Showing 6001 words to 9000 words out of 17109 words

Chapter 3 - ALJANA CE KO MUTUM. complete Hausa Novel

Nusnim   

07 Oct 2024

2643

awwal yace sameeratu wai bamu iso bane! wlh nagaji nikam, sameeratu tace yi hakuri saura kadan mukarasa, Allah dai ya kaimu lafiya amin.

*Ambar* ne zaune da kiyara suna hira sai sukasa ajuyo musu madubin dazai sada su da ameenatu bin saifulllah , aiko anajiyo dashi sukaga abu bakin kirin, Akbar yayi saurin mikewa, yana cewa garin yaya wannan abun yafaru?tayaya ba aganin hoto? kiyara tace lallai akwai wani bakon al'amari ayi sauri aje abin cika, sannan kuma akira sameeratun nawwara , labari yaje kunnan sarki shima hankali tashe don ba'a taba mishi irin wannan abun ba.
kiyara ta dawo cikin sauri tace babu sameeratu , nan take aka bude madubin da kyar , kafin subude su nawwar sun Isa ga ameenatu , duk sun kashe masu tsaronta da ayar Allah, sameeratu ta rungume ameenatu bin sai fullah, daidai lokaci sarki dasu ambar, suka hango abunda ke faruwa, ambar yasaki wani irin gigitaccen kara nabakin ciki, saida su sameeratu sukaji , ameenatu tayi saurin cewa maza maza kuzo mu wuce dan sun ganomu, su nawwar gabansu sai faduwa yake, yana ta karanto addu'a" haka awwal ma.
sarki yace garin yaya haka tafaru bil adama har suka samu damar daza su shigo mana duniyar mu, cikin huci kiyara tace wannan duk aikin sameeratun nawwara ce, ambar yace mufar musu baza abar su da rai ba.
nawwar suna ganin bak'in abu natasowa da sauri duk suka tsorata , sameeratu tace ameenatu kiyi sauri kifitar da mu gasu nan zuwa, tace to ni yanxu ina zamuje, nawwar yayi saurin cewa musauka aduniyar mu kawai, aiko dafda wani guguwar iske ya kusa dasu suka mace bat, cikin nasara, sai gasu aduniyar bil adama, cikin office din doctor awwal , suka zube akasa awwal da nawwar kamar wasu matattu, can suka farfado bakinsu d'auke da addu'a' nawwar yace anya baza su iya biyo mu nan ba? aminatu tace a'a, nayi wani abun da baza su iya gano inda muke ba, nawwar yace akwai wani gdna dake kusa da asibitin nan, yakamata muje can.
suka ce to kowannan su zaune awwal dai shiru yayi don sai yanxu yakejin gajiya, bayan kwana daya da dawowan su duk kan su zaune afalo, idan kuka ga sameeratu da ameena bin saifullah sai ka rantse da Allah mutanene, sbd idan zasu hadu da bil Adam sukan fito asuffan mutane , yauma hakan takasance .
nawwar yace naje nasamu malamina nayi mishi bayanin komai, kuma ya amince dashima yataimaka mana , gashinan zuwa nan da yan mintuna, don agabanshi za awarware wannan kullalliyar al'amarin, amenat tace tabbas kayi tunani nawwar , hakan nada kwau ,bata gama rufe baki ba mallam yayi sallama , suka amsa nawwar yanuna mai waje ya zauna" duk suka gaisar da malamin.
saida mallamin yayi doguwar addu'a sosai sannan ya bukaci ameenatu bin saifullah data bayyana wacece sameeratun nawwara" kowa ido yazuba mata donson jin abun da zata fada, tace Allah y gafarta mallam sameeratun nawwara takasan ce ajinsin_____?

*kubiyoni agaba* don jin me zai faru.

*EDITED by UMMEE* *ADNAN*

TAKU A KULLUM UMMU RUMAN

*KUYI HAKURI DAJINA SHURUN KWANA 2 HAKAN YA FARUNE ASANADIYYAN LALACEWAN WAYAR TAWA AMMAN YANXU ALHMDLLH KOMAI YA DAI²TA*
*nusnim*
*pyar*
[1/11, 4:39 PM] ‪+234 806 448 1931‬: *ALJANA*
*CE*
*KO*
*MUTUM*

*By* *Nusnim*

3⃣6⃣➡4⃣0⃣


A hankali *Ameenatu bintu saifullah* tace Allah ya gafarta mallam hakika sameeratun nawwara ta kasance acikin jinsin bil adama gaba da baya, awwal ya zaro ido, yayi saurin cewa kina nufin asalinta mutum ce ba aljana ba? tace tabbas mutum ce ba aljana ba, nawwar da nawwara sai kallon aminat suke cikin mamaki da d'aurewar kai.

