Showing 3001 words to 6000 words out of 70788 words
musu iskanci suke na wuce shari'a , kar in wani damu kuma na daina ajiye damuwa idan ba haka ba hawan jini zai kamani na mutu a banza in bar yarana , shi kuma zaiyi jimamin rashina na kwana 3 daga nan yayi aurenshi ya buɗe sabuwar rayuwa ya manta da labarina , "ya "yana kuma ayi ta gana musu azaba , su tashi babu wani galihu ko "yanci kamar almajirai , itace ta bani shawara ƙauracewa ɗakin miji , daina bashi abinci , rashin kunya kuma saina cire shakkun Dikko dan matsoraci baya zama gwani ko waye , ta ƙara da cewa na fita sabgar kaf ahalin miji dan dasu ake haɗa duk munafurcin , wannan duk ɗabi'ar mahaifiyarta ne , idan suka samu matsala da Dadynsu bata zuwa ɗakinshi kuma batayin yaji saida tanayin gayu mai ɗaga hankalin namiji , tace idan anyi yaji babu ta inda za'aga miji bare a samu damar gasa masa aya a hannu , a gida za'ayi duk masifar ayi a gama , tou kundai ji matan aure , shine fa tun daga wannan rana na birkice na zama fitsararriya , abun bai tsaya a iya Dikko ba ya shafi kowa da kowa.
Wani irin gigitaccen mari na yankawa Papi tare da ce masa dan ubanka waye yace ka zubarmin lemu a kafet......? Tashi Papi yayi ya tafi wurin Dikko.......! Da fatan mai karatu ya gane...........???
Ci gaba nayi da cewa ni banajin tsoron wani zare²n idon banzar mutum , idan taƙamar mutum yace zai dakeni saina bari ya kwanta bacci in mishi wanka da ruwan zafi ko in dafa mai in toye mishi fuska , ko inda nake Dikko bai kalla ba yaci gaba da rirriga Papi da yaƙi ya daina kuka , ni har an nunamin iya zare ido ? Ko rashin kunyar kafi ni iyawa ne ? Nima nan na iya ai shiru² ba tsoro bane ba , kace tuf ka gani , saboda nasan nayi masa nisa , dan tunda na mari Papi na koma matakal bene na zauna daga wurin nake yanko magana , { idan kun tuna benen g r a ya sauke lokacin dana faɗo , na goruba kuma na hau nace zan faɗo ? Yace shine zai jefani na faɗa na mutu , wanda bayan na gudu da yake bani labari yace shi ya ɗaure kanshi da wayar wuta ya faɗo daga sama , wanda ya tafi doguwar jinya.... } fita yayi yaje ya bada Papi ya dawo , har lokacin ban daina zage² ba , shine yajani yakaini ɗakinshi ya rufe bakin rashin kunya.
An mata wai meke damunki ne ? Gaba ɗaya kin zama mahaukaciya , cike da ɓacin rai nace kaine mahaukaci........ , duk girman kwanakin da kake saukewa ai ba'a kaina kakeyi ba , wannan matsalarki ce , tunani da neman mafita ya rage naki ƙaramar yarinya......! Riƙe yatsana yayi a bakinshi....... ` saida ya gama duk abinda zaiyi ya shirya ya fice abunshi.....
Wasu irin zafafan mata ne zagaye dashi ,,,,,,,,,,,,, duk girman daren nan batajin shi bata kuma ganin shi.````, tsaye take a jikin madubi , fitowarta daga wanka kenan , da wayarta ta saita kanta bayan ta danna video , cire towel in dake jikinta tayi taci gaba da ɗaukar kanta tana iskanci .......... Madaidaicin gida ne a cikin anguwar kwaɗo duk yara²n mata ne suke ta gulmar mazajensu , wayarta ta kanga a jikin ƙugunta tayi wasa da jigidar dake ɗaure a ƙugunta , Jiddah bata da burin daya wuce Yazeed yayi auren kishin wuta da ita , *KWARATA RETURN...* fatan mai karatu ya fahimta ko....?
