Showing 15001 words to 17163 words out of 17163 words
Chapter 6 - BABBAR SAKAYYAH BY HAFSAT UMAR DANGORO FRE PEGEs(1)TAKUN FARKO.txt
iskancin "batare da tace Bata amsa ba Tace" Ina NABEHA?" Wakike tambaya kamar yadda kika tafi karuwancin ita Kuma a gida tayi nata Dan Haka kije kinemeta don bazan iya zama da fasika a gidana ba nakoreta kije kinemeta a can waje ba a gidana ba" " hawaye ne suka zubo suka wanke fuskar ta zuciyarta tana tukuki tinawa datai da mafarkin da tayi yanzu Wai dama' dagaske ne mafarkin da tayi innalillahi wa'inna ilaihirraju un ABBO FAHIMNA na tsaneki wllahi kijira BABBAR SAKAYYAH muddum NABEHA ta rasa ranta kema saina kasheki muguwa azzaluma kawai wadda batasan darajar mutum ba Wallahi kinyi asarar rayuwarki kirasa wazaki cuta sai yayan "yar'uwarki tire da wanan hali naki "tana Gama fadar Haka ta juya ta fita daga dakin take tayi Karo da jini akasa duk ya bushe arazane ta sunkuya ta karewa jinin kallo kwalla na bin kuncinta ta dinga bin tsatin jinin har ta Isa waje daga Nan Kuma Bata Kara. Ganin Saba Nan ta tsaya a bakin gidan ta Shiga waige waigen daga Ina zata fara neman "yar,uwarta tabbas tasan idan Bata Nemo NABEHA mahaifiyar su bazata taba yafe mataba.
*DORAYI*
Gabakidaya zaratan Mazan haduwa sukayi a Gidan alhaji ABDULHAMID ME NASARA susu biyar ne akawai abdul kanin mus,af saï muhsin shima kanin mus,af ne sai mus,af baisamu damar zuwaba Yana asbiti ba a sallameshi ba jukin nasa yayi tsanani, saï "yayan uncle ABDULHAMID su uku nafarko shine Fahat sai me bimasa zaidu, sai na ukunsu autansu me suna faruq Gaba daya Haka suka rankaya G.G.S.S dorayi domin Kai ziyara mota 15 ne suka tafi dasu motoci biyu suna tsakaiya sune wadda suke ciki.
__________________________________________________________
Tun da akaji jiniya tana tashi aka shiga bude musu get din makarantar nafisa kuwa tun da taji ance ga alhaji ABDULHAMID ME NASARA ya iso ta Kama kanta tashiga kallon inda motocin za su shigo ,kaitsaye parking space sukayi parking .sai da aka yi kusan minti 5 kafin abude motar sufito wayyo Allah jama,a kuzo kuga kallo a gurin dalibai da malaman makarantar mata abin sai wan da yagani wata marainiyar kwallace me cike da so da kauna ta soma fitowa daga idon nafisa tsabar so da kaunar alhaji ABDULHAMID da take Masa tabbas yau Allah ya cika mata burinta taga jaruminta wan da ta Dade tana son gani , fateema kuwa kallon ta ta tsaya tana yi Tace" nashiga uku nafisa wanan wane irin so kikewa wanan mutumin tun kan kisan zaki ganshi zuciyarki takamu da sonshi acikin sakonni kawai sabi da jin labarinsa da kikayi Anya kuwa nafisa wanan so haka?" "Uhm! Bazaki gane ba fateema son sa ajinina yake Dan allah fateema inason na tsaya kusa dashi na tabashi ko zuciyata zata Sami sassauci " "ke baki da hankali tafada tare da zaro ido kinsan saye shi kuwa,nafisa kodai son shi kike kikeson aurensa ?" Aurensa Kuma Baki Gandhi ba me a haihuwar kaji ya haifeni Dan Allah ki bar maganar Nan bakiga yaransa ba ne" au toenene aciki Dan kin soshii da aure " a,a ba Haka nake nufi ba kawai dai BURINA na rungumeshi "suna cikin wanan maganar Basu rufe bakiba suka jiyo karar bindigu suna tashi tako Ina ga jiniya ta motocin sojoji abin dai gwanin Sha,awa gaba daya student din Ido suka zuba domin ganin me su zuwa shiko alhaji ABDULHAMID farinciki ne ya kaashe Sabi da ganin abin kaunarsa ya tashi har ya hallacci taron, parking motocin sukayi tukunna aka bude murfin motar Nan take ya fito da kekkewar kafarsa wadda taji gyra da tsafta kamar madar Dan haske da Kelli batare da ya sake jiraba ya dakko farin glass dinsa ya saka tare da fitowa wow Masha Allah yau Kuma sanye yake da blue din shadda wadda taji dinki babbar riga ta haujikinsa tayi Masa kyau kwarai shi Daman gashi fari ga kyau dan ma ya dan rame jin yar da yayi a asbiti, tin da yafito ake cewa wow wasu ko har da dilalaln yawu wasu kuwa sai neman faduwa suke tsabar kallo kamar sa cinyeshi ,cikin takun kasaita yashiga takowa sojoji n'a biye a bayansa har suka Isa inda alhaji ABDULHAMID yake atsaye Yana kallon abin kwaunar nashi cike da so da kauna, Daga Nan Kuma aka shiga gabatar da abin da ya kawosu bayan angama ne alhaji ABDULHAMID ya musu kyauta ta daban daban tun daga kan malamansu har dalibai .
