Showing 3001 words to 6000 words out of 17109 words
haka tayi ta bibiyar rayuwar nawwar da yadda yake tafiyar da ibadunshi, anan take son nawwar yasoma mamaye duka sassan jikinta, taji bazata iya rayuwa batare dashi ba" tun daga lokacin zuwa duniyar bil adama yazame ma sameeratun nawwara wajan zuwa,,tun tana zuwa ma nawwar amafarki, har takai da zuwa mai azahiri, anan ne shima yasoma kamuwa da son sameeratun nawwara, yakasa tantan cewan *Aljana ce ko mutum?* kuma taki bashi dama yamata tambayoyin dazasu gamsar dashi, taki gaya masa wacece ita, yana cikin tsaka mai wuya.
*wannan shine mafarin kulluwar soyayyar su*
*******************bayan nawwar yatashi daga bacci awwal yasa aka kawo mishi abinci yaci" sannan yabashi magani yasha, Dr awwal ya gyara zama da kyau ya kalli nawwar, wanda haryanxu tun tashinsa baiyi magana ba.
Dr awwal yace nawwar meke damunka halan? jin yayi shuru bai amsa masa ba, yakuma cewa wani irin damuwa kasama ranka haka? wanda ke barazana da lfyr ka, duk irin amintar dake tsakaninmu ka kasa fada min matsalarka?, kana wasa da lafiyarka nawwar, gashi ciwon zuciya na kokarin kama ka, what" sai a sannan yayi mgn, ciwon zuciya fa kace doctor, kai ya d'aga masa alamar tabbatarwa, mekasa aranka haka? me kanema karasa, me kakeso wanda baka samu ba? kana so ka kashe kanka ne, kar ka manta kaifa likita ne, mai kare lafiyar al'umma, to meyasa kai kake wasa da taka lafiyar?
hawayenda awwal yagani a idanun nawwar shiyasa shi saurarawa ga tambayoyinda yake jero masa, jikinsa yayi sanyi, duk yabi ya rude, yasan ba karamin abu zaiza jarumin abokinsa kuka ba" haba nawwar meye damuwarka? kafada min ko zan iya taimaka maka," nawwar ya kalli auwal, yace duk akan *SO* ne awwaal,,Allah ya jarrabi zuciyata dason *AlJANA* bama *MUTUM* ba, a tsorace Dr awwal ya mike tsaye da sauri, yana yima nawwar kallon wanda yayi gamo, yace anya nawwar kana cikin hankalin ka kuwa, kataba ganin Inda akayi soyayya tsakanin aljana da mutum , wlh nawwar kayi gamo, kana bukatar rukiyyar gaggawa, idan ma mafarki kakeyi,kara ka farka, wannan abu ne da bazai taba yuwa ba" kafin nawwar yabashi amsa sai ji sukayi ance , karya kakeyi awwal sai na auri nawwar koda zan rasa raina ne wlhy saina aureshi, ae tuni awwal ya kwasa a guje sai bayan kofa yana salati jikinsa na karkarwa"
*EDITED* *BY* *UMMEE* *ADNAN*
_TAKU UMMU RUMAN_
*nusnim*
*pyar*
[1/11, 4:39 PM] +234 806 448 1931: *ALJANA*
*CE*
*KO*
*MUTUM*
2⃣0⃣&2⃣5⃣
taci gaba da cewa awwal karka shiga hurumin da ba naka ba, kar kasa nawwar ya gujeni, zuciyata bazata iya jurar rashin saba" awwal ina matukar son nawwar" idan ban sameshi ba banajin zan cigaba da numfashi a duniya!! shi dai nawwar yananan akan kujera ya zuba maa sameeratun nawwara ido, cikin wani irin matsanancin sonta" dakuma jindad'in ganinta aransa' tabbacin yanxu andaina azabtar da ita kenan, kamar yadda matar nan tafad'a masa"
awwal da har yanxu yananan a bayan kofa' ji yake kamar kasa ya bude yanitse aciki, saboda tsabagen tsoro' tuni ya rufe idanunshi, cikin dauriya yake cewa baiwar Allah kiyi hakuri baso nake nashiga rayuwarki ba, ina so ne inceto amini na daga hadarin daya shiga" sbd zuciyar shi tana dab da bugawa" wanda hakan zai iya rasa ranshi ako wani lokaci ta dalilin sonki" nawwar ya runtse idanunshi, ya juya da kallonshi wajan awwal, yace aboki na taho ka zauna baza ta maka komai ba!!! saneeratun nawwara tayi dan murmushi, tace awwal kenan, ni ba muguwa bace kuma banida niyyar cutar da mutane, kasaki jiki dani, kutaimaka ma rayuwata kai da nawwar.
