Showing 15001 words to 18000 words out of 29121 words

Chapter 6 - FITAR TSIRO

22 Oct 2024

6539

girma, tsayawa ta yi tana bin tsakar gidan da kallo. Ba wani babba ba ne, ɗakuna biyu ne sai kuwa wani gefe da ta ke zaton nan ne kicin sai ƙofar banɗaki daga ɗan lungu. Haka ta yi ta nazarinta har Haulatu ta shimfiɗa musu tabarma.

"Wai dama tabarma ki ka shiga ɗaukowa? Wallahi sauri ma muke zamu je islamiyya ne, dama Mama ce ta aiko mu, tana maki sannu. Ga wannan kuma ta ce a kawo."

"Lallai, wato kin fi ƙarfin ki zauna a tabarmar gidanmu ko? Ai shikenan. Ki ce mata da sauki, an gode."

Riƙe baki Bahijja ta yi.

"Kai Haulatu, ni ba haka nake nufi ba don Allah kar ki fassara ni. Ai ke kin sani na shiga ajin ƴan hadda. Kiyi hakuri, ai yanzu muka soma aminci, na tabbata sai kin gaji da gani na a gidanku."

Haulatu ta ɗan taɓe baki.

"Ni dai mai ƙwacen samari?"

Maganar ba ta yiwa Bahijja dadi ba, cikin sanyi ta amsa.

"Kiyi hakuri, ki yafe min duk abin da na furta mai muni gareki a baya. Rashin sani ne da kuma jita-jitar mutane. Amma ina tabbatar maki yanzu na fahimceki."

Murmushi kawai Haulatun ta yi, ai ita ta sani babu wani mai fahimtar ta bayan uwar da ta haife ta. Kawai dai ta bi ta da to, haka suka rabu ta taka musu har bakin ƙofa tana ƙara jaddada saƙon godiya ga Mamarsu.

Abinci ne lafiyayye, shinkafa dafaduka a wata cooler ɗin kuwa farfesun kaza ne. Sai leda mai ɗauke da sabulai na wanka da kuma wanki sai kuwa omo. Kai har da auduga na mata leda biyar da mayuka har kala biyu na shafawa. Shiru ta yi tana kallon kayan, karon farko da irin wannan abin arziƙin ya haɗa su da makwaftansu. Haka ta mayar da komai cikin ledar, ta ajiye su a gefe. Ba ta tare da yunwa don haka  ko sha'awar abincin ba ta yi ba. Ta gaji da zaman tunani ta ja guntun tsaki ta miƙe, gaba ɗaya zaman gidan ba dadi yake yi mata ba ta ji inama ta bi Umma zuwa kasuwa, ƙarshe kawai sai ta ƙara zura hijabin da ta cire ta fito ƙofar gidan ta ɗan tsaya. Yana ɗaya daga cikin abin da Umman ba ta sonta da shi sai dai tana ji hakan kaɗai ta fi buƙata a yanayin da zuciyarta ke ciki. Hankalinta ya kai ga su Maada waɗanda suka ɗan kalli inda take. Ta kauda kai gami da ƙara tamke fuska. Ta rantse wataran sai ta sa ƴan sanda sun kawomusu cafka muddin ba za su daina zama a ƙofar gidansu ba. Ta tsinkayi muryar wani cikinsu mai suna Kwarkwar ya buga wani ihu na ƙwararrun ƴan daba kafin ya ce.

"Kai! Ni fa barewar can tana kashe ni billahillazi! Oga Maada! Ya kamata idan Ciyaman ba zai iya farautarta ba mu, ya bari mu shiga da ƙwarinmu."

Maada ya ja tsaki yana fesar da hayaƙin sigarin da ya zuƙa.

"Kai don tsohuwarka ina tambayarka inda Ɗan Aljan ya shiga kana yimin maganar banza da wofi. Ai inda amana ruwa ba zai dafa kifi ba, duk runtsi kar wanda ya ƙara kai idanunsa ga irin gidan Boss."

Kwarkwar da sauran mutane ukun da ke zaune tare da shi, suka harɗe hannuwansu suna kirarin kowa ya bi. Can kuma Kwarkwar ya ce.

