Showing 9001 words to 12000 words out of 15190 words
gudu,suna cewa aljana ce shima zai diba aguje.😂😂😂😂😂😂😂
[9/22, 12:18] Sadnaf: 🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*ðŸ˜ðŸ˜
*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l
*TRUE LIFE STORY*
🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*ðŸ˜ðŸ˜
*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l
*TRUE LIFE STORY*
Aunty Fannah kisa
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
PAGE 8
*wanan shafin naki ne ke kadai Auntyna (Aunty sis* 💞) tnx for your love and support
*Jinjinar ban girma gareku*,
*Zauren* *Adda Bena*
*MieMiebee* 👄 *Novels 2*
*Musha karatu na Ybk inasan yanda kuke comment Kuna yi ina jin dadi dafatan babu wacce ta saki fitsari awando garin dariya*
😂😂😂😂😂😂😂
Wani dake zaune a can gefe da duk abinda yake faruwa yana gani adai daita sahun ya fara lek'awa Dan yaga ko wani abun ne aciki shi yasa suke gudu, babu abinda ya gani acikin adaidaita sahun ,da gudu ya bi su Abdulmajeed,ya kamo Mai daidaita sahun da tsabar gudu kamar ya tuntsira,Mai adaidaita sahun juyowa yayi afirgice, mutumin ya tambayeshi mai ya faru suke gudu,da sauri mai adaidaita sahun ya gaya mishi yana Neman kwace rigarsa daga hanun mutumin Dan tunda ga lokacin da ya tab'a mak'ala earpiece a kunensa ya shiga band'aki yana jin waka,yaji an sharara masa mari,yake tsoron aljanu ko sunansu yaji sai ya tsorata,mutumin kwantar masa da hankali yayi yace ya kwantar da hankalinsa ya lek'a adaidaita sahu babu komai,mai adaidaita sahun mukulin adaidaita sahun ya bashi yace masa Dan Allah ya taimaka masa ya d'auko mishi adaidaita sahun shi dai tsoro yake ji.
Abdulmajeed sai da yayi nisa sosai ya tsaya gabad'aya ya gama tsorata,bus ya Tara ya hau Dan bazai iya kuma hawa adaidaita sahu ba,hankalinsa ne ya kwanta da yaga bus d'in acike,ajiyar zuciya ya ringa saukewa yana bin mutanen cikin bus d'in da kallo in banda zare ido babu abinda yake yi.
Muhibba kuwa aranar barci bai ga idonta ba dan kasa barci tayi,tunda tayi aure bata tab'a raba shimfid'a da Abdulmajeed ba,gashi yau sabida tashin hankalin da masifa da Aljanar da ta taimakawa ta sata yasa ta zo cikin kanenta ta kwanta,kewar Abdulmajeed ne yabi ya dameta tana tunanin yau ko mai yaci,tasan tunda bai zo ba,bai kuma kira awaya ba tasan bak'aramin fushi yake da ita ba,dan ya d'auka karya take yi babu wata aljanar da take tsorata ta, agogo ta duba taga k'arfe biyun dare,wayar Nafeesa ta d'auko ta kuna, tayi dailing number Abdulmajeed,ji tayi yanata ringing bai d'auka ba,ahaka ta cigaba da kiransa,sai da ta gaji Dan kan ta ta ajiye wayar,kuka ta fashe dashi tana tunanin yana ganin kiran kin d'auka yayi,sabida Fushin da yake yi da ita,Dan tasan halin Abdulmajeed ya tsani yaga ya bata umarni ta tsallake,to ya zata yi, zuwa gidan shine mafita agareta Dan in ta cigaba da zama agidan aljanar Zata iya zautar da ita, ga Abdulmajeed yaki yarda da ita, dana sani ta ringa yi na Taimaka aljanar da tayi,yanzu Surayya da ta rufe k'ofarta bata bari aljanar ta shigar mata gida ba tana can hankalinta kwance babu abinda ya raba ta da mijinta,ahaka Muhibba ta zauna tana kuka tana tunani,sai da aka fara kiraye kirayen sallah ta mik'e ta nufi band'aki Dan tayi alwala.