sai alokacin nawwar yafara magana yace baiwar Allah me na mikine kike wahalar da rayuwata? kin hana min sukuni"" sonki yana azalzalan zuciyata, ban taba zama nayi second guda ba tare da tunaninki ba, sannan kuma ban san ke wacece ba? ban san ke wace jinsi bace? shin ke ALJANA ce ko MUTUM? meyasa kuma kika zabe ni amatsayin nazama abokin rayuwanki? dan Allah don son annabi ki amsa min tambayoyi na, shima awwal dake mak'e haryanxu a bayan kofa yace kitaimaki abokina please.
Ta numfasa tace duk naji bayaninku, tabbas baku san koni wacece ba' hakazalika nima bansan nid'in wacece ba" illa abunda nasani shine!!!
sunana sameeratun nawwara, nakasan ce aduniyar aljanu' nataso naganni a fadar sarki *GULMIYANU* tare da ya'yan shi biyu mace da na miji *Ambar* da *kiyara* ambar ne yake son aure na, ni kuma bani sonshi adalilin hakan ne nake fuskantar mummunar azaba" ban san su waye iyayena ba, kawai nata so naganni awajan kanwar sarki" *gulmiyanu* wato me suna *gimbiya *sameeratu* duk fadin duniyar aljanu ana jin maganar *gimbiya samiratu* sbd ita take mulki alokacin, amma yanxu ta mutu kuma bil adama su sukayi ajalinta, wanda ban san dalili ba" nayi nayi binciki afada min ni wacece amma haryanxu ban samu amsata ba"haka rayuwata taci gaba da gudana.
Akwai watarana da bazan taba mantawa ba ina zaune bakin ruwa ina wasa da tsuntsaye domin suke debe min damuwar dake zuciyata!! sai naji abayana ana min magana juyawan dazanyi, naga wata kyakkyawar matashiya kuma bafulatana" dauke da kwaryan nono tana min murmushi, tace nawwara ko zan iya zama kusa dake? na daga mata kaina tare dayin murmushi, kafin tazauna sai naji tace *bismillahi*sannan tazauna na kara kallonta, itama ta kalle ni, sai naji ta ambato sunana, tace nawwara, nasan baki sanni ba kuma baki taba ganina ba" amma ni nasanki, nasan asalinki, nasan labarinki me dauke da tausayi.
kullum in zan wuce ta bakin ruwannan ina ganinki kina cikin damuwa, abun na damuna" shiyasa nace bari yau nazo nafada miki asalin wacece ke, kuma suwaye iyayenki, kuma infada miki" awani jinsi kika fito , *jinsin aljan* ko *mutum* dannasan shine abinda kikafi damuwa akai" cikin murnata na rungumeta ina cewa nagode yar uwata, tace bakomai, yar fulani taci gaba da cewa amma inaso kimin alkwarin bazaki fada ma kowa idan nafada miki asalinki ba" sbd idan akaji sai ankasheni.
