Showing 6001 words to 9000 words out of 13895 words

Chapter 3 - KIN CUCE NI Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

1416

Gidan.




_____
A kwana a tashi babu wuya wurin mai duka. A Ranar wata Laraba ce misalin ƙarfe sha ɗaya na safe aka ɗaura auren Malam Dauda Mai Allo da Amaryarsa Marka lakadan ba ajalan ba.


An yi shagali kamar ba gobe zuwa dare Amarya da tawagar ta waɗan da mafiya yawa 'yan bariki ne suka iso gidan Amarya ta tare lafiya tare da Yarinyar ta Iyami sai fatan zaman lafiya.



Wata ɗaya da Bikin zuwa lokacin har cikin Aisha ya fita a watan haihuwa amma Shiru kakeji kamar malam yaci shirwa.


A yammacin wata Ranar Juma'a ce Aisha ta haifo santalelan Yaron ta fari sol mai kama da uban sa a haske amma Komai na mahaifiyarsa ya ɗauko har Dogon hancin haske ne kawai na ubansa yaro ya zo duniya cikin ƙoshin lafiya haka ma A'isha lafiyar Allah ta haihu. Sai dai me??.


Cikin dare ta fara zubar da jini sosai abin da ya ɗaurewa mutane kai tasha wahala sosai domin kuwa ba ƙaramin jini ta zubar ba ko kafin safiya Allah Ubangiji da ya fi mu son ta da ƙaunarta ya amsa abin sa A'isha ta tafi gidan gaskiya ta bar jaririnta.


Wannan rasuwa na A'isha ba ƙaramin Girgiza al'umma ya yi ba musanman ma 'yar uwarta Salamatu da mahaifiyar su Hajiya ba ƙaramin bugun su mutuwar tayi ba balle kuma uwa uba Mijinta Abdulyasar kusan susucewa za'ace ya yi kusan ƙaramin hauka a lokacin domin kuwa har aka yi bakwai na Aisha bai dawo daidai ba har sai da aka yi arba'in ne ma sannan ya fara magana. Yayin da Salamatu ta ci gaba da kula da yaro da yaci suna Aryaan bayan tataburza aka kwasa tsakaninta da Dangin ubansa kafin yaron ya dawo hannunta....✍️


*KIN CUCE NI*




_Story And Writing_


_By_



(Oum Yasmeen)
And
*_Khadeejarth Sabi'u Yahyah Kaduna_*
(Nainarh KD)_

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k


*Tambas rayuwa komai na rayuwa me wuce wane ya Ubangiji ka bamu iƙon aikata dai dai arayuwar mu Allah ya jiƙan ki aneesa Allah yasa kin huta wannan page sadakar wace agare ki nayi rashin yar uwa bazan taɓa iya samin madadin ki ba anee wanda ya fimu sonki ya amshe ki Allah yasa Allah janna CE nakomar ki*





*Ep 7*






Nanfa adamu mijin salamatu yayi tsalle ya dure yace


"Be yarda ta dauki wani ɗaba inku wa ki ka yarda ki ka dauka shinkafa wannan silli ɗaya be yarda a bashi ba ke Ruwa maƙwarwa ɗaya banyar da ki bashi ya shaba in har nawa ne domin bani ne a hakku na in ciyar da shi ba ,


Kuka tasa ta fyece majina tace



"Na yarda da duk abin da zaka shinfiɗamin inde zaka barni in ruƙe Aryan Zan yiwa yaru uwata halatci,


Malin malin ya buɗa yace



"Owo miki har yayi gaba ya dawo ya ce


"Yauwa ƙarkiji a gari kice ban miki a dalciba gobe za a ɗauramin aure hhhh aikinsan shi aure kamar jahadi ne musamman ko ka auri kilaki ko mara gata tasana diyar haka sai Allah yayi maka gafara a'a bawe gajiya nayi da baki kina ci ba ba haihuwa sai dai aimin kashi a shatda (masai) inkira me yasa ya kwashe min yasa kafa ya fita ,


