Showing 33001 words to 36000 words out of 37667 words

Chapter 12 - Sabon Salon Gidan Uncle

da ita yace “yunwa mijinki
yakeji amarya" kifa wayar tayi a cikinta tace “inajin akwai abinci a dinning"




Miqewa yayi ya nufi dinning din ya zauna ya bude food flast din yaga wayam ya
kallesu Suma suka kalleshi suna miqewa sukace “to yaya saimunzo cin na dare" juyawa

yayi ya kalli Hudah yace “Ki tashi ki dafamin wani abincin wannan dai babu" miqewa
tayi da sauri tace “babu?" Daga Mata Kai yayi tayi murmushi tace “tabdi aikuwa
saidai ka fita ka nemo abinci wlh na gaji ba iya yin wani girkin zanyi ba"
Baice Mata komai ba ya miqe ya sanya kayansa ya fice tabisa da kallo tare da tabe
baki ta miqe tayi komawarta daki sai dare ya shigo tayi masa sannu da zuwa ya amsa
Mata babu yabo babu fallasa ya ajiye kayan daya shigo dasu ya nufi bedroom yayi
wanka ya dawo ya zauna tayi sallar Isha tayi shirin kwanciya tazo zata dauki
wayarta ya janyota jikinsa ya kwantar da ita yace “kamar akwai abinda yake damunki
ko?"




Girgiza masa Kai tayi yace “ok don Allah kada ki tankawa su Abidah duk abinda
zasuyi Miki kiyi hqr mama batason bacin ransu sannan ki rinqayin girki dasu harma
maman ana Kai mata bakiga fadan da tayimin ba dazu dana shiga wai anyi mawa yayanta
wulaqanci akan abinci harma kinyi musu gori kince kayan abincin a daga gdanku
kikazo dashi" janye jikinta tayi tace “kuma kai ka yarda nayi musu?" Sake janyota
yayi yace “ya zaayi na tabbatar tunda bana gurin nidai nasan matata ta gaji arziki
batada halin matsiyata" daga haka bai sake bata damar cewa qalaba ya hade bakinsa
da nata ya fara tsotseta da sarrafata sunyi nisa sosai sukaji an banko qofar suka
miqe da sauri tana gyara rigarta Mama tayi tsaki tace “aikin banza qiba a muqamuqi
wahalalle sallamamme daga shigowarka harta fara lalubeka wannan bazata barka kayi
qibaba, kika wani tsareni da idanunki na karuwai ki tashi ki dafamin ruwan zafi
kisamin a flast dinnan zanyi wanka dashi"
Saurin dagowa yayi yace “amma mama duk yayanki ki rasa me dafa miki ruwan wanka
saikin tsallako titi kin taho nan?" Karkacewa tayi tace “yanzu dai tuhumata kakeyi
kenan ko saboda nasa matarka aiki ko?" Miqewa Hudah tayi tana maqale qirjinta ta
dauki hijjab ta sanya ta nufi kitchen ta dora ruwan zafin zuciyarta na suya tana
tunanin wanne irin dangin miji Allah ya hadata dasu a haka ta tafasa ruwan ta zuba
a flast din ta dauka takai Mata ta karba tace “kin taimaki kanki Kuma idan naje
naji bai tafasa ba komai dare saina dawo"
Hudah kam taga tasku tana fita ya rufe qofar da key ya janye matarsa suka shige
daki yanata rarrashinta saida komai ya kammala shidai yana samun gamsuwa 100%
itakam tsokanota kawai yakeyi yau mararta har ciwo tayi ganin hakanne yasashi dole
ya rinqa amfani da yan dabaru ya samu yaga ta samu gamsuwa sannan ta tashi tayi
wanka shidai baiyi ba da janabarsa ya kwanta abinda bata taba gani ba gurin
Shattima iyakar jarabarsa indai ya kwanta da mace sai yayi wanka yake bacci.




