Showing 6001 words to 9000 words out of 13059 words
yace "Kai
yaro! Yanzu tunda makamanmu sun gaza yanzu sai mu fidda sharadi,
WAHASHINFALA yace wane sharadi? SA' ADUNUJJANJI yace sharadin shine
yanzu zamuyi kokawa nida kai duk wanda ya kada wani sau uku to shi ya cinye
wannan gasar, idan kai ka kadani sau uku to kai ka cinye wannan gasa sai kayi yanda
kakeso dani, haka zalika idan ni na kadakai sau uku to sai nayi yanda nakeso dakai.
Koda WAHASHINFALA yaji haka sai ya yarda da wannan sharadin, suka fara
kokawa kici-kici, can sai SA'ADUNUJJANJI yayi wuf! Ya suri WAHASHINFALA
ya daga sama zai fyada da kasa, kawai sai WAHASHINFALA ya Kama kunnen
SA'ADUNUJJANJI ya murda cikin ikon Allah sai ga SA'ADUNUJJANJI ya fadi
kasa tim!.
Haka dai WAHASHINFALA yayi ta kada SA'ADUNUJJANJI har sau
uku, da SA'ADUNUJJANJI yaga haka sai yace yaro kayi nasara aikata abinda
kakeso dani ya durkusa bisa gwiywoyinsa.
Da WAHASHINFALA yaga haka sai ya
dauko gariyonsa yayi niyyar sare kansa, da SA'ADUNUJJANJI yaga haka sai yace
yaro amman da zaka kyaleni, da raina, ka kuma riqeni na zama bawanka domin kila
wata rana zan maka amfani.
Da WAHASHINFALA yaji haka sai ya ajiye wannan
gariyon yace gaskiya ne na yarda da maganarka.
SA'ADUNUJJANJI da kaf yaransa suka jinjina ga WAHASHINFALA sukace
"Gaisuwa gareka ya shugabanmu" anan suka kwana.
Da gari ya waye
SA'ADUNUJJANJI da yaransa suka zo gurin WAHASHINFALA suka kwashi
gaisuwa Sannan suka zauna daga gefen WAHASHINFALA.
WAHASHINFALA
yace da SA' ADUNUJJANJI da mutanen sa to ai saiku tashi mu tafi kasar DUWAR
domin kuwa nasan Sarki AFARAU yanacan yaba jirana.
Nan da nan SA'ADUNUJJANJI suka dora wa giwayensu sirdi, shi kuma
WAHASHINFALA da SHAMATU suka haye kan dawakansu suka kamo kan
hanyarsu ta dawowa kasar DUWAR.
Bayan sun samu Kamar kwanaki uku suna
tafiya sai suka fara hango katangar birnin DUWAR, anan sai shamatu ta rigasu shiga
cikin birnin dankada a gane cewar tare suke, takoma gida ba tare da wani ya ganta ba.
A wannan lokacin kuma sai akayi sa'a boka SAKARAJUNA yace da Sarki
AFARA'U cikin gatse zomu je bayan gari muga ko wannan yaron zai dawo, Sarki,
Waziri da sauran fadawa suka fito bayan gari suna diban hanya.
Can sai suka hango
WAHASHINFALA ga kuma SA'ADUNUJJAN.JI da yaran sa bisa giwaye, "kagani
ko gashinan abinda kaja mana kasa wannan yaron ya tsokano mana
SA'ADUNUJJANJI, ya matsa mashi ya sanar dashi cewa mu muka turo shi, gashinan
sun sakoshi a gaba suzo su halakamu".
Koda jin haka sai Sarki, boka da jama'ar gari
suka ruga da gudu cikin gari suka rurrufe kofofin gari, da suka karaso sai
WAHASHINFALA yasa daya daga cikin yaran nan ya bubbuga kofar amman ba'a
bude ba.
Koda WAHASHINFALA yaga haka sai yayi tsawa ya umarci
SA'ADUNUJJANJI daya karya kofar birnin.