Nawwar yace ameenatu munaso kifad'a mana tayaya sameeratu tazama aljana" alhalin kuma kince asalinta mutum ce, daman mutum na rikid'ewa ya koma aljan? ta dago ido ta kalli mallam da baice dasu komai ba sai kallonta yake hana nazarin wasu abubuwan" ta juya takalli su nawwar da suka zuba mata ido suna jiran amsarta,
sannan ta maida kallon ga sameeratu data matsu taji ko ita wacece' dafata tayi ,tace karki damu yau zakiji asalinki" kuma zakiji ko suwaye iyayenki.

🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹
*shekaru bakwai*
*da suka wuce*
🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸
Akwai wani bawan Allah me suna Alhaji idrisa da matarsa hajiya maimuna, dukkan su haifaffun garin kano ne, Alhaji idrisa dan kasuwa ne kuma Allah ya hore mashi arziki, babban danshi na mijine me suna muktar, sai nabiyu mai suna isma'il sannan na uku macece mai suna sauda sai abba, sameeratun nawwara sannan zainab, yayanshi biyar kenan ukun sunyi aure , sai yarage daga sameeratun nawwara sai zainab.
sameeratun nawwara yarinya ce me hazaka sannan tana da kyanta daidai gwargwado, tsakaninta da kanwarta zainab babu wani jaa, don ba ayaye sameeratu ba aka samu cikin zainab.

gidan Alhaji idrisa babba gida ne, daya gada ga iyayensa" gidan hade yake d gdan gona, ko ta ina acikin gdan akwai bishiyoyi, kama daga bishiyar mangwaro, kashu, Tsamiya, dalbejiya, zogale, kukan Fulani, da dai sauran su"" lokacinda sameeratu na karama mamanta kan shimfida taburma da yamma sai ta ijye nawwara akai ita kuma tana aiki ga kuma tsohon ciki datake fama dashi, da haka sameeratu take gangarawa cikin wayannan bishiyoyin tayita wasa da y'ay'an aljanu, duk mahaifiyarta bata sani ba, dan duk sanda ta gama aiki tazo d'aukarta, zata isketa a inda ta barta" da haka yarinyar tasaba dasu, yakasance duk lokacin dabata je wajanba ta dinga kuka kenan, tun mahaifiyarta na hanata har ta kyaleta.

akwai wani rana da ake meeting na aljanu, wacce shugaban aljanu itace *gimbiya sameeratu* ta garde akan kujeranta na sarauta kowa na girmamata, ga kayan marmari anjere mata agabanta, alokacin ne hajiya maimuna ta ijye nawwara agefenta don tayi sallar magriba afalo, tafara sallah bada dadewa ba nawwara ta rarrafa tafito waje har ta Isa wajan da aljanun suke taro ba su lura da itaba, sai dataje daidai kusa da gimbiya sameeratu, sukayi ido hudu, abunka da yaro sai nawwara tasakar ma gimbiya sameeratu dariya, itama ta maida mata tare da daukan nawwara tabata kayan marmarin dake gefenta, tundaga lokacin gimbiya sameeratu taji tana son nawwara, alakacin ne ambar yaji shi bawadda yake so aduniya irin nawwara.
dahaka dai nawwara tashiga ran aljanu, amma tana karamanta ne take ganin su, data fara girma sai sukayi kamar sunbarta , alhalin basu barta ba, Alhaji idrisa yasa ansare duka bishiyoyin gdansa inda yatada Gini aciki, sare bishiyoyin nan bakaramin tashin hankali ya afku a duniyar aljanu ba" don alokacin daza asare bishiyoyin gimbiya samiratu tana kwance tana hutawa, abun ya afka da ita daidai tsakiyar cikinta aka sare, sai yatsar ta mai duke da wani shegen zobe mai kyau yafado kasa, daidai saitin dakin nawwara" .
anan rai yayi halinsa, duniyar aljanu sungirgixa da mutuwan gimbiya sameeratu, sarki gulmiyanu yayi takaicin rasa yar'uwar shi da sauran aljanun su," mutumin dayasare bishiyar ba ayi kwana biyu ba yarasu , mutane suka fara jita jita akan cewa ai bishiyan daya sarene agdan Alhaji idrisa na aljanune, kuma ba shakka su suka kashe shi, kuma daman sai da akace ma alhjy karyasa asare don dadewar bishiyoyin , yace shi sam bai san da wasu haittu aljanu ba, kuma koda akwaisu badai a gidansa ba"