Washegari su Aunty Ubaidah sukazo da Amba ta yini tana murna duk da bata samu zama
ba saboda hidimar gurkin da taketayi ranar Amba taga ikon Allah qannan mijin yarta
kamar zasu takata sukazo suka dauki abinci suka tafi bayan fitarsu ne ta zauna suka
taba hira nan suke sanar da ita ashe tun ranar da aka kawota Shattima yana kwance
baisan waye akanta ba tausayinsa ya cikata tayi qasa da kanta tana share qwallah
magunguna Amba tabata sukayi sallama suka tafi suna fita ta dasa gurbin kuka
tananan zaune tanata yi Musaddam ya shigo ganinta haka yasashi qarasowa da sauri
yace “lfy waye ya mutu?" Cikin zaquwa tace masa “Uncle" gabansa ne ya fadi yace “to
me Kuma yayi?" Dagowa tayi tace “don Allah kakaini na dubashi bashida lfy baisan ma
waye ke akansa ba" ga mamakinta sai taji yayi tsaki yace “yanzu akan wannan zaki
dagamin hankali to bazaki ba" yana fadin haka ya shige daki tabisa da sauri tana
kuka tana “don Allah Saddam badan ni ba hankalina bazai kwantabs idan banje
nagansa ba" cikin masifar kishi yace “idan an rataya ajalinsa a rashin zuwanki to
yau ya mutu wlh indai Dr Musaddam ne yake amsa sunan mijinki bazaki duba wannan dan
iskan kawun nakiba bakisan dama ciki nake dashi ba akansa zan iya cimiki mutunci
fiye da tunaninki sakara kawai da batasan haqqin aure ba daga zuwanki kwana biyu
har danginki sun fara gorantawa qannena suna cewa su talakawane kalmar da wannan

shashashan qanin babar taki ya dade yana fadamin ‘me nasama yaci balle yaba na qasa
harta fara zagaya dangina to kisani inma zaki cireshi aranki ki cire na rabs duk
wata alaqa dake tsakaninku har abada idan kalma daya ta shiga tsakaninki dashi ko
bana guri ban yafe ba"
# *UMMUH HAIRAN*
[9/26, 7:35 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: *FTROGU24* Kallonsa takeyi cike da mamaki
saidai ta kasa cewa dashi komai ta juya zata fita ya riqota yace “bazan rinqa binki
dakinki kamar wani yaronki ba ki dawo ki kwanta anan" hakanan ta kwanta babu yanda
ta iya tanata jan zuciya shikuma yana danne dannensa a system har batasan lkcn da
bacci ya dauketa ba saida ya gama abinda zaiyi sannan ya hauro gadon ya kwanta.
Hakanan ta daukarwa kanta kullum zasuyi waya zata tambayi jikinsa amma bata taba
kiransa ba har zuwa lkcn da suka fita Cairo aka dorasa akan magani ya dan samu
sauqi ya dawo.
Rayuwarta a gidan mijin nata babu wani Abu na dadi da zata dorar kullum qannensa
cikin yimata rashin kunya suke idan tayi mgn shikuma yace batada hqr idan ta sanar
da mahaifiyarsa sai tahau sababi tana fadin zata raba Mata kan yaya, duk ba wannan
yafi damun Hudah ba aa rashin son ibadar Saddam shine abinda ya fara gallabar
rayuwarta zata iya qirga adadin lkcn daya tashi yayi sallah da asuba, Koda tama
matsa masa da tashin kashedi yayi mata me nauyi akan cewa kadata qara tashinsa.