kuma addinina dana su ba daya bane, ni musulma ce sunana *Ameena Bintu saifullah* , taci gaba da cewa nawwara ke diya ce ga abdullahi da asma'u, kin kasan ce ajinsin _____ sameeratun nawara tayi ajiyar zuciya, awwal yace kinyi shiru baki karasa ba,ta dago idonta wanda yayi jajir ta kallesu, nawwar ya rikice yace lafiya nawwara" cikin murya mai rauni tace Aminatu bintu saifullah bata karasa fada min ba, naji tasaki wani uban ihu tafadi kasa, juya wan dazanyi naga *kiyara* ce da wasu kartan maza, su suka aikata ma ameena haka, ashe sunji abunda ameena zata fadamin shiyasa suka mata haka" nashiga rokon kiyara dasu bar azabtar da ameena amma ina, tun ameena tana cewa nawwara ki taimakeni nawwara kitaimake ni, nayi nayi iya kokarina" intaimaki ameena amma ina sun bace da ita!!! nawwar da awwal wanda hawaye yagama wanke musu fuska nawwar yace yanxu ina suka kai ameena bintu saifullah? tana raye ko bata raye? tace tana raye amma tana cikin wani ma ajiyan mu da ake kulle me lefi, tana shan azaba kala kala, banta6a mantawa lokacin dana yima ambar wayau ta sigar soyayya daya kaini wajan ameena dana ganta, da kyar ya amince" da mukaje naga duk ta canxa kamanni sbd azaba, kalmar data fadamin shine, tace nawwara kibazama duniyar bil adama kine mi addinin musulunci domin shi zai iya taimaka miki wajan gano asalin jinsin da kike.
*EDITED* BY *UMMEE* *ADNAN*
TAKU UMMU RUMAN
*nusnim*
*pyar*
[1/11, 4:39 PM] +234 806 448 1931: *ALJANA*
*CE*
*KO*
*MUTUM*
2⃣5⃣&3⃣0⃣
Tun daga lokacin da ameenatu bintu saifullah tace nabazama duniyar bil adama don neman addinin islama"daga ranar na dau niyyar shiga duniyar bil adama, da haka rayuwata taci gaba da tafiya, ba abunda nasa agabana sai neman addinin musulunci, nayi yawo dayawa acikin duniyar bil adama, narasa wazan tunkara da wannan batu nawa" ana haka ne ranar sallar ku ta edi na hadu da kai, alokacin da kake k'ask'an da kanka wurin ubangijinka' kana addu'a, kana niman taimakon Allah.
tun a lokacin naji ka burgeni' zuciyata ta aminta dakai, naji bawanda yadace na tunkara sai kai, daga ranar nafara bibiyarka, atunani na kaine zaka taima kamin gurin gano wacece ni, kuma ka koyar dani addinin islama""nawwar kataimaki rayuwata ina cikin tsaka mai wuya, ka taimakeni ka tsamoni daga duhun jahilci" ta karashe mgnr muryarta na rawa"
Nawwar ya numfasa yace sameeratun nawwara naji bayaninki, amma wannan batu da kika zo dashi daidai yake darasa rayuwar mutum, ayanayin labarin da kika bada na fahimci duk wanda yayi yunkurin taimaka miki gurin gano asalinki, to shima dai dai yake da rasa tashi rayuwar gun wad'ancan azzaluman!!" amma addu'a itace takubin mumini, *innallaha laa' yamli lizholimin.* _lallai Allah baya kyale azzalumai_ da sannu zai nuna musu isar sa....
zan taimaka miki don Allah da kuma son dana ke miki, sannan da yar dan mahaifiyata" idan ta amince shikenan sai mu tsananta addu'a Allah ya mana jagora.
Tace nagode nagode sosai kuma insha Allahu wani abu bazai taba samunka ba, namaka alkawarin haka" kuma mami hafsat baza ta hanaka taimako ba da yardar Allah"" dr awwal ne yayi gyaran murya yace wani hanxari ba gudu ba, kun manta abu guda daya, kar ku manta sai da taimakon ameenatu bintu saifullahi zaku samu cikan burinku, saboda ita ta turo nawwara duniyar bil adama don tasamu mutumin daya rike addu'a don suje su taimaketa tafito daga hannun su ambar, ta bakin ameena ce za agano wacece nawwara!!! yanzu dai abunda zakuyi shine kutaima keta tafito, ko ba hakaba" sameeratun nawwara tace tabbas gskyan kane awwal dole sai yar fulani tafito, amma gurin da take akwai hatsari, nawwar yace karki damu da taimakon Allah zata fito.
