Showing 6001 words to 9000 words out of 16055 words
k'ofar yyi da k'arfi,Surayya da bata dade da koma wa gida ba sabida tsabar tsoron da take ji,ganin biyar tayi ne yasa ta nufi gida dan ta d'ora girki,tana cikin jajjage taji an buga k'ofa wurgar da tabaryar hanunta tayi ta shige d'akinta da gudu ta rufe k'ofa jikinta sai rawa yake,jin da tayi an k'ara buga k'ofar ne yasa ta fara" wa innahu sulaimanu wa innahu bismillahi ku kuke ganin Mu, ba mu muke ganinku ba"duk adduar daya zo bakinta karantawa kawai take in banda gumi babu abinda ta keyi,Abdulmajeed jin shiru ba amsa bane yasa yayi tunanin ko basa gidan,suna gidan Hadiza d'aya makociyar tasu da wanan tunanin ya nufi gidan Hadizan yana shirin kwankwansa,ta bud'e k'ofar ta fito da alama wani wajen zata,da sauri ta gaishe shi,ya amsa yana tambayarta ko su Muhibba na nan,ce mishi tayi,Muhibba bata nan amma Surayya bata Dade da barin gidanta ba,ta tafi ta d'ora girki,godiya ya mata ya nufi gidan Surayya yana mamakin inda Muhibba taje,k'ara kwankwasa gidan yayi,Surayya da tun lokacin tana jikin labule sai addua take,jin an k'ara buga k'ofar ne yasa ta saki fitsarin daya matseta,dan duk a tunaninta aljanar ce take buga gidan tunda taga Muhibba bata nan,Abdulmajeed gajiya yayi da buga k'ofar ya koma kan lifan d'insa ya zauna ,zuciyarsa sai tafarfasa take, Yana zama da minti biyar,Ayuba shima ya k'aryo kwana parking yayi a k'ofar a gidansa ya sauk'o daga machine d'insa ya nufi wajen Abdulmajeed dake karkada k'afa hannu ya mik'a mishi suka yi musabiha yana kallon k'ofar gidansu Abdulmajeed,tambayarsa yayi Muhibba bata nan,cikin tsananin Bacin rai Abdulmajeed yace masa bata nan shima bai San Inda ta tafi ba ya ma d'auka tana gidansa Ashe itama surayyar bata nan,Ayuba juyawa yayi ya kalli k'ofar gidansa,ganin babu padlock daga waje ne yasa yace mishi Surayya ta nan k'ofar gidan ya nufa shima ya fara kwankwasa k'ofar,ganin ya kwankwasa sau hud'u ba a bud'e bane yasa yayi yayi amfani da mukullin gurinsa ya bud'e k'ofar,Surayya kuwa tana jin an bud'e k'ofar ta saki ihu tana " wayyo Allahna kiyimin rai Ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba,Allahu la illah ha illa huwa Al hayul al qayyum,inna anzalnahu fi lailatul kadir,wa shamsu wa duhaha,kowane sura kamowa kawai take jikinta na rawa,Mamakine ya rufe Ayuba yace " Surayya kina da hankali kuwa mai yake damunki,"?shiru Surayya tayi da taji muryar Ayuba lek'a wa tayi ta windown d'akin sai da ta tabbata shine tafito daga bayan labulen ta bud'e k'ofa ta fito,Ayuba jikakken skirt d'inta yafara bi da kallo,ya dawo da kallonsa kan fuskarta da ta had'a gumi,sai muzurai take,"Surayya lafiyarki kuwa? Ayuba yace yana k'ara binta da kallo,"ina fa lafiya ayuba aljana ta sako Mu agaba tun dazu take buga min gida,Muhibba ma ta tafi gida tace bazata iya ba ta tafi gidansu,Ayuba mamaki ne ya rufe shi yace "bangane mai kike nufi ta da tafi gidansu ba"? Surayya kwashe komai tayi ta fad'awa Ayuba,girgiza kai yayi yace mata Abdulmajeed na waje bari ya fad'a masa Muhibba ta tafi gidansu,Surayya