
Babban kwamandan rundunar juyin juya hali ta Iran ta IRGC Manjo Janar Hossein Salami, ya tsaya a gaban wata tuta a wani ɗaki na yaƙi yayin da yake waya yana bayar da umarnin ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami 200 kan Isra'ila a ranar Talata da dare, a cewar wani bidiyo da kafofin yada labaran Iran suka wallafa.
Tutar ta nuna hotunan mutum uku, waÉ—anda Iran ta ce za ta É—auki fansar mutuwarsu, a wasu manyan hare-hare - shugaban Hamas Ismail Haniyeh, da aka kashe a Tehran a harin watan Yuli da Iran ta É—ora alhakin kisan ga Isra'ila.
Akwai shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah da kuma wani kwamandan rundunar IRGC ta ƙurdawa Birgediya Janar Nilforoushan wanda aka kashe a wani harin sama na Isra'ila a Beirut a makon daya gabata.
IRGC ta yi iƙirarin cewa hare-haren sun ƙunshi makamin linzami na Fattah wanda ya yi minti 12 ya isa Isra'ila kuma cewar sun yi nasarar abka wa wasu sansanonin sojin Isra'ila da shalkwatar Mossad ta leƙen asirin Isra'ila.
Sai dai, rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta yi nasarar kakkaɓo galibin makaman tare da taimakon Amurka," kuma ta ce "wurare kaɗan ne hare-haren suka samu" a tsakiya da kudancin Isra'ila.
Jim kaÉ—an bayan harin, an É—aga wata babbar tuta a dandalin Falasdinawa da ke Tehran, da ke nuna makamai masu linzami na shawagi.
Iran ta ɗan nuna kamar ta haƙura bayan kisan Haniyeh - amma wannan rashin nuna damuwar ya zama wani abin cin mutunci inda Isra'ila ta sake yi mata mummunan lahani ga ƙungiyar da take goyon bayan Hezbollah, a wani harin ranar Juma'a da ya kashe Nasrallah da Nilforoushan.
Makaman Iran da horo da kuma tallafi sun kasance mafi muhimmanci ga sauya Hezbollah ta zama mai ƙarfi a soji da kuma a siyasance tun da rundunar IRGC ta taimaka wajen kafa ƙungiyar a shekarun 1980.
Kafin wannan watan, shugabannin Iran sun yi fatan yaƙi da Hezbolla zai taimaka wajen gurgunta sojin Isra'ila da ke ci gaba da yaƙi da Hamas a Gaza.
Sun kuma fake da hare-haren Hezbollah na rokoki da makamai masu linzami a matsayin martani ga hare-haren da Isra'ila ke kai wa cibiyoyin nukiliyarta.
Shugaba Masoud Pezeshkian, wanda aka zaɓa a watan Yuli, ya zargi Isra'ila da ƙoƙarin fusata Iran domin neman ɓarkewar yaƙi a yankin wanda zai sako Amurka a ciki.
"Muna son tsaro da zaman lafiya. Isra'ila ce ta kashe Haniyeh a Tehran," kamar yadda kafofin yaÉ—a labaran Iran suka ruwaito shi yana cewa a wata ziyara da ya kai a Qatar a ranar Laraba.
"Turawa da Amurka sun ce idan ba mu rama ba, za a samu zaman lafiya a Gaza cikin mako É—aya. Mun jira su domin samun zaman lafiyar amma sun ci gaba da kashe mutane."
Masu tsattsauran ra'ayi a Iran sun ta yin matsin lamba kan rashin É—aukar mataki kan Isra'ila
Masu sharhi a gidajen talabijin da dama - da ke goyon bayan jagoran addinin ƙasar Ayatollah Ali Khamenei da IRGC - sun nuna cewa matakin jinkiri ga ɗaukar fansa kan kisan Haniyeh ya ƙara wa Firaministan Isra'ila ƙwarin gwiwar kai wa aminan Iran hari a Lebanon.
Bayan harin makamai masu linzmi na ranar Talata, babban hafsan sojin dakarun juyin juya hali Manjo janar Mohammad Baqeri ya bayyana cewa "haƙuri" ya kawo ƙarshe.