Dole ta qyaleshi idan Kuma garin ya waye saidai taga ya shirya ya fice lamarin da
yafara sanya Mata kokwanto, lkcn da tayi watanni hudu ta kasa jurewa saboda daren
jiya tayi masa mgn akan ibada har cewa yayi da ita shifa zai iya sakinta akan
wannan takurar da takeyi masa, ta kasa jurewa hakan yasa ta kira Nusaiba tana kuka
take zayyane Mata komai Nusaiba tayi salati tace.
“Au shikuma haka yake? Aa bafa zai yuwu ba addini shine gabada komai ki fadawa
uwarsa tayu masa nasiha idan yaga dama saiya gyara idan Kuma bai gyaraba ba ke ki
fadawa iyayenki su sai su nema Miki mafita" hakan kuwa akayi washegari tashirya
taje gidan momy tasameta da mgnr budar bakinta tace “yo ai ba kabarinku daya ba ina
ruwanki da rayuwarsa ko dole sai yayi abinda kikeso"
Hakanan ta taso jiki babu qwari ta taho gida ranar tayi kuka dz nadamar abubuwa da
yawa ga Saddam ya qaro wulaqanci sai yakai 1:00am awaje sannan yake shigowa gidan
idan tayi masa mgn yace aikine ya riqeshi,




A cikin wannan yanayin Allah ya azurtasu da samun qaruwar juna biyu sosai takeshan
wahala ciwon ciki da Kuma kasala ga rashin son warin komai hakanan dai take daurewa
tayi abinda ya zama dole sauran ta qyale, da farko tana qoqarin girka abinci badon
kanta ba saidon mijinta da yan'uwansa Amma lkcn da cikin ya fara qwari sai ta ke
kasa hassala komai saidai bacci, nanne fah baba binta ta sakota gaba kullum da
tsirfar da zata tsiro da ita yau tace sakwara takeso gobe tace dambu,
Koda tace bazatayi ba bazata iyaba saboda batajin zata iya yima uwar mijinta
gardama, yau tun dare ta tambayesa zataje gda takuwa yi saa yabarta ta tashi tayi
duk abinda zatayi ta shirya bazata iya tuqiba hakan yasa yace tazo ya sauketa, lfyr
Allah yakaita gida yanata Mata Hira ita Kuma abinda ke damunta daban yau dai tayi
niyyar fadawa Abba gskyr abinda ke akwai saboda takasa hqr Kuma tasan zamansu bai
dace ba indai bazai gyara ba"
Yana sauketa ya juya a cewarsa sauri yakeyi ita Kuma taja qafarta ta shiga gdan da
sallamarta Adnan da Jiddah sukayo kanta a guje suna “ga aunty Hudah ga aunty
Hudah" wannan ihunne yasa Shattima dake kwance ya tashi zaune gabansa na faduwa ya
zuba mata ido ta kawar da nata dake cikin nasa ta zauna tana tambayar yaran Ammi,

Saukowa Ammi tayi tace “gani amarya wannan mijinaki da kullen masifa yake cikin
wata takwas wannan shine zuwa na biyu tabe baki Fatah yayi ya koma ya kwanta,
batare da yace Mata qala ba to itama kashedin Saddam yasa taqi tanka masa Ammi tana
latsata tace “meye ya ramar dake haka Hud?" Murmushi tayi cike da kunya tace
“bsnida lfy ne Ammi ga aiki don Allah ki samamin me aiki take Dan kamamin aikin
gidan ya fara yimin yawa musamman yanzu da nake fama da ciwon ciki"
Jinjina kai tayi tace “bayan nan akwai wani Abu Hudah kada ki boyemin" satar kallon
Shattima tayi idanunta ya ciko da qwallah ta miqe da sauri ta shige dakin Ammi,
itama miqewa Ammi tayi tabita ta isheta tanata kukanta ta zauna kusa da ita tace
“ni nasan da damuwa Hudah meye kuma" bata boyewa Ammi komai na abinda yafi damunta
a zaman aurenta ba sosai ammi ta Jinjina lamarin tace “aikuwa wannan ba qaramar
matsala bace bari na Kira Abba yana sama yayi baqo" fita tayi bata jima ba ta dawo
tace taso muje saiku gaisa da Alh Ibrahim dinma" miqewa tayi suka fita yanzu
Shattima bai parlour suka nufi saman




