Showing 3001 words to 6000 words out of 29121 words

Chapter 2 - FITAR TSIRO

22 Oct 2024

6536

ba na kaucewa hanya ba. Anan za ta taimakawa Umman su wanke abin da ya kamata a wanke, su shirya kayayyakin cikin ɗan sahu su koma gida. Kusan kudin sai tace Baban ake nemowa, don duk sadda aka dawo toh fa sai Umma ta ba shi nasa kason, wataran ma sai ya ce dole ta ba shi duka kudin zai biyata ana binsa bashi. Sun sha yin kwanaki ba su yi sana'a ba saboda Umman ta yarda da romon baka wani sa'in kuma tursasawar Baban ta ba shi kudaden. Haulat kan ji haushi ƙwarai har kuka take yi da daukar alwashin ba za ta ƙara bin Umman kasuwa ba tunda kudaden Baba take damƙawa. A ƙarshe kuma ta huce. Idan zaman babun ya ishe su Baban ya ƙi ba su kudin da zasu ci su sha, takan faki idanun Umma ta shiga dakin Baba wanda koyaushe yake garƙamewa (bai san ta zare mukulli daya cikin muƙullayensa ba) ta lalubo musu kuɗi a ma'ajiyarsa. A ranar ba ta ba Umma ba sai a washegari ta ce ai ta ranto mata ne a hannun Mamar ƙawarta don su koma sana'arsu idan an tara riba za ta mayar mata da kuɗin. Duk ranar da ta yi haka kuwa Baban zai zo ya yi ta ɗura ashariya yana tambayar wa ya taɓa kudadensa sai dai ba ya wani faɗan kirkin a zo a gani yake bari tunda ya sani shi kaɗai keda muƙullin ɗakin babu wanda ke shiga yana dai mamakin lamarin, tun Umma ba ta gane abin da take yi har ta fahimci idan sun rasa jari ga yanda Haulat din ke samo musu. Anan fa za ta dinga fada da nunamata illar sata, Haulat ko a jikinta don kuwa a ganinta raba arne da makami ma ai ibada ne tunda akwai haƙƙoƙinsu da yawa da bai damu da saukewa ba. Ranar da ya gano Haulatu ke ɗaukar masa kudi ta ci duka tamkar zai kashe ta. Daga wannan lokacin ne ya ci alwashin aurar da ita ga wani ubangidansa da yake yiwa bangan siyasa a baya, Ciyaman Nazifi.

Ta runtse idanu sakamakon sarawar da kanta ya soma, tabbas idan ta ce za ta zurfafa cikin tunane-tunanen abin da ya faru da su a rayuwa sanadin mahaifinta toh lallai za ta kwana cikin azabar ciwon zuciya da na gangar jiki wannan ne dalilin da ya sa ta fidda komai a ranta ta yi addu'ar kwanciya bacci, tana jin Umma ta miƙe ta fita ta dora alwala ta dawo dakin ta rufe, a haka bacci ya dauketa.

