tambayar sa
"Ina keys d'in?"... Jiki a sanyaye daddy ya tashi ,ya d'auko mata makullan ya mik'a mata. Karb'a tayi tana bubbuga k'afad'ar shi tare da cewa
" wise man!" Sannan ta mik'e ta nufi drawern da kud'in suke. Bud'e wa tayi bata wani sha wahala ba dan tasan pin d'in bud'e akwatin kud'in. Kud'i kubra ta iba bani da kud'i ba ,kud'i bana wasa ba ,ni kaina bazan ce ga adadin kud'in ba. Bayan ta iba ,maida wa tayi ta rufe tare kai masa sambata a goshi ,sannan ta cillamai makullin ta fice abunta. Bayan ta fita ne daddy ya fara tunanin Maya faru dashi cikin 'yan mintunan nan ,yadai ga shigowar kubra har zuwa zaman da tayi ,amma baya nan kuma baze iya tuna komai ba. Kai ya dafe tare da furta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Hasbunallahu wani'imal wakil" har so uku ,nan danan yaji komai daya faru kamar a mafarki ne ,tashi yayi ya d'auro alwala ,ya gabatar da sallan nafila ,yana kan dadduma har aka kira sallan asuba ,seda ya shiga d'akin su suxee ya tashe su sannan ya fito da niyyar zuwa masallaci ,fitowar shi keda wuya, yaga wucewar hasken motar kubra ,alamar fita tayi. D'an tsayawa yayi kamar me tunani ,se kuma ya girgiza kai ya wuce abun shi...
Misalin k'arfe Tara na safe ,suxee da haseena suka fara shirye-shiryen breakfast kamar yadda suka saba. Ruwan zafin tea suka fara d'orawa ,sannan suka soya Doya da k'wai ,indomie suka dafa wa auta ,Dan bata da abun breakfast daya wuce wannan ,shi kuma daddy suka dama masa kunun gyad'a ,kasancewar yafi qaunar karyawa dashi sama da komai.
Goma da rabi daidai suka kammala tare da tsaftace ko ina. parlorn daddy suka kai komai ,akan dining suka jera. Suxee tace
"Yauwa haseena tunda mun gama komai inaga ,kije ki ta do Auta ,ni kuma in taso daddy! Kuma Dan Allah kiyi mata a hankali nasan halin ki"
Kwashewa da dariya haseena tayi tana cewa
"Kai Yaya suxee, ai Autar ce wata sa'in da k'ule me rai wallahi "
Suxee tace "nidai na gaya miki...
Bayan sun kammala karyawa ,daddy Yace
" inaga tunda kun samu Hutu ,kamata yayi mu shirya muje mu gaida Hajiya ta(mahaifiyar shi kenan). Tsalle auta ta daka tana cewa
"Daddy yaushe zamu je?"
Murmushi daddy yayi irin nasu na manya ,kafin yace
"A yau ma idan kuna so ai se muje Auta, kano aina maida ta kamar gida ,inaga se mubi jirgi kawai ma"
Nan danan suka cika parloun da ihu ,murna sosai suke yi zasu je ganin Hajiya. Cikin tsantsar so da qauna daddy ke bin su da kallo daya bayan daya ,idan akwai abunda daddy yafi so a duniya be fi sama da farin cikin 'ya'yan shiba.
cikin k'ank'anin lokaci suka shirya komai nasu ,a akwati daya suka shirya komai, misalin k'arfe biyu suka fita ,koda ukku tayi suna garin kano...
_Nijar..._ kubra ce zaune ita da hajja Fati a gaban boka RUBATSI... Wani arnen dariya RUBATSI ya fashe dashi irin nasu na abokan Iblis ,a lokaci d'aya kuma yana duba tsatsubar tsafin sa.
Ihu ya saki Wanda ya k'are d'e gaba d'aya dajin tarnak'aki , nan take tsuntsaye suka fara tashi ,wasu kuma sedai suka fad'o k'asa a mace ,saboda tsananin girman tsafin RUBATSI...