bayan mutuwan gimbiya sameeratu da sati daya, nawwara ta tsinta wannan zoben gimbiya akofar dakinta, taji yabata sha'awa tasaka a hannunta, ya mata kyau sosai.
suko can duniyar aljanu sun kudirta aniyan raba alhaji idrisa da farin cikin shi kasan cewa Allah ya daura mai son nawwara, gashi yarinyar akwaita da haddan alqur'ani akanta,tana zuwa islamiya sosai.
tun lokacin data sa zoben nan taji kamar bata da lafiya, kuma tayi rauni akaratunta, tun mahaifiyarta namata fada har tagaji takyaleta, ikon Allah kuma babu wanda ya ta6a lura da zoben hannun ta.

akwai wata rana taje islamiya taji sam takasa zaman ajin duk ranta abace yake kuma tarasa dalili' tashi tayi tafita waje tasamu wuri ta zauna' me zai faru kawai sai jitayi ance sameeratun nawwara kitaho gareni zan yaye maki damuwarki' zan baki duk wata kulawa data dace ke tamuce har abada, a tsorace take waige² bataga kowa ba" mikewar dazatayi saiga___?

*EDIDTED by UMMEE ADNAN*

TAKU UMMU RUMAN

*nusnim*
*pyar*
[1/11, 4:39 PM] ‪+234 806 448 1931‬: *ALJANA*
*CE*
*KO*
*MUTUM*
*By* *Nusnim*

4⃣1⃣➡4⃣5⃣

Mikewar dazatayi saiga maciji yayi saurin bi ta kafafunta, tasaki wani uban ihu tare da sumewa kasa , nan take yan makaranta suka rufa mata, aka kira mallamin su, yasa yan ajin sanawiya su dauke ta sukaita aji.

yasa aka kawo mai ruwa a kofi yayi addu'oi aciki ya watsa mata fuska, a firgice ta farka tana cewa gasunan suna kirana, wayyo Allah zasu..... mallam yayi saurin cewa suwaye ke kiranki nawwara?

kasa magana tayi ta tafi suuu zata fadi aka tare ta, shugaban makarantar ne yazo, yace yana ganin alamar jinnu ne ajikin yarinyar nan" ayimata ruqiya agani idan aljanun ne za'a gane" mallamin su yace hakane don nima nayi tunanin haka.

nan aka shiga yiwa sameeratun nawwara ruqiya , nanda nan aljanun suka bayyana ajikinta, alokacin ambar ne ajikinta, abisa umurnin mahaifinsa dayace yasoma bayyana gareta " don ya isar musu sakon dasuke dashi.

mallam yace kai waye' kuma me kuke nema awajen wannan baiwar Allah'n, me tamuku kukeson cutar da ita? shuru ambar yayi' mlm yace zakuyi mgn kosai na kona ku da ayar Allah, cikin wani irin murya da babu dad'inji ambar yafara magana "" yace mallam kar ka kona mu zamu fita dama sakone muke son isarwa ga mahaifinta" kiransa zakayi mufad'a masa ko kai zamu barwa sakon ka isar gareshi!"

mallam yaga idan yace akira mahaifin nawwara ana iya d'aukar lokaci, ga yarinyar nabuk'atar taimakon gaggawa" tunda sunce zasu iya bada sakon aba mahaifinta ai shikenan' yace wace irin sako ne! kafad'a zamu isar zuwa gareshi"


ambar yayi wata irin dariya tukum sannan yace ciki tsawa mallam muna so afadama mahaifita zamu dauke sameeratun nawwara zuwa duniyarmu......