"Nifa Oga ban dan inda Ɗan Aljan ya yi ba, na fi tunanin ya haɗu da Kashi (ƴan sanda) sun sa mishi lalle (sun kama shi).  Kasan fa shi Boss ya aika gidan Cuna ya kai tayoyi! To ka san halinsa, ya fiye Nakura (tsoro), ƙila ya yi saranda." Ya ƙarashe yana mai ƙamewa kamar wanda ke gaban soja.

"Aikuwa da matsala. Amma ina zuwa bari na sallami waccan ƙaguwar." Faɗin Maada, Haulatu ta saci kallonsa ta gefen idanu, can kuma ta kai duba ga inda ya nufa, wata budurwa ta gani daga can kan kwana ta rufe fuskarta da niƙab. Waige-waige ya yi kafin ta ga ya sa hannu cikin aljihu ya fiddo wani abu da ba ta iya tantance ko mene ne ba, ita kuwa ta karɓa da sauri ta cusa a jaka ta fiddo kudi ta miƙamasa daga haka ta bar layin da sauri. Shi kuwa ya dawo ya zauna suka bi shi da sowa. Iya Haulatu mamaki ma abin ya ba ta, ba su ko tsoron ta tona asirinsu?
 
  'Tsoron me za su ji tunda dai halinsu guda da mijin Ummanki?' Wani sashi na zuciyarta ya ba ta amsa.
  Hirarsu ta ƙara ɗaukar hankalinta, magana suke yi akan budurwar. Maada ke labartamusu cewa ai yau taro ne da su na birthday hakan ya sa zasu gwangwaje.

Ganin tun tana fahimtar kan hirar har ta bari ga wani jiri da ta ke ji sakamakon jimawar da ta yi a tsaye yasa dole ta juya ta shige gida gami da zura sakata.

Yinin ranar sam bai yiwa Haulatu dadi ba, har Umma ta dawo ba ta da wani walwala. Sosai Umma ta yaba da karamcin Maman Bahijja. Sai da aka yi Magriba suka ci suka ƙoshi, tana da lura da Haulatun. Anan take sanar da ita kiran da Hindatu ta dinga yi a wayar Umman tana nemanta. Yamutsa fuska kawai Haulatu ta yi, ita fa mamakin Hindatu take har lokacin, ta kuma ci alwashin sai ta nunamata rashin jin dadinta a fili.

Umma na so ta tambayi ɗiyar ko Mahaifinta ya shigo gidan, sai dai ba ta kaunar ta tayarmata da abin da ya wuce. Yau kwana biyu da faruwar al'amarin kuma tun sannan ba su ƙara ganinsa ba a gidan. Ga diyar, hakan ya fi nono fari har addu'a ta ke yi a ranta akan Allah ya sa mota ce ta kaɗa shi ya mutu. Ga Uwar kuwa, duk ta damu. Zuciyarta na mata ba dadi, ko ba komai uban ƴarta ne.
  A ranar ma har suka kwanta bacci babu labarinsa, tun Haulatu na jin Umma na juyi da sintirin fita tsakar gida, har dai bacci ya yi awon gaba da ita.

***
  Hajiya Adama, mace ce mai jiki sosai, tana zaune a ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun falonta. Ta ci ado har ta gaji kamar koyaushe don tana saka ran tarbar manyan Alhazai da za su zo zaɓar iri daga cikin sabbin ƴanmatan da ta tanada musamman domin su. Daga ita sai Danmutuwa a falon. Shi ne abokin mutuwarta kamar yanda ta ke faɗi "Ɗanmutuwa abokin mutuwata." Haka kirarinsa yake a wurinta. Duk wani sirri nata ya sani kamar yanda ta yi mishi farin sani. Ya labartamata duk abin da ya faru tsakaninsa da Haulatu da Na'ima.
  Ta yi murmushi yayinda take cigaba da taunar inibin da aka sanyamata cikin wani ɗan bowl na tangaran. Dama ta lura tun zuwansa daga yanda yake ta faman yiwa kansa mankas wata damuwar ce sai dai ba ta ɗauke ta mitsitsiya hakanan ba.
 
  "Ita Haulatun ba za ka iya kawomin ita mu gaisa ba?"

Shi ne tambayar da ta jefamasa ba tare da nuna wata damuwa akan cin kashin da yarinyar ta masa ba a nasa tunanin.

Ya yi shiru, sai lokacin ta dube shi dakyau har sannan murmushin bai bar saman fuskarta ba.
 