toh yanxu dayaushe ne zaka fara koya min addininna ku?, inshaAllah nan da sati daya ok nagode, bayan sunyi sallama sai ta bace.
nawwar da awwal sunshirya yadda zasuyi su samu mami hafsat da wannan zance, labari har yakai kunnan mami hafsat, sai da ta girkiza dajin labrin" amma dayake da awwal ne kuma shi yake mata bayani sai ta amince musu tare dayi musu addu'an samun nasara,nawwar yaji dadi sosai da maminsa ta amince daman mace ce mai hakuri da tawakkali!!!
*wanene nawwar*
da'ne ga alhaji isma'il da hafsat, alhaji isma'il haifaffan garin yola ne iyayenshi duk acan suke gaba da baya shi ba fulatani ne, yayi makarantansa tun daga primary zuwa universty abti yola, yayin daya gama ne, aminin mahaifinshi wato alhaji kasim shiyasa ma mishi aiki a jahar kaduna" isma'il tun yana karami alhaji kasim ke sonshi" anan gdan alhaji kasim na kaduna isma'l ya zauna, yana da yaya mata uku, maza biyu babban dan alhaji kasim namiji ne me suna abdalla, sai ibrahim, sai hafsat da mariya sai khadija autar su kenan, mahaifin isma'il takanas yazo kaduna wajan amininshi alhaji kasim, don ne mama dansa auren hafsat, , kasan cewar dan nasa yaje masa da batun son auren hafsat , alhaji kasim yaji dadi sosai" kuma antambayi hafsat din itama ta amince, mafarin auren iyayen nawwar kenan!!" bayan auren su da shekara biyu Allah ya albarkace su da d'a namiji wato nawwar sai kuma sulaiman, daga sulaiman sai autar mami wato, maryam wace ake ma lakani da mimi, macen ta daya tal maza biyu,, mami hafsat ta bama ya'yanta tarbiya dai dai gwargwado, ga kuma addini daya ratsa jikin su, dukkansu suna da haddan alqur'ani mai girma, don shi sulaiman ma baban malamine a islamiya, yayin da nawwar shi kuma doctor ne, sai autar su mimi itama karatun take afannin boko tana ss 1, afannin islamiya kuma tana *sanawiyya* .
wannan shine lbrin su nawwar.
*****************
*dunyar aljanu*
sarki gulmiyanu ya tara dukkan aljanu yana shaida masu" nan da wata daya za ayi gaga rumin bikin dansa *ambar* da *sameeratun nawwara*, nan take taji gabanta yafadi, shi ko ambar da kiyara me zasuyi inba murna ba har gaban mahaifin nashi yazo yana godiya" ambar ya dago ido yana sakar ma nawwara murmushin samun nasara, sarki gulmiyanu yaci gaba da cewa' nan da sati biyu ina son akashe ameenatu bintu saifullah' cikin tashin hankali samiratu taje gaban sarki ta tsugunna tana rokonshi da abar yar fulani da ranta!!" amma ina sarki yaki amince wa, ganin sarki yaki sauraronta" tuni ta garzaya duniyar bil adama wajan nawwar don neman mafita, tafada mashi abunda ke faruwa shima hankalinshi atashe yana innalillahi wa inna ilaihi raji'un , la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalumin"" ai bashiri nawwar yashiga koyar da sameeratun nawwara addinin islama, addu'oi iri2 yasoma koya mata' kan kace kabo sameeratu tayi zurfi sosai, idan yana koya mata wani abun ma sai ta dinga tunanin kamar ta tabayin abun ada:!!.
