Showing 6001 words to 9000 words out of 17277 words

Chapter 3 - Kwai Cikin Kaya Complete Hausa Novel

12 Oct 2024

2367

ta wannan zamanin, inhar baka da shi to kaida banza duk ɗaya kuke, kai tsaye ma ake mantawa da kai a cikin dangi. To ballema irin iyayena da suka kasance naka sassu, inhar za'a iya mantawa da mai ƙafafu da hannu da idanu saboda talauci ya masa katutu ta yaya kuke tunanin ba za'a manta da musakan iyayena da bayan rauni da ALLAH ya jarabcesu da shi na halittar jiki harda talauci?.
Ni kaɗai iyayena suka haifa a duniya, nima an jima ba'a sameninba, sai da ga baya ALLAH ya azurtasu da samuna matsayin ƴa ɗaya tilo a garesu, duk da talaucin iyayena da kasantuwarsu nakasassu ni ƴar gatace, dan gwargwadon iko iyayena tsaye suke a kan bani tarbiya, nakanje makarantar gwamnati kamar yanda sauran ƴaƴan gidanmu ke zuwa, hakama ina zuwa islamiyya. Sai dai aduk lokacin da aka buƙaci wani abu da ga makaranta da yafi ƙarfin ƙarfinmu hankalin iyayena kan tashi da ni kaina, wannan yasa da yawan lokuta karatun nawa ke kwan gaba kwan baya, dan kuwa ƴan ajinmu sunsha tsallakewa gaba su banni da maimaita aji saboda rashin kuɗin abu idan an buƙata tamkar ba makarantar gwamnati ba.
Badan bani da ƙoƙaru bane, a wannan ɓangaren ma ina sahun farko na gwarzayen yara masu ƙwaƙwalwar karatu da fahimtarsa, sai dai rashin kuɗi ke daƙileni a kulum.
A yanzu haka shekaruna sha takwas, amma har yanzu ss2 nake na makaranta, saboda matsalar komawa baya da naita fuskanta.
Bani kaɗaice budurwa a gidanmu ba, a ƙalla zamu iya kaiwa fin mu ashirin kuma duk yawancin sa'oin juna, sai dai kowa da gwaninsa (inji masayin taliya ƴar murji😆), dan kuwa kowaccenmu tanada abokiyar mu'amularta daga cikin ƴammatan gidan, dan haka muka kasance kusan nau'i uku zuwa huɗu a ɗaukar rayuwa.
A kwai sahun farko da suke ɗaukar kansu masu matuƙar aji da jin sunfi kowa hakama iyayensu sunfi na kowa arziƙi a gidan, a group ɗin sun tasarma su kusan bakwai, sai sahu na biyu da ajinsu bai kai waɗancan sahun farkon su sakasu a cikinsu ba, sai suma sukaja tasu zugar da zama abokan takarar waɗancan ta fuskar sumafa ba bayaba, sai kaso na uku da suka ɗau rayuwar saisa-saisa saboda ƙoƙari na tsawatarwar iyaye da gudun jefa kai a halaka, sai mu da ke karshe da muka kasance ba kowan kowa ba, hasalima mune akema kallon ƙarshen ƙasƙantattu marasa gata da galihu, ta kowacce fuska bamu da wani amfani sai tarbiyyar iyaye da ke jagorantar dukkan haƙurunmu da ɗaukar duniyar wajen maƙalewa kafin wa'adin barinta ya cika.
Ba wani yawane da muba gayyar ƙarshen, dan kuwa da ga ni sai Firdausi ne da take ƙawata jallin jal a gidan, dan kuwa matsayin iyayenmu kusan ɗayane, itama mahaifanta suna fama da ciwon talauci tamkar mu, sai dai su sunma ɗan ɗaramu, dan babanta nada sana'ar saida kayan miya itama anan ƙofar gidan, shinema ke taimakawa babana a tashi sana'ar idan anzo saya da idan za'a danƙa masa kuɗi, kuma ita iyayenta duk lafiyayyune, sai yazam har kwancen kayan sawa itace mai bani, dan saka sabbin kaya a gareni sai sallah, suma kala ɗaya ne da ƙyar ake ƙulla kuɗinsu saboda ƙoƙarin iyayena nason ganin sun sharemin hawaye a cikin tsarata.
