Showing 3001 words to 6000 words out of 13895 words

Chapter 2 - KIN CUCE NI Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

1412

ganin Sarkin fawa kawai sai miya tayi zaƙi."



Ya yi Murmushi wanda ya zame masa ɗabi'a ko cikin wani yanayi yake bakya rasa murmushi saman Kyakykywar fuskarsa ya ce.


"Gimbiya ta ke nan kin manta da zafi zafi akan daki ƙarfe. Yanzu dai ba wannan ya kawoni gareki ba kafin na kiraki nan sai da na nema iznin Hakan wurin Mahaifin ku kuma ya amince. Aisha wallahi tallahi tsakani da Allah nake ƙaunar ki kuma Indai kin amince a shirye nake dana turo magabata na domin maganar aure."


Aisha tayi Shiru jikinta ya yi sanyi, Allah mai iko wai da gaske ɗaya daga cikin Dangin Turaki turba shi ne tsaye gaban ta da ƙoƙon bararsa na son aurenta.

"Bakomai Allah Ubangiji ya shige mana gaba amma kayi haƙuri zan fara shawara da Mahaifiyata tukunna."


Cikin sauri yana Murmushi ya amsa ma ta da faɗin.


"To ai Shikenan babu damuwa Allah ya sa naji Alkhairi gobe zan dawo."


"Ameen."

Ta amsa tana yunƙurin barin wurin.


"Bakiji ba."


Ta juya ta kallesa ba tare da ta ce komai ba.


"Ga wannan a kai ma 'yan ƙannina."


Ya faɗa yana miƙa ma ta ledar hannunsa.


"A'a wallahi da ka barshi Allah amfana."


"Ki karɓa Kawai kinsan dai babu kyau mayar da hannun kyauta baya kuma ai ƙannina nace ki kai ma."


Tayi Murmushi sannan ta karɓa ta ce.


''Sun gobe."


Sallama suka yi sannan ya tafi ita kuma ta shiga gidan su da isarta ta sama Mahaifiyar su a ɗakinta tana zaune ita da Salamatu da alama fira suke yi nan bada ɓata lokaci ba ta sanar musu yadda suka yi da Abdulyasar.



Hajiyarsu tayi Murmushi irin na manya ta ce.


"A'isha ki tsaya ki nutsuwa idan wannan yaro ya yi miki falillahil hamdu haka ake so sai a girmama zancen idan kuma bai yi Miki ba Ubangiji ya haɗa kowa da rabon sa, sai dai ni aso samu na kuyi Aure gaba ɗayanku a wannan shekarar."


Aisha tayi Shiru cike da nazarin Maganar Mahaifiyar tasu sai dai ba tace Komai ba sai da aka ɗan jima sannan ta amsa da faɗin.


"To Mama In sha Allah."


Hajiya tayi Murmushi.

"Kuje ku kwanta dare nayi Allah ya bamu Alkhairi."


Suka amsa ma ta sannan suka yi ma ta sallama suka wuce zuwa Ɗakin kwanarsu basu daɗe da fita ba ita ma ta fito kai tsaye ta wuce ɗakin Mijinta ta sanar da shi dukkanin yadda suka yi da Aisha.


Washe gari koda Abdulyasar ya dawo ba tare da ɓata lokaci ba Aisha ta sanar masa da ta amince da ya turo magabatan sa. Ya yi farin ciki sosai domin kuwa tsakani da Allah yake ƙaunar Aisha da zuciya ɗaya. Aikuwa bai jira komai ba ko sati ɗaya ba'a cika ba ya turo magabatan sa domin tsaida Maganar auren bayan tataburza da aka sha tsakaninsa da su na cewa ba zasu taɓa yarda jininsu ya aure jinin talakawa ba wulaƙantattu sai dai babu yadda suka iya Abdulyasar shi ne jinin jikinsu ganin yadda ya rikice musu ne yasa ba don suna son auren ba suka je aka nemawa ɗan su Abdulyasar Auren A'isha, kuma cikin ikon Allah an basa Aisha nan dai aka tsayar da Rana Watanni uku masu gaba towa za'a ɗaura Aure, sosai Abdulyasar ya yi farin ciki da murna abin har mamaki yake bawa Aisha nan ta fahimci cewa lallai ba ƙaramin so yake ma ta ba, to amma danginsa fa shin suna sonta kwatankwacin yadda Abdulyasar yake son ta?. Wannan shi ne tambayar dake damun zuciyarta a koda yaushe.