Abdulmajeed kuwa ana sauke shi ko canji bai tsaya k'arba ba ya nufi gidansu da sauri,a tsakar gida ya tarar da mahaifinsa mallam Isah yana shan koko da kosai,mahaifiyarsa kuma tana kitchen,Mallam Isah mik'ewa yayi da sauri da ya ga yanda Abdulmajeed ya shigo yace "Subhanallahi Abdul lafiya daga ina"? Abdulmajeed zubewa yayi a kasa yana sauke numfashi kamar Wanda yayi gudu,Hafsat Mahaifiyarsa itama lek'owa tayi tana kallonsa,Abdulmajeed bai ce komai ba ya cigaba da sauk'e ajiyar zuciya,Hafsa fitowa tayi daga kitchen d'in tace "Abdul ba tambayarka ake ba daga ina kake da sassafe nan?,ina Muhibbar? Mallam anya lafiya kuwa ka ganshi fa duk a firgice kamar Wanda aka koro" Hafsat tace tana k'ara kallan Abdulmajeed,"kai bana San Shashanci ana tambayarka lafiya kazo mana gida da sasafe ina ka baro iyalin naka?" Mallam isah yace atsawace.
" Abba aljana ce ta sako in agaba ta hanani sakat,wlh jiya ban runtsa ba,yanzu ma Dana taho sai da ta biyoni,watak'ila ma yanzu ta biyoni gidanan"
Mallam Isah da hafsa had'a baki suka yi wajen rafka sallati Mallam isah yace, "Aljana kuma bangane ba kayi min bayani sosai mai ya had'a ka da Aljana ina Muhibbar?share zufa yayi,ya fara basu labari,tundaga lokacin da Muhibba ta taimakawa Aljana ta shigar musu band'aki,zuwa lokacin da Muhibba ta tafi gidansu sabida tsorata ta da aljanar take yi,da yanda shima aljanar ta ringa tsorata shi har a adaidaita sahu,ya k'ara da "gaskiya Abba bazan iya cigaba da zaman gidanan ba Dan aljanar tana gidan,tashi zanyi daga gidan,wlh badan na ga aljanar da idona ba,na d'auka karya Muhibba take yi,Umma wlh baki ga aljanar ba, sallati Hafsa tayi tana tafa hannu tace "Ikon Allah D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO kun janyowa kanku masifa,ni Muhibbar ma nafi tausayawa abinda zai firgita namiji kamar Abdulmajeed sabida tsanin firgita da yayi rigar ma abaibai ya sako ta,lailai tashin hankalin da Muhibba tagani ba kadan bane," Mallam Isah cewa yayi "Hafsa ba dole Aljanu su ringa bibiyarsu ba,kin San irin sakacin Abdulmajeed tun Kafin yayi aure, babu irin fad'an da bana mishi,shine wasa da sallah,baya azkar yanda yaga kanensa nayi,kai tsaye zai shiga band'aki batare da yayi add'ua ba,ballantana azo gasu karatun Qurani ,yanzu da zaki tambayeshi yaushe Rabin da ya d'auko Qurani ya karanta wlh bazai iya gaya miki ba,
Abdulmajeed ne zai ga abinda ya tsorata shi amadadin yayi addua sai dai ya kurma ihu,
nan massallaci yaje bazai je ba,sai dai yayi sallar agida,ki gayamin ya aljanu baza su sako shi agaba ,duk wani Abu dazai kareshi daga sharrin aljanu ba yi yake ba,ko karya ne"? Mallam Isah yace yana kallon Abdulmajeed da ya sunkuyar da kai,Dan yasan tabbas duk maganar da mahaifinsa ya fad'a gaskiya ne,Dan Muhibba ma bata fiye sa dankwalli ba kullum gashinta a bud'e yake, tunani ya hau yi, yanzu akan wanan d'an k'aramin dalilin sai Aljana ta sako su agaba,maganar mahaifinsa ne ya katse masa tunanin da yake,Dan haka in zaka gyara halinka ka gyara,matarka ma naji ance zama take babu dankwalli Nura da yaje gidan kwanaki naji yana fad'awa mamanku,duk wata k'ofa abud'e take da aljanu zasa dame ku,da kake cewa zaka tashi kabar gidan kana da kud'in kama wani gidan ne, Dan in kana tunanin ni zan kama maka Nima nan bani da kud'i,gwara ma ka hak'ura da zancen tashi,zan sa mallamai suje suyi sauk'a agidan,kuma sai Ku daina sakaci da addua,insha Allahu zata daina tsorata Ku,gidan ya daina rabo da karatun Qurani,in bazaku iya karantawa ba kuringa kunawa, awaya,"nasiha Mallam Isah yayi mishi sosai ya bashi addu'oi,godiya yayi wa Mahaifinsa ya mik'e ya nufi d'akinsu da samarin gidan ke kwana Dan barcine a idonsa yana kwanciya ya hau tunanin babu yanda zaayi ya cigaba da zama agidan zai nemi kud'i ya kama wani gidan,da wanan tunanin barci yayi awon gaba dashi.
