Showing 15001 words to 15190 words out of 15190 words

Chapter 6 - Daga Taimako

SADNAF   

09 Oct 2024

3022

Muhibba nurse ta lek'o tace Abdulmajeed yazo yaga jaririya matarsa ta sauka lafiya,da saurinsa ya nufi d'akin,har yana Neman yayi tuntub'e Surayya na biye dashi abaya,Gani yayi Muhibba ta kau da kanta, bata kallon inda jaririyar ke kwance,bai kawo komai aransa ba,ya nufi inda aka kwantar da jaririyar,abinda yagani ne yasa yaja da baya,jaririyar bak'a ce irin k'irin d'inan,gata katon kai ne da ita, muni iya muni wanan jaririyar ta had'a,cikin tashin hankali,ya d'ago zai yi magana,Muhibba tayi sauri ta ce yayi shiru,anan ta tuna mishi abinda Aljanar tace na zata rama,shiru yayi bai ce komai ba.



A takaice duk Wanda yaga jaririyar da Muhibba ta Haifa sai ya girgiza,ahaka aka lallaba akayi suna Muhibba ta cigaba da kula da jaririyarta Dan ita bata k'i jaririyar ba,Abdulmajeed kuwa shima haka ya ringa ririta jaririyar Dan yasan abinda ya shuka shi ya girba.



Ahaka Muhibba ta k'ara haihuwar yara hud'u amma kyawawa Zainab ce dai ta banbanta acikinsu wato ta farin, Dan muni kamar ayanka a b'oye,Abdulmajeed kuwa tunda ga lokacin ya daina wulak'anta mutane,duk wanan zafin kan babu.




Anan na kawo karshen daga taimako kuskuren Dana yi aciki Allah ya yafemin.

4
5
6
Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login