***

 FITAR TSIRO

Rufaida Umar

Paid book: 500
Account details: 7145096012 Ibrahim Rufaida Umar. FCMB

Phone number: 09034973645

Free page 2


Cikin sauri ta shirya cikin kayan makarantarta na sakandire mallakin gwamnati dake a unguwarsu, ta kusan makara wannan dalilin yasa ko tsayawa shan ruwan shayi da ƙosan da Umman ta ajiyemata ba ta yi ba. A gaggauce ta kammala ta fice bayan ta shaidawa Umman ta ɗauki muƙullin gidan don ba za ta bi ta kasuwa ba yau, Umman na kwalamata kira akan ta zo ko a leda ne ta ƙullamata abin karin amma ko waigowa ba ta yi ba face sakin guntun tsaki. Babban burinta ta ganta a ajinsu tare da Hindatu kawai don ta labarta mata yanda suka yi da Mijin Umman. Ba ta ko damu da gwajin ajin da zasu yi ba a ranar don ko nutsuwar karatu ba ta samu damar yi ba, koda ta isa abin takaicin ba ta ƙaraso ba. Hakanan ta shige ciki ta fiddo ƙaramar dardumarta a jaka ta shimfida ta zauna don kusan rabin ajin a ƙasa suke. Har Malaminsu na koyon turanci ya shigo, babu alamar Hindatu, sai can ta shigo kamar an wurgo ta. Kayan jikinta duk sun yi ƙura saboda aikin shara da aka sanya ta matsayin hukuncin makara. Hasken fatarta kusan ya zarce na Haulatu don ita tana haɗawa da mayuka hakan yasa har wani ja take yi, sai dai daga ta buɗe ƙafafunta za ka fahimci hasken ba na halittar ba ce, ƙafar baƙiƙirin. Ba ta da tsayi kamar yanda ba ta kasance cikin jerin gajeru ba, tana da jiki da girman halittar mama wanda hakan ya ƙara mata girma, ta zama kamar wata uwar mata a cikin abokan karatun nata. Wannan ya sanya ƴan ajin suka fi yi mata laƙabi da BigMama. Ba ta daukar raini, ba ta da munafunci balle gulma, faɗa ko ba da ita ake yi ba, za ta shigarwa mai gaskiya ta buga rashin mutunci son ranta. An sha ba ta hukuncin zaman gida (suspension), hakanan an sha kiran mahaifiyarta. Da yawa na mata kallon ƴar mace don a hannun mahaifiyarta ta rayu ba don wai Babanta ba ya raye ko wani abun ba, ko kusa, ana cewa ma ko Uban bai ji dadin zama da mahaifiyarta ba, dakyar da karfin addu'a ya samu ya fitar da ita daga rayuwarsa. Ko gidan Uban ba ta zuwa balle ta saba da wani a can, ita kuwa Uwa ƴar kasuwa ce, ba ta can ba ta nan, sai ta fice daga garin har ma wasu lokutan ta tsallaka boda zuwa Nijar da zummar kasuwanci ta bar Hindatun a gida daga ita sai sauran masu zaman haya sai abin da ta ga dama take yi da taƙamar gidan mallakin uwarta ce, a haka dai uwar ke samarmusu abin rufawa kai asiri su ci su sha, su sanya sutura mai kyau daidai gwargwado don kuwa suturunta ya take na Haulatu. Burin duniya kuwa ta ɗora akan Hindatu, tana mata kallon wata kadara da nan gaba za ta ci riba a kanta. Ta sanya a ranta da zarar Hindatun ta kammala sakandire za ta yi cuku-cukun kai ta jami'a don ta ƙara wayewa da gogewa. Wannan yasa tarbiyyar Hindatun ya zama sai a hankali, babu wani ko wata da ya isa ya juya tanƙwarata hakan yasa ta ke cin karenta ba babbaka.

"Ke! Tsayuwar me kike?"

Malamin ya yi mata magana a tsawance, ta ɗan bishi da kallo tana ƙunƙuni, a duniya idan da wanda ta tsana cikinsu har da Malam Bukari, yana cikin wadanda ba su fiye ba ta ƙofar kawomusu wargi ba. Ta kauda kai ta yi ciki, sai da ta gama kallon mazauna saman bencinan da ba su fi biyar ba a ajin, ta watsa musu harara kafin ta yi ƙwafa ta zauna gefen Haulatu saman darduma. Malam Bukari na juya baya ciki bada umarnin a yi sauri a bada amsoshin tambayoyin da ya rubuta a allo a ƴar takarda, ta kalli Haulatu cike da ɓacin rai da murya ƙasa-ƙasa ta ce.

"Wai ke meyasa idan kin zo ba kya tashi shegu daga benci ki kama mana wuri? Kinsan dai na tsani zama a ƙasa ko?"

Haulatu ta wurga mata harara.

"Toh sannu Uwani, tunda kin zo ai sai ki tashe su. Kinsan tun lokacin da nake jiranki ne?"

Hindatu jin haka ta ɗan fiddo idanu kaɗan.

"Haba? Ki ce da labari."

"Akwai labari amma fa ba wani mai dadi ba. Bari dai wannan ya fice naga idanunsa a kan mu."

Wannan bai sa Hindatu damuwa ba, kallonsa ta yi kadan sannan ta ja guntun tsaki bayan ta kauda kai tana mai karɓar takardar da Haulatu ta fillo mata a cikin littafi.

