Showing 1 words to 3000 words out of 86229 words

Chapter 1 - GIDAN MISBAHU COMPLETE BY SIDIYA SIDI

21 Aug 2025

111

 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*


*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*






DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI. DIKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH S.W.T. TSIRA DA AMINCI SU K'ARA TABBATA GA SHUGABAN HALITTU S.A
W ,IYALAN SA DA SAHABBAN SA, DA WA'YANDA SUKA BIYO BAYAN SU DA KYAUTATAWA HAR ZUWA RANAR K'ARSHE...


*INA ROK'ON ALLAH YADDA NA FARA WANNAN LITTAFI LAFIYA ,SUBHANAHU YA BANI IKON ISAR DA SAK'ON DAKE CIKI AKAN DAIDAI. DA FATAR MASOYA NA ZAKU CI GABA DA NUNA MUN K'AUNAR DA KUKA SABA NUNA MUN?...*




*LABARIN GIDAN MISBAHU, LABARI NE MAI D'AUKE DA DARUSSA IRI DABAN-DABAN. LABARI NE WANDA NASAN INSHA ALLAHU ZAI ILIMANTAR ,YA KUMA K'AYATAR DAKU MASU KARATU. INA FATAR ZAKU BIYO NI DAN JIN YADDA LABARIN ZE RIK'A ZUWA MUKU SAND'A-SAND'A!..*









*_BABI NA D'AYA..._*
*____________________*










_Garin sakkwato. Unguwar Sama Road . Unguwa ce ta hamshak'an mutane, Wanda kuwa ke mallakar muhilli a unguwar se Wanda yaji gishiri ma'ana Naira ,ya kuma amsa sunan shi ,shi, shi d'in ne. Unguwa ce ta manyan mutane ,manya-manyan 'yan siyasa ,hamshak'an 'yan kasuwa da kuma masu hannu da shuni, kai duk wani me fad'i aji indai a garin sakkwato ne ,to zaka samu yana da gida a wannan katafaren unguwar, hatta 'yan zaku zamu masu zuwa suyi kud'i a garin ba'a barsu a baya ba..._




_Gidan misbahu na d'aya daga cikin manyan gidaje a layin NAIRA... Babban gida ne ginin zamani da aka kashe ainahin abunda ake kira NAIRAR,,, gida ne Wanda aka qawata shi da duk wani abun more rayuwa. Kai da ka kalla gidan kasan k'erarren gini ne,,, Gate d'in gidan wato babban k'ofar shiga ,shi kad'ai kanshi abun kallo ne ,daga ciki kuwa misalta irin tsaruwa da had'uwar gidan b'ata lokaci ne ,dan kuwa se Wanda ya gani..._


_Apartment wato sashe -sashe a gidan kusan akwai fanni sama da goma,,, fannin wasar yara ,wato playground daga hagu , idan kuma ka mik'e hanya ce daze sadaka da Swimming pool ,Wato wajen wanka. Daga nan kuma zuwa ainahin babban store da ake zuba komai da komai na buk'atun rayuwar gidan na yau da kullum, shima tafiya ce da ak'alla zata kai Nisan kilometres ukku._
_daga bayan gidan kuma Sashen kiwon dabbobi ne daban, wato GIDAN GONA,,,kama daga kajin gida Dana turawa, tsuntsaye ,gidan kifi, raguna ,shanaye dadai sauran su._

_ko wani fanni an keb'ance masa nasa ma'aikatan masu kula da sashen kacokam..._




_KUBRA ce zaune kan kushin ,cikin shiga ta alfarma. A zagaye take da k'awayen ta 'yan duniya ,ko wacce da kalan nata fetsarancin_.


_Kwalbar shisha ce a hannun jakadiyar uwar 'YAN BARIKi, tana zuk'a ,tana busar da hayak'in cike da k'ware wa. A cikin k'adangarun barikin kowacce da fannin data fi k'ware wa, wannan ta zuk'i sigari ,waccan k'waya ,wata kuma ainahin syrup na shaye-shaye ,idan aka d'aga sedai a sauke kwalban an shaye_


_Sannu a hankali k'arar sauti ke tashi daga babban parloun. Daga inda suke zaune suke taka rawar su ta 'yan bariki, cike da shauk'i da nanaye._


_Wata dakakkiyar mota k'irar marsandi ce tayi parking ,adaidai inda aka tanada Dan ajiye manyan motocin gidan. Matsakaitan 'yan mata ne su ukku suka fito daga motan. Ko waccen su saye take da purple uniform , hannayen su kuma rik'e da alqur'anai ,da alama daga makarantar islamiyya suka dawo.
Kai da kalli yaran base an gaya maka kiwon cornflakes da madara bane ,zallar Hutu ce ta bayyana a fuskokin su ,gasu kyawawa,farin su daidai gwargwado.