Ƙwas׳ ƙarar takalmin ta kakeji a saman tayils , duk lokacin data motsa dan takawa sai jigidar dake ɗaure jikin ƙugunta ta wani ce cas׳ , idan tayi girgiza kuma sai ta wani ce kacau׳ , gyara zaman ɗaurin kallabinta tayi tana ci gaba da tafiya , harta bayyana a cikin palon , sai yanzu ta samu damar fesa turare bayan ta tsaya a gaban wani mutum wanda shekarunshi zasu kai kimanin 50 , Alaji barka da safiya , ta faɗa a shagwaɓe tana kwarkwasa , ɗagowa yayi da niyar ansa gaisuwar , ita kuma ta ɓalle botiran gabar rigarta dake sanye a jikinta , after dress ce a jikinta. Tana buɗewa ƙanan kayan data saka daga ciki suka samu damar bayyana , a aljihun wando ta tura kwalbar turaren data gama shafawa dakel tare da gyara kitson atach ta watsoshi ta gaba da bayanta , miƙa tayi sosai tana cewa yi haƙuri Alaji na rashin fitowa ta da wuri take maganar tana wani mimmiƙewa kamar macijiyar data samu wurin sanyi a lokacin zafi , cikin ɓacin rai mutumin yace ke me yasa baki da ɗa'a ne ? Kuma ni bake nake nema ba mijinki nake kira ,
Cire after dress in tayi ta wurgar a ƙasa ta ƙara matsawa sosai kusa da Alhaji tana cewa taya zanyi ɗa'a , mai siyar da kayan ƙara kuzarin maza me ya haɗata da ɗa'a tarbiyya ko kunya ? Kaje anguwarmu kayi binciken Sa'adatu mai gilashi kaji me zasu ce maka ? A wannan duniyar idan akwai wani sirri daya kamata al'umma ta sani akan mu'amalar aure tou bai wuce na mata da miji ba , dalili kuwa shine sirrin da ba'a koyar dashi a makarantu ko a gidaje , shi kaɗai ne sirrin da sai wani da wani ke saninsa , to amma kasancewar hanyoyin isar da saƙon sun yawaita nake ganin ta wannan hanyar ya kamata kasan wani daga cikin irin nawa sirrin , matar malam bahaushe ce kan gaba wajen shiga matsalolin aure , kamar yanda zakaji matan na faɗa babu soyayya tsakanina da mijina , shi yasa nake fuskantar matsaloli a gidan aure na , ni gaba ɗaya wannan matsalar duk na tattarata na jibgata akan mata , ɗan yatsina fuska tayi tare da ci gaba da cewa nima dai hakan take daga gareni tunda banyi auren soyayya ba , tsoki tayi sannan taci gaba da cewa , kawai ƙusani akayi wanda ni ba haka naso ba , wannan auren baya hanani neman mazan waje kamar dai yadda nake nemanka. Ci gaban da aka samu na sanin sirrin rayuwar da nayi maka magana shine , hanyar kula da mazaje ta yawaita , wayewar kai da buɗewar ido , zamani ya kawosu sun kuma yawaita ta haryar gidajen karuwa da kuma ganin wannan sirrin ta kafofin yaɗa labarai a nahiyar yana giza gizo a maimakon da can zamanin iyaye da kakanni da wannan sirrin yake ɓoye , an samu ci gaba sosai wanda har takai yanzu idan za'ayi ma yarinya aure basai an faɗa mata cewa idan mijinki yazo yaja zariyar wando karki gudu , ko kuma idan yayi haka , ta zage zif in wandonta , cikin yanayin jin kunya Alhaji ya kauda kanshi gefe guda , wata "yar munafikar dariya tayi tare dayin wasa da yatsun hannunta taci gaba da cewa , suma ƙawaye dake zuwa gidajen ƙawayensu idan sunyi aure danjin labarin sirrin auratayyar yadda yake sun daina zuwa saboda zamani ya kawo manashi sauƙaƙe , ni da kuma kai kowa yasan abinda yake faruwa tsakanin namiji da mace idan suka keɓance , amma ci gaban zamani yasa yanzu su kansu iyaye sun daina wannan huɗubar wa "ya "yansu saida kaji ana cewa yi nayi bari na bari , me zakiyin me kuma zaki barin ne......?