* * *
Tabbas rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya, lokaci na wucewa sauri sauri yayin da sakanni mintoci awanni suke shuɗewa ranaku satikai watanni suma su shuɗe su wuce wucewa na har abada haka wannan lokutan da suka gabata gaba ɗaya cikin shirya shirye na bikin ake, da yake da Bikin Salamatu za'a haɗa ita da masoyinta Adamu da suka daɗe suna tare kuma an yi bincike kam ba laifi bashi da wata mummunar hali dai a zahiri wannan dalilin yasa aka haɗa auren nasu gaba ɗaya za'ayi lokaci guda.


A Ranar wata Litini misalin ƙarfe biyu na Rana aka ɗaura Auren Abdulyasar Turaki Turba tare da Amaryarsa A'isha Dauda Mai Allo bisa sadaki mafi daraja da dacewa lakadan ba ajalan ba. Yayin da gefe guda ma aka ɗaura na Adamu Jibril tare da tasa Amaryar Salamatu Dauda Mai Allo.


Wannan rana ita ce ta kasance Rana ta farin ciki ga kowa musamman Amare da angwaye kowa ka kalla fuskarsa wadataccen farin ciki ne kwance.

*KIN CUCE NI*




_Story And Writing_


_By_



(Oum Yasmeen)
And
*_Khadeejarth Sabi'u Yahyah Kaduna_*
(Nainarh KD)_

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k


*Tambas rayuwa komai na rayuwa me wuce wane ya Ubangiji ka bamu iƙon aikata dai dai arayuwar mu Allah ya jiƙan ki aneesa Allah yasa kin huta wannan page sadakar wace agare ki nayi rashin yar uwa bazan taɓa iya samin madadin ki ba anee wanda ya fimu sonki ya amshe ki Allah yasa Allah janna CE nakomar ki*