Har sun kama hanyar da zata sada su da babban sashen gidan ,se kuma babbar cikin su taja ta tsaya tare da dafa kai ,a lokaci d'aya ta fadi


"Oh shit!". K'aramar cikin su ce ta dube ta tare da cewa


" Yaya suxee lafiya?" Wacce aka kira da Yaya suxee tace


"Wallahi waya na ,na manta a wurin sayyadi ,Dan d'azu na bashi ya tura mun wasu wa'azuzzuka ,to kamar ban karb'a ba! " ta dubi ta tsakiyan tare da cewa


" Dan Allah Haseena kije ki karb'a makullin mota wajen baba lawan ki duba mun daga daga inda na zauna ,kiga ko tana ciki"


Wacce aka kira da Haseena naga ta amsa da


"Toh Yaya!". Sannan ta mik'a mata Qur'anan hannun ta ,ta juya zata yi kamar yadda yayar tata ta umurce ta. Har tayi nisa ,Se k'aramar su ta juya ta kalli suxee tare da b'ata fuska. Murmushi suxee ta sakar mata tare da cewa

" ya ne Auta kin gaji ne?". Cike da shagwab'a Auta tace


"Ni kam na gaji Yaya suxee. Allah ni tafiya ta zanyi". Ta fad'i tare da juyawa ta fara tafiya.


" Lalalala! Yanzu Auta bazaki jira muba ,shine zaki tafi?". Suxee tace tare da rik'e hab'a. Ita dai Auta bata ma jiyo ba ,se tafiyar ta take tana wani karya wuya. Har takai daidai volcony d'in daze sada ta da main parloun gidan ,se kuma ta fasa shiga ,juya wa tayi ,Wanda yayi daidai da dawowar Haseena ,tana cewa


"Allah Anty na duba ban gani ba. Ki Bari gobe idan munje islamiyya se ki tambayi sayyadi ,inaga dai acan kika bar wayan". Haseena ta fad'a cike da kulawa ga 'yar uwar ta ta.


" O-Ow!" Inji suxee sannan tace

"Toh bakomai muje".


Har sun kusa k'arasa wa inda Auta ke tsaye. Auta ta k'wala mata kira


" Yaya suxee! " d'agowar da zata yi ,se Auta ta Ciro wayar da suxeen ke nema tace


"Kinga fa wayar ki nan. A jikin ki ya fad'o da zamu shiga mota ,shine ni kuma na d'auke miki ,nace sena baki wahala sannan zan baki" Auta ta fad'a cike da tsokana. Zaro ido Haseena tayi tana cewa


"Dan Iskanci Ashe wayar na hannun ki ,shine kika bari na wahala! To kawo ki karb'a chocolate"... Haseena tace cike da wayo ,a cewar ta idan ta kawo seta doddoke ta ,na wahalan data saka ta.


Auta yarinya ce me wayon tsira ,gwalo tayi wa Haseena, tare da murd'a handle d'in k'ofar ta shige. K'yacci Haseena tayi tana cewa


" zan kama ki ne ai." Duban ta ta maida wajen suxee tace


"Yaya suxee kina gani fa kuma kin k'i kice komai?" Dariya yadda Haseena tayi magana yaba suxee ,tace


" To in banda abun ki Haseena ,aika-aikatan auta wani iri ne baki gani ba dahar wannan ze dame ki. Kar ki manta itace sanadiyyar lalacewar waccan tsohuwar wayar nawa ,ta tab'a d'aukan wayan ta shige toilet d'in mu tana buga game ,da taji wayar tayi zafi ,sink ta cika da ruwa ta jefa wayan, wai wayar ta huce ,a cewar ta wai Dan kar in gane"..


Dariya dikkan su suka saka ,suxee tace
" to kinga ni yanzu sha'anin Auta sedai in bi ta a hankali ,da Yaya ma na samu swt daddy canza min wannan? "



"ai kau dai Yaya ,b'annar Auta sedai mu had'a ta da addu'a". Haseena ta fad'a tana dariya.



A tare suka k'arasa cikin gidan. Se hirar rashin jin Auta suke yi...




Tun daga babban parlour ,suka fara jiyo k'arar sauti na tashi daga parloun sama ,ko basu tambaya ba sun San mahaifiyar su ce ,kuma inda sabo yaci ace sun saba ,amma da yake rayuwar su da nata ya banbanta ,har kawo yanzu sun kasa sabawa da bahaguwar rayuwar ta.


B'ata fuska suxee tayi ,tana fad'in


" mum again?". Gyad'a kai haseena tayi tare da cewa


"Ai kema kin San se ita ,madushiyar duk duniya kenan indai wajen jin sauti ne ,ba tada aikin daya wuce wannan." Haseena ta fad'a ,fuskar nan nata ko oho.