Wani bak'in madubi ya daka ,cikin k'ank'anin lokaci se ga daddy ya fito a ciki. Dariyar shi me tsinka hanjin me saurare ya sake fashewa dashi ,kafin ya gimtse fuska a take kamar be tab'a dariya a duniya ba.
"A yanzu haka mijin ki yana kano tare da 'ya'yan ki ,sannan wannan zuwan nashi ba alkhairi bane Dan kuwa ,a wannan zuwan mahaifiyar shi ta gama shirya komai Dan tabbatar da ya sake k'ara aure"...
Wani zaro ido kubra da hajja Fati suka shiga yi ,a lokaci d'aya hanjin kubra ya shiga k'ugi...
MUJE ZUWA💃
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
[7/13, 1:13 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠
*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*
_BABI NA HUD'U_
*_____________________*
_Tsabar kad'uwa da mamaki ne ya cika kubra ,Wanda ya assassa mata tunani iri daban daban._ _A tunanin ta tunda take da Misbahu bai tab'a tunanin k'arin aure ba sama da shekara goma sha takwas makamancin wannan be tab'a tasowa ba se ayau kuma ayanzu kamar yadda boka RUBATSI ya sheda mata._
_Hajja Fati ce tayi k'arfin halin cewa_
"Tsafi ya da fa! Yanzu menene abun yi kenan?"
Se a lokacin kubra ta dawo daga garin tunanin data je.
Wata fajirarriyar dariya Boka RUBATSI ya fashe dashi tare da cewa
"Menene kuwa bazamu iya ba, wani aiki ne a doron duniya ze buwayi RUBATSI? Nine fa na gagari na gagari kowa,,, gagararren ma ni RUBATSI gagarar shi nake yi! A kashe,,,,a b'adda ,,,, a raba,,,,a yanka ashanye jini,,, gigitarwa ko hauka,,, wannan sune aiki mafi sauqi a wajen RUBATSI... Duk abunda kuke so Ku k'addara anyi an gama kawai"...
Cikin jin dad'i hajja Fati tace" ni fa aganina kawai boka a b'adda ta, ta yadda hatta mahaifiyar ta data haife ta bazata k'ara tunanin ta haifi me sunan taba. Kawai a jefa ta wata uwa duniya."
Kundin tsafi boka RUBATSI ya buga ,kafin Yace
"Wannan Abu ai me sauk'i ne da k'arfin tsafi." Hannu ya maida cikin kundin tsafin dake gaban shi ,tare da rufe ido ,se wasu sambatu yake yi irin nasu na guma-guman arna. Cikin mintin dabe Gaza sha biyar ba ,se ga aljani ya bayyana. A firgice kubra ta k'ank'ame hajja Fati, Dan kubra badai tsoro ba. Ita kanta hajja Fati dukda taurin rai irin nata ,ba k'aramin girgiza tayi ba.
Cikin wani harshe wanda ba wanda yake gane me suke cewa ,irin nasu na tsakanin Aljani da wakilin aljanin RUBATSI ke magana da wannan aljanin. Suna gama wa kuma b'at aka neme aljanin aka rasa, a wannan karon fitsari ne ya kusa tsiyayowa daga marar Kubra...
Boka RUBATSI Yace
"Wannan da kuka gani aljani SUFURSUNARI kenan. Cika aiki nake kiran shi. Kada Ku damu shine ya karb'i aikin Ku. Sedai ya buk'aci da akawo gashin kan wannan matar da aka d'aura auren ta da mijin ki ,da kuma d'ankwalin dake d'aure akan ta lokacin dazata shiga gidan. Ga wannan " ya mik'a musu wasu k'ullin magani da SUFURSUNARI yazo dashi. Yace "wannan Jan maganin ki tabbata Mijin ki yaci a abinci ko abun sha, sannan wannan bak'in kuma inaso kiyi girki ki had'a shi a ciki ,ki aikawa Amaryar. Wannan kenan ,na sallame Ku..."
Mak'udan kud'i Kubra ta Ciro ta zube su a gaban boka RUBATSI, sannan suka kama hanyar komawa gida.