Kuka salmatu tasa ta rungume aryan ganin irin ruƙon da tayi mai yaron yasa kuka sausauta ruƙon tayi ta goyashi ta fita ta ɗeɓo ruwa a fanfon kusa da gidan ta ajiyewa tayi kuɗi ta ɗaga langarta ta ɗauko ta fita ta siyo icce lufuf aryan yayi a bayan ta hura huta tayi ta ɗora ruwan wankansa wan tayi mai haka rayuwa ta cigaba da tafiya adamu yayi sabon aure yanzu ba ko da yaushe yake bawa salamatu abinci ba duk dan aryan ya rayu ba sana'ar da batayi ba


Jinsa take tamkar yaya indo bayan auran hansatu da wata daya Allah ya bata ciki kar kuzo kuga murna harta dangin mijinta sai su ɗinga ya da mata da habaici suke ko a fuska ba ta damu ba yau haka ta shirya bayan ta gama surfe zata gida shi kansa mahaifin aryan yawa an kaudamai da hankalinsa daga kan yaron baya zuwa gunsa yana dashi dai dai da sabulu be taɓa kawo mai ba tafiya take aƙafa har ta isa unguwar su a bakin ƙofar gida ta tarda yaya dan juma yana zaune yana al'wala da sauri ya tashi ya toƙare ƙofar gidan ya ɗauki wani sanda yace



"Yasin kika matso nan sai na shemeki haka ƙurum ki ɗinga zuwa kina cinye mana abinci Ni kai na nida matata be wada cemu ba ke kizo keda shirgegen ɗanki me ƙaton kai kuci da idanuwansa yawa mujiya maza koma inda kika fito,


Kuku salamatu ta tace



"Yanzu yaya in duniya ta juyan baya bantaɓa tunanin kai zakai min haka ba yanzu yaron nan ɗafa marigaiyane fa,


Tsaki yaja yace


"A to yanzu dan marayane me yahana ubansa ruƙe shi ke wallahi fa ki kiyaye ni kar inyi ƙuliƙulin kubura da ke ?,


juyawa tayi ta koma bata ce mai ƙala ba tafiya take kamar zata waɗi abubuwa summata yawa tana komawa gida ta tarar an kwashe mata kaya an mayar da shi ƙaramin ɗaki wai amarya yau za a kawo mai sosai ta shiga mamaki amma ganin hansatu tana ta shiga tana fita tana turo ciki bata kulata ba tasan neman magana take akanta malam ya dawo ya daketa akan hansatu sauko da aryan tayi yaron yayi wayo sosai jikin sa taji zafi da alama awon haƙuri ya fara kwanciya yayi a cinyar ta taɓa shi tayi taji jikinsa ya saki gaban tane ya waɗi ta ɗauke shi ta goya ko motsi bayayi asibiti ta kaici cikin gaggawa akan amsheshi wata allura aka rubuta mata me tsada ce zata kai dubu goma aikuwa bata da zaɓi sai ta tafi gidan su abdulyasar a kafa ta tafi tana kuka ba kuɗin hawa mota domin ance tayi sauri ta kawo ƙar jijjigar da yake ta taɓa mai ƙwaƙwalwa da ƙƴar me gadin ya barta sai da tayi zaman jiran abdulyasar can sai ga motarsa ta shigo cikin sauri ta tashi ta isa gunsa wata mace ce tafito kamar balarabiya ga uban ciki a ƙƴar take tafiya cikin sauri tace


"Abdulyasar ,


Cikin sauri ya juyo sai da ya ƙura mata ido sannan ya gane ko wace huyanta tamkar zaka zura hannu ka ɗauko ƙashi saboda rama yace


"Salamatu yakike?,


miƙo mai ta ƙarda tayi tace



"Lafiya lau abdulyasar aryan babu lafiya ance in maza in kawo ta ƙar ta taɓa mai ƙwaƙwalwa,


Ƙansane ya sara masa da sauri ya dafe yace


"Ki haƙuri Wallahi yanzu nan na dawo daga asibiti bani da shi na biya dubu dari Domin duba halin da ɗan cikin juwud yake ciki gwara shi ya zo duniya ta kuwa kin ga kuwa dole inbiya a dubata gobe ma zan koma dan haka bazan baki kuɗi ƙar muyi rashi biyune ga ita gashi to ina amfanin haka amma zaki iya zuwa gidan radiyo ki faɗa ko a samu me tausayi ya bayar......✍️


*KIN CUCE NI. 8*




_Story And Writing_


_By_


*
(Oum Yasmeen)
And



(Nainarh KD)_


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k


_____
Zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana muzuru ana shaho sai ya yi.
____

Life is beautiful with full of badly destiny against the Unjustly.🔥
___


Sam bata bari ya ƙari sa faɗan abin da yake niyyar faɗa ba cikin wani irin tsawa da tuƙuƙin baƙin ciki ta katsesa ta Hanyar ɗa ga masa hannu ta ce.