K'arfe hud'u na yamma ya shirya ya nufi gidansu Muhibba a machine d'in kaninsa,yana isa gidan ya samu Mallam Hashimu a k'ofar gida yana zaune shi da wani makocinsu,parking yayi ya tsuguna har kasa ya gaishe su,suka amsa,Mallam Hashimu tambayarsa ya hau yi lafiya suke ta gwada wayarsa yana ringing bai d'auka ba,sai a lokacin ya tuna wayar na gida,karya ya mishi da wayarsa fad'uwa tayi shima yana kira ba a d'aga ba,Malam Hashimu ce masa yayi jiya Muhibba tazo ta fad'a musu abinda ke faruwa dama shi yasa yake neman shi ,anan yake fad'a masa yasa ayi musu sauk'ar Qur'ani a gidan,insha Allahu aljanu zasu daina damunsu,godiya Abdulmajeed yayi mishi,Mallam Hashimu yace ya shiga ciki bari yah kira masa Muhibba,d'akin da suke zance da Muhibba kafin suyi aure ya shiga ya zauna,Muhibba da bata Dade da fitowa daga wanka ba tana zaune agaban mudubi tana so ta shafa mai Abdulmajeed ne ya fado mata arai ta kasa shafa man,tana cikin Tunanin Abdulmajeed Mallam Hashimu ya d'aga labulen d'akin yace mata taje Abdulmajeed na kiranta yana d'akin yayanta,wani irin farinciki ne ya rufe ta,ta mik'e da sauri ta zura doguwar Riga ta fesa turaren Nafeesa tayi waje,tana zuwa k'ofar d'akin gabanta ya hau fad'uwa Dan bata san ya zasu kwashe da Abdulmajeed,sallama tayi ta shiga ahankali,Abdulmajeed kuwa Dama yana Shiga ya had'e rai,Muhibba sunkuyar da kanta tayi sakamakon kallon da yake jifanta dashi,"sannu da zuwa " Muhibba race tana k'ara sunkuyar dakai,Abdulmajeed wani mugun kallo ya mata yace " Muhibba Ashe baki da hankali ni zaki yiwa karya kice min tsohuwa ce tayi bara kika bata abinci Ashe aljana kika bud'ewa k'ofa ta shigar min band'aki,"Muhibba jikinta ne yafara rawa Dan bata tab'a ganin b'acin ran Abdulmajeed haka ba,cikin rawar murya tafara magana " Dan Allah kayi hakuri nayi kuskure wlh bansan aljana na bud'ewa k'ofa ba," Dalla rufemin baki wane irin gargadi ne ban miki ba akan kwashe kwashe ai gashi nan kin janyo wa kanki D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO,Dan babu abinda ya shafeni,haka zamu koma gidan ayau duk abinda tayi miki ke kika janyowa kanki,Dan da baki bud'e mata k'ofa ba babu yanda zata shigo gidan,Surayya da ta ganta ta kulle k'ofarta kinga tana can hankalinta kwance,tunda ya fara magana hawaye ke zubo mata,"Abdul wlh bazan iya kwana agidanan ba ni nasan mai nake gani," Abdulmajeed d'aga mata hannu yayi yace " wa ya janyo?babu abinda ya dameni jiya barcina nasha lafiya lau babu komai a gidana ke da kike bud'e mata k'ofa ke kike ganinta dan haka" shiru yayi sakamakon ganin aljanar nan daya yi abayan Muhibba ayanayi na ban tsoro ta gwalalo idonta gabad'aya tana kallonsa,jikinsa ne ya hau rawa ,cikinsa yayi wani irin murd'awa ya saki tusa mai shegen d'oyi ihu ya saki yana " kiyi min rai wlh karya nake jiya ban runtsa ba wayyo Allahna" Muhibba ido ta gwalo tana kallonsa cikin tsananin mamaki Dan ta waiga bata ga komai ba,Abdulmajeed ganin Ajanar ta nufoshi yasa yayi waje dagudu,sabida gigicewar da yayi d'akinsu Muhibba ya shige ya kullo k'ofar.