B'angaren hajiyar Daddy kuma. Bayan sun kammala cin abinci da daddare ,tace "idan ka gama kazo d'aki inason ganin ka" ta fad'a tare da mik'ewa ta wuce gaba ,shi kuma daddy yana bin ta a baya, har suka shiga d'akin ta. Gefen gado ta zauna ,shi kuma ya samu guri a k'asa ya zauna. Hajiya ta kira sunan shi "Daddy!" Dan haka kowa ke kiran shi saboda sunan kakan shine yaci.
D'agowa yayi cikin ladaba Ya amsa da "na'am Hajiya!"
Ajiyan zuciya Hajiya ta sauke kafin ta soma masa magana cikin sigar lallashi
"Daddy sanin kan ka ne ,duk uwa baza yi abunda ze cutar da 'ya'yan ta ba koda kuwa 'ya'yan shegu ne balle na sunnah. Hak'ik'a rayuwar gidan ka kullum dashi nake kwana arai ,kwatakwata Allah be baka matar azziki ba, kubra mata ce da sedai ace Allah ya kyauta kawai, to na gaji da d'abi'un ta ,Sam baza'a ci gaba da tafiya haka ba. Saboda haka na binciko maka wata 'yar azzikin daga 'ya'yan qawaye na. Na shirya komai ,har ma an d'aura auren Ku d'azu da ranannan. Fatar zaka karb'a wannan auren hannu bibbiyu?"...
Darammm!!!Dasss!!! Gaban daddy yayi wani mummunan fad'uwa kamar an buga durom. Kasa cewa komai yayi se ma k'asa da yayi dakai.
Lura da yana yin daya shiga Hajiya tayi. Tace
"Daddy ko hakan me yi maka bane? Idan baka so base anje ko inaba se a warware auren ,tunda burin ka ka watsa min k'asa a ido, ka kuma nunawa duniya ban isa ba ,to ai shi kenan". Hajiya ta fad'a a fusace.
Cikin nuna damuwa daddy yace " Hajia kiyi hak'uri ,dama kubra nake tunani ,kar taga kamar ba'ayi mata adalci ba, sannan kinsan yadda zaman namu yake"
Jinjina kai Hajiya tayi kafin tace
"Naji kuma nasan komai ,sannan ka kwantar da hankalin ka ,wannan auren na maka shine dan ka samu kwanciyar hankali da nutsuwa a gidan ka. Kubra kuma bata isa tayi maka abunda Allah be nufa akan ka ba ,saboda haka ,muna nan mun sa rok'on Allah, komai kuma ze zo da sauk'i ,albarka ta na tare dakai. Allah yasan ya wa abun albarka"
"Ameen" daddy ya amsa. Kafin suka fara tsare-tsaren yadda komai ze kasance.
A washe gari ,a ranar ne daddy ze koma ,kuma lallai lallai Hajiya tace sedai ya wuce da Amaryar shi, ba yadda ya iya haka ya amince
Amarya kaltum ce a zaune taci ado ,ba lefi kuma tana da kyawun ta daidai misali daka ganta base an gaya maka kasan shuwa ce. Hajiya khairi itace mahaifiyar kaltum. Zaune suke tana gayawa kaltum yadda shirin su ze kasance
"Kaltum kin dai ga yadda nasha bak'ar wahala na kuma b'ata naira kafin na samu auren nan naki ya tabbata ko? To ba bacci zaki je yi ba ,tun wuri ya kamata ki San me kike yi ki kuma San gidan da zaki shiga. Kin dai ji abunda malam ya gaya mana ,matar shi kanta hatsabibiyar mata ce ,idan ba munyi da gaske ba zata ma iya kad'o ki... Ungo wannan" ta mik'a mata wasu qullolin magani tare da wata laya. Tace
"Wannan maganin ki tabbata dashi zaki rik'a masa girki ,wannan layar kuma a cikin filon da yake kwana akai anan zaki tsaga ki sake se ki d'inke da farin zare, daga nan magana ta k'are ,se na ji labari daga wajen ki."
