Showing 1 words to 3000 words out of 13895 words

Chapter 1 - KIN CUCE NI Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

1411

KIN CUCE NI





Gargadi





Bamu yarda wani ko wata suyi amfani da shashi na littafin nan ba ko juya shi batare da izinin mu ba ko mai da shi document 📄📃 in kunne ya ji jiki ya tsira


Ya Ubangiji kabamu iƙon rubuta dai dai ka hanamu rubuta ɓarna ya Allah ba bamu iƙon gamashi lafiya kamar yar da muka fara lafi
Wannan labari kirkirarre ne duk wanda yaga yayi dai dai da rayuwar sa to ya ɗauka arashi ne





*KIN CUCE NI*






_Story And Writing_


_By_


*
(Oum Yasmeen)
And
*_Khadeejarth Sabi'u Yahyah Kaduna_*
(Nainarh KD)_


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

```Duk kan yabo ya tabbata ga Ubangijin talikai ya Allah ka bamu ikon gama littafin nan lafiya, kamar yadda cikin amincewar ka zamu fara lafiya..```

*GARGADI!!!!!!*


_Bamu yar da wani ko wata suyi amfani da wani shashi na littafin ba ko kuma mai da shi Document in kunne yaji jiki ya tsira_




*_Ep one_*



Taƙu take ɗadɗai duk inda ta taka sai kaji yace ƙas tana taunar chewing gum wani ƙwai ta saki jikake yace tussh glass ɗin fusƙarta ta ɗaga sama ta saki dogon tsaki. Msssswww tace


"Wallahi in har ba zaku dena kwaso matattun ƙafafuwan ku ku kawo min gidana wallahi ba zaku dena ganin hulaƙanci kala kala ba nace muku me gidan nan yafi ƙarfin ku kuƙi yarda taurin kai yayi muku yawa ni wallahi na tsani in dinga ganin ku baki duk goro ,


Cikin baƙin ciki naseeba tace


"Yan zu fateesat hulaƙancin ki har ya kai haka Inna mai towo ƙanwar mama ba ce fa in kin manta in tuna miki?,


Ƙara sa saukowa tayi daga stairs case ɗin ta sheƙe da wata uwar dariya ta tafa hannaye tace


"Naseeba ce miki akai na kamu da cutar mantuwa nagane ko wace ce ita ƙanwar gyatumar ki ce domin ba zan ce mahaifiyar mijina ba domin tun ranar da ya auro ni na cire shi daga cikin dan gin ku tun huri ki faɗawa tsohuwa tayi gaggawar cire shi a sahun ƴa'ƴan ta domin ita ta haife shi amma yafi ƙarfin ta ?,


Kuka mai tuwo ta saki tace


"Amma fateesa kin cuce mu in Allah ya yarda sai kin ga ƙarshan ki naseeba ta shi mutafi kuma gida ba zamu fasa zuwa ba tun da ba na uban ki bane ,


Ƙaro sowa tayi cikin floor iya huɗuwa ya haɗu daga gani zaka san gidan me arziki ne ɗaya daga cikin luxury sofa ta zauna ta ɗora ƙafa ɗaya ƙan ɗaya tana gir giza kafa hannuwanta shaƙe da zoɓe daham da awarwaron daham tace


"SALAMATU DAUDA ME ALLO wallahi wanda kike ta ƙama ɗan yayar kine zan kira shi ya ci miki mutunci ,


hy my sweetheart lafiya nake jin warin talauci duk ya cika floor nan


Juyowa tayi tace


"Baby hayaniyar su ta tayar da ke daga baccin da ya ɗauke ki jiya mun kwana muna cin juna ,

Daga ita sai sleeping dress wata me net shara shara ba abin da ya ɓoye a jikin ta komai ana gani tace


"Ehwllh me ya kawo wan yanan old human ɗin ?,


Tsaki taja ta kamo hannun abokiyar sheɗancin nata ta zaunar da ita kusa da ita hannunta ta ɗora akan breast ɗin ta tana shafawa tace


"We wata aljanar ƴar ta ce ba lafiya shine tazo ya bata kuɗin magani ,


Ai kafin ta ƙarasa naseeba ta yo ƙan su hannunta me tuwo ta kama tace


''Naseeba barta kina ga sunana ta faɗa gatsal ba sakayawa zo mutafi Allah ya isa tsakanin mu da keee,



Dariya suka saki baby tace



"Yau nake jin wata jarabawa me kuma mukai miki ko talauci ne ya motsa kai wannan matar tana shan kebura,


Wallahi kuwa zo mu shiga ciki tashi tayi suka shiga

Tafiya suke yawa zasu faɗi ga yunwa ga zafin rana yawa zai fasa musu ƙwaƙwalwa tun daga tudun Yola har asibitin Murtala a ƙafa ɗakin da aka kwantar da ita ta shiga tana kwance rai a hannun Allah ba abin da a kai mata saboda ba ta siyi abin da aka rubuta mata ba wata nurser ce ta shigo tace


"Umma ku ceci rayuwar yarinyar nan ko ba kuga halin da take ciki ba blood transfer za ai mata jinin ta ya ƙone dole juyan jini za ai mata O+ muke nema shini jinin sa zai mata ,


Mayafin ta tasa ta share hawayen fusƙarta tace
"To, zan nemo ,


Juyawa tayi ta fita Naseeba tace