Hijabinta ta zura ta bishi suka yi waje dan tace tsoro take ji,Ayuba bayani yayi wa Abdulmajeed,Surayya itama ta bashi labarin yanda aljanar ta ringa tsorata su tana ita bata San tsautsayin da ya kai Muhibba ta bari aljana ta shigar mata band'aki ba,Ayuba Shawara ya hau bawa Abdulmajeed akan yasa ayi mishi sauk'ar Qurani,tunda suka fara mishi magana ya saki Baki yana kallonsu dan ba haka Muhibba ta ce mishi ba,kenan karya muhibba take mishi data ce Almajira ce tayi bara,aljana ta bud'ewa gida ta shigar musu band'aki,wani irin tafasa yaji zuciyarsa nayi yana ganin Muhibba ta gama rainashi duk gargadin da ya mata Ashe bata ji ba, godiya yayi wa Ayuba ya k'arbi mukullin padlock d'in daga hanun surayya ya bud'e gidan ya shigar da lifan d'in sa
[9/22, 12:18] Sadnaf: ππ *Dπ
°Gπ
° Tπ
°IMπ
°KO*ππ
*Written by*
π
π
*SADNAF*π
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l
*TRUE LIFE STORY*
ππ *Dπ
°Gπ
° Tπ
°IMπ
°KO*ππ
*Written by*
π
π
*SADNAF*π
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l
*TRUE LIFE STORY*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
PAGE 6
Abdulmajeed ransa a mutuk'ar bace ya zauna a Palo sai karkad'a k'afa yake yana tunanin matakin da zai d'auka akan Muhibba,ga yunwan da ya koro shi,gashi bai iya girki ba,tsaki yayi a fili yace "zaki gane kurenki bazan je gidan naku ba,in kin gaji zaki dawo da kanki" kwanciya yayi akan dogon kujeran yana jin yanda cikinsa ke k'ugin yunwa.
B'angaren Muhibba kuwa sai wajen k'arfe 2:30 ta tashi daga barci wanka ta farayi,tayi sallah abincin da Nafeesa ta zubo mata ta jawo taci ta koshi,ta nufi d'akin Mahaifiyarta,ganin bata d'akin ne yasa ta koma d'akinsu ta zauna ta rafka tagumi tana kallon Nafeesa dake shirin tafiya islamiyya,tunanin Abdulmajeed ta fara yi tana tunanin ko ya zai ji idan ya dawo ya tarar ba ta nan,tunani tayi na ta kirashi a waya, ta fad'a mishi da kanta,wayar Nafeesa ta k'arba tayi dailing Number Abdulmajeed,taji switchoff,mik'awa Nafeesa wayarta tayi ta cigaba da tunaninta,ta rasa mai yasa aljanar data taimaka wa take bibiyarta,Muhibba ahaka ta wuni tana tunanin sai wajen k'arfe shidda Mallam Hashimu Mahaifinta ya dawo daga kasuwa,sai da yayi sallar isha yaci abinci Maryam take bashi labarin abinda ya faru da Muhibba,sallati yayi yasa aka kira mishi Muhibba,ya k'ara tambayar ta abinda ya faru ta k'ara bashi labarin abinda ya faru,ba k'aramin firgita Mallam Hashimu yayi ba daya ji abinda Muhibba tace dak'ewa yayi bai nuna mata ba ya rufe ta da fad'a yana mai ya kai ta ta bud'e k'ofa ai gashi nan Dπ
°Gπ
° Tπ
°IMπ
°KO ta janyo wa kanta fad'a ya ringa mata sosai yana kar ta sake irin wanan gangancin,gobe zai bata adduoi ta koma gidanta insha Allahu,Allah zai kareta daga sharrin aljanar,jin abinda yace ne yasa Maryam tayi magana tana "bai kamata Muhibba ta koma gidanan ba tare da anyi saukar Qurani ba ita ganinta a kira Abdulmajeed awaya ace masa yazo inyaso sai su bashi shawaran yasa ayi saukan,da wanan shawarar suka yanke zasu nemi Abdulmajeed,Muhibba ta tashi ta nufi d'akinsu tana tunanin Abdulmajeed.