Daga Haka Kuma suka nufi parking space tare da sauran malaman ,nafisa ce kusa da fateema take cewa" Dan Allah kizo muje kina gani zasu tafi fa kizo ki rakani " ke walalhi bazani ba " ay juyowar da fateema zatai ta hango nafisa har ta Isa gaban alhaji ABDULHAMID ta fada jikinsa "innalillahi wa'inna ilaihirraju un shikkenan tqjama bala,I cewar fateema " hannu Mus,af ya saka cikin zafin nama ya funciko ta tare da hada ido da ita yace" kina da hankali kuwa ?" Harara nafisa ta watsa masa ta fincike hannunta ta Kara makale wa ajikin alhaji ABDULHAMID Haushin hararar da tamasa ne yasa mus,af ya sake funciko ta tare da tsinka mata Mari jikike Tau luuu, wani gigitaccen Kara ta saka tare da cikukuyo gaban rigar mus'af ta saki kuka ,batare da mus,af yace komai ba sojojin suka karaso suka janye nafisa daga jikinsa tare da yin gefe da ita , afusace mus,af yacire blue din shaddar jikinsa tasama ya fada cikin mota cikin fishi sanan ragowar suma suka Shiga suka ja motar Banda alhaji ABDULHAMID da ya ruko hannun nafisa cike da taisayinta yadda fuskarta tayi kunburi tayi Shari" cikin voice dinsa me dadi yace" yarinya meyasa kikayi Haka kidaina kinji ko Babu kyau kiyi hakuri da Marin da yamiki" kuka nafisa tasaka Tace" Wallahi ni kaunarka nake jinayi bazan iya jurewa ba shiyasa nazo na rungumeka nadade Ina kaunarka tun da naji ance Kai mutumin kirkine" tana Gama fadar Haka tasake fashewa da kuka, shiko alhaji ABDULHAMID rukota ya sakeyi tare da mannata akirjinsa cikin rarrashi yace" to ya Isa Haka kiyi hakuri kinji yarinya ta " Yana Gama fadar Haka da ya tabbatar ta Yi shiru sai ya saketa tare da Bata kudade masu yawa da harta ki karba taga ya hade Rai sai ta amsa tare da yimasa godiya.
*DOGUWA*
Tun da mahaifiyar amra tayi addu,ar Allah ya tashi kafadun amra ,daga lokacin ta Mike tare da dagata suka cigaba da tafiya har suka hadu da me kura ta riban ruwa ya taimaka aka saka umman su amra aciki ya kaisu bakin titi ,suna ta tsaye a bakin titi sunfi awa 5 suna faman neman n'a allah wqn da zai daukesu ya ragemusu hanya ay ko saiga wani tsoho Nan da Yar kurkurarsu ya daukesu suka tafi sai da sukayi tafiya menisa suka iso cikin jejin falgore tukunna ya ajiyesu yace su samu wani ya sake taimaka musu. Alokacin da ya ajiyesu ya tafi amra tashiga tashin hankali sabi da yadda taga jejin Babu kowa tsit ga duhun gaske cikin tsoro da furgici amra tashiga yin addu,a Nan take tsoro ya fita daga cikin zuciyarta ta daga mahaifiyar su suka shiga cikin jejin sai da suka Yi nisa aciki daidai wajan wata bishiyar tsamiya suka tsaya amra ta tsinko ciyayi ta hadasu dayawa akasa yayi tudu sosai kamar gado sanan ta kwantar da mahaifiyar su akai.
10....
Bayan sun kwantar da itane amra tashiga cikin jejin domin neman abin da zasuci dakuma sassakar itacen da zata hada bukka, tare da sauran "yan uwanta maza su uku da Jafar da Jamal da Abed ,saï da sukayi tafiya medan nisa sannan suka samu bishiyar Mango Nan take suka shiga murna da farinciki Daman rabonsu da cin abinci tun jiya hakanne yasa Abed da yake shine babba ya haukan bishiyar yashiga karkadiwa nunannu masu jaki su amra suna kwasa ,sai da suka dibi me yawa sannan ya sakko suka cigaba da tafiya har suka tadda bishiyar inibi manya manya sunyi marun har wani Baki Baki suke tsabar nuna, wannan lokacin ma abed ne ya au ya debo musu sannan ya sakko suka shiga sassakar ciyayi da itace ,sosai suka loda da yawa sannan suka koma inda suka bar sauran "yan uwansu da mahaifiyar su lokacin da suka koma mahaifiyar su tatashi daga bacci hakanne yasa su jaber suka tsallaka bakin kogin dayake gurin suka wanke abin da suka tsinko sannan suka dawo suka tarar har amra ta fara dasa bukkar agurin Dan Haka suma suka Kai kayan Mango da inibin gaban mahaifiyar su sannan suma suka shiga Taya Amra hada bukka , Masha Allah sai da suka hada bukka uku manya sannan suka sassake ciyayin gurin yayi sarari tukunna suka zauna suka Shiga shan Kayan da suka tsinko, bayan sungama amra suka raka bakin rafin tayi wanka sannan suma sukayi ,suka Sami wata babbar Leda suka zubo ruwan aciki amra ta wankewa mahaifiyar su jikinta daganan kuma Gaba dayansu baccci me dadi yayi awan gaba dasu sabi da dadin iskar da takada tako ina.