"Inna bara in tafi gida ko mama ta ajiye muni abinci in kawo miki kici tun da kin ga bata san na tawo gun ki ba,


A jiyar zuciya ta saki tace


"To Nagode naseeba Allah yayi albarka ,


Ameen Inna Allah ya bawa ƙanwata lafiya


Amin tace domin yanzu rayuwar duniyar ta fitar mata a rai yayan ta uwa ɗaya uba ɗaya yana gudun ta ɗan bata da shi ciwon ƙafar ta ta duba ya ƙara kumbura yan zu ta mutu ta bar ilham bata san wanne halin zata kasance ba ji tayi ta saki salati jini yana zuba a baƙin ta da sauri naseeba ta dawo ta yo kanta cikin kuka tace.........





"Inna Inna Dan Allah inna ki tashi ?,


Da ƙƴar ta iya buɗe baki tace



"Naseeba ki tafi ƙar ane miki kar ki damu ba abin da zai same ni insha'Allah,


A jiyar zuciya ta saki tace


"Inna ba zan iya tafiya in barku ba ,


Murmushi tayi wanda ake kira da yafi kuka ciwo tace


"Ƙar ki damu Allah zai kare mu ,


Tashi tayi tace


"To inna natafi ,


Allah ya kiyaye hanya bayan tafiyar ta tashi tayi da ƙƴar ta zauna a kusa da gadon ilham ta ƙura mata ido kowa na ɗakin sai harƙar gaban sa yake zuba ta gumi tayi wata shawara ce ta waɗo mata da sauri ta tashi ta nufi wani gado kusa da su tace


"Assalamu alaikum ya me jiki ,


Matar ce wacce ta ke jinyar yar ta ta amsa bata fuska a tsuke ganin haka yasa jikin inna ƙara sanyi tace


"Dan Allah baiwar Allah ki temaka min ki bani aron wayar ki zan kira ɗana ,


Duban wayar hannunta tayi ta ƙara haɗe rai tace


"Bani da chaji,


Baiwar Allah ungo tawa da sauri ta fito da wata ta ƙarda a zanin ta duk taji jiki tace


"Nagode dan Allah saka min ki kirami ita ,



Yarinyar ta dubi ta ƙardar tace



"Baiwar wannan ai bata ƙasar nan ba ce,


Gaban inna ne ya waɗi domin ba zata taɓa manta waba ganin ta na ƙarshe dashi hannun sa ya bata wannan number yace ko wani abu zai tashi tace iya sannin da tayimai baya karya dan Adam me canzawa amma duk Inda yake tasan zuciyar nan tasa da tsayawa a kan gaskiya tace


"Yanzu kenan ba zata yi kira ba ?,


Aa inna zata yi amma sai ansa kuɗi masu yawa kamar dubu biyu


Dan Allah yarnan ko flashing ne ki yimai


To Allah yasa ya kira a hand free ta sata har ta gama ƙarar ta ba aɗauka ba duban Inna tayi tace


"Ba aɗauka ba ,

To yarnan Nagode ai kina asibitin nan insha Allahu zaikira


Eh ina nan Allah yasa

Amin tace ta koma ta zauna shiru shiru naseeba bata dawo ba ga wata yunwa da take ji ilham ko motsi bata yi kadan kadan take fusgar numfashi

Wannan kenan



Tun daga soro zaka fara cin karo da yara kowa na sabgar gaban sa daga bakin titin unguwar dan dago in kace a kai ka gidan yan adakawa har gidan za a kai ka gini ne na da ya kusan ruttawa wata ƙatuwar kwata ce a soron da ƙƴar na huce ciki gidan na shiga saboda jin alamun ana magana da karfi wani tsoho na zai kai shekara saba'in rigar sa duk a ƙode yace


"wanne dan iskanne ya shigar min ɗaki ya dauke sabuluna ?,


Ko wacce aikin gaban ta take ba wacce ta kula shi sauran yaran da suke cikin gidan sun yi tsuru tsuru ɗakin inna salamatu yaje domin ya ɗan ƙo ilham ya naɗa mata duka a cewar shi tun da aka haife ta ya dena Samu motar da yake ja ta ƙune ƙurmus ƙafa yasa ya tura ƙofar wayam ya gani juyowa yayi yace


"Ke hansatu inna salamatu,


tuƙunyar da ta wanke ta shinkafar siyarwar ta ta ɗora akan murhu sosai huta ke ci ga wata irin rana da ake yi gyara baƙin zaninta tace



"Owo ka bani ajiyar ta ?,


Wani yaro ya yake zaune ya goge majinar hancinsa yace


''ilham ce ba lafiya ,

Tuƙunyar kusa da shi ya ɗauka yayi cilli da iya yace


"Wato raini ya shiga tsakani na da salamatu to wallahi kar ta dawomin da arjanar ƴarta gidana fuuuuuu ya fita ,

Wata dariya maryamu ta saki suka tafa da hansatu tace


"Duniya juyi juyi tab salamatu ta taɓo sama da faɗi ,


Dan kwali ta gyara tace


"Hansatu an faɗa miki ni din ta wasa ce ,


zani ta gyara tace


"Dan Allah yar uwa me kikayi na lura shirinki yafi nawa,


Ɗariya ta saki tace.....


Ku tayani da addu'a Allah isa in gama jarabawata asa'a


*KIN CUCE NI*




_Story And Writing_


_By_



(Oum Yasmeen)
And
*_Khadeejarth Sabi'u Yahyah Kaduna_*
(Nainarh KD)_

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k