mallam yace wa'iyazu billah meyasa zaku aikata wannan mummunan abun, ambar yace sbd mahaifinta yaraba mu da farin cikinmu, saboda haka muma zamu rabashi da farin cikinsa ta hanyar d'auke y'ar wacce yafi so aduniya" daman kuma tamuce.

mallam yace menene wannan abun daya rabaku dashi!, ambar yace yasa ansare bishiyoyin dake gdansa batare daya sanar mana ba, balle mu kwashi muhimman ajiyarmu' kuma alokacin gimbiyarmu me suna sameeratu, tana kwance akan gadon hutawarta abun ya afka da ita' da sauran yan uwan mu, saboda haka baza mu yarda ba, muna so a Isar masa da wannan sakon" mun sassauta hukuncinmu akansa ne sbd sonda muke ma nawwara" badan hakaba damun dad'e da d'aukar mummunar fansa akansa"

kafin mallam yace wani abu har yafita daga jikinta , ita kuma sai tari take aka bata ruwan addu'a tasha sai bacci ya dauketa.

Bayan kwana daya da faruwan haka shugaban makarantansu da mallamin ajin na su suka je gdan Alhaji idrisa , bayan sun gaisa ne suke bayyana mishi abunda ke faruwa, yace sam shi bayyarda da wasu aljanu ba, yar shi kuma bazai wuce maleria bane ke damunta, ai wannan ma tatsuniya ce, aljanun banxa aljanun hufi, duk wannan ta tsuniyace, da karyan yara, mallam yace a'a Alhaji, kar kamanta fa Allah da kansa yana fad'a acinkin alqur'ani cewa ( *wama khalakatul jinna wal insa illa liya'a budun* _bamu halicci mutane da aljanu ba face dan su bauta mani_ )


Ashe kuwa kaga aljanu gskya ne, su suna ganin mu amman mu bama ganin su, kuma maganan gsky sare bishiyan nan da kayi batare da kasan matakan daya dace kayiba kafin hakan akwai matsala, sannan kasan bishiyoyinnan sunyi sama da shekara talatin da y'an doriya ba asare su ba sai yanxu? kaima kasan dole asamu matsala,

zaman lafiyarka da iyalinka shine kabasu hakuri, inba haka ba, watarana zakayi kuka da idanun ka, don bakasan kaidin aljanu bane shiyasa, muna kara baka shawara da kabasu hakuri kawai" dan tsira da iyalanka"

, Alhaji idrisa mutum ne mai taurin kai da kafiya akan ra'ayinsa, da kuma karyata aljanu, ya tashi cikin fushi yace mallam dan Allah kutashi kutafi sun dad'e basu dauke ta dinba makaryata kawai, cikin fushi suma suka bar gdan.

aljanun sunji duk abunda Alhaji idrisa yace, kuma sun dau alwashin sai sun dauke sameeratun nawwara, duk ranar da taje islamiya sai suntashi mata kuma sai sunkara fada zasu sace ta.

Ranar jumma'a sameeratun nawwara taci kwalliya zataje gdan yayar babanta ta gaidata daganan ta wuce shagon dinkin su"" dayake tana koyan dinki, bayan taje gdan goggon nata ta wuce shagon su, kawar tace khadija tace kin makara nawwara yau nariga ki zuwa , nawwara tayi murmushi" tace wlh nabiya gdan goggona ne, Ayya ke kadai ce ashagon ina aunty marry, khadija tace taje kasuwa ,ok, nan sukaci gaba da hirar su har la' asar tayi, nawwara tace Khadija bara nashiga gdansu baba rabi nayi sallah tunda ke kina fashin sallah, tace to fad'awa duniya bana sallah yau takarashe fad'a tana dariya, nawwara tayi dariya.

ta kama hanyar zuwa gdan kenan sai ga wani guguwar iska yataso ya dumfaro nawwara, kiyara ce tazo ta dauke ta, tun daga lokacin nawwara bata sake sanin ita wacece ba, kawai ta ganta ne aduniyar aljanu , duk sun tsafeta da abubuwan su tazama irinsu, amma kuma kana ganin nawwara sai kace ruwa biyu ce, wato aljana da mutum, haka takoma"" wannan zoben dake hannunta shi yakara bata duk wani karfin tsafi, shiyasa tazama kamar aljana, amma kuma akwai wajajen dabaza ta iya zuwa ba aduniyar aljanu, kasan cewarta ita ba asalin aljanar bace.