"Mun kai wa sansanonin soji da na leƙen asiri hari a Isra'ila kuma da gangan muka ƙi kai wa cibiyoyin kasuwanci da masana'antu," in ji shi. Amma kuma idan Isra'ila ta yi gangancin mayar da martani, namu martani ba zo da daɗi ba.
Hare-haren sun nuna damuwar da ake ci gaba da nunawa kan shugabannin Iran na yin shiru bayan hare-haren Isra'ila wanda zai nuna su kamar suna da rauni - a gida da kuma idon aminan ƙasar da suka haɗa da Hezbollah da Hamas.
Iran da Isra'ila sun daɗe suna yi wa juna barazanar yaƙi tsawon shekaru, suna kan tsarin "ba yaƙi, ba zaman lafiya." Amma yanzu ga alama wannan ya kawo ƙarshe.
Isra'ila ta sha alwashin mayar da martani, inda Netanyahu ya yi gargaÉ—in cewa "Iran ta yi babbar kuskure kuma za ta É—anÉ—ana kuÉ—arta."
Haka kuma an samu sauyin salo da martani daga ɓangaren Amurka.
A watan Afrilu, shugaba Joe Biden ya nemi a kai zuciya nesa bayan Isra'ila da dakarun Amurka sun kakkaɓo makamai 300 da Iran ta cilla Isra'ila domin mayar da martani ga harin Isra'ila a ofishin jekadancin Iran a Syria wanda ya kashe kwamandojin IRGC.
Isra'ila ta yi biris da kiran na Amurka ta ƙaddamar da harin makami mai linzami a wata cibiyar tsaron Iran.
Amma a wannan karon, mai ba shugaba Biden shawara kan tsaro Jake Sullivan ya yi gargaÉ—in cewa hare-haren Iran "ba za su tafi a banza ba" kuma Amurka za ta yi "aiki da Amurka domin tabbatar da hakan."
Kafofin yaÉ—a labaran Isra'ila sun ce a ranar Laraba Isra'ila na shirin kai harin ramuwa kan Iran "a kwanan nan." kuma za su kai hare-haren ne kan muhimman wurare, ciki har da cibiyoyin man fetur.
Jami'ai kuma sun yi gargaÉ—in cewa za a kai hare-haren kan cibiyoyin nukiliyar Iran.
Manyan jami'an Iran sun nuna cewa sun yanke shawar mayar da martani ne kan kisan Haniyeh da Nasrallah da Nilforoushan sai idan an sake fusata ƙasar.
Ministan harakokin waje Abbas Araghchi sun miƙa saƙo ga Amurka ta hanyar ofishin jekadancin Switzerland a Tehran ta gargadin ta cewa "kada ta shiga yaƙin."
Ya yi gargaɗi cewa"duk wata ƙasa da ta taimakawa Isra'ila ko ta bari aka yi amfani da sararin samaniyarta domin kai wa Iran hari, yana nuna ita ma za a iya kai mata hari.
An ƙiyasta cewa Amurka na da dakaru 40,000 a Gabas ta Tsakiya, yawancinsu a Iraƙi da Syria. Waɗannan dakaru za su iya fuskantar barazana daga mayaƙan Shi'a da ke samun goyon bayan Iran a ƙasashen.
Yanzu dole Iran ta yi shirin tunkarar martanin Isra'ila tare da fatan kwalliya ta biya kuÉ—in sabulu kan kasadar da ta yi.
1 Comments
Leave a Comment
Your email will be kept private. Required fields are marked *
Search
Categories
-
(7)
Recent Article
2025 Fully Funded Japanese Government (MEXT) Scholarships at Asia Pacific University The 2025
Read More
Idan Ka Cike Tallafin 25,000 Na Renew Hope RRR Kaduba Wannan
Read More
Best Premium Fonts Pack For Designers 2024
Read More
baba ijebu result for today
Read More
Kasadar Iran ta kai wa Isra’ila hari bayan yin illa ga Æ™awayenta
Read More
Abin da ya sa muka kori Seaman Abbas daga aiki – Rundunar soji
Read More
Shin rikicin Fubara da Wike zai bari a yi zaɓen ƙananan hukumomi a Rivers?
Read More
07, October 2024
School Fee
ghhhhhhhhhhhhh