```_-_Ita Rayuwar Haka Take Muddin Kace Ruwan Wani Bazai Tausa Ba. Tabbas Naka Ko D'umi Bazai Yi Ba. KOMAI YA YI FARKO ZAI YI K'ARSHE```



*Ep two.*



"Hansatu ke nan an faɗa miki ni ɗin shashashar mace ce kamar ke?. Wannan zamanin kissa da kisisina sune kawai ke aiki ba boka balle Malam."



Ta faɗa tana sheƙewa da dariya.



"Uhum na lura bakya gane karatun bari ki gani na ci gaba da abin da ke gabana."


Tayi maganar tana kallon Maryamu da ta saki baki tana kallon ta.




*Asibiti Kuwa....*

*Wuraren Ƙarfe Bakwai na Marece.*

Bakinta ɗauke da sallama ta shigo Room ɗin.
Inna Salame dake naɗe Sallaya ta dubeta ta ce.


"Naseeba kin dawo ke nan nayi zaton ma sai da safe zaki dawo ya hanya ya mutanen gidan?."


"Uhum Alhamdulillah Inna Salame ga abinci na kawo muku nasan bakici komai ba tun safe kiyi haƙuri kici abincin ki kwantar da hankalin ki in sha Allah komai mai wucewa ne a Rayuwa, Ilham zata warke garau Bi'iznillah."


Shiru Inna Salame tayi domin ba abin da zata iya faɗa koda zatayi Maganar kuka ne, zuciyarta a karye take, ta dubi gadon da tilon Ɗiyar tata take kwance rai a hannun Allah Hawaye na ƙoƙarin zubo ma ta, tayi saurin sharewa tare da faɗin.



"Bakomai Naseeba na gode da kulawa Allah ya miki albarka."


"Ameen Inna Salame bakomai ke tamkar uwa ce a gareni."



Tayi maganar tana miƙa ma ta Plate mai ɗauke da Jollot na Shinkafa da spoon a ciki ta yadda zata fi jin daɗin ci.



"Naseeba a'ina kika sama wannan abincin haka in ce ba roƙo kikayi ba?."