in baku manta ba ko wajan da aka daure ni bata karasa daku ba sai da kafa fuwanku kuka karasa, sbd batada karfin isacan, da sunyi niyyan kasheta ne sai ambar yace yana sonta , acan kuma duniyar bil adama, khadija tajiki shiru baki dawo ba.

nan aka bazama neman nawwara lbrin batanta yazagaye ko ina, har makarantar islamiyar su, mallaman su sunyi takaicin haka' shiko mahaifinta kamar zaiyi hauka, yana cewa karya kuke kud'auke min yarinya ta, yayi ta sambatu yana tsine musu, abu wasa² har anfidda tsammanin ganinki, kowa ya dangana anmik'ama Allah lamuransa"

sai bayan batanki ne mahaifinki yafara daya sani sai alokacin mahaifinki yayarda da akwai aljanu, shi sam daya karyata aljanu, yana ganin duk karya ne, damuwa tamasa yawa' wanda hakan ya kwanta ciwo na tsawon shekaru biyu sannan y warke duk yan uwanki sun dangana.

ke kuma kina can kina rayuwa da aljanu, sun gusar miki da kwakwalwa, wannan shine abunda ya faru deke nawwara, awwal saida ya zubda hawaye , nawwar yace wai meyasa mutane ke son karyata aljanu, bayan kuma Allah yafada, da akwai, acikin aljanun ma akwai masu bauta mai, kamar yadda akwai amutane akwai musulmai a kwai kafurai, sameeratu dake zaune tazuba musu ido tarasa meke mata yawo a kwakwal warta.

nawwar yace to meza ayi mata ta dawo yadda take cikakkiyar mutum,ameenatu bin saifullah tace kunga wannan zoben dake hannunta za'ayi kokarin cireshi, sannan kuma sauran aikin malllam ne yasan yadda za'ayi.

mallam ne yayi magana yace nawwara ba ita kadai bace akwai gimbiya sameeratu ajikinta kuma karya wayannan asiren dake jikinta bakaramin aiki bane, zamuje da ita Maiduguri, don nikadai bazan iyaba , bai gama rufe bakinshi ba sukaji gdan y girgiza yayin da nawwara ta xube kasa wani bakin abu nafita Daga bakinta,duk kan su suka nufo kanta cikin tsoro wutan dakin ya dauke ko ina bakin kirin.

*EDIDTED* BY *UMMEE* *ADNAN*

TAKU UMMU RUMAN

*Nusnim*
*pyar*
[1/11, 4:39 PM] ‪+234 806 448 1931‬: *ALJANA*
*CE*
*KO*
*MUTUM*
*By* *Nusnim*

4⃣6⃣➡5⃣0⃣

wutan dakin ya dauke ko ina bak'ik'irin baka iya ganin komai" ameenatu bin saifullah tace mallam ya kamata kayi wani abu don suna dab da isowa inda muke, kuma ga nawwara cikin wani yanayi, wannan bakin abun dake fitowa daga bakinta alamun suna son fitowa ta jikinta ne, wanda hakan daidai yake data rasa rayuwarta, nawwar yana jin haka yace mallam kataimaka dan Allah.

bani son in rasa nawwara arayuwata" shikansa mallm al'amarin yasoma firgitashi' bayyi tsammanin abin yakai hakaba' karatu yasomayi cikin gaggawa, suma su nawwar suna karanto duk ayar datazo abakinsu"saida sukayi kusan minti 30, sannan hasken dakin yasoma dawowa , gdan kuma yadaina girgiza, nawwara ta bud'e ido, sai dai takasa magana, sai binsu take da kallo
kamar wata tab'abb'iya.

*DUNIYAR ALJANU*
lokacin da su ambar suka karaso basuga su ameenat bin saifullah ba' don sunriga sun bace musu, sunyi sunyi su bisu amma ina sun kasa" sarki yayi takaicin haka sosai, suna tunanin ta ina zasubi suje duniyar bil adama, saboda wani katanga dake tsakanin su, sunyi tsafin su amma ina sunkasa rusawa, shine suka yenke shawaran fitowa ta jikin nawwara, amma

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login