"Ke dallah rabu da shi, ni faɗamin kawai, duk na matsu na ji me Mijin Umma ya aikata don nasan dai tatsuniyar gizo bai wuce na ƙoƙi."

Ita dai Haulatu sai ta yi dariya kawai ganin idanun Malamin dai na kansu, a dole Hindatu ta bar zancen sai bayan ya fita ne ta tashi wasu akan tebur suka koma, ganin haka Haulatu ta basu aron dardumarta su zauna a ƙasa. Ba yadda suka iya face su karɓa sanin da suka yi idan ma sun ƙi wannan zaluncin da Hindatun da ta yi musu babu wanda zai iya taka mata burki. Koda kuwa an yi magana, toh fa abin da zai biyo baya bai wuce ta tare su a hanya ta ci zalinsu son rai ba.

"Ina jinki." Cewar Hindatu.

Hakan ya ba Haulatu damar fayyace mata batun Ciyaman Nazifi. Wani uban ashariya da Hindatu ta yi murya a ɗage, sai da ƴan ajin duka suka dube su. Ta banka musu harara.

"Uban me ku ke kallo?" Sai kuwa suka kauda kai, wasu kuwa suka ja tsaki.

"Amma mijin Umman nan ya cika azzalumin ƙarshe, wallahi kar ki sake ya tauyemaki haƙƙinnan. Ke me kike jira da ba za ki bi shawarata ku bar masa gidan ba?"

Cikin rashin kulawa da kiran Baban da azzalumi da aka yi, Haulatu ta taɓe baki gami da jan guntun tsaki.

"Wannan matar ce za ta yarda mu bar gidan? Ai ko asiri ya yi mata sai haka. Amma wallahi kin ji dai na rantse, ko sama da ƙasa za ta haɗe ba zan bari ya cimma wannan halakakken burinnasa a kaina ba. Zan nuna masa nima na iya rashin kirkin."

"Ato, idan ba haka ba ko mu zo mu sha biki."

Faɗin Hindatu cike da tsokana tana dariyar shaƙiyanci, duka ta kai mata a baya, aikuwa ta gantsare. Haka suka cinye lokacin babu wani Malamin da ya shigo ajin da har aka fita hutun rabin lokaci. Dama sun saba, malamai ba su wadaci makarantar ba wannan ta sa ɗalibai da yawa suna zuwa ne kawai ba don suna samun wadataccen ilimi ko fahimtar abinda aka koyar ba yanda ya kamata. Zasu iya zuwa su wuni amma bai fi su sami darussa uku kacal ba. Wannan na ɗaya daga cikin illar da dalibai ke fuskanta a ire-iren makarantun na gwamnati. Hakan kan jawo nakasu da koma baya a harkar iliminsu. Sai ka ga ƴar sakandire babu turanci a bakin, hakanan shi kansa rubutun ba kowanne ya iya yanda ya kamata ba. Sassauƙar kalma sai ta gagari ɗalibi rubutawa.

Haka suka cinye ranar a makaranta da darussan da basu wuce uku ba aka tashe su. A hanya su na tafe su na hira inda Hindatu ke ƙara rura wutar tsanar haɗin auren a zuciyar ƙawarta. Aikuwa haƙanta ya cimma ruwa don Haulatu sai da ta ji ƙarfin gwuiwa fiye da na baya akan shirin yin gudun fanfalaki don tseratar da kai daga wannan mugun nufi na Mijin Umman.

Har suka zo hanyar da ta raba su hirar da suke yi kenan, ƙarshe dole suka bar sauran da zummar gobe Juma'a zasu hadu a gidan su Hindatun.