"Karki damu hajiyar kaltum ,kisa aranki anyi an gama komai ,be matar shi kad'ai ba hatta hajiyar shi se ta dawo k'ark'ashin iko na"...cewar kaltum da kwatakwata ma idan ka ganta bazaka ce tana magana ba ,zubin ta irin zubin salihan matan nan ne ,sedai masifar dake cikin kaltum ya fita girma ,ita da kanta tsoron shu'umancin ta take yi...
Dariya suka fashe dashi tare da kashe hannu... Hajiyar kaltum ta dafa kaltum tare da cewa
" nasan ki sarai kaltum. Barewa bazayi gudu d'an ta yayi rarrafe ba. Fatar Nasara 'ya ta"...
Wani irin shu'umin murmushi kaltum tayi me k'ara wa fuskar ta kwarjini da haiba tare da lumshe manyan idanuwan ta ,tace
"Nagode Hajiya ta"...
MUJE ZUWA💃
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
[7/14, 6:32 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠
*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*
_BABI NA BIYAR_
*_____________________*
_GARIN SAKWKWATO_
_Tun kafin su k'araso, daddy yasa aka gyara d'aya daga cikin sassan dake gidan shi ,sashen dake tsakanin na kubra Dana shi ,nan yasa aka gyara wa Khaltum._ _Duk wani abunda ake buk'ata kama daga ,kayan d'aki Dana kitchen da duk wani abunda yasan ana zuba wa a d'akin amarya seda yasa aka zuba wa khaltum su, kaya masu kyau da tsada na zamani ,duk daddy yasa an zuba su a sashen Khaltum._
_Tun da aka wangale musu gate suka shigo ,khaltum ke santin gidan ,komai na gidan me tsari ne ,bata gasgata maganar hajiyar taba ,seda suka shiga harabar gidan anan ta gane wa idanuwan ta aljannar duniya._ _shiru ita dai ta kasa cewa komai. Bayan driver yayi parking ne ,daddy yace wa suxee_
"Yauwa Hajiya k'arama (sunan dayake kiran ta dashi kenan ,kasancewar sunan hajiyar shi ya saka mata). Kije ki nuna wa Antyn Ku sashen ta ,na gaya miki ai shine na tsakayi ko?"
Suxee k'ara fad'ad'a murmushin dake fuskar ta tayi ,Dan ita tun lokacin da daddy ya sanar musu auren ,dad'i taji mishi sosai ta kuma taya shi murna ,Haseena ce dai ke aikin kumbure-kumburen ta ,da k'ananan maganganun ta ,a cewar ta ,suna fama da kubra ,shine za'a tashi a k'ara musu wani jangwam d'in. Seda suxee tayi da gaske ,sannan haseena ta sassauto. Amsa masa tayi da
"To daddy"! Sannan ta kalli haseena tace " Haseena ke kuma kid'an taya mu d'aukan kayan zuwa ciki"
Yatsine fuska haseena tayi ,kafin tace
"Nifa Yaya suxee gaba d'aya na gama gajiya ne ,ga baba lawali nan kisa ya shiga muku dasu" tana gama fad'in haka ,anan tabar su ,tayi wuce war ta.
Murmushi daddy yayi ,shida kanshi shakkar haseena yake yi ,Dan haseena badai masifa ba kam ,ita bata iya Abu da zuciya biyu ba ,ko ya maka dad'i ko karya maka ,idan gaskiya yazo zata fad'eta. Magana yawa baba lawali akan ya taya su suxee shiga da kayan ciki. Suxee ce ta fara yin gaba d'auke da jakar kayan Khaltum ,ita kuma tana biye da ita a baya sad'af sad'af kamar wacce tayi k'arya.
Da talatu suka fara cin karo a sashen khaltum, gaishe su tayi sannan tace wa suxee
"Hajiya k'arama Dama Alh ne yayi waya akan mu gyara wannan sashen za'ayi bak'i ,sannan yace daga yanzu ni zan ci gaba da kula da sashen".