"Stop Haseenaaaah!" Suxee ta daka mata tsawa ,tace


"Bana hana ki fad'in wani kalami Mara dad'i akan mahaifiyar mu ba? Uwa fa uwa ce. Ya kamata ki kula sosai".



" I'm so sorry ,Yaya insha Allah bazan sake ba, amma fa da ana sake uwa wllh Dana dad'e da sake mummy ,Dan Sam bata cancanci ta zama uwar mu ba." haseena ta fad'a. Bata jira amsar da suxee zata bata ba, da canza hanya.


Cikin tsananin b'acin rai da takaicin hali mahaifiyar tasu suxee ta haura parloun sama ,inda ta tabbatar daga nan sautin ke tashi...
























MUJE ZUWA💃




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[7/11, 5:45 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA BIYU_


*____________________*








_A fusace suxee ta haura ,tana zuwa bata bi takan kowa ba ta nufi homes theatres d'in dake fitar da wani irin sauti ,Wanda hatta dakin na k'asan gidan amsa wa yake yi. Takai hannu zata kashe hajja Fati da daka mata tsawo (babbar k'awar kubra kenan indai a fannin shan sha'ani ne) ,se akayi sa'a kuma duk aciki Suxee tafi tsanar ta, a cewar ta idan da badan hajja Fati ba ,komai na mahaifiyar su ze zo da sauk'i._


"Ke suxee! Kar ki kuskura ki fara kashe mana sauti, kar ki fara". Hajja Fati ta fad'a cike da gargad'i. D'an d'agowa Suxee tayi tana mata wani irin kallon tsana ,bata bi takan taba kawai takai hannu ta kashe sautin.


Takun dabai Gaza biyar zuwa shida ba hajja Fati tayi ,se gata a gaban Suxee ,d'agowar da Suxee zatayi base kawai taji saukar wani gigitaccen mari ba. A razane ta d'ago tana kallon ta tare da dafe kuncin ta.


" Akan na kashe sauti shine zaki mare ni? Naga cewar duk abunda kuke yi banga na samu ladan a ciki ba ,se ma tarin sab'o da zunubi da kuke kwasarwa kan Ku"...


Kubra dake daga zaune tana kallon duk abunda yake faruwa ,tashi tayi tsaye tana tafi hannu bibbiyu. Har ta k'araso inda suke tsaye sannan ta dena tafin.


Wani kallon yaushe kika girma dahar zaki gaya mana Allah kubra ta watsa wa Suxee tare da cewa


"Dube ki fa ,dika dika tashin yaushe ce ki? Suxee tun kafin kisan zaki zo duniya nayi islamiyya na kuma San Allah." Kubra maida duban ta tayi kan hajja Fati tayi tace


"Hajja Fati wallahi kin mata da sauk'i ma ,a tunani na sekin kusa sumar da ita ,Dan na fuskanci k'wak'walwar ta na buqatar saiti."


"Ai ki manta kawai hajia kubra ,dika dika suxee guda nawa ne ,yarinya ce bata San inda duniyar tasa gaba ba. Ina ganin wannan ma yayi mu bata lokaci ,nasan idan ta k'ara girma zata gane abunda muke ba kuskure bane kamar yadda take tunani ,ke wallahi ma se ta nemi ki d'ora ta a hanya ma" ...cewar hajja Fati



"Allah ko?" Kubra ta fad'a cike da jin dad'i


"Sosai ma kuwa" inji hajja Fati ,tana wani murmushin su na 'yan duniya. Hannu kubra ta bata suka kashe.




A lokacin Wasu sababbin hawayen bak'in ciki ya shiga wanke wa Suxee fuska. Cikin muryar kuka ta fara magana


"Tir da irin wannan shed'aniyar rayuwar taku ,dahar kuke tunanin zaku wayi gari Ku ganni a tawagar Ku, to idan ma mafarki kuke gara Ku farka ,Ku kuma sake tunani ,ni suxee bazan tab'a kasancewa a cikin Ku ba ,a yayin da bazan tab'a aikata abun da kuke so na aikata ba na sab'on Allah."




Lubcy dake daga gefe tana jin ruguntsumin da ake tafkawa. Tasowa tayi cikin tafiyar ta ta k'asaita ta k'araso inda suke ,tafe take tana busar da hayak'in sigarin da take zuk'a. Tafa kafad'ar Suxee tayi a lokaci d'aya kuma tana zagaya ta ,kai kace me shirin lashe mata kurwa. Murya can k'asa kamar me rad'a ,lubcy tace


"Cool down mana 'ya ta ! Dube ki fa yadda kike ta asarar hawayen ki ,kan abunda be taka kara ya karya kiyashi ba. Ki kwantar da hankalin ki ,wannan d'in da kike ganin muna yi bakomai bane ,waye ce da zamani. Suxee ki kalle ki ,kina da kyan fuska Dana sura ,zaki yi fitting ko wani namiji ehn. Ki ajiye guntun wa'azin ki a gefe kizo ki mori rayuwar ki ,kai kima gode wa Allah dahar ya baki uwa me tunani da hangen nisa."


