Showing 3001 words to 6000 words out of 16055 words

Chapter 2 - DAGA TAIMAKO

SADNAF   

23 Oct 2024

1242

d'an kwandon dake mak'ale ajikin mudubin dan ta d'auko brush d'inta da MacLean itama tayi brush,kamar cewa akayi ta kalli madubin,matar nan ta hango a mudubi tana tsaya ajikin bango tana mata murmushi hakoranta amadadin farare jajaye ne,wani irin gigitacen k'ara ta saki ta zube a band'akin a sume,sallati Abdulmajeed yayi ya kinkimeta yayi waje da ita, a d'aki ya kwantar da ita, ya debo ruwa yazo yana yayyafa mata,ajiyar zuciyar tayi ta bud'e idonta ahankali,kuka ta fashe dashi ta rungume Abdulmajeed tana "Abdul na shiga uku na lalace D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO na janyo wa kaina masifa laifine dan na taimaketa,meyesa take San cutar dani" duk maganar da take kuka take jikinta na rawa,Abdulmajeed d'agota yayi yana share mata hawaye yace " Muhibba mai ya faru wa kika taimakawa? Ki fad'amin gaskiyar abinda ya faru dan ni ina dawowa nasan ba dai dai kike ba,dan gabad'aya a firgice kike" tunanin Muhibba ta fara yi na ta fad'a mishi gaskiyar abinda ya faru,wani tunani tayi kwanakin baya wasu 'yan mata sun zo lokacin Abdulmajeed yana nan, 'yan matan suka ce ta taimaka musu da ruwan sha,shigowa tace suyi tayi musu jagora har palo,ta debo musu ruwan suka sha daga nan kuma hira ta b'arke musu kasancewar mata akwai saurin sabo,suna cikin hirar Abdulmajeed ya shigo yace su fita su bar mishi gida,jiki na rawa suka bar gidan,aranar Abdulmajeed kwana yayi yana mata fad'a kamar ya daketa,Ya kuma ce mata duk lokacin da ta k'ara barin bakon mutum ya shigo masa gida,sai ya d'auki mumunan mataki akanta,da wanan tunanin tak'i gayawa Abdulmajeed gaskiyar abinda ya faru,Abdulmajeed ganin tayi shiru tak'i magana ne yasa yaji ransa na b'aci wani irin tsawa ya daka mata yana " ina tambayarki kin yi shiru wa kika taimakawa yake Neman cutar dake" jikinta ne ya hau rawa tsoron Abdulmajeed ya rufeta magana tafara yi tana kuka "wata tsohuwa ce dazu tazo bara tace na taimaka mata da sadakar abinci,shine na bata,ta tafi,tunda ta tafi take tsoratani duk Inda nayi sai na ganta"wani mugun tsaki yayi ya mik'e "Dana San abinda kika yi kenan wlh ko saurarenki ba zanyi ba badai bakya jin magana ba ki cigaba watak'ila ma aljana kika taimakawa,ke gaki uban yan San taimako,hanyar waje yayi ta bishi da gudu,tana tsaye a band'akin yayi wankansa ko kallonta bai yi ba,itama cire kayanta tayi dasauri ta watsa ruwan duk abinda take yi idonta a rufe dan gani take inta bud'e idonta zata iya ganinta,a tsakar gida ta k'arasa sa towel dan Abdulmajeed fitowa yayi ya barta a band'akin,alwala tayi tabi bayan Abdulmajeed daya shige d'akinsa yana shimfid'a sallaya,doguwar Riga tasa ta zura hijabinta ta tsaya daga bayansa,sai da suka yi sallar magriba kafin suka yi isha,Muhibba addua ta ringayi a sujadar karshe tana addua'r Allah ya rabata da sharrin matar da ta taimaka wa,Abdulmajeed Palo ya nufa bayan sun shafa,biyo shi tayi da sauri ko hijabin jikinta bata cire ba, a tsakiyar palon ya zauna inda ta jera abincinsa,zama tayi ta ta d'auki plate tafara zuba abincin jikinta sai rawa yake dan har yanzu tana ganin fuskar matar a idonta,ajiye plate d'in tayi a gabansa bayan ta zuba mai abincin,bismllah yayi,yafara cin abincinsa Muhibba kuma ta zauna tayi tagumi tana hawaye,"ke bazaki ci abincin ba kenan"? Abdulmajeed yace batare da ya d'ago ya kalleta ba,Share hawayen daya zubo mata tayi tace " a koshe nake bana jin yunwa" Abdulmajeed d'agowa yayi ya kalleta ya ajiye cokalin Hanunsa,yace," Wai Muhibba kukan mai kike yine,wani ne ya aike ki bawa tsohuwa abinci,ke kika fi kowa San kiyi taimako,haka kika ga sauran makotanki nayi,ban hanaki taimako ba amma na fad'a miki kinsan irin wayanda zaki na taimakawa dan tun daga lokacin da Aunty Ainau (yayarsa) ta bawa Almajiri sadaka ta kamu da rashin lafiya mai tsanani sai da akayi dagaske aka gano Ashe almajirin nan ba mutum bane Aljani ne,Ashe kud'in nan da ta bashi sadaqa dashi ya ringa cutarta sai da aka runga adduoi ana sauk'ar qurani kafin ta samu lafiya,wlh tunda ga lokacin nake tsoron in taimakawa Wanda bansani ba,dan kai da zuciya d'aya za kayi taimakon amma akarshe Wanda ka taimakawa ne yake cutarka shiyasa nake hanaki kwashe kwashe," tunda ya fara magana taji wani tsoro ya kuma rufeta,matsawa tayi kusa dashi da sauri tana " Abdul yanzu ya zanyi wlh bansan ba mutum bace"tace tana fashe da kuka,"ki kwantar da hankalinki kiyi Addu'a insha Allahu,Allah bazai bata ikon cutar dake ba,this would serve you a lesson next time zaki San irin wayanda zaki ringa taimaka wa,yanzu dai ki zuba abincin nan kici sai na raka ki kiyi alwala kizo ki kwanta,"Abdulmajeed yace yana bud'e kular abincin,dak'yar taci cokali uku ta ce mishi ta koshi,kwashe kwanukan yayi da kansa ya kai kitchen, yace mata tazo tayi alwalar,alwala tayi a tsakar gidan kanta a sunkuye dan gani take inta d'ago zata iya ganin Matan nan,d'akinsa ta nufa dasauri ta rufo k'ofar,dan Abdulmajeed har ya kwanta,shiryawa tayi cikin kayan barci,ta fesa turare ta kwanta agefensa kamar zata shige jikinsa sabida har yanzun a tsorace take,tashi yayi zai kashe fitilar d'akin tayi sauri ta rik'o shi "dan Allah Abdul karka kashe wutan d'akin wlh tsoro nake ji" wani kallo ya watsa mata yace " kin tab'a ganin nayi barci fitila a kune,kashewa zanyi dan bazan iya barci ba ina barshi a kune,ke kika sa tsoro aranki amma ina gefenki mai zai tsorata ki,"sauk'a yayi ya kashe fitilar d'akin tayi sauri ta runtse idonta da k'arfi dan tuni duhu ya mamaye d'akin,yana kwanciya ta rungumeshi gam,shi kuwa ya lalubo bakinta ya fara kissing d'inta,duk abinda yake idonta a rufe yake gam,ko kwakwaran motsi bata yi,shi kadai yayi kidansa yayi rawansa,sai wajen k'arfe biyu ya k'yalleta aikuwa nan da nan barci yayi awon gaba da ita, wajen k'arfe hud'u ta juya da zumar ta gyara kwanciyarta,ji tayi hanunta ya sauk'a akan Abu kamar gashi,shafawa tayi dan ta gaskata gashin ne,ji tayi gashi ne mai tsayin gaske,bud'e idonta tayi a hankali tayi tozali da wanan matar a kwance a gefenta ta kura mata ido bakinta a bud'e jajjayen hakoranta kuwa awaje, wani mugun ihu ta saki ta rufe idonta gam.b
[9/22, 12:18] Sadnaf: 🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭





*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞






PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l



*TRUE LIFE STORY*


🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭





*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞






PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l



*TRUE LIFE STORY*







*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


PAGE 4



A firgice Abdulmajeed ya tashi yana sallati lalubota yayi ta rungumeshi gam jikinta na rawa sai cusa fuskarta take a k'irjinsa girgiza ta ya fara yi yana "Muhibba menene mai yake damunki" ahankali ta fara magana tana k'ara rungumeshi "ka kuna wutan d'akin matan nan tana gefena"tace cikin rawar murya,atare suka mik'e da ita dan kankameshi tayi sosai kamar zata koma jikinsa,kunna wutan d'akin yayi bai ga komai ba dafe kansa yayi yace " cikani ki duba kan gadon ba kowa,kankameshi ta k'ara yi tana cusa fuskarta a k'irjinsa " wlh a gefena ta kwanta tana kallona Abdul na shiga uku ka taimaka min matar nan tana Neman ta zautar dani" d'ago da fuskarta yayi ta rufe idonta sosai dan gani take idan ta bud'e idonta zata ganta,"Muhibba tsorata kawai kika yi babu kowa a d'akin nan,kina barci taya akayi kika ganta wlh tun jiya kin hanani sakat sai d'aga min Hankali kike, gashi wlh barci ne a idona dan Allah ki cikani muje mu kwanta" Abdulmajeed yace yana k'ok'arin raba jikinsa da nata,kankameshi ta k'ara yi sosai tace "Abdul ankusa Kiran sallah asuba dan Allah muje muyi wanka muzo muyi sallah,agogon bangon d'akin ya kalla yaga hud'u da minti goma,"yanzu k'arfe hud'u lokacin sallah bai yi ba,barci nakeji idan wankan kike so kiyi, jeki yi wankan ni sai na tashi zanyi,",Abdulmajeed yace yana nufar kan gadon,k'ok'arin magana take ya daka mata tsawa " dalla ki rabu dani kin dameni tun jiya in bazaki koma barcin ba ki koma d'akinki ki barni nayi barcina" yace yana kwanciya,da sauri ta hau kan gadon jikinta na rawa sai hawaye take,juya mata baya yayi,tayi sauri ta rungumeshi ta baya ta cusa fuskarta a bayanshi,Abdulmajeed barcinsa yake hankalinsa kwance,ita kuma idonta biyu in banda tsoro babu abinda take ji,tana jiyo kiraye kirayen Sallah amma babu dama ta tashi sabida tsoro,wajen Biyar da rabi tafara jin motsi a gefenta,kasan gadon ma motsi take jiyowa,k'ara kankame Abdulmajeed tayi cikin tsananin tsoro da firgita jikinta sabida tsabar rawa gadon ma har dan motsi yake,rufe idonta ta k'ara yi hawaye kuwa sai ambaliya yake a fuskarta,a zuciyarta kuwa duk addu'ar daya zo bakinta karanta wa take,acikin wanan yanayin take har k'arfe shiddan safe in taji motsi sai ta k'ara rungume Abdulmajeed, Tashin Abdulmajeed tafara yi tana bubuga bayansa dan taga gari yafara haske,zai je makaranta,motsawa yayi yana bud'e idonsa yaga haske ya d'an shigo d'akin,mik'ewa yayi da sauri itama ta mik'e,tabi bayansa,atare suka yi wankan tsarki ,suka yi alwala suka fito,shi ya jasu sallar asuba suna idarwa yace tayi sauri ta d'ora mishi breakfast kar yayi lati,mik'ewa tayi gabanta na fad'uwa dan gani take in taje Kitchen d'in ma zata iya ganinta,kwai kawai ta soya mishi sai ruwan tea da ta dafa dan ba zata iya soya dankali ba dan duk abinda take yi waige waige kawai take,k'arfe bakwai dai dai ya shiryaa zai tafi makaranta,Hawayene ya hau zubo mata dan gani take yana fita zata ga matar,Abdulmajeed kuwa ko kallonta bai yi ba yafara k'ok'arin fita da machine d'insa dan aganinsa abin nata har da iskanci,Muhibba d'aurewa tayi ta share hawayen fuskarta tace " Abdul ni kadai zaka bari a gidanan wlh tsoro nake ji,dan Allah kabani izini naje gida Idan ka dawo daga makaranta sai ka biya ka d'aukoni" d'agowa yayi yana kallonta,Sunkuyar da kanta tayi hawaye na k'ara zubo mata dan tasan ma'anar kallon da yake mata ,Abdulmajeed bai ce mata komai ba ya hau kan lifan d'inshi sai da ya tayar,yace "Muhibba bazan yi tolerating wanan iskancin da kika tsiromin dashi ba,babu ko mai a gidana ke kika sa tsoro aranki,kike Jin tsoron dan haka ban yarda ko nan da k'ofar gida ba ma ki leka," yana gama magana yaja lifan d'insa ya tafi,durk'ushewa tayi awajen ta fashe da kuka,tana " wayyo Allahna na shiga uku na lalace D🅰G🅰 T🅰IM🅰Ko na janyo wa kaina Baiwar Allah laifine dan na taimake ki mai yasa kike san cutar dani"?Muhibba sai da ta samu minti 30 a zaune tana surutu ita kadai,sai da ta gaji dan kanta ta mik'e ta Shiga ciki,d'akin Abdulmajeed ta shiga dan ta gyara dan ta sa aranta ko da taga matar bazata gudu ba,zata tsaya ta tambayeta akan mai yasa take San ta cuce ta alhalin ita Taimakonta tayi,

gyara d'akin ta fara yi amma duk a tsorace take,cikin ikon Allah ta gama gyara d'aki,hakan da ta gani ne yasa hankalinta ya d'an kwanta,Palo ta nufa ta gyara,ta gyara d'akinta,daga nan kitchen ta nufa tayi wanke wanke ta goge ko'ina,tsakar gidan ma wanke shi tayi tas ta moper,ganin babu ruwa a gidan ne yasa,tayi deciding ta ja ruwa a rijiya ta wanke band'aki,bud'e murfin rijiyar tayi ta zura gugan ta fara Jan ruwan,saura guga d'aya bokitin ya cika,tana jefa gugan dan ta debo ruwan,taji an rik'e gugan, gabanta ne ya yanke ya fad'i ta lek'a rijiyar,Fuskar Matan nan ta hango akwance a saman ruwan ta wangale baki jajjayen hak'oranta sun k'ara tsawo,ruwan rijiyar yana yowa sama, wani irin ihu tasa,ta saki igiyar ta nufi d'akinta
a guje ta rufe k'ofar ta fad'a kan gadonta ta ja bargo ta rufe kanta,adduoi ta ringa yi jinkinta na rawa,tsayawa tayi cak da addu'ar da take sakamakon jin da tayi an bud'e k'ofar d'akin,tsayar da numfashinta tayi ta yaye bargon daga fuskarta,babu abinda ta gani a bak'in k'ofar hakan ne yasa wani mugun tsoro ya rufeta dan ta ciki ta kulle d'akin waige waige ta fara yi ganin bata ga kowa ba yasa ta fashe da kuka tana " mai nayi miki kike San cutar dani? Laifine dan na taimaka miki, kiyi hak'uri dan Allah bansan ke ba mutum bace"ji tayi an dafata ta baya,fitsarin da ya matseta ta saki awando,ta juya ahankali,numfashinta ne ya d'auke na wucin gadi sakamakon tozali da tayi da matar a zaune a bayanta,ji tayi matar tace da muryar yara

" _ba cutar dake zanyi ba sanki nake_ "






wani irin hantsila wa
muhibba tayi daga kan gadon ta d'iba aguje,bata tsaya a ko ina ba sai gidan Surayya,Surayya da itama mijinta bai Dade da fita ba, fitowa ta yi dan tafara 'yan aikace aikacen ta Dan jiya kwana tayi tana mafarkin wanan matar,da tuni ta gama aikinta,ganin da tayi Muhibba ta shigo aguje ne yasa ta wurgar da tsintsiyar hanunta,ta shige d'akinta da gudu tana k'ok'arin rufe k'ofa.
[9/22, 12:18] Sadnaf: 🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭





*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞






PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l



*TRUE LIFE STORY*


🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭





*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞






PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l



*TRUE LIFE STORY*





*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


PAGE 5

Wuf Muhibba ta shige itama,Surayya kuwa ta kulle k'ofar sabida tsananin tsorata da tayi wardrobe d'inta ta nufa da gudu ta bud'e tana k'ok'arin shigewa dan ta d'auka Aljanar ce ta biyo muhibba,,Mubibba da a gigice take,binta tayi itama a gujen ta rik'eta tana "bani Hijabi gidanmu zan tafi bazan iya ba"Surayya zare ido kawai take tana kallonta tace" Aljanar ce ta biyoki?" "Nidai kawai ki bani Hijabi inkina da d'ari biyar ki bani aro in yi kud'in mota" Muhibba tace tana share hawayen da suka zubo mata,Surayya dafata tayi tace "haba Muhibba ki fad'a min abinda ya faru mana kike so ki tafi gida" muhibba kuka ta fashe dashi tana "Surayya gida zan tafi tun jiya banida kwanciyar hankali matan nan dana taimakawa in banda tsorata ni babu abinda take yi,jiya ban runtsa ba,nayi wa Abdul bayani bai yarda dani ba,dan haka gidanmu zan tafi bazan iya zama a gidanan ba" tunda Muhibba ta fara magana jikin Surayya ya hau rawa,cikin tsanin tsoro tace " yanzu Muhibba idan kika tafi ta shigo min fa,dan Allah karki tafi ko ina ki zauna anan inya so idan Ayuba ya dawo zan sa ya kira Abdulmajeed ya mishi bayani in bai yarda. ba ma da kaina zan mishi bayani kinga bai kamata ace kin tafi gidanku ba da izininsa ba kin kuma San halin mijinki" Muhibba kallonta tayi tana girgiza kai tace " Surayya bazan iya ba ni nasan mai nake gani D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO na janyo wa kaina masifa,gidanmu zan tafi,idan Abdulmajeed ya dawo ki fad'a masa na tafi gidanmu,Surayya babu yanda bata yi ba akan Muhibba ta zauna a gidanta kar ta tafi,amma Muhibba tak'i Hijabi ta bata,ta d'auko dubu d'aya ta bata da sauri Muhibba ta saka hijabin dan burinta kawai ta ganta a gida padlock ta k'arba awajen Surayya ta kulle gidan,Surayya ma kulle gidanta tayi dan cewa tayi bazata iya zama ba ita ma gidan d'aya makociyar ta su ta tafi,Muhibba kuwa ta dau hanyar bak'in titi,dan gidan nasu a dan lungu ya ke,tana isa bakin titi ta tari adaidaita sahu ta hau,tafiyar minti 20 ne ya kai ta karkasara,tana sauka ta shige gidansu dan gidansu a bakin titi yake, atsakar gida ta tarar da Nafeesa kanwata dake binta tana wanki,da alama uniform d'in islamiyya take wanke wa,Sallamar da tayi Nafeesa ta amsa cikin murna ta tafi ta rungumeta tana "oyoyo" murmushi Muhibba ta yi tana kallo k'ofar palonsu tana "ina Umma"?

"Tana d'akinta" Nafeesa tace a dai dai lokacin da ta cika Muhibba ta na kallonta dan taga Muhibban a firgice ba kamar yanda ta saba ganinta ba.





ita kuwa Muhibba d'akin Maryam mahaifiyarta tayi da saurinta,da sallamarta ta shiga d'akin Maryam dake linke kayanta ta juyo da sauri tana amsawa,Muhibba dan dukawa tayi tana gaisheta,Maryam ta amsa tana leka fuskar Muhibba," Muhibba lafiya dai na ganki awani firgice" Maryam tace a lokacin da take ajiye kayan hanunta,shiru Muhibba tayi nan da nan hawaye ya hau zubo mata," Subhanallahi Muhibba mai ya faru? ina Abdul d'in?
Fad'a kuka yi?" Duk ajere Mahaifiyarta tayi mata tambayar,shiru muhibba tayi bata yi magana ba,"ina tambayarki kin min shiru mai ya faru" muhibba d'agowa tayi ta fara magana cikin sheshek'ar kuka "Umma Aljana ce take bibiyata D🅰 G🅰 T🅰IM🅰KA mata wlh na d'auka mutum ce bansan aljana bace"

Ware ido Maryam tayi tana "bangane mai kike nufi ba,taya ya kika taimakawa Aljana"? Muhibba share hawayen fuskarta tayi tafara bata labarin abinda ya faru,sallati maryam ta ringayi bayan ta gama jin labarin abinda ya faru,"muhibba mai ya kai ki bud'ewa aljana k'ofa har ta Shiga band'akinki? Mai yasa kika b'oyewa mijinki gaskiyar abinda ya faru ai dole yak'i yarda dake ya d'auka karya kike" oooo ni maryam daga taimako kin janyo wa kanki,Allah ya kareki daga sharrinta,bari babanku ya dawo ya kira mijin naki awaya ya fad'a masa abinda ya faru Idan addua za adage da yi kafin ki koma gidan dan hatsarine komawarki gidan yanzu, wuce kije d'akinku ki kwanta tunda kince jiya bakiyi barci ba" mik'ewa Muhibba tayi ta nufi d'akinsu dan barcine a idonta sosai,tana kwanciya barci yayi awon gaba da ita.








K'arfe biyar da rabi Abdulmajeed ya dawo gida,mamaki ne ya rufeshi daya ga k'ofar gidansa a kulle,parking d'in lifan d'insa yayi ya nufi k'ofar gidan Surayya dan yana kyautata zaton Muhibba a gidan take,aransa kuma yana ayyana irin rashin da zai yiwa Muhibba wato shi zai ce ko k'ofar gida kar ta fita,amma sabida bata jin magana shine zata tafi gidan makota har da kulle gida,buga

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login