Haka rayuwa ta zaɓar mana, badan wanda ya haliccemu baya sonmu ba, badan mun kasance masu saɓa masa ba, sai dan kawai haka ya tsara son ganin bayinsa a cikin duniyarsa dan yazama ilimi ga jahilai, izna ga masu wauta, rahama ga masu haƙuri, sake girmama mulkin ALLAH ga masu mulki.
Gidanmu wani irin gidane da bansan yanda zan fassara muku shi ku fahimta ba sam, dan duk wani mugun hali ya ƙunsa saboda jama'ar daya tara masu kalar hali iri-iri a zukata. A duk lokacin da kake barci to ka tabbata sai ka samu wanda ke maka munshari a gidan, hakama akwai masu kallo da ido ɗaya, akwai masu gani ta ƙeya kuma. Tsabar iya annamimancin gidanmu ko faɗa ba'a yawan yi, kasan kuwa duk zaman da ya haɗa jama'a irin na gidanmu kaga ba'a faɗa to lallai ka jinjina wannan zaman kuwa.
Ɗakinmu shine a can ƙarshe sai na su firdausi, hakan yasa baban firdausi samun damar yimana ƙaramar baca ta katako a ɗan lungun da ke gaban ɗakinmu wanda dalilin ginin banɗakuna ya fita. wannan bacar ce ta zama ɗakinmu ni da firdausi, dan ɗakunan gidan duk falle ɗai-ɗai ne, hakan yasa mafi yawan ƴammatan gidan daina kwana a ciki sai dai suje maƙwafta kwana.
Rana mafi muni da razani a rayuwata itace ranar da muka wayi gari mahaifiyata babu lafiya, tun a daren jiya amai da gudawa suka saukar mata, kafin safiya tayi ligif, lokacin da ɗaya daga cikin mazan gidanmu mai tuƙin a daidaita ke ƙoƙarin sakata a napep ɗin dan zuwa asibiti sai rai yayi halinsa.
Tashin hankali ba'a sa maka rana, dan kuwa yanda na tsinci kaina a cikima ai ɓata lokacine, har aka kai gawar mahaifiyata makwancinta ban san ina hankalina ya ke ba, sai bayan komai ya dai-daita har rana ta doshi faɗuwa sannan na dawo hayyacina.
Abinda ya daɗa harmutsa dukkan tunanina shine babu kowanne ɗan uwan mahaifana da ya zauna dan karɓar gaisuwa a gidan, tun bayan binneta da aka dawo sukai ɗan zaman awoyi uku zuwa huɗu sai kowa ya kama gabansa.
Nayi kukan da yafi na rasuwar innata a wannan lokacin kam, hakama babana da ruɗani ya maidashi kurman gaske bai uhm baya uh-uhm, dama gashi babu ijiyar gani.
Matan gidanmu sun ɗan tausaya mana a tsakanin nan, dan kuwa kullum sai an samu mai bamu abinci ni da baba, dama maman firdausi kullum saita bamu na rana da dare, dan mafi yawan jama'ar gidan basa abincin safe, kowa sai dai yaje ya siyo a waje, sai ƙalilan a ciki dake ɗanyi shima da risho a ɗaki gudun idanun masu ƙwalama.
Bayan kwanaki uku na makokin mahaifiyata akai addu'ar uku, sai aranar ne naga wasu tsiraru a cikin dangin iyayena, harma sukaimin gaisuwa. Ko da aka kammala addu'a sai kowa ya sake kama gabansa aka barni da ga ni sai babana kawai.
Rayuwa ta cigaba da shurawa duk muna fama da tabon rashin innata ni da mahaifina, dukda baba yana dannewa da aro jarumtar rashin inna a gabana har ya lallasheni, nasan shima yana a cikin wani hali. A haka kwanaki sukaita shuɗewa har inna ta cika watanni uku da rasuwa. Zuwa yanzu naɗan saki jikina, amma ba da kowa ba, dan dama can ni miskilace kamar yanda ake jifana da zagi a cikin gidanmu, (akance sai miskilancin tsiya tamkar ƴar wani da wata), idan naji hakan iyakata murmushi kawai, dan bani da abin faɗa.