  "Ina fatan ka gane inda na dosa?"
Ɗanmutuwa ya gyara zama bayan kora ruwan lemun da ke ajiye saman tebur a cikinsa. Ya dubi Hajiya Adama.

"Wannan tunanin shi ya yi silar da ki ka ga na zo gareki da zancen. Ai nikam idan har kwalliya ta biya kudin sabulu to ba ni da wata matsala face na cigaba da sheƙa ayata son rai. Sai dai kuma ba nan gizo ke saƙar ba."

"Ban fahimceka ba."

Ya ɗan dakatar da ita da hannu.

"Yanzu zan fahimtar da ke. Na'ima mace ce mai haƙuri na sani koda dai haƙurin na dole ne don duk faɗin ƙasarnan ba ta da gatan da ya wuce ni Ɗanmutuwa. Duk ranar da na yi watsi da ita, ina mai tabbatar maki sai kare ya fi ta gata."

Hajiya Adama ta ɗan yamutsa fuska.

"Ni fa daɗina da kai kenan, inda aka dosa daban, inda ka ke nufa daban. Mene ne haɗin abin da na nema da wannan soki-burutsun?"

Ya yi ɗan murmushi.

"Ai da ba ki katse ni ba, kin fiye ƙawa zuci, dalilin yin maganar Na'ima don na nunamaki ƙarfin ikon da nake da shi a gidana. Duk taurin kai irin na wannan yarinyar ba za ta gagare mu juyawa ba. A shirye nake na kawo maki ita ko ta ƙarfi da yaji ne. Ya rage naki ki san dabarun da za ki yi ta bada kai bori ya hau. Kinga gaba ta kai mu gobarar titi."

Suka yi dariya.

"Ko kai fa, yanzu ka yi magana mai kyau. Sai dai fanakwai sauran rina a kaba, kana da tabbacin ta cika duk sharuɗɗan da nake nema a wurin ƴan shila kafin ɗora ta kan network?"

Bai ji ko ɗar dangane da tambayar ba sai ma dariya da ya yi karo na biyu.

"Kin manta wace ce uwarta Na'ima ne? Ɗawisu muke kiranta fa. To ai ko ni ba don na ga jiya da yau ba, ba za ki jera ni sahun..."

"To sarkin yabon kai, kar ka sauka daga kan layin da muke kai. Ka kawo min yarinyar kawai."

"An gama Hajjaju."

Da wannan suka ajiye zancen inda suka shiga tattaunawa dangane da abinda ya shafi kasuwancinsu.

"An sanar da ni an kama yarona ɗaya, Ɗan Aljan, ya kamata a san abin yi kafin lokaci ya ƙure." Faɗin Ɗanmutuwa kenan. Ta duba lokaci a wayarta sannan ta ja guntun tsaki. Sai da ta fara watsi da maganarsa ksfin daga bisani ta dawo kan turba.

"Nifa mutanen nan ba su san bana son saɓa alƙawari ba, mun yi da su ƙarfe uku amma ka ga har huɗu ta gota. Batun Ɗan Aljan ai ba matsala ba ce tunda muna da Kwamishina, ka sani ai dole ya fito. Yanzu fa nima na ƙara samun wata babbar kwastoma ta kaya. Kar ka yi mamaki a cikin garin nan ta ke fa, ita matan aure su ne abokan cinikayyarta. Matar inda ta burgeni duk wata hanya da za ta bi ta shigewa mace ta sani, za ta nunamata wannan hanya ita kaɗai ce ta gusar da damuwa, ya kuma sanya bacci mai dadi da munshari. Nifa Ɗanmutuwa duk inda zan ga masu jarumta da rashin tsoron gudanar da aikin kasuwancinsu burge ni suke yi ba kaɗan ba. Kaga akwai matashiyar da na sanya ta ke kawomin matasa cikin tafiyar, codein sai ya ƙare a ƙasa da minti talatin. A hankali su na sabawa da shi mu kuwa mu dinga ƙara farashi son ranmu."

Ɗanmutuwa ya dara.

"Ai sosai lamarin na tafiya yadda ake so. Ni fa kinga akwai wani yaro ana ce mishi Prince, ɗa ne ga wani babban Soja, ai idan kina neman hatsabibi ki ka sami ɗan gidan Major Musa Ahmad Gwadabe kin gama. Yana min cinikin sama da dubu dari biyu a wata."