[9/22, 12:18] Sadnaf: 🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*ðŸ˜ðŸ˜
*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l
*TRUE LIFE STORY*
🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*ðŸ˜ðŸ˜
*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l
*TRUE LIFE STORY*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
PAGE 9
Muhibba itama waje tayo da gudu duk tabi ta rude,kicibis suka yi da Mahaifiyarta Dan itama agigice tafito daga palon data ga shigewar Abdulmajeed abakin k'ofar palon "Muhibba lafiya kuwa mai ya faru naga Abdulmajeed ya Shiga d'akinku da gudu," "wlh umma Nima bansani mai yagani ba muna cikin magana ya fito aguje," Muhibba tace a dai dai lokacin da take kwankwansa k'ofar d'akinsu tana ",Abdul lafiya mai ya faru ne,"? Abdulmajeed da sabida tsabar tsorata da yayi dan ayau Aljanar tafi masifar bashi tsoro,Dan fitsari ya saki ajikinsa,ya had'a gumi in banda rawa babu abinda jikinsa yake,sai da Muhibba ta k'ara kwankwasa k'ofar ya tuna Ashe a gidansu muhibba yake, wani irin kunya da tsoro ne ya k'ara rufeshi,ya kalli jikinsa da ya jike da fitsari,muryar Mallam Hashimu ne ya dawo shi daga tunanin da yake Dan Maryam k'ofar gida ta tafi ta gaya mishi abinda ke faruwa,"Abdulmajeed kunya ce ta k'ara rufeshi ya kasa bud'e k'ofar Dan fararen kaya ne ajikinsa,suna ganinsa zasu San yayi fitsari"Abdulmajeed ka bud'e k'ofar mana mai ya faru ne"? Mallam Hashimu yace yana k'ara buga k'ofar,bud'e k'ofar yayi ahankali yayi waje da gudu,Mallam Hashim ya rufa mishi baya, Muhibba sallati ta saki tana " Umma na shiga uku ko dai Abdul gamo yayi"? Maryam itama bayansu tabi tana sallati Dan itama Abdulmajeed ya tsorata ta Dan ta rasa mai yasa shi gudu, Abdulmajeed na k'ok'arin hawa machine d'insa Mallam Hashimu ya rik'eshi yace" Abdulmajeed lafiyarka kuwa mai yake damunka mai ka gani daya tsorata ka haka" da sauri yace " Wlh wanan aljanar ce ta sako ni agaba duk in da nayi sai na ganta,narasa mai yasa take bibiyata,tun jiya ta hargitsani, ta hanani zaman lafiya duk da ba ni na bud'e mata k'ofa bar,na rasa yanda zanyi,"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Aljanar kagani ka gudu kenan" Mallam Hashimu yace atsorace,"eeee wlh yanzu haka ma tana gidanku,yace yana k'ok'arin Tayar da machine d'insa, Muhibba a gigice itama ta fito waje Dan gabad'aya Abdulmajeed ya rudata,hangosu da tayi da Mallam Hashimu ne yasa ta fasa k'arasawa wajensu,Abdulmajeed kuwa hango Muhibbar da yayi a k'ofar gida ne yasa ya ja machine d'insa da gudu yatafi Dan yana jin kunyar karyar da ya mata,binshi su kayi da kallo, Muhibba ta k'arasa gurin Mallam Hashimu da ya daskare a tsaye,"Baba wai mai yace ma ya tsorata shi ne"? Muhibba tace cikin tashin hankali, ajiyar zuciya Mallam Hashimu yayi yace "Muhibba kuna cikin tashin hankali ke da mijinki kuna bukatar taimako,"
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Baba wai mai yace ma ko shima aljanar ce take tsorata shi" Muhibba tace hawaye na zubo mata
"Zo mu shiga ciki Muhibba maganar bata tsayuwa bace"
Mallam Hashimu yace yana shiga ciki bayansa Muhibba tabi da saurinta Dan ta matsu taji abinda ya tsorata Abdulmajeed tsorata haka,atsakar gida suka zauna Maryam itama ta matsu taji abunda ya tsorata Abdulmajeed,Dan har d'akin da suka zauna ta lek'a bata ga komai ba,magana Mallam Hashimu ya farayi bayan ya goge gumin fuskarsa,"Maryam Abdulmajeed da Muhibba na bukatar addua Dan sun had'u da sharrin aljanu,ba iya Muhibba aljanar ke tsoratawa ba,har da Abdulmajeed,yanzu ma haka ita ta tsorata shi shi yasa kika ga ya gudu"