Mutumin da suke tare da Abba kawai ta zubawa ido tana kallonsa gabanta na faduwa
shima abinda takeji yakeji aransa tadai samu ta zauna suka gaisa Abba yace “Hudah
ga Alh Ibrahim nasan bakisanshi ba rabonki dashi tun kina wata bakwai" sake
gaisheshi tayi ya amsa da fara'arsa yana binta da kallo waiwaye na hasko masa
shekaru ashirin baya kawai sai yake hasko fuskar Ummuh matarsa data rasu da cikinsa
a jikinta akan fuskar Hudah tsoro ya kamasa yanajin wani yanayin qauna me tsuma
zuciya yana zagaya zuciyarsa game da Hudah.
Abba ne yace “kafin Mahaifiyarta ta rasu ta sanar da Khadija cewa ita yar Adamawa
ce Maybalwa sannan ta ambaci sunan wani mutum waishi Moddibo Almud...." Dagowa yayi
da sauri yace “Moddibo Almud?" Kallonsa sukayi dukka jikinsa yana rawa yace “me
waye yane sunanta?"




Shiru Abba yayi yana tunani can ya dago yace “ummuh Salma" wata kabbara Alh Ibrahim
yayi yace “ya akayi haka ta faru ko zan iya ganin hoton wani abu wlh Hudah ko
kokwanto banayi yatace ta cikina rungume Hudah Alh Ibrahim yayi yana kuka me taba
zuciya yana shafa kanta yana cewa ashe dama qaunar jini nakeyi Miki Hudah tunda
nabar qasarnan zuciyata taqi hutawa da tunaninki"
Sun jima a haka kafin daga bisani komai ya daidaita Alh Ibrahim yayi musu sallama
ya tafi nan Ammi ta zayyane masa komai Abba yayi shiru yana nazari ya dago ya
dubeta yace “ki shirya kawunki yakaiki gida zan nemi musaddam din zamuyi mgn"
Shattima dake shigowa ya tsaya yana kallonta yace “driver yakaita mana Abba ni
inada abinyi" daquwa Abba ya watsa masa yace “kai nace kakaita ba driver ba"
kallonta yayi yace “kuje Hudah duk yanda mukayi dashi zakiji" miqewa tayi ta fita
har ya shiga motar ta bude gabanta na faduwa ta shiga yaja a fusace ya fice ta
rinqa yimasa kwatance har suka isa bakin get din ta bude ta fita ta shiga gidan
yabi bayanta da kallo yana furzar da iska yace “Allah ya isana wlh duk ya qararmin
da Mata kawai don qaddara tasa tashiga gdansa"




_Kuyi hqr na jina Shiru da kukayi jiya nayi fama da ciwon Kai har yanzun ma ba
sauqi yayi ba_
# *UMMUH HAIRAN*
[9/27, 6:28 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: *_Pls paid before read, account Fauziyya
Tasi'u 0255526235 GTB ko hoton card MTN ta wagga number 09013718241 or VTU for
this number 09031307566 regular 200 VIP 500_*

*FTROGU25* Juyawa yayi da kan motarsa daidai lkcn da ta shiga gdan ta bude ta shige
ciki ta nufi dakinta domin zafi takeji sosai, ruwa ta watsa ta fito parlourn ta
zauna tanashan iska daidai lkcn da Saddamya shigo kamar an jefoshi batayi aune ba
taji ya dauketa da mari ta miqe da sauri tana Shirin yin mgn ya sake dauketa da
mari yace “ubanwa ya baki izinin kula wannan dan iskan dama ashe munafurta ta
kikayi kikace min zakije gda ashe gurinsa kikaje?"
Tsuma jikinta yakeyi sosai tana hawaye tace “zargina kakeyi Saddam?" Nunata yayi da
yatsa yace “an zargeki din ai dama ke abar zargi ce a gurina komai ma zaki iya wato
dokar dana sanya Miki ita kika karya ko to ki koma inda kika fito na sakeki saki
daya...."