Murmushi Alhaji yayi tare da kallon Sa'adatu , ɗan girgiza ƙirjinta tayi cewa tou ya kaga nan , da kuma nan tayi maganar tana nuna gabanta da kuma bayanta , bayan ta tabbatar ya kalla ta fara bada step tana tafiya cikin salon mai ɗaukar hankali , saida ta ɗanyi tafiya kaɗan ta juyo tare da ɗan zira yatsunta a aljihun wandonta , gaɓar hannunta riƙe da ƙugunta taci gaba da karkaɗo ƙugunta tana tahowa wa da girgiza , girjinta yaci gaba motsawa , dariya tayi a dai² lokacin data dawo gaban Alhaji ta riƙo kanshi ta ɗora fuskarshi a saman ƙirjinta cewa ya kagani ne ? Shiru Alhaji yayi , ita kuma tace karka damu ina da sirri , sakin kanshi tayi tare da ɗaukar rigarta bayan ta ajiye mishi number wayarta a rubuce jikin takarda tace idan kana da buƙata ka kirani , tana faɗin haka ta rataya rigarta a ƙafaɗar ta fice ba tare data maida rigar ba....... Kamar wani gelele haka yabi bayan Sa'adatu da kallo. 👇🏻
Cikakken sunan nata shine Sa'adatu Ibrahim , iyayenta talakawa ne na bada misali , babu arabi ba boko haka ta taso a sake kamar ɓatattar dabba , bata nan bata can , bata da aiki sai tallace² , cikin tasha kasuwa da sauran madakatar "yan iska , idan kuma dare yayi sai a kasa mata tallar kayan mata take bin gidajen karuwai , a gidan karuwai ta fara sha'awar shiga sabgar karuwanci dan tana ganin yadda karuwai keyin sabgoginsu , da kuma yadda suke wasa magungunanta da faɗar irin matsayinsu da aikinsu idan sunyi amfani dasu , ita abinda yafi bata mamaki shine , yadda karuwa ke cika ƙatuwar roba irin ta wankan jego da ruwa , mintuna kaɗan namiji yana jiga ɗaki zai fito ya bada maƙudan kuɗaɗe , idan namiji ya fita sai ita karuwar ta shiga cikin robar ta wanke ƙasanta da wannan ruwan , ashe lemun tsami ne ake matsawa a ciki shine ke hana namiji daɗewa idan ya kwanta da mace , yana zuwa akan mace batsal² zai sauka ba tare da ya biya buƙatarshi ba yadda yaso ,
A gidan karuwai ta fara laɓe jikin window idan mace da namiji sun keɓe , nan ta fara sanin muhinmancin kanta da kuma taƙama da ƙatuwar ƙaddarar da gareta , jin manyan maganganun da suka girmi tunaninta yasa itama ta farajin shauƙin buƙatuwa da abun , wannan dalili yasa ta fara kokowa da maza a tasha , da namiji yayi mata abu saita kamashi da kokowa , shine ta samu wani damen ɗan iska ya fara ɗora mata hannu akan alƙalaminshi , daga nan abun ya zame mata abun tunani da san ganin alƙalamin rubutun maza yadda yake a bayyane , tun daga wannan ranar taci gaba da binshi da kokowa , shi kuma duk lokacin data kamashi saiya ɗora mata hannunta , a hankali ta fara warwarewa ta kwace gaba ɗaya , ta daina bari saiya taɓa mata , daya zo sai kawai ta cafko wurin , shi kuma idan ta taɓo sai yake ƙara gudun numfashin alƙalamin , a hankali dai ya samu ya maida ita "yar hannu ,
Itama lokaci guda ta faso ta zama riƙaƙƙar "yar iska , tafi ƙarfin iyaye ta daina ɗaukar talla , kafin wani lokaci ta zama Sa'adatu mai gilashi , bayan wani lokaci kuma ta koma mai gilashi kawai , ganin tana ta ansar wuta a harkar bariki yasa iyayenta suka kwantar da ita da aure , tsaye take har yanzu , tunda akayi aurenta taga ita bata dace da zaman BQ ba , Alhajin ne ya kamata ya aureta ko kuma kawai taci gaba da saƙashi a ɗaki tana ci mishi uwa a gado , tunda tazo gidan ta fuskanci yadda Alhaji ke zama da iyalinshi shi yasa take ta mishi tayin kanta , amma ya cika kafiya har yanzu bai amshi tayi ba , ita kuma ta duƙufa akan saita farautoshi ya zama nata ita ɗaya , ta bashi yaƙi ansa , shine wata rana taje ta bashi number wayarta , yadda ya fara kiranta har aka ƙulle duk zamuji....