Abdulmajeed kuwa da k'yar yayi sallar magriba dan jikinsa har rawa yake sabida yunwar da yake ji,mik'ewa yayi daga kan sallayar ya d'auki mukullin lifan d'insa dan bakin titi yake so yaje ya siyo tsire yazo yaci,ji yayi ana kwankwansa gidan,hanyar waje yayi yana bud'ewa yaga Ayuba a tsaye da flask a hannu,Ayuba mik'a mishi flask d'in yayi yana cewa "ga abinci nan yaci tunda madam bata nan,da sauri ya k'arb'a yana mishi godiya,kulle k'ofar gidan yayi,ya ajiye flask d'in hanunsa sai da ya fara tada engine tukuna,ya nufi Palo, a tsakiyar Palon ya zauna ya bud'e flask d'in lafiyayyen jollof d'in shinkafa da yaji kayan had'in kayan lambu yayi tozali dashi,aikuwa da gudu ya nufi kitchen ya d'auko plate da spoon, yazo ya zauna ya zuba ya fara ci, sai da yaci ya koshi sosai yayi hamdala,dak'yar yayi sallah isha sabida koshin da yayi,plasma dake mak'ale a jikin bango ya kunna bayan ya idar da sallah ya fara kallo Dan ya rage dare,Dan ji yayi gidan ya mishi fad'i ya kuma rasa mai yake mai dadi,tsaki yayi a lokacin da ya dau remote Dan ya chanza tasha yana " gida idan babu mace tamkar kango ne" kallo yake amma tunanin
Muhibba yake ahaka ya ringa zuba tsaki shi kadai,wani irin tsoro ne ya rufeshi a lokacin da yaga horror film akeyi dan Inda aka nuno yanzu ba k'aramin tsorata yayi ba da sauri ya kashe kayan kallon,yayi waje band'aki ya nufa Dan ya d'auko bokiti ya zuba ruwa ya watsa Dan kwanciya ya keso yayi duk da bashi da tabbacin in zai iya baccin,ganin babu ruwa abokitan gidan ne yasa ya ja ruwa a rijiya,ya kai ruwan band'aki ya koma d'akinsa ya cire kayansa ya d'auro towel ya nufi band'akin brush ya farayi kafin yayi wankan Dan ya Riga ya saba,takun takalmi ya fara jiyowa daga tsakar gida,takalmin ma irin mai tsinin nan,"kwas kwas kwas " kawai yake jiyowa,gabansa wani irin fad'uwa yayi Dan yasan ya kulle k'ofar,towel d'insa ya janyo da sauri yayi waje yana "waye" waige waige ya fara yi yayi hanyar k'ofar gida yaga k'ofar na nan a kulle,ciki ya koma ya duba ko ina bai ga kowa ba,rufe ko ina yayi ya koma band'akin yana tunanin kunensa ne ya jiyo masa takun takalmi towel d'insa ya cire ya fara wanka,yana wanka yana kallon mudubi,duk'awa yayi Dan ya debo ruwa ya watsa yana d'agowa idansa ya sauka akan mudubin band'akin Matan nan ya hango abayansa ta zuba mishi ido tana kallonsa idonta jajaye kamar jini, dogwayen hak'oranta awaje,gashinta kuwa har kasa,wani mugun ihu Abdulmajeed yayi,yafita waje dagudu,cal cal cal ya shige d'akinsa ya kulle jikinsa na rawa, Numfashin sa kamar zai d'auke sabida tsabar tsoro,ahankali ya zauna akan gado yana mai da numfashi ya ma manta babu komai a jikinsa" adduoi yafara yi yana dafe da k'irjinsa ahankali ya fara samun nutsuwa,sai da kai Minti talatin azaune,ya mik'e ya d'auko gajeran wandonsa yasa,yana shirin sa vest yaji an bud'e k'ofar kitchen aguje ya hau kan gado ya janyo bargo ya rufe kansa jikinsa kuwa sai rawa yake,hawaye ya hau zubo mishi yana " Ashe Muhibba dagaske take da aljana a gidanan shi kenan tawa ta kare" ahaka ya cigaba da rawar d'ari yana adduoi ganin bai k'ara jin motsi ba yasa ya yaye bargon da ya rufe Kansa ya zauna akan gadon sai da yafara lek'a ko ina ya duro daga kan gadon,Touch light ya d'auko ya kuna,yasa agafen gadon,duk da engine a kunne yake fitilar d'akin a kunne yake,wayarsa ya d'auko ya kuna torchlight d'in Dan ba k'aramin tsoro yake jiba Dan in ya rufe idonsa aljanar nan yake hangowa,gadon ya hau ya kwanta yana kalle kalle,bakinsa d'auke da addua Dan babu yanda zai yi ne in ya fita zai iya ganin aljanar da ba abinda zai sa ya kwana a gidan,ahaka ya kwanta a tsorace said wajen k'arfe d'aya da rabi barci ya d'aukeshi,wajen k'arfe uku na dare yaji motsi a gefensa ahankali ya bud'e idonsa cikinsa wani irin murd'awa yayi gudawa mai k'arfi ya taho masa sakamakon tozali da yayi da aljanar nan azaune a gefensa tana murmushi idonta ya k'ara girma razanan ihu ya saki ya mik'e aguje ya bud'e k'ofa yafita waje,ganin zai iya kashi awando ne yasa ya nufi band'aki da gudu ya rufe k'ofa ya hau kan Masai ya hau sakin gudawa jikinsa na rawa rufe idonsa yayi gam,kirjinsa sai dukan goma goma yake,babu abinda kake ji sai sauk'ar gudawansaπππ(readers Ashe dai Abdulmajeed matsoraci ne) ji yayi kamar an bud'e k'ofar band'akin,cikin tsananin tsoro da firgita ya fara ihu yana " kiyi min rai karki cutar dani kiyi hak'uri Dan Allah" ihu yake sosai jikinsa na rawa shirun da yaji ne yasa ya bud'e idonsa ahankali ganin bai ganta a band'akin bane yasa ya d'iba a guje ko tsarki bai tsaya yi ba,ballantana akai ga yasa wandonsa,k'ofar gida ya bud'e ya fita waje,kasancewar babu wuta garin duhu,wandonsa yasa da sauri ya nufi gidan Ayuba ya fara kwankwansa da sauri yana waige waige ,Surayyan dake rungume ajikin Ayuba tana barci,jin da yayi ana kwankwasa gidan ne yasa ta tashi a firgice ta hau kan Ayuba tana nuna mishi k'ofa.