"Naji Abdulyasar Tabbas ka bani mamaki ban taɓa tunanin zaka yiwa jinin Adda Indo haka ba kuma ɗan ka na cikinka sai dai ba laifin ka ba ne na gode da kulawa sannan ina maka fatan gaggawar dawowa cikin hayyacinka domin wannan mutumin dake gabana ba Abdulyasar mutumin kirki da na sani ba ne, wannan mugu ne mara imani da tausayi."


Da gama faɗin hakan ta sa kai ta wuce abin ta zuciyarta cike fal da baƙin ciki da damuwa yayin da Abdulyasar ya yi tsaye yana bin ta da kallon mamaki sam ya gaza motsi ko kaɗan jikinsa ya yi sanyi ƙalau da maganganun ta.



****


A taƙaice haka Rayuwar ta ci gaba da kasancewa Salamatu cikin wannan mummanar hali da ta tsinci kanta. Aryaan yana asibiti rai a hannun Allah gaba ɗaya hankalinta a mugun tashe yake bata da wani Buri da ya wuce samun lafiyar Aryaan wannan dalilin ya sa ba tare da wani dogon tunani ba ta kwashe gaba ɗaya kujerun ta tun na aure duk sun fara fita hayyacinsu ma sakamakon katakon da aka yi amfani da su wurin haɗawa ba masu inganci ba ne ta siyar gaba ɗaya. Da kuɗin ta samu ta biya aka yi ma Aryaan Allurar sannan aka haɗa su da magunguna suka dawo gida tana ci gaba da kula da shi ragowan kuɗin dake Hannunta ta tattala abin ta ta fara sana'a. A Rayuwar Salamatu babu kalar baƙar wahala da sana'a komai wuyanta da batayi ba domin ganin Aryaan bai kwana da yunwa ba haka da kuɗin sana'ar ta samu ta ƙuƙuta wuya da daɗi ta saka sa a makaranta ta arabi da boko bayan ya fara tasawa....



Ta ɓangaren Rayuwar aurenta da Adamu mijinta kuwa abin sam babu daɗi domin kuwa sam bai ɗauke ta da wani muhimmanci ba da ita da babu ma a wurin sa duk ɗaya dan shi har mantawa da ita yake musamman ma da ya sama mata 'yan Duniya Hansatu Tantiriyar mace da banda bin bokaye da malaman tsubbu domin mallakar miji babu abin da ta iya. Haka ma Maryamu sai dai ita ba boka balle Malam sai shegen kissa da kisisina Wurin ta shi ya sa gaba ɗaya suka susuta Adamu ko kallon Salamatu ma ba ya yi dama kuma can halinsa ne wulaƙanta mata suma su Hansatu ɗin ba tsira suka yi ba domin duk Ranar da abin nasa ya motso ko su ba ya bari..


Tohm haka dai Rayuwar ta ci gaba da tafiya Salamatu tana kula da ɗan ta mafi soyuwa a gare ta sama da komai na Duniyar ta wato Aryaan tana son sa sosai domin ita ce uwansa kuma ubansa bai san kowa da komai ba a Duniyar sa sai ita ɗaya....



Aryaan ya taso yaro ne shi mai matuƙar kaifin basira sosai wannan dalili ya sa ya kasance zagwagwurin jajirtaccen ɗalibi mafi hazaƙa cikin Makarantar su sam Aryaan ba shi da wani sake wa sosai da mutane domin ba mutum ne mai son yawan surutu ko hayaniya ba yana da sanyin hali da kyakyawar zuciya kyakyawa ne shi sosai domin komai sak mahaifinsa ya yo sai dogon hancin ne Kawai irin na Mahaifiyar sa. So da yawa idan ya tambaya Salamatu akan ainihin iyayensa sakamakon yawan gori da Adamu da matansa Hansatu da Maryamu suke ma sa akan shi ɗin agola ne cikin gidan ba kowa ba. Idan ya yi ma ta tambayar sai dai ta sha re hawaye Masu zafi ta faɗa masa kyawawan halaye irin na mahaifiyarsa Maragayya Aisha. Zuwa lokacin ya san cewa Mahaifiyarsa ta rasu sai dai bai san komai Dangane da Mahaifin sa ba duk da sanin da ya yi yana raye.