Nan da nan SA'ADUNUJJANJI yayi
wa toron giwarsa qaimi ya bangaji kofar garin ta karye, suka kutsa kai izuwa cikin
MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
littafi na daya 1
kashi na daya 5
fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Mr Hausa Ebooks
Da WAHASHINFALA yaga haka sai yace "Baba yanaji kace dani Sarki bayan ba
haka bane, kuma ka kirani da wani suna wai MAALIKUS-SAIF bayan ni sunana
WAHASHINFALA.
Tsoho ya dubeshi yayi murmushi yace "Katahone daga garin
DUWAR kuma yau kwananka sittin kana tafiya kafin kazo nan, kuma
WAHASHINFALA ba sunanka bane sunan ka wanda Allah ya nufa shine
MAALIKUS-SAIF, mahaifinka kuwa shine Sarki ZIYAZINUN mai mulkin kasar
HAMRA'U YAMEN wanda ya rasu, kuma kaine wanda adduar Annabi Nuhu zata
fada a kansa zai samu mulkin duniya baki daya, ya kuma tambayarsa ya
MAALIKUS-SAIF yanzu mai kake bautawa? Ya amsa masa da cewa "Eh nidai naga
mutanen nahiyar mu suna bautawa rana da wata ne, amman ni bana bauta masu sabo
da nasan Allah ne ya halicceni saidai ban samu Wanda zai koya mani yadda zan
bauta mashi bashiyasa ni ban bauta wa komai Tsohon yace "Ka dogara ga Allah
yanzu zan musuluntar da kai. MAALIKUS-SAIF yace na dogara ga Allah, Tsohon
yace kace na gasgata babu abin bauta sai Allah kuma na gasgata da Annabi
Muhammadu Annabi da zaizo a karshen zamani da Annabin wannan zamanin Annabi
Ibarahim alaihissasatu wassalam.
MAALIKUS-SAIF ya maimaita shahada kamar
yadda Tsohon nan ya fada masa. Bayan ya gama sai Tsoho yace masa ni sunana
Shehu ZAJJADA, yanzu tunda ka musulunta ka zama dan uwana kuma ya zama dole
na taimakeka nasan ka fito neman littafin kogin NIL zan fada maka inda yake amman
inaso kafin ka tafi ka kwana a nan domin inason sanar dakai hanyoyin bautar Allah.
Shehu ZAJJADA ya koya wa MAALIKUS-SAIF alwala da zikirin Allah suka zauna
suna ta zikiri har cikin dare sannan shehu ZAJJADA ya mike ya daga hannu ya roki
Allah ya kawo masu abinci daga arzikinsa.
Nan da nan sai ga abinci da abubuwan sha
iri-iri a gabansu, MAALIKUS-SAIF ya cika da dunbin mamakin ganin wannan
abinci saboda baiga yadda ya kawoshi ba. Shehun ya umarceshi da yaci abinci
amman kafin ya fara ci yace Bismillah.
MAALIKUS-SAIF ya fadi haka ya fara dibar
gara abinka da maijin yunwa. Haka yayita ci har saida yaji ya koshi sannan ya sha
ruwa, sannan ya kwanta ya huta.
Kwanciyarshi keda wuya bacci ya kwasheshi, shi
kuma Shehun ya ci gaba da zikirinsa.
Can da gari ya waye Shehun ya tada MAALIKUS-SAIF yayi masa wa'azi sannan
ya kuma cewa ka dogara ga Allah, zaka kubuta da duk wani yanayi da ka samu
kanka.
Sannan ya zagaya da shi bayan wannan dutsen ya nuna masa yace yanzu
kabar dokinka anan domin baya da amfanin tafiyar da zakayi dashi, ya nuna masa
yace kabi gefen kogin nan kayi dama zakayi tafiyar kwana uku zakaga wani fili,
bayan ka wuceshi zaka kuma ganin wani kogin mai matukar girma dan girmansa
babu iyaka, to saika tsaya a nan. Akwai wata dabba mai suna HATSHA.
Ita wannan
dabba tunda Allah ya halicceta idan rana ta fito daga gabas tana daga tsakiyar wannan
kogin sai tayita tsalle wai sai ta kamo rana, idan rana ta tsaya daidai a sama sai
bakinciki ya kamata, sai ta fito da kanta daga bangaren gabas tayita turmutsa kanta a
cikin yashi dan hushi, haka kuma idan rana ta koma gabas sai tayita tsalle da niyyar
ta kamota har rana ta fadi, idan ta fadi nan ma sai ta fito da kanta a bangaren yamma
ta rinka turmutsa kanta a yashi nan ma dan haushi.