Abdulmajeed buga gidan yake da sauri yaji an dafa bayansa fitsari mai zafi ya saki awando a juya ahankali aljanar nan ce ta da fashi tace da muryar yara "Abdulmajeed ina zaka ni Dana zo na ta yaka hira"Abdulmajeed zubewa yayi akasa sumame.
[9/22, 12:18] Sadnaf: ππ *Dπ
°Gπ
° Tπ
°IMπ
°KO*ππ
*Written by*
π
π
*SADNAF*π
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l
*TRUE LIFE STORY*
ππ *Dπ
°Gπ
° Tπ
°IMπ
°KO*ππ
*Written by*
π
π
*SADNAF*π
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l
*TRUE LIFE STORY*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
PAGE 7
πππππππππππππππππππππππππππ *Readers bari dai na rufe bakina kar ya yage garin dariya Ashe haka page 5 da 6 yake da abin dariya sai da na karanta nima Dana yi posting naci dariya na gode Allah bare wajen matuniyata Surayya mai karatu kala kala gaskiya naji dadi babu laifi duk inda na lek'a jiya dariya kawai ake,masoyana.burina a kullum na saku nishadi*πππππ
*Note*- *yar uwa maman mamy sorry for scaring you,i don't mean to scare you please,like serious wanan novel d'in ya faru agaske amma ba exactly yanda nake rubutawa ba na k'ara abubuwa sosai sabida kawai na nishadantar,zan iya cewa adaidaita Sahu na hau kunsan mata da hira naji wasu suna labarin wacce abun ya faru da ita Dan da dukan alamu 'yar uwarsu ce, labarin ya mutuk'ar tsumani Dan sabida naji karshen labarin har an wuce inda zan sauk'a kunsan marubuci da San kwasan rahoto tuni jikina ya fara rawa nafara tunanin yanda zan juya labarin ya zama novel,aikuwa ina zuwa gida na sungumi wayata na fara typing, Dan haka sis ban yi novel dinan Dan in in tsorata kowa ba,nayi ne Dan na nishad'antar kuma Alhamdulillah ba laifi Sadnaf sunsa mutane dariya in kika kwantar Da hankalinki gajeran novel ne ba mai tsayi ba stay blessed everyone love you oll* πππ
Ayuba tashi yayi ya zauna ya duba agogon wayansa yaga k'arfe hud'u saura shima jikinsa ne ya fara rawa tsoro ya rufeshi yana tunanin Wanda ke kwankwasa k'ofa uwar haka,Kallon Surayya yayi da ta jike da gumi sabida tsananin tsoro yace ta d'aga shi yaje ya duba Wanda ke kwankwasa k'ofar,kankameshi tayi tace kar yaje ko ina yasani ko aljanar ce take kwankwasa musu k'ofa,ce mata yayi ba bud'ewa zai yi ba zai lek'a ta ramin k'ofar ne yaga waye, Surayya kin cika shi tayi,suka mik'e tare Ayuba ya bud'e k'ofa ahankali suka fito suna dab da isa k'ofar suka jiyo guje gujen maguna asaman kwanu, taku biyu Surayya tayi ta shige d'aki,Ayuba ya rufa mata baya,karkashin gado Surayya tafara shirin shigewa,Ayuba ya rufe k'ofar har da Dan tusar sa.