Dafe kanta tayi da sauri tace “Innanillahi wa innah ilaihirraji'un Saddam akan dan
wannan abin" juyawa yayi ya shige ciki shima kuma sai jikinsa yayi sanyi wanka yayi
ya sauko da sauri lkcn tagama hada komai nata tana Shirin fita yace “kada ki fita
wlh bansan na furta ba ki dawo muci gaba da rayuwarmu Hud kishinki ne yasa har nayi
wannan subutar bakin"
Janyewa tayi zata fita yayi saurin datse qofar ya fusgota ta fada jikinsa ya
matseta yana sunsunarta yace “ki daina karyamin doka Hud inasonki bana fatan rasaki
don Allah" duk yanda take kuka Saddam Bai kulata ba saida ya gamsu ya qyaleta ta
miqe daqyar ta shiga dakinta tayi wanka ta kwanta tanajin zazzabinta na qaruwa da
haka bacci ya dauketa,
Washegari kam kulleta yayi a ciki saboda tsoron kada ta fita ya fita bai jima ba ya
dawo ya shigo dakinta ya isheta a galabaice yayi Mata sannu ya fita, wasa² saida ta
kwana uku tana jinya ko gdansu bata fada ba Nusaiba kawai ta fadawa ita taketa
taimakonta da ayyukan gdan tana tausayawa qawar tata halin da take ciki.



Kwanaki sun danja tafiyar ba wani dadi takeyi ba babu wata kyakkyawar jituwa
tsakanin ma'auratan ga Kuma dangi miji a gefe da basa uzuri duk da halin da matar
yayan nasu take ciki qa'ida ne sai tayi musu abinda ta saba tanayi musu idan batayi
ba kuma matsala ta haifi, yaudin ma kamar ko yaushe tana kwance cikinta na damunta
da ciwo sai juyi takeyi babu wani mataimaki sai Allah taji an banko qofar an shigo.
Daqyar ta daga idanunta ta dubi me shigowar Mama Binta ce da yayanta biyu ta
yunqura a hankali ta miqe zaune tace “sannu da zuwa mama" daga mata hannu tayi tace
“sannunki rama take sani nazo jin ba'asin dalilin da yasa kika daina yimana girki
ne" qasa tayi da kanta idanunta ya ciko da qwalla tace “banida lfy ne mama kwana
uku komai bana iyawa saidai qawata tazo ta taimaka min...." Daga Mata hannu ta
sakeyi tace “ko asibitin murtala ce ke dole tunda kike auren dana kayimin abinda
nakeso idan ba hakaba Kuma a dauki hanya a koma aci gaba da abinda aka saba sannan
yanzu maza ki tashi ki kirbamin sakwara da miyar ganda"




Girgiza kai tayi cikin kuka tace “wlh Mama bazan iyaba kiyi hqr idan naji dama zuwa
gobe sai nayi miki ..." Dauketa tayi da mari kafin tayi tunanin wani abu sun rufeta
da duka ta ko Ina ta rinqa ihun neman taimako qarshe dai bata tashi farkawa ba sai
ganinta tayi a gadon asibiti tana waiwayawa taga Ammi da Abba suka matso gabanta
sunayi Mata sannu bata iya amsawa ba sai hawaye da takeyi daidai lkcn da Shattima
ya shigo ya dubeta yace Mata “ya jikin?" Daqyar tace da sauqi tanajinta kamar a
daddaure Abba ya dubeshi yace “ya kukayi dashi" sunkuyar dakai yayi yace “yace