Kamar kullum na dawo da ga makaranta a gajiye yauma, dan dukda tazarar nisan da ke tsakanin makarantarmu da gidanmu kullum a ƙafa nake zuwa na dawo, idan kinga na hau napep sai dai idan baba ko innata sun sami rarar kuɗi a cikin sana'arsu, to shine za'a ɗan bani talatin na break, maimakon naci wani abun sai na maƙale kuɗin idan an tashi na hau napep, shima da ƙyar ake ɗakkoni, wataranma bana samun maimun alfarmar sai dai na taho a ƙafar dai dana saba. To yanzu ma tun bayan rasuwar innata sai komai ya sake taɓarbarewa, dan baba baya da isashshiyar lafiya, wataranma ko ƙofar gidan bai iya fita wajen sana'ar tasa sai baban firdausi ya takura masa.
Tunda na shawo kwanar anguwarmu gabana ya ƙara ƙarfin faɗuwa, dama tun daren jiya nakejin girata ta haggu na rawa, ci gaba nai da takowa tamkar kazar da ke shirin sakin ƙwai zunɓutu a ƙasa, matasan anguwarmu da dattijai zagaye da wani abu a ƙofar gidanmu, ga jini faca-faca a gefen titin wajen, dan gidan mu nakan titine sosai, kuma titin irin wanda ake yawan bi ne saboda shine babban titin anguwar.
Yanda wasu da ga mutanen suka zubomin idanune ya sakani sake komawa jan ƙafa, dan kallon yafi kama da na wadda ake tausaya mawa. Yayinda na iso daf da su sai naga an fara darewa ana bani hanya, mamaki ya sake kamani, dan kuwa basu tsaremin hanyar da zan shiga gidaba, suna da ga gefen jikin gidanne. Dubana nakai ga ƴar sirɗaɗen hanyar da suka ƙirkira sai karaf idanuna akan mahaifina kwance jikin jini. A hankali jina ya fara nisa, duhu ya mamaye ganina sai ga duniya na juyamin, kafin na gama fahimtar mike faruwa har na rasa komai da ga motsin jama'ar duniya, na koma wata duniya can daban mai nisan zango da ta mutane.

Yau ake yinta gobe sai labari ne ya sake riskar rayuwata a karo na biyu, dan kuwa na sake rasa mahaifina da lilin bigesa da mai motar akori kura yayi yayinda yake ƙoƙarin tsallaka titi. Kowa ya shaida baiga fitowar baba ba balle ƙoƙarin ƙetara titin da ya yi, ƙararsa kawai sukaji tare da mugun jan birki da mai akori-kuran yayi. Hakan yasa kowa yayo kan baba, ganin hankalin mutane ya raja'a kansa ne ya bama mai akori-kuran ƙofar samun hanyar guduwa, baiko sakkoba balle ya ga halin da ya jefa mahaifina ciki da ni tilon ƴarsa. Bakin babana ni yaketa ambata har aka ɗakkosa aka maido gaban gidan, faɗi yake a kira masa Bilkisu, a kira masa ɗiyarsa dan ALLAH, sai dai abin tausayi da yankewar rabon sake haɗuwa numfashinsa na tsayawa ina isowa ƙofar gidan.
A wannan karon nafi tsintar kaina a ruɗani fiyema da rasuwar innata, banbancin da aka samu zaman wasu a cikin dangin mahaifina tare dani har akai sadakar uku.
Randa akai sadakar uku kowa ya kuma kama gabansa, babu wanda yay min tayin na bisa, sai abubuwan ɗakin masu amfani da suka tsince duk suka tafi dasu, aka barni da ga ni sai tarkacen matattun tsunmokaran iyayena da ƙwanƙwatsatstsun kwanikan cin abincinmu...............✍🏻