To idan kaga wannan dabba tana
tumurmusa kanta a cikin wannan yashi to kar kaji tsoro ka kana gashin wuyan
wannan dabbar ka dafeta, bazataji komai ba saboda girmanta, kai koda cikin idanunta
zaka shiga bazataji komai ba. Ka zauna kana makale a kanta har ta maida kanta
yamma, bayan ka sauka zakaga wani mutum, to ta dalilin wannan mutumin zaka
samu wannan littafin.
Daya gama wannan bayanin sai MAALIKUS-SAIF yayi
godiya Sannan yabi wannan hanyar da Shehun ya nuna masa, ya shafe kwana uku
yana wannan tafiyar har ya isa wannan filin da Shehun ya fada masa....
Anan zan dakata
Zamu cigaba zuwa Gobe Ana yin comment yan uwa
MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN
littafi na daya 1
part 6
post by Shuraih 99%
.
Isar sa keda wuya kuwa yaga wannan dabbar tanata tumurmusa kanta a cikin yashi
kamar dai yadda Shehun ya sanar dashi.
Nan da nan sai yayi maza ya dane kanta har
rana ta fadi,takai bakin gabar daga bangaren yamma, koda MAALIKUS-SAIF yaga
haka sai ya fado daga kanta ji kake tik!. Ya tashi ya fara tafiya.
Can yana cikin yafiya sai yaga wani mahayin doki a sukwane ya yi yo kanshi, koda
mahayin yazo gab da MAALIKUS-SAIF da niyyar bankeshi sai MAALIKUS-SAIF
yayi sauri ya banke dokin, haka suka rinka yi har sau shidda ko da mahayin dokinnan
yaga haka sai ya zare takobinsa ya kaiwa MAALIKUS-SAIF Sara da suka shi kuma
yana gocewa, hardai ya harzuqa MAALIKUS-SAIF, MAALIKUS-SAIF ya dubi
mayin sai yace kaidai Allah wadaranka ragon banza, ai ba haka ake gwanimtar yaki
ba, haka kawai mutum yana tafiya ka tasar masa dan ganin yana kasa Kai kana doki,
kuma ga makami a hannunka, bari in nuna maka yadda sadaukai suke nasu sha'anin.
MAALIKUS-SAIF yayi wuf! Ya damki wuyan dokinnan da hannun dama, ya
kuma sake yin wif! Ya shaqo Wuyan mahayin da hannun hagu ya daga sama ya
jinjina shi sannan ya saukeshi a hankalı ya ce "Kaga yadda sadaukai suke nasu
lamarin".
Da ganin haka sai wannan mahayim dokin ya sakko daga bisa dokinsa ya tsaya
gaban MAALIKUS-SAIF ya yaye kyallen dake rufe a fuskarshi koda ya yaye sai
MAALIKUS-SAIF yaga shema mace ce ba namiji ba ne ya dubeta yaga kyakkyawa
ce, sai tace barka da zuwa MAALIKUS-SAIF Dan ZIYAZINUN koda yaji ta kira
sunansa sai yace kekuwa yaya akayi har kika san suna na? bani labari mana.
Yarinya ta fara da cewa "Suna na DAMATU, na samu labarin kane a wajen
mahaifiyata wacce itace Sarauniyar bokayen birni KAIMARA, sunan ta Bokanya
AKILA.
Wata rana muna zaune da ita sai nace mata ta buga mani qasa taga waye
wanda zai aureni, sai ta amsa mani da cewar Wanda zai aureki sunansa MAALIKUS-
SAIF na ainahi amman yanzu ana kiransa da suna WAHASHINFALA, kuna asalinsa
dan wani Sarki ne mai suna ZIYAZINUN Sarkin kasar hamra'u yemen amman yanzu yana
qasar wani sarki mai suna AFARA'U, bayan an kwana biyu, sai tace mani shi
wannan wanda zaki aura ya nemi auran wata yar Sarki aka nemi ya kawo kan wani
dan fashi kuma gashi can ya dawo.