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" Muhibba da Maryam suka ce atare, "Baba yanzu har Abdulmajeed aljanar ke tsoratawa cemin fa yayi Jiya lafiya lau yayi barci babu abinda ya gani"
"To haka dai yace jiya bai runtsa ba duk inda yayi sai yaga aljanar" Mallam Hashimu yace yana kallon d'akin da suka zauna Dan gani yake kamar aljanar tana ciki,
"Yanzu mallam mai abin yi Dan bamu ga ta zama ba"
"Ai yanzu nan zanje insamu Mallam Isah muyi magana Dan dole sai ansamu mallamai sun taya mu da addua,Allah ya rabasu da sharrin aljanar idan baha ka ba,haka zata cigaba da bibiyarsu Dan Allah dubi yanda Abdulmajeed ya firgice,dole Muhibba ta dawo gida,Dan abinda zai firgita irin Abdulmajeed ba k'aramin abu bane,
Mallam Hashimu Sunan Muhibba ya kira dake ta risgar kuka yace "Muhibba duk yanda akayi har yanzu kina nan da jin wanan wake waken Dana hanaki,kina zama babu dankwalli akanki,kina shiga band'aki babu addua abakinki,Dan matsawar kina nan da wanan halin Dana sanki dashi dole aljanu su dameki" Muhibba d'agowa tayi da Sauri tana kallon Mallam Hashimu Dan duk abinda ya fad'a gaskiya ne Dan hasali ma in zata Shiga band'aki da wak'a take shiga,wayarta kuwa kullum cikin rashin chajin chaji yake sabida jin kid'a,ita da dankwalli kuwa dama sai dai in zata je unguwa,itama tunani ta hau yi yanzu akan wayanan 'yan dalilan sai aljana ta sako ta agaba,bata ga arna dake yawo ba dankwalli ga Karin gashi da suke da chineke suke Shiga band'aki su fito da chineke sai ita aljanar zata takurawa,ita bata yarda akan haka Aljana ke takura mata ba,To Abdulmajeed da ta takura wa fa shi kidan yake ji ko dankwalli shima zai sa ya d'aura kansa,sam bata yarda wanan dalilin ne yasa aljanar take bibiyarsu ba,mugunta ce kawai,Nasiha shima Mallam Hashimu yayi mata na inta San duk abinda ya zayyano tana yi to ta daina Dan duk hanyo yi ne da aljanu zasu iya takura mutum.
B'angaren Abdulmajeed kuwa yana zuwa gida ba zarce ko Ina ba sai band'aki Dan Allah Allah yake ya k'araso gida,sai da ya samu Minti goma aband'aki kafin ya fito,wajen Mahaifiyarsa ya nufa dake Palo a zaune tana kallo,,sallamar da ya yayi ta amsa ta zuba mishi ido har ya zauna,ganin shi tayi awani hargitse, jiran tace " Abdulmajeed lafiya kuwa naganka haka yasu Muhibbar,"?
"Umma ina fa lafiya Aljana ta sako ni agaba na rasa mai nayi mata,yanzu ma da naje gidansu Muhibba sai da ta biyoni,bansan mai nayi mata ba,ni bani na bud'e mata k'ofa ba amma ni ta sako agaba, yanzu a haka zan na fita tana tsorata ni sai dai kawai aga ina gudu,sai kace mahaukaci Dan babu Wanda yake ganinta sai ni kadai"',Abdulmajeed yace cikin tsanin damuwa da tashin hankali,Hafsa shiru tayi ta kasa Magana Dan abun yanzu ya wuce tunaninta,to wai mai yasa aljanar ta daina bibiyar Muhibba ta koma tana Bibiyar Abdulmajeed,kwantar masa da hankali tayi tace ya bari Abbansa ya dawo zasu nemi mallami suyi mishi bayanin abinda ke faruwa.
Abu kamar wasa ya zama gaske,Dan babu dama Abdulmajeed yafita sai anga ya dawo da gudu,Dan Duk inda yayi sai yaga aljanar,dai dai da makaranta da ya shiga Dan ya koyar da dalibai sai da ta bi yo shi,yana tsaka da koyar da Maths ya hangota acikin dalibai wanan Karin a sifar yara ta bayyana,Abdulmajeed bai San lokacin da ya wurgar da chalk d'in hanunsa yasa gudu ba,daliban kuwa ganin Mallaminsu ya diba aguje yasa suma suka rufa mishi baya, makaranta tuni ta hautsine dalibai suka ringa tik'ar gudu a bakin titi,Jamaar gari hankalinsu ya tashi da su ka ga yanda dalibai da mallamai ke zuba gudu a bakin titi,Abdulmajeed da k'yar ya k'arasa gida, yana shiga gidan yaga aljanar abakin k'ofa a tsaye,ja da baya ya fara yi yana " wai mai nayi miki kike bibiyata?,mai kikeso awajena? Mai yasa kike