Kwab'e hannun lubcy suxee tayi dake kafad'an ta ,ta gudu ta fice daga parloun tana k'ara fashewa da wani kuka me ban tausayi. Ta gama sauka stairs kenan taji tayi karo da mutum ,d'agowar da zatayi ta duba ,se taga daddyn ta yana sakar mata murmushi. Fad'awa jikin shi tayi tare da sake wani sabon kukan, lallashin ta ya shiga yi yana bubbuga bayan ta, kamar wata k'aramar yarinya 'yar goye ,ko be tambayi me ya same ta ba ,yasan baze wuce ita da ballagazar mahaifiyar taba. Janta yayi suka k'arasa cikin parloun ,ya zaunar da ita kan kujera ,sannan ya mik'e ya nufi parloun sama a fusace


"Kubra!" Ya kira ta cikin kakkausar murya. Wani kallon raini ta d'ago tana bin shi dashi.


Be jira ta amsa ba ya fara mata gargad'i


"Duk iskanci da shed'anancin da kika San kina ji ko kike yi ,ya tsaya iya kan ki ,kar ki kuskura ki tsoma 'ya'ya na a ciki ,hakan kuwa ba k'aramin sab'ani zamu samu ba, zaki iya mun komai ,ya tsaya iya kaina amma kar ya shafi 'ya'ya na. Na gaya miki". Ya k'arasa naganan tare da nuna ta da d'an yatsa.


Kallon lallai kinyi sake d'an zaki ya girma hajja Fati take yi mata ganin bata ce masa komai ba. Ita ma ido tayi mata alamar kar ta damu.


Daddy ci gaba yayi
" sannan Ku kuma..." Cak ya tsaya kamar Wanda aka zare wa lakka, sakamakon wani kambu da kubra ta murza Wanda ke mak'ale a tsintsiyar hannun ta.


"Fita ka bani waje sakarai kawai" shine kawai abunda kubra ta furta ,a mamaki na se naga daddy ya fita da sauri. Dariya dikkan su suka saka ,hajja Fati tace


"Haba yanzu dai naji magana ,amma yazo ze wani ishe mu da wak'e-wak'en shi na banza da wofi".




" Dama na barshi ne ya sarara kwana biyu ,amma tunda be San azziki ba ,yanzu ze dawo yin rayuwar kambu ,se yadda kambu yayi dashi." Kubra ta fad'a cikin isa da gadara.


Wani dariyar shed'anancin suka sake fashewa dashi, a lokaci d'aya suna mata wani irin kirari Wanda su kad'ai suka San me hakan ke nufi...




















MUJE ZUWA💃




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[7/12, 3:07 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA UKU_


*_____________________*

















_Da daddare misalin k'arfe goma sha d'aya na dare ,kubra ce a side d'in ta cikin shigarta na bacci , har ta kwanta ,se kuma ta tuna cewar gobe zata je k'asar NIJAR ita da hajja Fati Dan sako kambun ta, gashi ba wani isash-shen kud'i a hannun ta, wani guntun tsaki taja ,kafin ta sauko daga kan gadon._


_makeken wardrobe d'in ta ta bud'e ,ta d'auki kambun ta ,murza shi tayi sannan ta mak'ala shi a hannun ta. Gaban daddy ne yayi wani mummunan fad'uwa a lokacin da kubra ta murza kambun ta ,duk se yaji ya rasa me ke masa dad'i a wannan lokacin. Kai tsaye sashen shi ta nufa ,a d'aki ta same shi zaune da system a gaban shi ,sedai ga dikkan alama hankalin shi ba a wajen yake ba. Kamar ba kubran daya Sani ba ,k'arasowa tayi har inda yake zaune ,tad'an matsar da system din da ke gaban shi sannan ta samu guri ta zauna. D'an d'agowa yayi da mamaki yana bin ta da ido ,sanin kanshi ne azziki baya kawo kubra sashen shi._




_wani irin shu'umin murmushi ta sakar mishi tare da shafo gefen fuskar shi ,a lokaci d'aya kuma tace_


"Makullin drawer-n kud'in ka zaka bani" ta fad'a kamar me rad'a. Wani irin d'agowa daddy yayi yana mata kallon baki da hankali. Magana ze yi ,kawai se ta murza kambun hannun ta, nan take yaji kanshi yayi wani mumunan sarawa ,murmushin zaka bani ko Yaya ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login