"Amma ba'a gani a jikinka, daɗina da kai ba ka iya tattalin kuɗi ba Ɗanmutuwa. Ka ƙi gina gida balle ka siyawa kanka suturun arziƙi. Ba dole irinsu Mahadi su rainaka ba su na ganinka da Ciyaman? Dubi fa suturar jikinka yadi duk ya koɗe."

Ya yi ƙwafa bayan ya bi jikinnasa da kallo.

"Shege ba, idan akwai wanda na tsana to fa ya biyo bayan mutumin nan. Amma kin yi magana, zan yi ɗinkunan kece raini don kwanan nan ma zan yi aure. Ba zan iya zama da Na'ima kaɗai ba."

Ƴar dariya Hajiya Adama ta yi, kafin ta tanka sai ga sakatariyarta ta gidan ta shigo da sauri. Nan ta ke sanar da ita isowar manyan Alhazawan, hakan yasa suka miƙe.

"A tabbatar yaran can sun kimtsa kinsan ba na kaunar matsala." Ta amsa da toh sannan ta fice. Su kuwa suka nufi waje domin yi musu tarba ta musamman.

***
Cikin kwanaki uku Haulatu ta wartsake kamar ba ita ba, ta shiga harkokinta na yau da kullum. Ta koma makaranta, koda suka haɗu da Hindatu ko kallonta ba ta yi ba. Maganar duniya Hindatu ta yi amma ta share ta, haka har aka tashi ba ta bada wata fuska ba. Ta kama hanyar tafiya don yau kasuwa za ta leƙa wurin Umma, har ta isa bakin titi tana tsaye ta ji muryar Hindatu a gefenta.

"Wai Haulatun Umma ni kike yiwa wannan wulaƙancin? Magana ta ƙi ci ta ƙi cinyewa? Matar da har haƙuri na ba ki? Ni wallahi kinsan dai ban iya gaaba ba, don sonki da Allah da Ma'aiki s.a.w ki yi hakuri. Kin ji? Haba Aminiyar kirki."

Sam ba ta ma zaci tana bin ta ba, ba tare da ta kalle ta ba ta amsa.

"Ai komai ya wuce."

"Me kike nufi da ya wuce? Tun a aji kike nanata wannan kalmar, kina nufin kin yanke zumuntarmu ko me?"

Cikin ɗaure fuska Haulatu ta amsa.

"Aa, ai ba duka na yanke ba, da kika shigo ajin ba mun gaisa ba?"

Kai, Hindatu haka ta dinga naci, ƙarshe sai ga ta a cikin ɗan sahu sun kama hanyar kasuwa tare. Haulatu dariya ta taso mata amma ta danne a zuciya, ta fiddo niƙaf ɗinta ta ɗaura gudun kar ta aikata abin da Umma ba ta so. Tun tana share ƙawarta tana mata mitar ba ta sauka ba ta da kudin da za ta biyamata na mota ita kuwa Hindatu na rantsuwa sai ta bi ta sun shirya a gaban Umma har tana fadin.

"Kuma ma ai kasuwar tawa ce tunda ina da miji a cikinsa, kudin mota kema na hutar da ke zan biyamaki."

Duk shariyar da Haulatu ta dinga yi haka ta haƙura ta sauko, kafin su ƙarasa sai hira da dariya kamar ba su ba. Anan Haulatun ke labarta mata ciwon da ta yi ba ta kuma ɓoyemata dalili ba, hatta da ɗasawar da suke yi da Bahijja da ƙawayenta ba ta ɓoyemata ba tunda dama Hindatun ta san da batun Bahijjar. Itama nan ta hau ba ta labarin zuwan Alhajin da kuma yanda ya ruɗe dagaske aurenta zai yi da zarar sun fita daga ajin da suke. A lokacin su na dab da rubuta jarrabawa wanda idan sun ci sun haye gwamnati za ta biyamusu NECO.
Sosai Haulatu ta taya ta murna, ta kuma bi ta da fatan alheri. Har hotonsa ta nunamata a waya, babba ne ba yaro ba, yana da mata ɗaya da yaransa biyar. A iyaka ra'ayi irin na Haulatu, ko da ace tana da ra'ayin aure ba ta tunanin auren irinsu balle kuma babu auren ma a zuciyarta kwata-kwata. Tsakaninta da samari, sai ɗaure fuska da kallon banza. Duk wanda ya nuna yana sonta to fa taka masa burki take yi. Cikin samarin unguwa dama ba wanda ya taɓa nuna yana sonta a yanda gidansu yake. Sai ko ƴan bana bakwai.