A lokacin ne kuma wani babban abu ya kasance musu na alhini sakamakon hatsarin motar da Abdulyasar ya samu shi da matar da aka Aura masa juwud suka rasu sai dai 'yar su ɗaya tilo ta rayu mahaifiyar Abdulyasar ta ci gaba da kula da ita.
Sosai Salamatu tayi kuka lokacin da ta sama labarin rasuwar Abdulyasar sai da ta ba uku lada ta bisa da addu'a shikenan kuma Aryaan ya zama cikakken Maraya. Sai dai ta ƙudirta a ranta ko wuya ko daɗi zata zame masa majingini na Rayuwa indai tana Raye bazai taɓa kukan rashin iyaye ba in sha Allah kuwa haka ta ƙudirta.


Har zuwa lokacin kuma haihuwa Shiru daga Salamatu tun abin yana damunta tana kuka da damuwa har ta haƙura ta fawwalawa Allah komai domin yana sane da ita tabbas Allah maji roƙon bayin sa ne......✍️🌹


*KIN CUCE NI*



Oum yasmeen


And

Nainarh KD


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k



EP 9



_Previous_


Har zuwa lokacin kuma haihuwa Shiru daga Salamatu tun abin yana damunta tana kuka da damuwa har ta haƙura ta fawwalawa Allah komai domin yana sane da ita tabbas Allah maji roƙon bayin sa ne......✍️🌹



_Continue_





Yayin da adamu ya kara tsanan ta mata yanzu ya zare hannunsa akanta ficikarsa baya bata yau kam tana zaune tun safe take wankau ɗin da aka kawo mata wasu ma tayi a hanata kuɗin sallamar Aryan taji cikin sakin fuska farin ciki ya mamaye ta farin cikin ta ya dawo tace


"Ɗan albarka andawo,


Be fiye fara'a ba da sai murmushi da yasakar mata yace


"Eh inna,


Taƙarda ya miƙo mata goge hannun ta tayi sannan ta amsa yace


"Taro ne na makaranta ance kowa abbansa yazo,


Wani tashin hankali ta shiga gumi ya dinga yanko mata ƙoƙarin saita kanta tayi tace



"Aryan Allah ya kai mu ai mace tana iya wakiltar namiji ni zanje,

Be nuna da muwarshi ba sanin halinsa na zurfin ciki inna tace


"Aryan,


Ɗago kyawawan idanuwansa yayi ya dube ta yace



"Na'am,




Kuɗi ta ciro agefen zaninta ta miƙo mai tace


"Inka cire kayan ka kasiyo karin kwaki ka sha kaji yau ban da kuɗin yin girki sannan ruwan da muke amfani da shi ya ƙare,


Amsa yayi yace


"TO,


Malam Adamu ne ya shigo hannunsa riƙe da yaro amma aryan ya girme sa yana kuka wuf aryan yayi saurin shiga ɗaki baya kaunar ganin wannan mijin inna azalimine jama'a yana cire kaya yaji wani ashar da ya lailayo ya ɗannawa inna da sauri ya toshe kunne sa malam adamu yace



"Wato dan rashin mutum ci shine kika yiwa musa faɗa to ke dan kutu mar uban ki kin haifa ne ko kinsan ciwon ƴa'ƴa da har zaki wa wani faɗa ke gaki yar gidan malam ko uwar iya?,


Ajiye wankin da take ta ɗurƙusa ƙasa muryar ta na rawa tace



"Malam kai haƙuri insha Allah bazan ƙara ba malam ganin su nayi shi da iliyasu almajinrin da ke yiwa hansatu tallah suna wasa da gaban su shine na ce mai babu kyau,