To a wannan lokaci sai na rinka damunta da
yaushe zai zo garin nan? Sai ta rinka ce mani ai ya kusa Zuwa, sai yau kuma dana
sake tamayarta sai tace dani inyu maza ai gakacan ma ka iso, amman ta fada mani
cewa inyi qoqarin yaqarka, indan naga baka da niyyar cutar dani sannan ka kama
wuyan dokina sannan ya dagani daga ni har dokin, sannan ya saukemu a hankali to
Wannan shine wanda zan aura, saboda haka kaji na kira sunanka kada kayi mamaki.
Koda MAALIKUS-SAIF yaji wannan yarinya ta fadi wadannan batutuwa a kansa sai
ya gasgata zancenta, amman a fili sai yace da ita "Ke kuwa wannan da qaryar tsiya
kike, sannan kin iya shirya batu, domin wannan mutumin da ki ke fada to ni ba ni
bane, kedai kawai kinyi niyyar ki yaqeni kikaga babu nasara shine kika shirya
wannan zantuka".
Koda 'DAMATU taji haka sai tayi murmushi sannan tace "Daman
uwata ta fada mani cewa kona fada maka bazaka gasgata ba, kuma kazo wannan qasa
tamu domin neman littafin tarihin NIL, kuma babata itace zata taimaka maka ka
dauko wannan littafin.
Tana gama wannan bayani sai ta yaye lullubin dake a fuskarta.
MAALIKUS-SAIF ya dubeta ido cikin ido yace yanzu ina babar taki take? Tace tana
gida, yace to mu tafi izuwa gareta.
Sai DAMATU tace "A'a ai a kaidar wannan garin bako baya shiga, domin kuwa tarihi ya nuna wa mutanen wannan garin cewa wani
bako ne zai zo ya sace shi wannan littafin tarihin NIL wanda ka fito nema, su kuma
wadannan mutanen tun kaka da kakanni wannan littafin shine abin bautarsu, tun
lokacin da suka samu labarin cewa wani bako ne zai zo ya sace wannan littafin sai
suka tsafe garin, suka sana' anta wani gunki mai suna GAMMAZI wanda duk lokacin
da bako ya shigo zai dinga îhu yana Ga... Bako! Ga Bako! Daga nan sai a kama
bakon a yankashi wannan dalilin ne yasa bako baya shiga, amman duk da haka,
babata ta fada mani cewa idan kazo qofofin shiga garinmu ka lissafa qofa ta tara sai
ka duba zakaga wata bishiya a kusa da wannan qofar zakaga akwatu ka shiga ciki
sannan ka girgiza igiyar sai mu jawo dakai daga cikin kwatun mu shiga dakai cikin
garin.
Koda DAMATU ta gama bashi wannan labarin sai ta haye dokinta ta tunkari
qofar birnin nasu.
Shi kuwa MAALIKUS-SAIF sai ya dinga bin sawun dokinta har ya fara hango
katangar birnin KAIMARA.
Daga nan sai ya juya bangaren gabas ya fara qirga
qofofin shiga garin koda ya qirga ta tara, da ya hango kofa ta goma sai ya dosheta,
Kamar yadda 'DAMATU ta fada masa, to daya isa bakin qofar nan sai ya boye ajikin
wannan bishiyar da yake duhun dare ne ba wanda zai iya ganinsa, can yana tsaye
jikin bishiyar nan sai yaga ana sako akwatu daga kan katangar, koda ya sakko qasa
sai yaje ya shiga cikin wannan akwatu, sannan yaja murfin akwatin ya rufe ya girgiza
igiyar sau uku.
Su kuma can bokanyanya AKILA da DAMATU da sukaji an girgiza
wannan igiyar sau uku sai suka jawoshi suka shiga dashi cikin birnin.