  Har suka isa kasuwar kwari su na ta hirarrakinsu. Haka suka dinga kutsawa Hindatu na faman mitar ya kamata Umma ta bar zuwa kasuwa tunda tana da suruki ɗan kasuwar yanzu (saurayin Hindatun kenan), ya fi ta dinga sarin kaya itama tana siyarwa yanda Mominta ke yi. Ita dai Haulatu murmushi kawai ta yi. Ba su ƙarasa ga Umman ba sai da Hindatu ta siya facemask ta rufe hanci da bakinta wai kar saurayinta ya hango ta wurin siyar da abinci.

Umma ta yi mamakin ganin Hindatu.

"Ke kuwa me ya kawoki nan daga makaranta? Kin sanar a gida ne?"

Ƴar dariya ta yi.

"Aa Umma, kar ki damu Momi ba ta gari ta je Katsina kai wasu kaya. Ni kaɗai ce a gidan."

Umma ta jinjina kai ba ta ce komai ba. Abincin ta zubamusu sai da suka ci suka ƙoshi ta ce su tashi su kama hanya har Haulatun ganin wajen ya soma cika da samari. Kuma ga Hindu duk wanda ya tankamusu sai ta ga ta cafe zancen har su na dariya. Ita dai Haulatu ba ta yi wannan karambanin ba don ta sani muddin ta aika to fa za ta ɗanɗana kudarta a wurin Umma, balle ma irin rayuwar ba burge ta take yi ba sam.

Sun bar wurin Umma sun yi nisa ta dakatar da ita.

"Lafiya?" Faɗin Haulatu.

"Don Allah muje ki raka ni mu gaisa da Noor. Minti biyar kacal."

Zaro idanu ta yi.

"Lallai ma BigMama, so kike Umma ta yanka ni ashe. Kuma ke yanzu girmanki ne ki bi saurayi har shagonsa? Nikam ba inda zan je. Malama zo mu tafi ko na bar ki anan."

"Kai Haulatu, amma dai kinsan ba ani abin zan yi marar kyau ba ko? Kawai dai mun yi waya da shi ɗazu ai kinga sadda na tashi, ya cemin idan ban shiga mun gaisa ba zamu yi rigima. Taimaka don Allah, ni wallahi ko a bakin shagon ki tsaya muna gaisawa sai mu wuce."

A dole, babu yanda Haulatun ta iya haka suka nufi shagon bayan ta ƙara gyara zaman niƙaf ɗinta. Ta gan shi a zahiri, ita sam ba ta ga abin burgewa a wurin mutumin da Hindatu ta kira da Noor ba, ainahin sunansa Alhaji Badamasi, ta shiga shagon ta zauna suka gaisa. Ta maida hankali ga matan da suka shigo siyayya, tana ji su na hira yana cewa meyasa ƙawarta ta rufe fuskarta, ba ta ce musu uffan ba. Can da ta ga abin ba na ƙare ba ne ta miƙe. Ganin haka tuni Hindatu ta miƙe itama suka yi sallama, ya takomusu har waje ya miƙawa Hindatu kudi har dubu uku su yi kuɗin mota.

***
Ya shigo gidan yana ɗaure fuska babu ko sallama. Haulatu na zaune tana wanke kayan makarantarta. Umma dake shara ta dube shi, zuciyarta ko ba komai ta yi sanyi.

"Sannu da zuwa." Ta furta baki na rawa.

Ita kuwa Haulatu tamke fuska ta yi ba ta ko ƙara kallonsa ba, ɗan waƙen nishadin da ta ke rerawa tuni ta daina. Ƙirjinta zafi ya shiga yi tsabar takaici. Tana kallo ya shige bai ko amsawa Umma ba. Ita kuwa har da sauke ajiyar zuciya fuskarta babu yabo ba fallasa ta cigaba da shara.

"Ke."

"Na'am." Umma ta amsa da sauri kafin ta shiga ɗakin. Tsabar bakin ciki ya sa Haulatu miƙewa ta bar wankin ta shige ɗaki.
 
 Fitar tsiro
Page 9
Watanni uku da suka biyo baya, a wajen Haulatu sam ba masu dadi ba ne a

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login