" good" suxee ta fad'a, kafin taci gaba da cewa "to bak'i dai gasu sun zo ,kuma ba masu tafiya bane ,masu zama ne insha Allah" a zuciyar khaltum kuwa cewa tayi zama daram-dam ma kuwa. Suxee nuna khaltum tayi tare da cewa
"Talatu wannan da kike gani ba bak'uwa bace ,Amaryar daddy ce ,da fatar zaki yi mata biyayya kamar yadda kike wa sauran manyan gidan?"...
Washe baki talatu tayi tana fad'in " Ah Ah! Kice Alh aure ya k'ara? To ubangiji Allah ya basu zaman lafiya."
"Ameen " suxee da khaltum suka amsa dashi ,kafin ta mik'a wa talatu jakar kayan khaltum, tare da cewa
"Anty Amarya muje ciki in nunna miki yadda gurin yake kafin in k'arasa cikin gida ko?"
Ba musu khaltum tabi bayan ta ,talatu kuma na biye dasu a baya. Wani had'iyar yawu khaltum tayi lokacin da taga irin dukiyar da aka narka a sashen ta. Komai na garin me tsari ne. Babban parlour ne a k'asa Wanda ke zagaye da d'akuna uku kowanne da toilet d'in shi a ciki. kitchen had'e da store a ciki ,se dining area daga cikin parloun. Yadda k'asan yake haka saman yake sedai shi d'aki biyu ne ,da babban parlour. Komai a tsare yake gwanin ban sha'awa.
Da murmushi shimfid'e akan fuskar suxee tace
"To Anty Amaryar ,wannan shine b'angaren ki ,da fatar komai ya miki? Idan da akwai abunda kike buqata zaki iya sanar da talatu se ta fad'a mun "
Wani guntun numfashi khaltum ta sauke ,kafin tace
"Kar ki damu kanki suxee komai yayi ,nagode sosai da kulawar ki. "
"Bakomai Anty Amarya kema ai yanzu kin shigo cikin mu. Ni zan wuce sashen mu" suxee ta fad'a tare da mik'ewa.
"A huta gajiya. ki gaida mumyn taku Dan Allah kafin in shigo" khaltum ta fad'a kamar mutuniyar kirki
"Zata ji insha Allah" suxee ta bata amsa sannan tayi ficewar ta...
Sashen su ta nufa. Seda ta fara laqewa d'akin kubra taga bata nan ,sannan ta sauko k'asa zuwa d'akin su. Wanka haseena tayi sannan tawa Auta. Suxee ce ta shigo d'auke da sallama ,kan gado ta fad'a tare da fad'in
"Wash Allah! Na gaji sosai. Haseena akwai ruwan zafi a hitan toilet kuwa naga kamar kunyi wanka?"
"Eh akwai" haseena ta bata amsa a tak'aice ,Dan gaba d'aya haushin suxee take ji ,musamman data ga ta fiye zak'ewa akan auren da daddy ya k'ara.
Kaya suxee ta cire ,ta fad'a wanka. Bayan ta fito ne ,tana cikin shirya take cewa haseena "kin shiga d'akin mummy kuwa?"
D'an d'agowa haseena tayi tana duban ta lokacin tana had'awa Auta cornflakes ,maida duban ta tayi kan abunda take kafin tace
"Banje ba! Da alama ma bata gidan nan."
"Taya akayi kika gane, keda baki duba ba?"
"Ji fa Yaya suxee, to ni a abubuwan mummy wanne ne ban Riga na gama karanta ba? Muddin kika shigo baki ji tashin sauti ba ,to karki ma wahalar da kanki da zuwa duba ta ,bata nan ne kawai. Mummy na nanne zata bari kunnuwan jama'a ya sarara?"
Murmushi suxee tayi ,ko ba'a fad'a ba tasan gaskiya Haseena ta fad'i. Tace " Hakane kam. Bata ma nan Dan na duba".
"Uhm" inji haseena alamar kan ki ake ji.
Waya Haseena ta janyo tare da dialing