Naseeba tayi Murmushi.



"Karki damu Inna Salame ba wanda na roƙa dama akwai wasu 'yan kuɗaɗe a jikina shi ne kawai nayi muku girki ko kin manta abin da na karanta ke nan fannin girke girke?."


Inna Salame tayi Murmushi kaɗan.


"Ban manta ba kam."


Ta faɗa sannan ta karɓa plate ɗin abin cin ta fara ci. Naseeba ta miƙa ma ta Ruwan Pure Water da ta siya musu a hanya ta na faɗin.


"Wai kuwa nace ya ake ciki maganar Yayah Aryaan ɗin, kin sama wayar da za'a kira lambar nasa ne?."


Inna Salame tayi shiru zuciyarta cike da rauni, Naseeba ta famo ma ta inda ke ma ta ƙaiƙayi.


"Ina fa har yanzu dai shiru na samu wata ta aramin wayarta ɗazu na kira lambar ba'a ɗauka ba da yake flashing ne, kuma mai wayar ta ce lambar bana nan ƙasar bane, kuma yana jan kati sosai wurin kira."



"Bana nan ƙasar ba, ikon Allah no wonder tunda ya tafi shiru bai dawo ba har yanzu amma kam Fateesa da Mahaifiyarta har da kakarta sun cuceki sai dai Allah yana ji kuma yana gani talala ya yi musu da sannu zasu girba abin da suka shuka Azzalumai kawai."


Naseeba ta faɗa cike da jimamin lamarin. Inna Salame kam shiru tayi tana kuma duban 'yar ta ta dake halin rai ko Rayuwa, sun daɗe basu sama haihuwa ba daga ƙarshe har sun cire rai da samu cikin ikon Allah da nufar sa sannan da yardar sa ta sama juna biyu duk da a lokacin sun fara manyan ta haka ta raina cikinta cike ta kulawa har Ubangiji ya nufa ta haihu, a tunaninta haihuwar nata zai canza gaba ɗaya Ƙaddarar da kallon da ake ma ta na juya, ashe abin ba haka yake ba a lokacin ne ta fara ganin jarabtar uƙubobi kala kala daga hannun mutane ba ita kaɗai ba harda 'yar nata da ta haifa kwayar idanunta ya banbanta dana sauran mutane da Sanadin hakan har uban 'yarta mahaifi ya tsaneta yake ganin ba 'yar sa ba ce, tun tasowar Yarinyar da girman ta bata san wani soyayya daga wuri ubanta ba sai kyara da hantara wasu lokutan har da duka da zargin ta yana kiranta da Aljanna mai shuɗayen idanu, ba daga garesa kaɗai take kwasan wannan uƙuba ba har ta wurin mutanen Gidan su bata tsira ba balle uwa uba mutanen gari haka Rayuwar Ilham ta taso cikin kyara da hantara daga kowa gani ake ita ɗin BA MUTUM BACE (By M Lumu) don kawai idanunta sun kasance shuɗaye.



Inna Salame taja gauron numfashi tana sauke idanunta daga kallon Ilham tare da lulawa Duniyar tunanin Rayuwar ta a baya Asalin ta...


*WAI WAYE.....*


Tunda daga bakin titin unguwar ƙoƙi kace a kaika gidan Malam daudah mai allo za akai ka bama iya nan kadai ba har da sauran unguwoyi da yake babban malamine kuma masani mu hudune gun mahaifan mu yaya inusa ana kiransa da danjuma sai yayata marigaiya mahaifiyar aryan wato A'isha sai Ni salamatu sai dan autan mu Mahmud mun taso cikin so da kaunar juna kowa yasan cikin gari akwai karatu tamkar tagwaye muka tashi Ni da yaya indo komai iri daya mahaifin mu yake mana muna shekara goma sha biyar muka sauke Alkur'ani me girma mahaifin mu bashi da wani buri a lokacin sai na mun ci gaba to Allah be nufa ba kasancewar bashi da wani hali ko wayasan karatun yanzu sai da hali tun muna yarana ya Danjuma Allah yayi mai son kansa a rayuwa ga son kuɗi a na haka ranar nan mun fito zamu gidan kanwar mahaifiyar mu dake goron dutsai wato hajiya Ruqayya Allah yayi mana diri dan haka ko ina zamu da hijabi malam ya harya gashi da korar mutane kunsan dai da ba adamu da mota ba sai tafiyar kafa haka muna tafi muna hira ji mukai ansha ga ban mu wani kyakkyawan matashine alokacin zaiyi shekaru ashirin da takwas da haihuwa sanye da jamfa da wando kallo daya zakai mai kasan dan gidan manyane kuma buzu ga wani uban saje ya kwanta mai sai sheƙi yake ba wanda
Zai yi zaton cewa ya iya Hausa shagala nayi da kallon sa yace