*Tunatar wa*



_Bawa ya taɓa tsairewa kaddararsa sai dai muyi addu'a Allah ya bamu me kyau in kuma ya jarabamu Allah ya bamu iƙon cinye jarabawar sa_



```ina sanar da masoyana cewa zan sabon littafi me suna DESTINY OF LOVE wanda da ga shi zan tsaya da rubutu sai kuma lokacin da Allah ya bani iƙon dawowa```






_Ep 5_




*End of previous of last episode*


Wannan rana ita ce ta kasance Rana ta farin ciki ga kowa musamman Amare da angwaye kowa ka kalla fuskarsa wadataccen farin ciki ne kwance.


*Continue*


Samalamtu aka fara kai wa gidan dake dandago indo sun rabu cikin kewar juna da ƙƴar aka raba su gidan salamatu dai dai na me rufin asiri ɗaki ciki da floor da toilet a cikin bedroom ɗin ga shareren tsakar gida ga wasu ciki da floor har guda biyu gidan ba matsatsi nan fa yan bani na iya suka fara cewa tab wata ran dole ya kara aure tun da har part biyu yayi ƙaton kitchen ne a tsakar gida kai kace shagon siyar da kayan kitchen

malam yayi bajinta ko wacce yayi mata gara ta ban mamaki nan fa mutane ne suka ƙara ruƙe haɓa cewa malam yana da zuciyar yi tafiya akai aka barta ita daya da yake bata da kawaye

___________________gidan malam


Shiru shiru ba azo daukar A'isha ba nan ba wasu da ga cikin yan gulma suka fara tsaigunmi daman sunyi mamaki da alhaji Junaid turaki turba har ya yarda ɗansa zai aure yar talaka ko wa yasan cewa wannan family turaki turba basa auran bare sai dan ɗangin su muzaye ne na asali mahaifiyar Alhaji Junaid kuwa baggara ce wato (shuwa arab ) shi yasa suke da kyau na bammamaki ba su yarda bare ya raɓe su ba yanzu fa Alhaji junaid shine chef accounter na Kano baki daya duk wani kudi da za'a fitar sai da sa hannunsa ƙanin sa kuwa Alhaji Zubair shine former governor


yanzu haka gari guda duka kwasa a unguwar janbulo suka gina estate duk wani dan family ɗin sun mai gida aciki kama baki wata tsohuwa tayi tace


"Tab ina tausayawa indo yanzu cikin wannan daular zata shiga ?,


Wata ta taɓe baki tace




"Ae kwaɗayi ya kai ta shi daman mabuɗin huya ne wace mata barno gabas ce duk irin samarin da suka dinga nunawa suna sonta amma ta bujire rabon huyane akanta,


A fusace hajiya Ruqayyah ta fito tace


"Sai de kiga huya a ya'yan ki me isa mutane baku da shedar kirki bakwai fadar alkhairi Insha Allahu indo da abdulyasar mutu ka raba banzaye ku tashi ku fitar mana daga gida ,


Sum sum suka fita har wannan tsohuwar girma yayi gardama ɗaki ta koma kai da gwiwa ta haɗa tana kuka yau sai de ta kwana a wanni gidan da ba nasu ba yau wata sabuwar rayuwar zata fara me cikin da kalubale kala kala tambas rayuwar aure ibada ce duk kuwa abin da aka ce ibada to sai anyi haƙuri


Wasu irin baƙaƙen Benz ne suka iso nan fa wa yanda aka kora suka ce ba ayi basu ba suka shiga cikin mota ai kawa akai anzo daukar amarya tana kuka tana ruƙe inna aka shigar da ita cikin mota a jere motocin suka fara barin unguwar


wata mata ce ta tsaya me mashin ya sauke ta kallo daya za kai mata kasan ba mutuniyar kirki ba ce tsayawa tayi tana bin motocin da kallo tace


" jar ubancan tab aliko daman ya'yan malamin nan me ƙudi zasu aura aliko?,


Gyara tsayuwar mashin ɗinsa yayi yace


"To yar hau ko kin ƙƴasa ne dan nasan halinki duk gidan da yake da danshi nan kike zuwa lokacin da da danshin ya ƙare sai kiyi gaba dan ma kefa ba me haihuwa bace yasin da ƴa'ƴan ki sunfi goma shegu da ya'yan sunnah,


Duka ta kai mai tace


"Wa wacce haihuwa tab ai saide in alahira anayi inyi ai wani matsiyaci na samu ashe ba mutumin kirki bane ya kaini gidan sa muka gama sex ɗin mu ina haka ya shaƙamim hoda sai tsintar kaina nayi a sabiti wai ancire min mahaifa ,


Dariya yayi harda ruƙe ciki yace


"Gaskiya tantiriya baki da rabon shiryuwa yanzu har haka ta faru a kanki baki dena bin maza ba ?,


Riƙe hannunsa tayi tace


"Hmmm aini ina tashi cewa nayi anragemin shan magani yanzu inzaka kwanta dani sau dari Zan dau ciki ne kai nifa wallahi gaba ta kaini kana ga huni nake a sabon gari ina kwalta,


Dariya yayi yace


"Tantiriya kifi karfin kaina yasin jakar ubancan nikam ina nan ina shirin barin harkar nan yasin,