_Turƙashi, lallai bilkisu kin cancanci shinfiɗa dogon bayani a farkon labarinki kafin mu masu binki mu fahimceki, ko wace rayuwa kuma zata riski gobanki tunda gashi a yau ɗinki dukkan ginshiƙanki sun janye da ga rayuwarki, rayuwa kenan, lokacin da wani jin dadinta ke ruɗarsa yana baza shirme, wani rakuɓe yake a cikinta domin alfarmar mafaka kawai koda bazata buɗa masa wani filin yin rawar banjo ba😭, ALLAH ya fimu kusanci dake, ya fimu kuma sanin wace rayuwa ta dace dake, wane tanadi yay miki a gobenki harma da jibinki da zata iya zama amfanuwa da wasunki a dangi ko abokan zama, bamu saniba ko kece zaki zama *ƙwai cikin ƙaya!!* ɗin watan watarana.☹️🤦🏻‍♀️_










*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭👏🏻_**_Typing📲_*





*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!_*🧺


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_SADAUKARWA:_*
_Aunty Fareeda Gachi_
_Aunty Rahma A-Majeed_


*_Wattpad_*:- _BilynAbdull😉_


_🤣🤣😂🤣😂🤣😂Kunsan miya sakani dariyarnan kuwa? 😆wlhy kune, sam na fuskanci ba kowa yama fahimci sunan littafinnan ba, dan wasu *ƙwai cikin kaya* suke cewa🤣, 😂dan ƙari, bafa haka nake nufiba, ku kula akwai lanƙwasa a jikin *Ƙ* ɗin, sunan littafin nana *ƙwai cikin ƙaya (Thorn)*, ƙaya dai ta gona mai tsini da haɗari idan an taka kota soki mutum a ƙafa, ina fatan kun gane yanzu kam😂._

*One luv my Sweet guys🥰🥰😉*.


*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na huɗu_
*______________________________________*