akwana atashi ba wuya a wajan Allah, a yaune su awwal da nawwar da sameeratun nawwara, suka shirya hanyar da za adauko *ameenatu bintu saifullah*
_sai ku biyoni agaba don jin shin zasu samu nasarar ku6utar da ameenatu bin saifullah ????._
*EDITED* by *UMMEE ADNAN*
~TAKU A KULLUM UMMU RUMAN~
*nusnim*
*pyar*
[1/11, 4:39 PM] +234 806 448 1931: *ALJANA*
*CE*
*KO*
*MUTUM*
3⃣0⃣&3⃣5⃣
sameeratun nawwara ta kammala shirinta tsaf tare da daukan makaman ta, saboda tsaro , bayan tagama ne ta garzayo duniyar su nawwar , ayayin da ta iskesu suna zaman jiranta shida awwal' nawwar ke kara karfafama awwal gwiwa akan wannan tafiya daza suyi.ganin yadda duk yake a tsorace,
yace haba abokina" kada kabada maza mana' kadafa kamanta *Allah yace yana nan aduk inda bayawansa yake tsammaninsa'*
kasa aranka Allah yana taredamu kumashi zai taimakemu" inafatan dai kayi azkar d'in safiya, da addu'ar dana baaka jiya? murmushi awwal yayi cikeda kwarin gwiwa yace nayi Allah ya taimakemu' Ameen...
Sallamar sameeratu ne ya katsesu da karatun suratul yaseen dasuke bayan sungama karanta wasu ayoyi acikin suratul baqara" takaraso ciki, dukansu suka amsa mata sallamarta,fuskarta dauke da murmushi yayin da take kallon nawwar, shima ya mai da mata martani, tace masu *masa'un khair* suka ce mata *masa'u *noor*.
auwal ne yace ai nayi zaton baza kixo ba, tace tab mai zai hanani zuwa, yanxun ma duk nakosa muje, nawwar yace ' ki kwantar da hankalinki insha Allahu zamu samu nasaran zuwa wajan ameenatu bin saifullah, tace toh Allah yasa nagode sosai" awwal yace ya naganki da makamai, tace ai saboda tsaro na dauko, yayi dariya, yace haba ai ayar Allah kadai ta ishemu makami' sbd haka karki samu damuwa, to awwal, yanxu sai kutashi muje don lokaci na kurewa.
nawwar yace to amma bari mugabatar da addu'a kafin mutafi, suka ce to, nan suka karanta *suratul iklas* *falaq* da *nas* sai *ayatul kursiyu* sannan suka shafa, sameeratu tace kurufe ida nuwanku, yadda ta umur ce su haka sukayi.
*duniyar aljanu* awani kurmin k'ogo suka sauka' tace subude idanunsu" nawwar ne yafara budewa tare dayin addu'ar neman tsari, shiko awwal yakasa bude idonshi saboda tsoro, don bai San me zai fara gani ba idan yabude idon.
nawwar da nawwara suka dubi awwal cikin mamaki, nawwar yace awwal lafiya bude idanunka mana mun isofa, cikin rawar murya awwal ya soma magana , yace nawwar wallahi tsoron budewa nakeyi" sameeratu tace kar ka damu ba abunda zaifaru da kai kabude , nawwar yace haba doctor be a man mana, Kasa aranka kana tareda sojojin kariya daga Allah ,
ahankali awwal ya bude ido shima tare dayin addu'a.
haka sukabi wajan da kallo cikin kurmin dajine , sameeratu tace nayi mana Rabin zuwa, sauran tafiya kuma da kanmu zamu karasa, saboda bani da karfin da zanjamu a iska mukarasa wajan, suka ce to " nan da nan suka doshi hanya tafiya suke sosai kowannan su da abunda yake tunani azuciyar shi, tafiya suke babu kakkautawa, har suka gaji suna samu gefe don su zauna suhuta.
Duk abunda ke faruwa su sariki *gulmiyanu* ba su sani ba' sbd kafin sameertu sutafi sai da taje ta to she madubin da suke ganin hangar da zai sadasu da ameenatu bin saifullah , cikin ikon Allah kuma dukkansu babu wanda ya hankalta da hakan, itako ameenatu tananan cikin dakin azaban da aka ijyeta, tanaji ajikinta sameeratun nawwara natunkaro wajanta don taimako.