bazai samu damar zuwa ba sannan idan ta warke ta wucce gda harsai zuciyar uwarsa
tayi sanyi da qannensa ko zata dawo"
Alh Ibrahim dake zaune ya miqe yace “kayyy Alh bafa zai yuwu ba wlh wannan yaron
dame yake taqama ne su uwarsa da qannensa su dakarmin ya har su zubar Mata da ciki
kuma tunda take jinya kwana uku bai tako yazo ba sannan yake fada mana son ransa"
figar hannun Shattima yayi suka fice Abba na kiransu Amma babu wanda ya saurareshi
suka shiga mota suka tafi Shattima na qara zuga Alh Ibrahim suka ishe Saddam a
gidansa yana Shirin fita Alh Ibrahim ya matsa ya damqi wuyansa ya gabza masa mari
jini ya balle ta hancinsa ya bugashi da mota yazaro qaramar bindiga ya dora masa a
wuyansa yace “sakarmin ya dan ubanka kafin na kasheka na kashe banza jahili mara
addini bandama qaddara uwarme Hudah zatayi dakai matsiyaci dakai"




Sosai maganganun sukayi masa daci ya kalli Shattima Shattima yayi masa murmushin
gefen baki yace “ka cika umarni kawai yaro dama ai bakin rijiya ba gurin wasan
makaho bane inyaso sai kaje ka auri uwarka ku zauna tare" kalmarce tayi masa daci a
zuciye yace “na saketa saki daya" yana furta haka Shattima yace “biyu kenan harda
wancan na baya ko?" Bai tanka masa ba Alh Ibrahim ya koma mota ya dauko biro da
takarda ya cilla masa yace “zana akai" dauka yayi ya rubuta suka karba suka tafi
suka barshi zaune a gurin asibitin suka koma suka zayyanewa Abba duk abinda ya faru
sosai abba yaga quruciyarsu Amma sai yace “Allah yasa hakance tafi alkhairi" tun
daga wannan ranar Shattima yake bawa Hudah kulawa ta musamman komai nata yana
kafkaf danma dai iyayen nasu sun sanya masa ido,
Tana qara samun qwarin jikinta Alh Ibrahim ya dauketa itada Shattima suka tafi
Adamawa wayyo sunga gata da qauna gurin dangi biyun dangin uwa dana uba sun nuna
musu qauna zahiran kamar su lasheta kowa cewa yake ga Ummuh Salma ta dawo haka suka
rinqa lelenta kwanan Shattima uku ya tafi itakam kakarta babar mamanta cewa tayi
tazo kenan abu kamar wasa rigima ta qarke itafa babu Wanda zai rabata da Ummuh
qarama dole aka barmata ita a waya take fadaws Nusaiba tana garinsu zatayi watanni
uku aikuwa washegari ta taho da ways da kwatance sai gata a gidan sunyi murnar
hakan ashema sudin asalinsu yan gari dayane kwanan Nusaiba uku a tare da Hud suka
tafi micchika dama mijin babar Nusaiba ya rasu suka sauka a gurinta suka kwana hudu
suka nufi gdan babanta suka kwana daya kwanan Babu dadi suka dawo Maybalwa Hud tana
rayuwa tsakanin gdansu babanta da har yanzu bashida mata da gidansu Ummuh rayuwarsu
ita da aminiyarta gwanin dadi......




_Zanyi amfani da wannan damar nabaku hqr tun daga wannan satin har zuwa qarshen
watan October bazanke samun lkc yadda yadda ya kamata ba wannan dalilin yasa
wasunku idan zasu tuna nace bazan fara typing din wannan littafin ba sai November,
yanzu dai insha Allah zanyi qoqari na rinqa yin ko babu yawa kullum, kuyi hqr! kuyi
hqr!! kuyi hqr!!! Lamari ne me girma da dayawanku idan kukajishi zakuce nama aje
saina gama na dawo hayyacina🙈🙈_
# *UMMUH HAIRAN*



[9/28, 7:17 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: *🌱F.T G.U RETURN🌱*
*26*



*_Pls paid before read, account Fauziyya Tasi'u 0255526235 GTB ko hoton card MTN
ta wagga number 09013718241 or VTU for this number 09031307566 regular 200 VIP
500_*

Wasa kamar gaske sai gashi ta dauki wata biyu lkcn da yayi daidai da kammaluwar
iddarta aikuwa kamar shattima na lissafi ranar ya kirata taqi dagawa dake

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login