Da suka isa gida, sai bokanya AKILA ta kawo masa abinci da ruwan sha, bayan ya
gama sai ya kwanta, bayan ya huta sosai bokanya AKILA tace barka da zuwa
MAALIKUS-SAIF Dan ZIYAZINUN.MAALIKUS-SAIF ya amsa mata da cewa
yawwa, kazo wannan qasa tamu domin neman littafin tarihin kogin NIL, kuma nice
zan taimakeka saka makon auren yata da zakayi.
Koda MAALIKUS-SAIF yaji haka
sai yace wai meye amfanin wannan littafin da har jama'ar wannan gari suke bashi
tsaro sosai kuma har suke bauta mashi? bokanya AKILA tace shi wannan littafin a
cikinsa ne akayi bayani yadda za'a zuqo kogin NIL, kuma duk kasar data mallaki
wannan littafin to fari na rashin ruwa bazata samesu ba, kuma qasar zata samu arziki
da yalwa na albarkacin qasa, haka kuma duk mutumin da wannan littafin ya zamto a
hannun sa to shi zai mallaki duniya.
Saboda haka tin iyaye da kakanni mutanen
wannan qasa suke girmamashi kuma suke bautamashi.
Kuma tarihi ya nuna cewa
wani baqo zaizo ya dauke shi wannan littafin, saboda haka ake bawa wannan littafin
kyakkyawan tsaro.
A wannan lokaci sai mutanen birnin KAIMARA sukaji gunki
GAMMAZI yana cewa "Yaku mutane birnin KAIMARA ga bako ya shigo maku
wannan birn?", ya fadi haka har sau uku nan da nan Sarki.. Ya fito shida tawagarsa
aka rinka bincike lungu-lungu, sako-sako har dare yayi amman basuga wannan bakon
ba.
A can cikin gidan bokanyanya AKILA kuwa, MAALIKUS-SAIF yaji hayaniya ta
yawaita sai yace da bokanya AKILA "Amman dai bazasu shigo nan ba ko?", sai bokanyanya
tace "Kada ka damu bazasu shigo nan ba ya kuma tambayarta yace meyasa kikace
bazasu shigo ba? bokanyanya tace ai duk manyan bokayen Sarki KABRUNU su dari
uku da cittin (360) nice shugabarsu, a karkashina suke kuma su waddan nan bokaye
sune suke tsaron wannan littafi dan haka ba yadda za' ayi su shigo wannan gida.
MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN
littafi na daya 1
part 7
post by Shuraih 99%
.
Da gari ya waye, Bokanya AKILA ta aika DAMATU gidan makwaftansu da yake
masunci ne ta siya masu wani katon kifi, da DAMATU ta kawo sai Bokanya AKILA
ta yanka kifin ta kwashe duka kayan cikin kifin ta saka qafafun MAALIKUS-SAIF a
cikin kifin ta mayar da dinke cikin kifin; sannan ta dauko wani qaton tsutsu ta daura
masa a wuya, sannan ta daura mashi igiya a girji, Sannan ta sakashu cikin rijiya, tace
kada ka damu nayi maka wannan ne domin na bata hankalin bokaye ma' abota tsafi da
Sarki zai sasu bincenka.
Bokanya AKILA ta shirya ta tafi fada da zuwanta fada ta
iske fada ta cika makil, ta fadi gaban Sarki tayi gaisuwa takoma mazauninta ta zauna.
Zaman ta keda wuya sai Sarki KAMARUNU yace da ita daman ke muke jira, domin
jiya GAMMAZI yayi mana kuwwa cewa wani bako ya shigo mana birni, to inaso ki
sa yaranki su binciko mana inda wannan bako yake.
Nan da nan Bokanya AKILA ta
umarci wadannan bokayen dari uku da cittin (360) dasu buncika qasa su gamo inda
wannan baqon yake.
Bokaye suka dukufa suka zana alkalaman duba bisa rairayi suka
shiga aiki, haka sukayita yu har tsawon wani lokaci, su zana su goge su sake zanawa
su kuma gogewa su shafe... Can sai suka tsaya da wannan duban sukace munga
wannan baqon.
Koda Sarki KAMARUNU yaji wannan bokayen sunce haka sai yayi
farat! Yace a ina kuka ganshi maza ku gaya mani.