Abdulmajeed dake kwance a kasa a sume,ji yayi an yayyafa mishi ruwa ahankali ya bud'e idonsa,ganin bai ga kowa bane yasa ya mik'e aguje yana bubbuga gidan Ayuba,Surayya da Ayuba da jikinsu tun a lokacin bai bar rawa ba,suna dunkulle awaje d'aya,jin da suka yi an k'ara bubbuga gidan ne yasa suka wage baki suna adduoi Ayuba na karanta Laqadjaakum,Surayya na karanta Fatiha Dan ba k'aramin tsorata suka yi ba Dan har a lokacin suna jin guje guje asaman kwanu,Abdulmajeed da shima a mugun firgice yake ganin babu alamar za a bud'e k'ofar ne yasa ya hau k'wallawa Ayuba kira yana yazo ya bud'e masa shine Abdulmajeed,cak Ayuba ya tsaya da karatun da yake,ya kasa kunne Dan kamar sunansa yaji ana kira,muryar Abdulmajeed ya jiyo yana Kiran sunansa,da sauri ya raba jikinsa Dana Surayya ya mik'e yayi waje Surayya sai kiranshi take ya dawo,Abdulmajeed
kuwa waige waige kawai yake yana kiran sunan Ayuba ga tsanin tsoro ga wani gudawar da yake ji,Ayuba na bud'e gidan ya shige da gudu,Ayuba kuwa yayi sauri ya rufe gidan,a tsakar gida ya sameshi yana kai da kawowa, " Abdulmajeed Lafiya kuwa daddaren nan waye ya koro ka"? Ayuba yace yana kallon gajeran wandansa dake Neman sub'alewa daga jikinsa "Ayuba bani touchlight na Shiga band'aki tukuna kashi nake ji" Ayuba d'akinsa ya shige ya tarar da Surayya a zaune akan gado duk ta had'a zufa sai ajiyar zuciya take Dan sai da ta jiyo muryar Abdulmajeed hankalinta ya kwanta,Touch light d'in dake gaban mudubi ya d'auka yayi waje da sauri Abdulmajeed ya k'arbi touch light d'in daga hanun Ayuba ya shige band'akin Dan ginin Gidansu iri d'aya ne kasancewar haya duk saka kama,yana hawa kan Masan yafara sukurkuta gudawan,Ayuba ciki ya koma ya zauna a gefen Surayya aikuwa suka jiyo karar sauk'ar gudawan Abdulmajeed ji kake "buut bubut" Surayya mai zata yi in ba dariya ba har da rik'e ciki,Ayuba shima duk yanda yaso ya gintse dariyar da ta taho masa kasawa yayi sai da ya saki dariyan,Surayya kasa tayi da murya tafara maganar " Ayuba duk yanda akayi Aljanar nan ce ta tsorata Abdulmajeed shi yasa kaganshi daddaren nan gashi sabida tsorata da yayi bar da su gudawa Ashe Muhibba ma ta fishi jarumtaka"Surayya tace tana k'ara kyalkyalewa da dariya,Ayuba shima kasa yayi da murya yace " aikuwa inaga aljanar ce ta koro shi Dan babu Riga a jikinsa da gashi sai gajeran wando" Abdulmajeed Sai da yayi minti goma sha Biyar a band'akin kafin ya fito,yana sauke ajiyar zuciya,Ayuba mik'ewa yayi, ya yi hanyar waje,palo ya bud'e yace wa Abdulmajeed bismillah,tare suka shiga palon, Abdulmajeed ya ajiye touch light d'in hanunsa yacewa ya Ayuba taimaka masa da Riga ya sa,Ayuba d'akinsa ya koma ya d'auko masa doguwar Riga Surayya kuwa ta biyoshi Dan tace bazata iya zama ita kadai ba,zura rigar yayi ya zauna,Ayuba yace "Abdulmajeed ina jinka mai ya faru,"
" Ayuba Allah ne yayi ina da sauran numfashi agaba da tuni kaji labarin na mutu tun k'arfe 11 Aljana ta sako ni agaba ina zaman zama na Muhibba ta janyo min" ba irin gargadin da ban mata ba akan tasan irin wayanda Zata na taimakawa tana Sanin irin wayanda zasu na na shigar min gida Sai gashi ta janyo min masifa Dπ
°Gπ
° Tπ
°IMπ
°KO,"Subhanallahi kace abinda ya faru kenan,Allah ya tsare mu da tsarewarsa ya kare mu daga sharrinta" " Ameen kai dai ai naga masifa wlh har k'ofar gidanan ta biyoni Allah Ayuba ba Dan ina da dauriya ba da tuni na mutu," "innalillahi wa inna ilaihi rajiun Allah ya tsare mu kace ba k'aramin tashin hankali Muhibba