Kai tsaye Haulatu gida ta nufa, tun daga nesa ta hango su zaune saman benci ƙasan bishiyar darbejiya dake ƙofar gidan nasu. Wani guntun tsaki ta ja, majalisarnan ta su Audu Maada ya tsaya mata a ƙahon zuci, babu wani a unguwar da bai san da zamansu ba. Duk wani hira na dabanci da ma bushe-bushen hayaƙi ya tattara ne a wurinsu. Rigima ba irin wacce ba'a yi ba a unguwar akan majalisar nan amma hakan bai sa ta rushe ba sakamakon ɗaurin gindin da suka samu daga shi Uban gayyar, wato Maigidan, inda ya ce ai ƙofar gidansa ce ba ta wani ba kuma babu wanda ya isa ya hana su zama tunda ba shirginsu suke shiga ba. Magana har wurin ƴan sanda sai dai kasancewar shi ɗin mutum ne mai idanu cikin gwamnati yasa babu inda ƙarar ta je aka yi watsi da ita. Wannan ce ta sa kowa ya zuba musu idanu kawai, iyaye na takatsantsan wurin ja wa yaransu kunne akan shiga sabgar su Audu Maada balle kuma su kai ga shiga gidan.

Ta ƙara jan guntun tsaki gami da ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa. Haka har ta ƙaraso ƙofar gidan, za ta gifta su ta ji sun soma maganar tasu ta rainin wayo inda ta tsinkayi muryar Ɗan Aljan ya yi wani busa da baki sannan ya ce.

"Kai! Kai!! Ni fa wallahi Oga Maada ba don da manya a gabanmu ba, babu abin da zai hana ni farautar wannan babbar tsokar. Billahillazee tana..."

"Kai dallah ware can! Kai daɗina da kai ka cika zalama. Ina kai ina shiga gonar Ciyaman? Ai babu mai ninkaya a wannan kogin idan ba shi ba!"

Suka kwashe da dariyar zancen Duuna, Haulatu ta dube su ta watsamusu harara kamar idanunta za su faɗo sannan ta ƙarasa tura ƙofar bayan ta fidda kwaɗon ta shige, tana jinsu suka ƙara sakin wata dariyar ba ta ko saurare su ba don ya ci ace ta saba da haukansu da ba shi da magani. Maida ƙofar gidan ta yi ta rufe ruf sanin da ta yi ba su da kai, don su ce zasu shigo kai tsaye ba komai ne a wurinsu ba. Wanka ta soma yi ta sanya riga marar nauyi gami da ɗaura zani, ba ta tare da yunwa saboda Hindatu ta siyamusu wainar fulawa sun ci sun yi nak a makaranta, madadin ta yi sallah kawai sai ta shimfiɗe a tsakar gidan inda iska mai sanyi da daɗi ke bugowa, aikuwa nan da nan bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita. Ba ita ta motsa na sai da ta ji kamar ana faman dukan ƙyauran gidan, a dole ta tashi tana murza idanu gami da ƙarewa garin kallo, ga dukkan alamu dai yamma ta yi ganin yanda rana ta yi sanyi sosai.

"Ina zuwa!" Ta furta cikin muryar bacci, tana jin sadda Garba ɗaya daga cikin almajiran Umma masu yi mata dakon kaya na fadin. "Tana ciki, yanzu tayi magana."

Hakan ya fahimtar da ita Umman ce ta dawo. Koda ta buɗe, ta gan su tsaye ga uban manyan kuloli biyu da tarkacen kasko da sauran kayan girki. Ba wannan ba har da su Ɗan Aljan tsaye da yake bin ta da kallo kamar wani tsohon maye.

Fadi yake "Ai Ranki ya daɗe dama na faɗamaki tana ciki, muna nan ɗazu ta shige. Sai dai ko ta ɗan harba duniyar Mass (Mars)." Ya ƙarashe da dariyar shaƙiyanci, ita kuwa daga yanda Umman ta haɗe rai tana kallonta yasa ta fahimci kuskuren da ta yi na fitowa kai babu ko kallabi sai zanin da ɗaura saman ƴar rigar, duk dai ga ta a birkice alamun mai bacci.

Bayan ta shige ciki, yaran su uku suka bi bayanta da kayan suka sauke, sai da Umman ta sallame su ta ba su abinci da kudi sannan ta dawo kan Haulatu. Rai a ɓace ta ce "Kin yi sallar Azahar da La'asar?"

Ta turo baki kaɗan. "Yanzu fa na tashi daga bacci, shi zan yi."

Cike da takaici Umma ta girgiza kai.