*_Gidan Jawaad_*

*_Jawaad Abdul-Azez Yuseef_* ɗane da ga. zuri'ar Alhaji Yuseef Tafida.
Alhaji Yusif talaka ne mai rufin asirin ALLAH, domin kuwa manomine kuma makiyayi, duk da a birni yake rayuwarsa da iyalansa to dukkan wani sabgoginsa na ƙauyensu, acan yake nomansa da kiwo, hakan yasa hankalinsa rabuwa biyu, harma zamansa a ƙauyensu ya so ya rinjayi zaman birnin.
Matan Alhaji Yusif uku ne cif, kuma kowacce a cikinsu ALLAH ya azurtata da haihuwa, matarsa ta farko hajiya Atika yaranta shida huɗu duk maza biyu mata, sai ta biyu badiyya yaranta huɗu itama, mata uku namiji ɗaya, sai amarya Rahina ke da uku maza biyu mace ɗaya.
Zamu iya cewa a gidan Alhaji Yusif tafida akwai tsaftataccen kishi irin na matan da da suka san kansu, dan kuwa baka taɓa jinsu suna wata hayaniya a tsakaninsu, sannan kowa na da ikon tsawatarwa ɗan kowa idan yaga yayi ba dai-dai ba, so rayuwar gidan dai akwai abubuwan birgewa.
Tabbas Alhaji Yusif nason ƙauyensa sosai, sannan shi mutumne mai bautawa zuminci iya iyawa, sam bashi da matsala, amma yanada zuciya idan aka kaisa maƙura.
Ganin rayuwarsa ta ƙauye tana neman rinjayar zaman maraya sai ya yanke shawarar ɗauke ɗaya a cikin iyalansa ya maida ta can ƙauyen. Amma yana tara matan nasa ya ambata musu wannan batu duk sai sukai tsale suka dire akan sam bazama ta saɓu ba, kowacce tace babu yanda za'ai ta koma rayuwar ƙauye bayan ALLAH ya tsamota da ga can.
Abin ya matuƙar ɗaure kan Alhaji Yusif, musamman idan yay dubi da cewar duka fa daga ƙauyen ya aurosu ya kawo birnin, dan shi bai taɓa sha'awar yin aure a bariki ba, duka matansa daga gida ya aurosu, amma gashi yanzu ƙiri da muzu sunce bazasu koma zaman tushensu ba.
Da farko sai ya kwantar da murya ya shiga lallashinsu da nuna musu muhimmancin komawar wata a cikinsu can ɗin, dan babu daɗi da girmansa ace bashi da mata a inda rayuwarsa tafi ƙarfi, kullum sai dai ake kawo masa abinci da ga gidan matan ƙannensa ko ƙannensa mata.
Ai sai tamkarma ya tunzurasu ne, dan kowacce sai ta sake sama akan bijirewar farko, ya kaɗa su danbu da taliya suka nuna sam bazasu yi mubayi'a ba. Ganin bazasu lanƙwasu cikin sauƙiba ya rufe ido ruf ya banbamesu da bala'i tamkar zai cinye naman jikinsu ɗanye, duk da sun razana da fusatarsa babu wadda taji zata iya sadaukarwa ta koma ƙauye da zama. Shima takalminsa ya buga yay gaba ba tare da ya sake bi ta kansu ba.
Tsawon lokaci bai sake tado musu zancenba, duk sun saki jiki akan yabar ma zancen kenan, sai gashi rana tsaka yazo musu da maganar ƙara aurensa, kuma zai auri ɗiyar maƙwafcinsu ne Alhaji Sunusi na Abba, yarinyar da ke yawan shigowa gidan matsayin ƙawar ƴaƴansu.
Wannan lamari ya harmutsa dukkan lissafinsu da jinsu harma da ganinsu, shiko yay tsayuwar sojan badakkare a kansu kan cewar duk wadda tai masa hauka zata ƙarasa zaman turu ne a gidansu ba da igiyar aurenta ko guda ɗaya ba a kansa. Wannan shine dalilin nutsuwarsu dan dole, kowacce ta shanye bala'in da kecin ƙahon zuciyarta zuwa maƙwallato sukabi yarima akasha kiɗa dasu.
Bayan an ɗaura aure kai tsaye ɗaukar amarya maryam akai zuwa ƙauyensu Alhaji Yusif. Duk da maryam a birni ta tashi taga iyayenta, annan aka haifeta har kawo girmanta, kusanma dukkan danginsu anan suke, hakan baisa ta bijire akan bazata koma rayuwar aure a ƙauyeba, sai tayi biyayya ga mahaifanta da kuma mijinta, ta zauna lafiya cikin ƙauyen tamkarma ta saba da rayuwa a cikinsa da can, ta saki jikinta da kowa danginsa da jama'ar gari, sannan tanama mijinta biyayya sau da ƙafa, ta tsaya tsayin daka wajen taimaka masa akan dukiyarsa da yake kiwo a kanta.
Shekarar maryam ɗaya cif ta haife ɗanta namiji san kowa ƙin wanda ya rasa, bakin Alhaji Yusif har kunne dan murna, sai kace yanzune akai masa haihuwar fari, ba komai ya girmama murnar tasa ba sai biyayyar maryam a garesa da ƙyautata masan da takeyi, (kunsan zuciya nason mai ƙyautata mata).
Sosai maryam ke ganin gata fiye da ta farko a kan wannan haihuwa wajen dangin Alhaji Yusif, dan kuwa hidima suketa mata da bajinta irinta mutanen karkara, tunda aka kawo maryam garin matan Alhaji Yusif suka ɗauke ƙafa da ga zuwa garin, dama ƴaƴansu ba zuwa sukeba sosai, amma wannan haihuwa yace musu tilasne su halarci taron suna daga su har yaransu. Badan sunso ba suka shirya ana gobe suna suka nufi ƙauye, kai tsaye kowacce gidansu ta nufa maimakon gidan mai jego, hakama yaran babu wanda ya nemi inda take, dan duk haushinta sukeji, musamman ma ƙawayenta su Atika.
Itama dukda taji sunzo sai bata kulaba, dan danginta da suka cika gidan sun share mata dukkan kukanta, ga kulawa ta dangin miji da jama'ar gari.
Washe gari yaro yaci suna Abdul-Aziz. Yanda hidimar suna ta gudana ma ɓata lokacine, amma Alhmdllh komai ya tafi cikin tsari, matan Alhaji Yusif basu shigo gidan sunanba sai da dare, koda sukazo sama-sama suka gaisa da dangin maryam suka ɗauki jariri suka ƙara gaba bayan sun ajiye kayan da suka kawo.
ALLAH sarki maryam

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login