Mayafin ta ta gyara tace


"Ai sai kayi ni yanzuma gobe zan tafi garin ogun state kauyen ilaro kasan fa su sun iya sari na tashin hankali kai wallahi daga su sai India kaga duk fadar asirin India dake to wallahi bokan yarabawa ya fisu zan je ariki tamin zuciyarsa malamin nan kai sufa tsafi suke yi ba asiri ba ,

Sakar baki aliko yayi yace


"Tantiriya anya kuwa kina da imani nasan halinki yanzu zaki tarwatsa mai gida kefa sheɗaniya ce Please dan Allah kibi wani ba malam ba wallahi yana da kirki kullum sai yayi min addu'a abokin mahaifina ne ,



Daurin kanta ta gyara tace


"Yasin sai de kayi Ni nayi nan tayi gaba abinta


________________*unguwar janbulo*


Motocin tafiya suke cikin tsari ba wacce take kauce hanya har suka isa unguwar janbulo tun daga farƙon layin akai ɗan allo aka sa *turaki turba Street* wani irin shegun gine gine ne turawa ne sukai ginin yawa kana Dubai tsarin ginin Dubai akayi ga wasu irin shegun benaye masu tsayi a harabar estate ɗin suka tsaya hajiya Ruqayyah da yayar malam wato saratu suka ruƙota kai tsaye

Bangaren Hajiya fa'iza aka kai ta domin ita ce mahaifiyar abdulyasar shiga sukai floor na alfarma tana zaune yawa kana afadar queen Elizabeth ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya hannunta shaƙe da dam wani irin swiss less ne ajikin ta colour army green da adon light purple a jikinta ta ci ɗauri ture kaga tsiya ta haɗa girar sama da kasa kai kace wata boss ce fara ce kal yawa balarabiya

gaban Hajiya Ruqayyah ne ya waɗi amma sai ta dake sukai sallama


Bata amsa ba me yimata tausace ta amsa tace


"Wa'alaikumussalam barka kun da zowa ku shigo Ita kuwa gimbiyar ko nuna alamun tasan da shigowar mutane batayi ba sai ma ɗaukar remote tayi ta canza channel zuwa Bollywood ai kuwa tayi sa'a suna Film ɗin khafi kushi khafi gamman mai da hankalin ta tayi kan sa sai da Hajiya Ruqayyah tace


"Barka da wannan lokaci uwar masu gida yau Allah yayi A'isha ta zama daya ga cikin ahalin ku ga amanarta nan ,


Ya tsuna fuskan tayi tace


"Yauwa barka dai ,


Duban gefen ta tayi tace wa yar aikin ta


"Jeki Sama ki kira min surayyah da kaltum,


Sannan ta juyo tace



"amma ban ɗau amanar k ........✍️


*KIN CUCE NI*




_Story And Writing_


_By_



(Oum Yasmeen)
And
*_Khadeejarth Sabi'u Yahyah Kaduna_*
(Nainarh KD)_


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k



*EP 4_6.*




Gaba ɗaya suka saki baki suna kallon ta cike da al'ajabi Hajiya Rukayya ta girgiza kai sosai take tausayawa Aisha da zata tsinta kanta cikin waɗan nan mutane waɗan da basu san dajara na 'yan uwan su mutane ba.


Daidai lokacin kuma Surayyah da Kalthum suka sauko Down suna bin mutanen da kallon ƙasƙanci suka sama wuri suka zauna.


Su Hajiya Rukayya basu ja zancen da nisa ba suka basu amanar amarya basu jira amsawar su ba suka fito Direct Apartment nata suka wuce da ita nan ma sai da suka kuma ma ta nasiha sosai kuma suka ja hankalinta sannan daga baya suka shishshiga mota domin komawa can gida dan kuwa sun ce ba zasu kwana ba.


Sosai A'isha taci kuka kamar ranta zai fita kanta har ciwo ya fara tsaban kuka da ta sha.


*_A TAƘAICE DAI_*


A Ranar ango ya shiga Dakin masoyiyar sa A'isha kuma Matarsa cike da Tsantsar so ƙauna da tarairaya ya mantar da ita dukkan wani damuwa da take ciki da tsoron danginsa da ya fara ɗarsuwa a ranta duba da irin tarbar da ta samu wurin Mahaifiyarsa, sun raya daren nasu ne cike da ɗin bin kula ga junansu cike da so da kauna haka ma ɓangaren Salamatu da angonta sai fatan zama lafiya.




_____
*_Marka Ba Tabbas _*


Shi ne sunan ta kuma wanda aka fi sanin ta da shi tsahuwar kilaki ce aurenta babu a dadi tana fitowa Sanadin hakan ne ma ake kiranta da Marka Ba Tabbas domin kuwa bata da Tabbas Indai akan maza ne kamar riga haka ta ɗauke su tana sakawa da cirewa a duk lokacin da ta ga dama ita kanta ba ta san adadin Auren da tayi ba balle kuma yawan mazan da tayi tarayya da su ba ta hanyar Aure ba, Balan tana uwa uba adadin cikin da ta zubar. Wa'iyazubillah.