"Bayin Allah dan Allah kuyi haƙuri na tare ku a hanya,

Yaya indo ce ta dauke kanta taja hannuna zamu tafi nan fa ya karya lagwonmu yace


"Dan girman Allah da Manzonsa ku tsaya,

Cak muka tsaya saboda an hadamu da fiyayyan halitta murmushi yayi har dimple din sa ya lutsai yace


"Dan Allah ina ne gidan ku da yake ba kamar lokacin yanzu ba waya bata karɓo ba sannan dan Allah ya sunan wannan ya nuna yaya indo,


Kamar ya asurce ni nace


"Sunan ta A'isha sannan mu yan gidan malam me allo ne,


Limshe kyawawan idanuwansa yayi yace


"Masha Allah nagode sunana abdulyasar turaki turba yana gama fadar haka ya juya ya hau mashin ɗinsa ,

Mamaki ne ya kusan karni nace


"Yaya indo kinsan wannan zuri'ar ta turaki turba?,


Shiru tayi sanan tace


"Haba salamatu kaf kano wane beson wannan family ba ai sunyi suna ,



"Amma kuma anya hausawa ne ?,


Dariya tayi tace


"Da kin sani kafin ya tafi kin tambaye shi ko mu bishi mu tambaye shi,


Nan muka rufe babin hirar muka dau wata har muka isa goron dutsai sosai Hajiya Ruqayyah tayi murna da ganin mu tace


"Yau Asma'u ta tuna zumunci ta toroku sai de tazo ba dai kuzo ba,


Dariya nayi da yake yaya indo bata da magana nace


"A'a yauma dan dai bamu da makaranta ne shi yasa muka zo makaranta ke hana mu zuwa kuma kinsan malam baya son mu dinga fita,


Haka ne yarnan ya'ya mata sai da sa ido da kafkaf da su


Sai karfe hudu muka dawo gida shaf mun manta da maganar abdulyasar bayan mun gama cin abinci mun idar da sallar isha Muna zaune muna hira autan hajiya yana kusa da ita suna cin gyaɗa bamu da kuɗi amma bamu san me ce damuba wani yaro dan maƙotan mu yashi go yace


"We inji wani yana sallama da A'isha,

Hajiyar mu tace


"Je ka kace tana zuwa da yake ita burin ta be huce ta aurar da mu ba,


Yaya aisha tace


"Hajiya ban son kowaye ba fa gashi bacci nake ji,


Dan murmushi tayi irin nasu na manya tace


"Ɗazu yazo ya tambayi izinin malam shi yasa ma nace kifita kuma malam ya bashi izini,


Tashi tayi badan ta so ba ta zunduma hijabinta fita tayi kamar ance ta dago sukai ido hudu da abdulyasar......✍️

*KIN CUCE NI*




_Story And Writing_


_By_



(Oum Yasmeen)
And
*_Khadeejarth Sabi'u Yahyah Kaduna_*
(Nainarh KD)_


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

_Ep 3_


"Assalamu Alaikum WarahamatuLlahi Wabarakatuhu."



Ta masa sallama da kyar mamaki bai kyaleta ba na Ganin sa.


Yana sakar ma ta wadataccen murmushi ya ce.


"Wa'alaiki Salam WarahamatuLlahi Wabarakatuhu Barka da ƙari sowa Gimbiya."


Tayi Murmushi kaɗan ba tare da ta ce komai ba, domin ba tasan menene zatace ba.


"Nasan zakiyi mamaki na ganina yanzu daidai wannan lokaci sai dai ba abin mamaki ba ne wannan duba da yadda lokaci guda da ganin farko kikayi Nasarar sace Zuciyata har nake tunanin ki zama mata a gareni uwar 'ya'ya na."


Aisha ta zaro ido jin abin da ya ce.


"Haba Bawan Allah daga

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login