*ADAMAWA*
Tun da NINEE ta fito daga gida ta nufi titi take ta neman n'a allah ya taimaka mata yakaita doguwa Amma Ina haryanzu shiru Bata samuba gashi Bata da kudi balle ta biya tatafi ,tana tsaye agurin sai ga Allah ya kawo wani me mota da alama haya yake ,Yana zuwa yayi Parking a gabanta tare da sauke gilass din motar yace " hajiya tafiya ne ina zaki Doguwa ko Abuja?" Yallabai doguwa zani saï dai bana da ko sisi wan da zanbiya natafi Dan Allah kataimaka min kamar yadda Allah ya taimakeka kakaini doguwa Dan Allah ,idan kamin wanan taimakon bakasan adadin ladan da zaka samuba Dan Allah kada kace bazaka taimakeni ba" kallonta yayi sosai Yana son ya gano wani abu acikin idonta sai da yagama karemata kallo Sanan yace shigo mutafi " murna da farinciki kamar sa kashe NINEE indakasan zata hadiyesa sabi da godiya ,Shiga tayi suka soma tafiya .
________________________________________________________
Gudu suke kwararawa a hanyar doguwa har suka Isa tashar doguwa anan me motar ya sauke NINEE bakaramar godiya tamasa ba daga Haka ta juya takama hanyar gidansu tun da take tafiya kanta yashiga juyawa sakamakon ganin canje canje da anguwar tasu tayi ,tun da take tafiya samarin anguwar da "yanmata kowa kallonta yake cikin mamaki da rashin sanin meya dawo da ita gida bayan tsawan shekaru da Bata nan.
Itako NINEE tafiya kawai take kanta tshaye Bata bi takan kowaba har ta karasa kofar gidansu , rass gabanta ya Fadi abin da yaganine ya sa ka kanta juyawa zuciyarta tashiga bugu dum dum hannu tasaka ta ruko kwadon dayake jikin kofar a datse tare da cewa" innalillahi wa'inna ilaihirraju un umma amrah duk ina suke kannena kenan ina NABEHA nashiga uku ta sulale agurin tare da fashewa da kuka Tace" idan danasan wanan bakincikin zanzo na tarar wallahi gwara nazauna na mutu a hannun sir muhsin wayyo Allah na " saki Kara tare da Dora hannunta duk biyun aka .
"Ikon Allah wanake gani haka kamar NINEE ?" Jajayen idanuwanta ta dago ta watsa masa su Tace " nice zubairu Ina su umman mu" zama rubairu yayi yace "duk da bananan abin da yafaru dasu yafaru Amma naji labari anan ne ta kwashe duk abin da yasani ya fadamata tun daga kan korar Karen da baba yayi musu da barin angusarna da sukayi ba asan inda sukeba sanan yakara dacewa " NINEE shawara zanbaki ki koma inda kika fito domin Babu me taimakon ki anan "Kinga tafiyata nabarki lafiya "daga Haka ya Mike ya cigaba da tafiya.
NINEE kuwa mikewa tayi cike da tashin hankali ta Mike daker tashiga Jan kafa tana waige waige tamarasa inda zata nufa.
*Abangaren NABEHA kuwa tun da take tafiya tana hutawa anamata kallon mahaukaciya har tagaji tayi likiss har dare tana faman tafe, yanzuma misalin karfe 8pm tana Tace bataji Bata gani sabida wahala da yunwa ga kishiruwa hakan yasa wata mota tataho hucewa ta layin tana tayi mata hown Amma ko gigau NABEHA batai ba gashi metuka motar soyake ya tsayar da motar take tsayawa har sai da yakaraso gurin motar tayi awan gaba da NABEHA Nan take tasulale akasa.
. ALHAMDULILLAH karshen book 1 kenan sai mun hadu a book 2 idan Allah ya kaimu ,abin da nafada daidai Allah ya bani ladan da kuskuren da nayi batare da nasani ba Allah ka yafemin.
Godiya ta musamman ga masoya littafin BABBAR SAKAYYAH TAKUN FARKO saï mun hadu a TAKUN TSAKIYA Wanda daga shi sai na karshe.
Kukasani ce tare Dani safhat ako dayaushe.
HAFSAT UMAR DANGORO ce
__MARUBUCIYAR__
BURINA MUAZZAM
RAYUWAR KASKANCI
UMMUH AMANI
BABANA NE SILAH
BA MAHAIFIYATA BACE
AMATULLAH
MECE RAYUWAR
ZUCIYATA
MAR'ATUSSALIHA
And new
BABBAR SAKAYYAH.....m