Aguje hansatu ta fito daga banɗaki tace



"To annamimiya ina gidan ban fita ba wato Ni za aiwa iya shege malam sai ta sa kuka ta shiga ɗaki ganin ran yar gold ya ɓaci ya tsinko igiyar da tayi shanya ya shiga labta mata yana ta sababi aguje aryan ya fito ya rungume inna yana kare mata


Aikuwa haka ya haɗa su ya zane zuciyar inna ta ƙeƙashe dan haka ba kukan da tayi sai na zuciya gajiya yayi yana hura hanci ya bar gidan


(Hattara iyaye yau duk wanda zai wa ya'yan ku faɗa to wallahi me ƙaunar ko ne musamman wannan yazu zamani yar da ake lalata ya'yan mu ba mazan ba ba matanba musamman masu ɗauko almajire ku ɗinga kula da irin wasannin da sukewa ya'yan ku yana gama ku bashi abin da zaku bashi ya tafi ƙar ku yarda wata alaƙa ta shiga tsakanin ku da ya'yan ku ya kama garuruwan da suke turo almajerai suji tsoron Allah baka san a ina ɗan ka ya ke kwana ba bakasan wake wa ya'yan ku tarbiyya ba wallahi ina jin ciwo in fito inga almajirai yara ƙanana a kawo su uwa duniya da sunan karatu abin mamakin shine har suna da kwanciyar hankali yaya su suna watan gaririya a gari

Wallahi wani ma sai yayi sati malamin nasa be son baya nan ba me yasa Ubangiji yake jarabamu iri iri ai daman ya fadi in har aka kauracewa faɗar sa to zai jarrabemu su ya'ya amana ce a gare mu akwai ranar da Allah zai tambaye mu kiwon da ya bamu )

Haka rayuwa ta ci gaba da kasan a gidan dangin uban Aryan ba wanda yake zuwa ganin sa duk da cewa kamar su ɗaya da mahaifinsa ko hakan ya ja hankalinsu su soshi amma ba wannan shekarar Aryan goma sha huɗu yana gab da fita junior school Allah ya bawa salamatu ciki tun daga fitowar cikin nan abubuwa suka cakuɗe mata malam adamu motar sa ta ɗinga lalacewa nan fa ya dorawa cikin ta shi ya jamai domin shi har ya manta yau she rabun da wata ma'amallah ta aure ta haɗa su nan fa yace aljanune sukai mata ciki billahir lazi sai dai ta nemi uban ta acan duniyar aljanu haka ta ɗinga jurewa saboda matsaloli sun mata yawa gana matar ubanta ga nata ta daina zuwa gidan jikin ta yayi nauyi ana haka Aryan kungiyar tallafawa marayu da mara ƙarfi ta America ta ɗauki nauyin su a lokacin ya shiga senior yana aji biyu ganin kwazon sa yasa suka zaɓe sa duk da secondary ɗinsa a college of Qur'an yayi makarantar kusa da S.A.S ranar da yaci jarabawa ranar Allah ya sauki salamatu


Ba tare da dugowar na ƙuda ba ranar kuma motar adamu ta kone ƙurmus shima sai zaro shi akai ga kuɗin mutane da kayan su yana dawowa aka shimfida mai tabarma ya zauna su maryamu da hansatu sai fifita akai mai ni kuwa ina ban ɗaki ina wanka fitowa nayi naga kafar shi duk akone sannu nayi mai da ƙƴar ya amsa shiga ɗaki nayi na ɗauko yarinyar da na haifa nace malam yau Allah ya sauke ni sa hannu yayi ya buɗe ta ihu ya saki ganin idanuwanta da kuma irin kyawun ta yace



"Haba ashe yar aljanu aka haifar min shi yasa na gamu da wannan ifti'ila'in to ke da ita kutattara ku barmin gidan nan,


Cikin kiss maryamu tace



"Haba malam ai yanzu ka koreta sai su ƙona mu muna kwai ka ƙƴaleta ta amshi gashi,


Dariya yayi yace


"Kuma hakane fa ,


Girgiza kai salamtu tayi ta tashi Aryan da yake me jikin girma ne ya zama saurayi ya shigo bakin sa da sallama fuskarsa ta ƙasa ɓoye murnar da yake ciki tace


"Inna na ci jarabawa ta nan da sati me zuwa zamu tafi kasar waje sun ɗauki nauyin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login