Can sukace shidai wannan bako
gashi mun ganshi cikin duhu kuma kifi ya hadiyeshi, ga kuma wani tsuntsu ya
ratayoshi, da sarki yaji haka sai yace wannan wace iriyar maganar banza ce kuke fada
haka mara ma'ana.
Sai Bokanya AKILA tayi farat ta rufesu da fada tace na fada
maku cewa ku daina cin abinci da yawa domin yana hanaku kuyi aikin ku yanda ya
kamata amman kunqiji ai ga irinta nan yanzu kun binciko wa Sarki shirme.
Koda
Sarki yaji haka sai ya fusata yasa hauni ya sare wa Bokaye biyar kawuna, sannan aka
tashi daga fadanci.
Koda Bokanya AKILA ta koma gida sai ta fito da MAALIKUS-
SAIF daga cikin rijiya ta fito dashi daga cikin kifin sannan ta kwance mashi tsutsun
data daura masa, kana ta kwashe duk abinda ya wakana a fada ta fada mashi.
MAALIKUS-SAIF yace lallai kina da yawan hikima, badan kinyu mani haka ba da
da tuni bokayen nan sun gano ni, haka sukayita fira da Bokanya AKILA tare da yarta
DAMATU har dare ya raba sannan suka kwanta bacci.
Da gari ya waye a rana ta biyu, Bokanya AKLA ta samo wata barewa ta daura
mata fuka-fukan tsuntsu, sannan ta sa MAALIKUS-SAIF ya durkusa
gaban
barewar ta daura mashi ita ta kuma daura wata igiyar ta raba qafafun barewa da qasa,
ta shirya ta yafi fada.
Da zuwan ta fada sarki ya umarce ta data sa bokayen nan da su
buga gasa su nemo inda baqo yake.
Nan da nan bokayen nan suka tsundum aikı, can
sai bokayen nan suka dago sukace sun ganshi.
Cike da zumudi Sarki ya tambayesu
yana ina? suka kada baki sukace ai gashi can wata barewa ta tashi sama dashi, nan da
nan Sarki ranshi ya qara baci yace me yasa kuke kawo mani wasa ne? Kun tabajin
ance yau ga barewa da fuka-fukai?, wannan ai rainin hankali ne yasa aka kuma yanka
bokaye biyar nan dai fada ta tashi.
Bokanya AKILA ta tafi gida tana dariya, taje ta kwance MAALIKUS-SAIF suka
cigaba da hira.
A rana ta uku Bokanya AKLA ta samo wata babbar tasa, ta yanka wata dabba ta
juye jinin a cikin wannan tasar, ta kuma samun wata tasar da dora a cikin tasar da ta
zuba jinin, Sannan ta umarci MAALIKUS-SAIF daya shiga cikin tasarnan zauna,
bayan ya shiga ya zauna.
Sai ta kama hanya ta nufi fada, isarta keda wuya ta umarci
bokayen dake karkashinta akan su fara aiki. Nan suka dukufa, bayan wani dan lokaci
suka dago sukace munga wannan baqon a cikin wani kogi na jini, sannan banda
wannan kogin da yake ciki akwai wani kogin wanda shi babu komai a cikinsa, jin
haka sarki ranshi ya qara baci ya umarci hauni daya kara sare kawunan bokaye
goma, sannan yace da bokanya AKILA ke ya kamata ki duba mana inda wannan
baqon yake tunda su sun kasa,
bokanua AKILA tace to tunda yau saura kwana biyar
bikin mu na shekara to a ranar zan kawo maka wannan baqo, koda jin haka sai fuskar
Sarki ta fadada da murshi a haka aka tashi daga fada.
Bayan kwana biyar yaune Bokanya AKLA tayiwa Sarki KAMARUNU alqawarin
kawo masa baqon daya shigo wannan gari nasu. Tunda sanyin safiya MAALIKUUS-
SAIF ya fara jin hayaniyar mutanen wannan gari, cikin firci ya tashi yace mekuma
yake faruwa ne tace ai na manta ban fada maka ba yaune muke bikin shekarar mu
kuma a cikin dakin da wannan littafin yake anan muke bikinmu, saboda haka kayi
zamanka acikin gida nida hannuna zan kawo maka