Riƙe take , ta wanku iya wankuwa , tana sanye cikin wasu irin sheɗanun kaya masu nuna shatin bireziya da fant , a haka ta tunkari Dikko tana tafiya irin ta riƙaƙƙin "yan bariki , ƙafa ɗaya ake fara shigar da ita ta gaba sai wata ta biyo bayan waccan ta fita , ba bazar² ake tafiyar ba a nutse akeyin tafiyar kuma takon bada tazara ake miƙashi ba , sai tafiyar taɗan riƙayi kamar mutum yana harɗewa kai baƙon abun sai kaga kamar mutum zai faɗi , ba kuma kamar yayi tuntuɓe ba , sudai "yan duniyar sune suka san dalilin yasa sukeyin irin tafiyar a gaban maza , ita kuma tafiyar idan anyita zata ba jiki damar motsawa , kafin ta ida isowa ya gama kalleta tsaf daga ciki , tunda munafikin gilashi ne motarshi , wato na ciki ke ganin na waje , shi kuma na wajen baya iya ganin ka dan duhun gilashin motar , ɗan taɓe baki yayi tare da ɗage girarenshi ya gyara gemunshi sannan ya saka cingom a bakinshi. Saida tazo jikin motar ta kama da niyar buɗewa taji ta a rufe ,
Ɗan fara kwanƙwasawa tayi , bata san ya ganta ba kuma yaga zuwanta iskanci ne kawai yasa ya basar da ita saiya gama kallonta zai fito , idan ya fito kenan bazai kalleta ba bare ta gane tayi ko batayi ba , har ta gaji da tsayuwa taɗan fara canja wuri Dikko bai fito ba kuma bai buɗe ba haka kuma bai daina kallonta ba , Sultana ya kawo ya jera kusa da Yusra , girgiza kanshi yayi tare da cewa kai An mata fa ƙarshe ce , murmushi yayi tare da kallon hotonta a waya yace rashin kunya kenan , Dikko ׳ suna na kenan a bakinki ƙaramar yarinya , dariya yayi tare da ƙara zuƙo hoton yace wai nine zaki dafa mai ki ƙonamin fuska ke mahaukaciya , in Allah ya yadda saina samu lokaci na zaneki An mata dan naga iskancin naki kullum gaba yakeyi , ya ƙarasa maganar yana sumbatar hoton yace ina sanki ƙawar faɗa ta. Ƙara kallo Yusra yayi sannan ya sake kallon hoton Sultana , yace An mata babu inda Allah ya rage ki amma da wannan yajuju wa majujun aka tsere miki , me na rage miki ne ? Fita goma idan zanyi saina shigo miki da duk abinda nasan zaki ƙara sama dashi a zuciyata so goma , ragamata gaba ɗaya na miƙa miki amma kin kasa riƙewa , babu abinda kika aje sai rawar kai kafiya da rashin kunya nan kaɗai kikafi auki.
Mafiya yawan maza da irin wancan ƙarshen duniya mata ke fizgar imaninsu su cusasu harkar bariki ko basu shirya shiga ba, wasu kuma mazajen laifinsu ne , misali , banbancin matar aure da karuwa , rashin adalci da wasu mazajen sukeyi shine , su kansu kaɗai suka sani kuma rayuwarsu kawai suke ginawa ta hanyar ba kansu cima mai gina jiki da kuma sutura mai martabasu , ka auri matarka ka kawota gida ka jibge , sabulun wanka da turare man wanke baki da kuɗin kitso da ƙunshi ka gagara tsare mata su , amma kai duk sabon yadi ko shadda takalmi da agogo sabuwar fitowa ko wata hula ka siya kai kanka kawai matarka kuma ko oho , kamar Babansu Sultana kenan , ka gagara ciyar da iyalinka da abinci mai kyau ka haɗata da ƙanzo ko garin kwaki , kwaɗon tuwo taliya da manja , kai ko kullum kana can biye da santa lungu da saƙo kana gano sabbin gidajen dahuwar abinci da aka buɗe , kabar matarka da koko kai kuma kaje ka raya kanka da lafiyayen shayi da biredi saboda rashin adalci , abin nufi anan shine ita matar aure ga Allah ta dogara gareka ta dogara , kaine duniyarta kuma kaine take jira ka bata komai na rayuwa , tou bakayi mata ba kuma baka bata ba , ba tada wata wadata ga kuma rashin kwanciyar hankali lokaci guda saita buge gaba ɗaya ta tashi aiki , ga masifar ka na yawan buƙatuwarta gareka , bata da wani ishashen ƙoshi bare ta samu ƙarfi da kuzarin anshe jarabarka kafin a ankara mace ta tashi aiki.
Shikenan kai kuma ka gama da ita , baka da aiki sai zaginta idan ka zauna majalisa , matarka ƙazamiya ce , bata kitso ba wanka ba ