Showing 18001 words to 21000 words out of 29121 words

Chapter 7 - FITAR TSIRO

22 Oct 2024

6540

rayuwarta cikin gidan, a makaranta kuwa sun zana jarrabawar qualify har kuma cikin ikon Allah tana cikin waɗanda suka yi nasara gwamnati za ta biyamusu kudin NECO.

Gaba daya rayuwar gidan ba dadi ta ke yi mata ba kuma ba dalilin kowa ba sai mijin Umman da ya zame mata tamkar ƙadangaren bakin tulu. Duk iyakar kokarin da ta ga yana yi a gidan don nuni da lallai ya shiga taitayinsa ya nutsu hakan ba burgeta ya ke ba, tana kuma ƙara ji a jikinta cewar duk wannan abu da yake yi na banza ne kuma akwai lauje cikin naɗi. Sosai take son samarwa Umma hujjar da yasa take kokwanto amma ya toshe dukkan wata ƙofa. Don ta jarraba shi har cewa Umma ta yi, ta nunamasa ba ta son zaman majalisar su Maada a ƙofar gidan. Ta sha mamaki da ya amsa da cewar daga lokacin zamansu ya zo ƙarshe, kuma abin mamaki hakan ce ta tabbata. Har shigowa suka yi gidan suka yi sallama da Umman wani salon bariki da Haulatu ta yiwa abin kallo har da neman gafara.
    "Madadin ki tsaya ƙoƙarin binciko laifukansa, kamata ya yi ki ƙara godiya ga Allah da ya karɓi addu'armu ya shirya bawansa."

Haka Umman ta taɓa ce mata, a take kuwa ta zabura.

"Wallahi ba dai addu'ata ba. Ni ban taɓa saka mijinki cikin addu'o'ina ba. Toh na tsaya ma na maida hankali ga yiwa kaina addu'ar mana. Hum um!"

Daga haka ta tashi a lokacin don ba ta kaunar a ja magana. Tun sadda kacokam ragamar abincin gidan ya koma hannun Ɗanmutuwa, daga lokacin Haulatu ta bar cin komai da Umman za ta girka. Ta gwammace shiga gidan su Bahijja ta ci ta yi nak, ko kuma ta ci sauran abincin siyarwar Umman. Yanzu sosai suke zumunci da su Bahijja, tare da su take zuwa islamiyya, a dole ma ta ke zuwa don babu yanda za ta yi ta zauna a gidan baƙin cikin mijin Umma ya kashe ta.

Cikin wannan lokacin ne aka sanya ranar auren Hindatu da ya kama watanni biyar bayan kammala sakandire ɗinsu. Ta shirya daga ita har Umma don zuwa yi musu fatan alheri. Suna tafe su na hira gwanin sha'awa, Umma har ta ɗan murmure kaɗan saboda kwanciyar hankali da nutsuwar da ta samu. Babu abin da ya kai damuwa jefa zuƙata cikin damuwa da takura. Idan ka gan su sai ka rantse Yaya ce da ƙanwarta, sam ba za ka kawo a rai wai Uwa ce da ɗiya ba domin Allah ya halicci Umma da kyawun jiki. Suna tafe su na hira abinsu, Haulatu cikin nishaɗi ta ke jinta da walwala sakamakon albishir da Umma ta yi mata cewa zuwa litinin, tunda yau su na Asabar, za ta ba ta kuɗin WAEC ta je ta biya. Sosai take murna, don dama Hindatu duka biyun za ta zana. Ba ta ci Qualify ba ita, amma Mominta ta biyamata duka jarrabawar guda biyu, daga Waec har Neco din.

  "Amma dai Umma kin tabbata kuɗin daga hannunki za su fito ko?"

Umman ta ɗan yi shiru sai kuma ta haɗe fuska.

"Kina tunanin zan aikata abin da nasan ba kya muradi? To shikenan, bari a hakura da biyan sai ki zana..."

Da sauri ta katse Umman ta hanyar ruƙunƙumeta tana dariya ita ta mance ma a hanya suke. Har sai da Umman ta tsawatar kafin ta sake ta.

"Na tuba Uwata ƴar aljanna. Kiyi hakuri don Allah."

Umma ta yi murmushi kawai ba tare da ta ce komai ba. Can ƙasan zuciyarta ta ji wani iri, tabbas kudin daga aljihun Ɗanmutuwa zasu fito, shi da kansa ya cewa Umman zai biyawa Haulatun kuɗin WAEC sadda ya ji tana maganar za ta haɗa ƴan kuɗaɗen ta biyamata, shi ne ya soma kwaɓarta akan kada ta sanar da ita don ya sani ko za'a yi me, kafiyar Haulatu ba zai sa ta amince ba. Ko an biya daga baya ta ji labari, to fa ƙarshenta a yi asarar kuɗi.

Har suka shiga abin hawa Haulatu hira kawai take jan Umman tana ba ta labarin saurayin Hindatun da irin kudin da yake shirin kashemata a bikin.

Sun iske mutanen gidan duk suna nan ba su fita ba, Amarya da kuma Baraka. Kamar kullum wannan karon ma buga ƙyauren gidan ta yi da ƙarfi wanda har sai da Umma ta ɗan razana.

  "Ya Salam, kina da hankali kuwa? Dama ashe har yanzu ba ki bar yi musu wannan sakarcin ba?"

"Ina fa za ta bari, ai mun riga mun saba da wannan idan dai Haulatu ce." Faɗin Baraka dake aikin tankaɗe garin tuwo. Ita kuwa Amarya dake zaune ƙofar ɗakinta tana gyaran salad ta yi dariya kawai. Suka gaida Umma, ta amsa fuska a sake. Itama Haulatun sai sannan ta gaida su.

"Wai ni ya naji shiru ne? Ko waccan yar duniyar ba ta nan? Bayan na fadamata zamu shigo."

"Hindatun ce ƴar duniya?" Fadin Umma.

"Lah, ai Umma idan dai su biyun nan ne kya ji abin da yafi haka ma."

Umma ta girgiza kai kawai tana murmushi.

"Ba sa nan ne?" Ta tambaya.

"Suna ciki. Hajiyar ce ba ta jima da shigowa gidan ba, suna ƙule a ɗaki."

Fadin Amarya cikin tsegumi. Haulatu dai dariya ta yi ta yi gaba Umma na biye da ita. Sallamar Haulatu da shigarta ɗakin duka lokaci guda ne, nan da nan ta ga Momin na tura wata leda ƙasan gado, ta kai idanunta ga layar da ta fito a ƙoƙarinta na tura ledar, tana gani ta wayance ta tura shi gami da hawa faɗan borin kunya.

"Ke dai an yi marar hankali. Yanzu ana girma ana cin ƙasa daga sallama kawai kik banko labulen ɗaki, ai sai ki jira a amsa maki ko?"

Ita kuwa Hindatu dake zaune gefe duk ta sha jinin jikinta, ta ɗan washe baki ganin har da Umma.

"Wa'alaikumussalam, lah Umma sannu da zuwa."

Momi ta ɗan saki fuska suna gaisawa da Umma, ita kuwa Haulatu zama ta yi gwuiwa a sake, wai ita Momi mene matsalarta da ita?

Nan suka yi musu fatan alheri, har dai aka gama zaman babu alamar za'a nuna musu kayan sanya rana. Haulatu da ba ta shiru tuni ta mance da wancan ɓacin ran ta dubi ƙawarta.

"Wai ke ba za ki nunamin leshin d kika ce ɗan dubu tamanin ɗin ba?"

Umma ta watsamata harara amma ko a kwalarta, Momi nan da nan ta daure fuska.

"Kayan ai an kai su ajiya, ba zan bar su anan ba kaya masu tsada a biyo dare a yi mana ɗan hali. Kinsan ban yarda da ɓerayen da muke zaune da su ba a gidannan."

Ita kuwa Hindatu ta rasa dalilin Momi na ƙin nunamusu kaya, a iyaka zatonta wannan na daga burin Momi, kowa ya zo ya ga kayan bajintar da aka kawowa ɗiyarta.

"Allah ya kyauta toh." Faɗin Umma sannan ta miƙe.

"Bari mu koma. Allah ya sanya alheri Hindatu. Ya nunamana lokacin."

"Ameen Umma nagode." Umma dai ta ɗan cika da mamaki, toh kenan su ma dai yaran yanzun ba kunya ne da su ba, irin amsawar da yarinyar ke yi ita kunya ma ta ji, tabbas dole ta yi addu'ar Allah ya fitowa da Haulatu miji itama ta yi aure duk da ta san yanda Haulatun ke fatattakar duk wanda ya zo da sunan soyayya wajenta.

Haulatu dai ta tsaya tana kalle-kalle har idanunta ya kai ga wata babbar akwati sabo fil, kamar ta yi magana sai dai ta fasa ta miƙe.

"To Amarsu, sai mun haɗu a makaranta. Allah ya sanya alheri Momi."

Momi ta harare ta bayan ta juya baya. A fili kuwa ta amsa cike da gadara.

"Ameen."

Hindatu ta miƙe da zummar yi musu rakiya, ta gefen idanu Umma ta ga sadda Momin ta danne mata hannu wanda dole ta sanya ta komawa ta zauna. 

Sai da suka fice ne Momi ta dube ta tana harara.

"Kina saka ran zan yi sake ne su ga kayan bayan kina sane da cewa duk duniya idan akwai waɗanda na tsani na buɗi idanu na gan ta tare da ke bai wuce wannan shegiyar yarinyar ba mai idanu kamar mujiya? Ke ki sani, muddin kika yi aure toh ƙawancenku ya zo ƙarshe. Ba zai yiwu ina can ina tufka ba kina gefe kina min warwara. Wannan da kike gani baƙar inuwa ce ita, gwamma rana da ita. Amma ya rage naki, idan kin ga dama ki sakarmata fuskar da za ta yi maki illah a rayuwa. Mutum da gishirinsa, in ya ga dama ya dafa ƙaho."

Hindatu shiru kawai ta yi, koyaushe idan Momi tana nusar da ita akan raba hanya da aminiyarta. Ita a iyaka tunaninta ai abokin cin mushe ba a ba a ɓoye masa wuƙa. A yau dai sam ba ta goyon bayan Mominta hakan yasa koda Momin ta fita ta dawo ta jawo ledar rubutuka da layun da ta karɓo wurin bokanta ba ta mayar da hankali wurin sauraronta ba. Ƙarshe ma miƙewa ta yi ta fice daga ɗakin uwar na kwalamata kira amma ta yi burus.

***
A hanya Umma ba ta ce uffan ba sai sauraron Haulatu take wacce ke faman mitar wulakancin da Hindatu ta yi mata ita da Babarta. Ta yi ƙwafa.

"Wallahi Umma na ga akwatin, kuma na tabbatar shi ne na sanya rana saboda shi Hindatu ta nunamin an haɗa bidiyo da hotonta har da su buhun shinkafa da su tabarma. Amma dai Momi ta rainamana hankali wallahi, toh kenan su Baraka ne ɓarayin ko kuma mu da muka shiga gidan? Kut! Ai..."

"Kin ishe ni haka, za ki kama bakinki kimin shiru ko sai mun raba hanya da ke yanzu? Ban da shashanci muna tafe kina ɗaga murya kina hayagaga kina jazamana kallo?"

Umma ta katse ta a zafafe, sai lokacin ta ɗan waiga ta ga wasu yara gefe suna ta kallonta can gefe kuma wasu samari ne su ma masu zaman majalisa sai ko na tafe da ke waiwaye. Turo baki ta yi ba ta ƙara magana ba. A ranta sai ayyana kalar rashin mutuncin da za ta yiwa Hindatun take yi, ta kuma ci alwashin ba za ta yi ankon bikinta ba.

Koda suka je gida Umma ba ta ce mata uffan ba.
Sai ranar litinin ne ma bayan ta ba ta kudin WAEC da kuma na karamin hoton passport sannan ta gargaɗeta akan nunawa Hindatu wani abu koda kuwa a fuska ne.

"Muddin kika yi magana za ki tabbatar da zargin Uwar na cewa kina hassada ga ƴarta ne. Ki nuna hakan da aka yi kamar bai dameki ba. Bana son kananan magana, kema dai Allah ya nunamin naki mijin na aurar da ke."

Dariya maganar Umma na ƙarshe ya sanya ta.

"Umma kenan." Iyaka abin da ta ce kenan kafin ta fice.

***
Kwanci tashi ba wuya a wurin Allahu, har lokacin jarrabawar su Haulatu ya yi. Hakanan suke zuwa, ba ta ko damu da karatu yanda ya kamata ba tunda a ɓagas ake rubuce musu komai a allo su rubuce. Wannan tsarin na jarrabawar sam bai yiwa Umma ba.

"To Umma ai komai yanzu sai da taimako. Ai iyaka nan ne, gaba ba zamu yi haka ba."

"Um um Haulatu, juma'ar da za ta yi kyau tun daga laraba ake gane ta."

Wannan amsar ta samu daga Umma. Ko a jikinta, ita dai ta san idan an yi abu a aji tana fahinta, matsalar bai wuce rashin Malaman kirki da ba su da shi ba a makaranta don akwai darussa kusan hudu da zasu yi jarrabawa a kansu, ba a taɓa koyamusu ba a makaranta. Sai a wurin Bahijja ne ta ɗan koyi wani abun a ciki. Ita sosai makarantar kudin da yaran gidan su Bahijjar suke zuwa ke burgeta. Sosai Bahijja ta iya turanci, aikuwa tun lokacin Haulatu ta ƙwallafa ran sai ta koyamata. Wannan yana daga abinda ya dauke mata hankali da wuni tare da Umma a gida tana shan takaicin yanda Umman ke rawar jikin yiwa Ɗanmutuwa girki da gyaran ɗaki.

***
Dariya suka kwashe da shi a lokaci guda. Hajiya Adama ta nuna Ɗanmutuwa ya yatsa.

"Kai, kai, wallahi kai kam ba ƙaramin ɗan bariki ba ne. Kuma gashinan har wani kyallin angonci ka ke yi."

Ya yi dariyar mugunta.

"Ai sai kin ga yanda Na'imatu ke faman rawar ƙafa a kaina. Komai take yi don ta burge ni ne."

"Lallai kam, kai dai shegen kanka ne. Yanzu dai wace mafita ka samo? Lokaci ya ja, ya ci ace yanzu mun san matakin ɗauka. Lokaci ya zo da za ka kawo su gidan nan, na ga Haulatu da idanuna."

Ya jinjina kai gami da sauke ajiyar zuciya.

"Hakane, kar ki samu damuwa, na gama yanke duk abin da ya kamata nayi ba tare da an zarge ni ba. Za su zo koda sau daya ne, amma ba yana nufin a lokacin ne zan bar maki Haulatu ba tunda dai ciniki bai faɗa ba, har yanzu da saura. Na fi kaunar ya kasance koda za ki ɗauke ta, ya zamana ko daga makaranta ko wani abin na daban. Kinga zai fi toshe dukkan wata kafa da za'a zarge ni. Af, ai na tuna, kwanaki Na'ima na cemin za'a yi bikin wata ƴar makarantarsu. Me zai hana a lokacin bikin ki sa yaranki su ɗauko maki ita?"

Ta yi shiru can ta ce.

"Idan kuwa hakane, babu amfanin zuwansu gidana, hakan kamar ƙofa ce wanda zai jawo zargi idan bincike ya tashi."

Ɗanmutuwa ya jinjina kai. Haka suka yi ta ƙulle-ƙullensu, yana ƙara koɗawa Hajiya Adama ɗiyartasa, yana mata rantsuwar sai ta ture fadar dukkan ƴan gaban goshinta saboda za ta kawomata ribar da wasu ba su taɓa kawo mata ba daga wurin Alhazawa. (Wa'iyazubillah).
Fitar tsiro
Page 10
Tafiya ta yi tafiya, har a yau aka wayi gari su Haulatu suna bikin kammala sakandire. Sabbin uniform din da ta sanya gaba ɗaya an mata kaca-kaca da shi da biro. Duk zare idanu irin nasu ita da Big Mama Hindatu, hakan bai yi tasiri ba a ranar. Su kansu ba su jin manyantan a wannan rana, sauran ɓurɓushi na fushi da Haulatu ta ɗauki lokaci tana yi duk a wannan ranar ta ji ya kau. Suka ɗinke tamkar ba su ba. Haka aka rabu cike da walwala da kuma jin kewa. Wasu har da hawayensu.

***
Zumuncin da ya ƙullu tsakanin Haulatu da Bahijja shi ne babban abin da ya fi faranta ran Umma. Shigowar Bahijja rayuwar Haulatu ya sanya ta a dole take mayar fa hankali wajen zuwa Islamiyya duk da kasancewar a sannan Bahijja ta yiwa Haulatun zarra a karatu. Ita tana cikin masu hafizan da ake saka ran makarantar za ta yaye, yayinda Haulatu ta koma ajin baya. Zuwa lokacin Malaman ba su yunƙurin dukanta idan ta gwaɓa musu zance sai dai ko hukuncin shara ko wankin banɗakin makaranta. A hankali kuma suka ƙara fahimtar cewa hakanan ta ke sai dai ko yau da gobe idan a na nusar da ita ta hanyar yi mata gyaran kalami zai taimaka ƙwarai wurin shiryuwarta.
Albarkacin zuwa makarantar da take ne ya jawo Ɗanmutuwa ke samun arziƙin gaisuwa, hakan ma a daƙile ta ke yi don har wani ɗaci take ji a maƙoshinta. Wannan albarkacin kaɗai ya soma ci a kwanakin, shi ɗin ma darajar Umma ya ci ganin sosai Umman na damuwa da yadda take nuna halin ko'in kula da duk wata kyautatawa da Uban ke yi mata. Har gobe dai ba ta taɓa yarda ta ci abin da ya fito daga hannunsa, wani tsire da kaza da yake kawowa Umma duka ba burge ta suke yi ba. Umma itama tun lokacin da ta gwada sau ɗaya ba ta ƙara ba don a gaban Ɗanmutuwa Haulatun ta rantse ba za ta ci kayan haram ba. Har a lokacin Umma ta so kai mata bugu sai dai Ɗanmutuwa ya tare. Wannan rana kusan kwana Haulatu ta yi tana kuka, wai yau ita Mahaifiyar za ta kai wa duka akan wanda bai taɓa daraja a idanunta ba. Washegari kuwa ta tashi da ciwon kai mai zafi, wannan ya tashi hankalin Umma, tsoronta kada ta jefa ta a ciwo irin na can baya. Ita kanta sai daga baya ta fahimci mugun kuskuren da ta yi na ɗaga hannu da zummar dukan ɗiyarta.

Tun ana sauran sati uku a fara bikin Hindatu, aka kawo lefe. Wannan karon Haulatu ko leƙe don ta rantse ba za ta ƙara zuwa Momi ta wulaƙanta ta ba. A lokacin Haulatu ta mallaki wayarta ƙarama wacce Umma ta yi mata kyautarta na taya murnar kammala sakandire. Ba ta ji mamakin komai ba kawai ta saka a ranta kuɗaɗen da Umma ke adashi ne ta karɓa. A sannan wani abu wai Chatting bai ko damu Haulatu ba, ba ta taɓa ma kallonsa da sha'awa ba. Iyaka saninta ba ta da wani ko wata da za su yi hira da shi. Ta gwammace duk sadda za ta yi waya da Aminiyarta ko Bahijja idan ba su haɗu ba, ta kira su ta waya, idan kuwa babu kudi ta yi ta dokamusu beep call har sai sun gaji sun kira don ji me ta ke so.

Ko kusa ba ta yi karambanin cusa kai a sha'anin bikin Hindatu ba gudun jin baƙar magana daga bakin Momi. Hindatu har abin ya ba ta haushi don sai da ta tako har gida ta kawo ƙararta wajen Umma akan ta ƙi yi mata rakiya gurin gyaran jiki da na gashi kafin ta amince su je.

Ranar da aka fara gyaran jikin, ta sha mamakin irin haɗuwar wajen, koda dai unguwar ma kanta ta manya ce, can wuraren Lamiɗo Crescent ne. Wurin na wata Basudaniyar mata ce ana ce mata Ayyush. Haka Haulatu ta yi zaune tana kallon ikon Allah yanda ake ta mulkewa ƙawarta jiki. Zuwansu na farko amma sai ta ga har ta sauya. Matar ta dube ta.

"Kema dai ya kamata a yi maki, za ki yi kyau sosai tunda na ganki ba baya ba Masha Allah."

Ɗan murmushi kawai ta yi, ita kuwa wace hidimar ce za ta tasar mata ta yi gyara irin haka? Ita da babu ma aure a ƙoƙon ranta, mene haɗin biri da gada?

"Ai wannan da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login