"Ki ji tsoron Allah Haulatu, wannan rayuwar da ki ke yi na rashin sauke haƙƙin Allah a lokacin da ya kamata babban kuskure ne. Kina tunanin matsalolinki za su warware alhalin kina yiwa Allah yanda ki ke so? Wato yau ma ba ki yi ko tunanin zuwa Islamiyyar ba ko? Kin kyauta, ki cigaba, nidai Allah na gani ina iyakar bakin ƙoƙar.."

"Kai Umma, nifa ba cewa nayi ba zan yi ba. Haba don Allah, wannan masifar ma da kike ta yi ai sai ya ƙara cinye lokacin."

Umma ta saki baki kawai tana kallonta har ta cika ruwa a buta ta shige banɗaki tana ƙunƙuni, yanke ta idan tana cikin magana wannan ba sabon abu ne a wurinta ba, amma kalmar tana masifa ya yi mata ciwo ƙwarai. Haulatu sau da dama idan ta yi magana kamar an buɗe masai tsabar rashin sanin abin da ya dace ta fadi. Sam, ba ta iya tauna harshe kafin ta furzar ba, komai ya zo mata hakanan ta ke jinsa daidai a wajenta.

"Allah ya shirya." Abin da ta iya fadi kenan zuciyarta babu dadi sannan ta shiga tattara kayan, tun a kasuwa ta saka yaran sun wanke komai, maida su ta yi kawai kicin ta adana, abincin da ta rage musu da zasu ci, shi ta juye cikin madaidaitan kwanuka sannan ta shige daki don rage kaya ta watsa ruwa. Koda ta fito daga dakin, ta iske ta a tsakar gidan ta tayar da sallah bayan ta zura dogon hijabin Umman dake ajiye saman tabarmar. Ita kuwa bokiti ta ɗauka ta cika ta shige.

Haka Haulatu ta yi sallolinta kafin ta miƙe ta dauko faranti, kai tsaye ta dibi shinkafa da waken ta sanya kabeji da mai a samansu. Tana cikin ci Umman ta fito, cikin sakin fuska Haulatu ta dube ta.

"Lah Umma yau dai kin yi sa'ar mai, babu warin nan irin na rannan."

Ganin yanda ko kallonta ba ta yi ba ta shige ɗaki sai ta sha jinin jikinta.

"Ita kuma wannan ita da wa?" Ta yi tambayar a fili babu mai amsa mata, sai kuma ta ja guntun tsaki tunawa da ta yi mai yiwuwa rashin zuwa islamiyyarta ne ya yi wa Umman ciwo. Hakan yasa ta miƙe duk abincin ma ta ji ya fice a ranta don ita fa ba ta kaunar ta ga ko alamar ɓacin rai a fuskar mahaifiyarta.

"Umma ni ce ko? Ban je makaranta ba, kiyi hakuri na dawo kaina na ciwo. Amma zan je ran Lahadi tunda gobe juma'a." Kasancewar makarantar hutun juma'a da asabar ake yi.

Umman dai ba ta ce uffan ba ta zura doguwar rigarta ta shan iska, ganin dagaske dai ba za ta kulata ba yasa hankalinta tashi. Nan fa ta shiga ban hakuri har da su hawaye, Umma ta dube ta, dagaske ita laifinta ɗaya ta ke hangowa kanta, wato na ƙin zuwa makaranta, a ganinta shi ne dalilin fushinta. Ta ɗan yi shiru tana nazarin wannan wauta na ɗiyarta. Can kuma ta numfasa gami da soma magana.

"Shikenan, amma ki sani kalmar da kika yi amfani da ita na ina masifa, ba daidai ba ne yiwa babba ita. Ba ma wannan kaɗai ba Haulatu, ko kaɗan bai kyautu ace babba na magana ka katse shi ba, wannan yana nuni da rashin ladabi gareshi. Sannan ba sau ɗaya ba, na sha nunamaki illar wannan tsakin da kike yawan yi ga babba balle kuma ni da nake mahaifiya gareki ba daidai ba ne, na lura ya riga ya zamar maki jikin da yanzu da kuma nan gaba zai iya haifar maki da tarin matsaloli, koda ace ba a wurina ba, za ki iya samun matsala da gidan da za ki je nan gaba."

Cikin rashin fahimta Haulatu ta ce.

"Gida kuma? Ni zan je? Wayyo Umma kin amince kenan mu bar

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login