Tana da Yarinya ɗaya da ita Kanta batasan Wane ne uban Yarinyar ba shin cikin mazajen da take Aura bata zama ne ko kuwa cikin shin mazajen da take mu'amula dasu a kan titi ne?.



Tun ranar da ta kyalla idon ta akan Malam Dauda Mai Allo Ranar da yake aurar da Yaransa kuma taga Irin tanfatsa tanfatsan motocin da suka zo ɗaukar Aisha Ranar ɗaura auren ta raya a ranta ta ga Mijin aure domin kuwa a washe garin Ranar asubanci tayi wurin zuwa ogun state wurin bokan ta da mummunar ƙuduri a ranta.



____
_Amare kuwa_


Watannin Aisha uku a gidan Abdulyasar tsakaninta da Mijinta sai sam Barka suna zaune Lafiya Qlau abin su cike da so da kuma ƙaunar junansu mara adadi yayin da gefe guda take karɓar wulaƙanci da cin mutunci tozarci duk daga wurin dangin mijin nata ba daga 'yan uwansa ba haka ma ba daga mahaifiyar sa ba, ko ta ina dukan ruwa take kwasa a wannan 'yan tsakanin ne kuma ciki ya bayyana a wurin A'isha da sanadin hakan ne kaɗan daga cikin uƙubar da take kwasa wurin mahaifiyar Mijin nata ya fara raguwa tun lokacin da ta fahimci Aisha tana da cikin ɗan ta ma'ana dai zata sama jika duk da ba ƙaunar Aisha take ba amma tayi farin ciki da hakan ta kasance kuma ta fara tsawatar wa sauran mutanen Ahalin Turaki Turba masu uzzarawa Aisha ɗin.


Ta ɓangaren Salamatu kuwa da fari lafiyar Allah suke zaune Qlau da Mijinta Adamu sai dai daga baya ya fara fito ma ta da mugayen halayensa da ya ɓoye ma ta a farko kaɗan daga ciki su ne Abu kaɗan zatayi ya hauta da faɗa wasu lokutan ma har da duka da zagi Sanadin hakan ma har gida tasha komawa yaci tun ba'aje ko'ina da auren ba amma haka zai zo yayi ta ma ta ƙaramar murya har ta haƙura ta koma kwanaki kaɗan su wuce ya ci gaba dama mai hali baya fasawa.



Ta ɓangaren Marka kuwa tuni ta aikata dukkanin muna nan ƙuduranta lokaci Kawai take jira domin kuwa ta ɗa na ma Malam Mai allo tarkon ta babu mai iya fidda shi sai Ubangiji.



____________


****


"Dan Allah Hajiya ki Dena wannan kukan mana sai kace wata ƙaramar Yarinya fisabilillah kin tasa yara a gaba kina ta wani kuka."



Hajiyarsu A'isha ta fyace majina tana gallawa Inusa harara cike da baƙin ciki da taƙaici ta ce.


"Ɗan juma ka kiyaye ni wallahi tun kafin raina ya ɓaci nayi maka abin da ban yi niyya ba shashasha kawai."


Gum Ɗan juma ya yi daga bisani ma ya fice daga gidan baki ɗaya ko kula matarsa dake zaune gefan Aisha da ta miƙar da ƙafafu ga cikinta da ya tsufa haihuwa Yau ko gobe bai yi ba.


Salamatu dake gefe tayi Murmushi a ɓoye ta ce.


"Hajiyarmu Dan Allah ki Dena wannan kukan ina ce dai idan Amaryar tazo ba'a kanki zata zauna ba kam nifa banga abin tayar da hankali ba anan wurin badai amarya ba ce Allah ya kawo ta lafiya."



Hajiyarsu A'isha ta kuma fyace hanci ta ce.



"Salamatu ba zaki gane bane wannan matar da uban ku zai Auro min ba kalar matan da kika sani ba ce tsahuwar kilaki ce fa fisabilillah da tsufan mu gaba ɗaya ni da shi ya rasa wacce zai Auro min sai tsohuwar kilaki."


Ta kuma rushewa da kuka.


Salamatu tayi ka saƙe tana Kallon ikon Allah. Yayin da Aisha taja ajiyar zuciya tana faɗin.


"Allah Sarki Rayuwa tunda nake ban taɓa tunanin koda a mafarki ba ne wai Baba zai ƙara Aure saboda bai yi ba tun ƙuruciya sai yanzu ni kam babu abin da zan ce sai Allah ya bada zaman lafiya. Hajiyarmu ki kwantar da hankalin ki Dan Allah ki Dena damuwa ita Rayuwar ma gaba ɗayanta nawa take da zaki dame kanki akan wannan ƙaramin abin, wata ƙila ma jahadi zai yi wata ƙila hakan ya zama sanadin shiryuwarta tunda ance tsohuwar kilaki ce."


Gaba ɗaya Shiru suka yi suna sauraren Aisha kuma tayi gaskiya a zancen ta Hajiya ta ja Ajiyar zuciya ta ce.


"To shikenan A'ishata zan gwada Allah ya muku albarka."


Suka amsa da Ameen gaba ɗaya.


Fira suka ci gaba da sama sama domin ranar sun zo ma ta wuni ne basu suka koma gida ba sai dare Alhaji Abdulyasar Matashin mai Dukiya a wancan lokacin ya zo ya ɗauki Matarsa A'isha daga nan suka rage wa Salamatu hanya suka kaita har gida sannan suka wuce nasu

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login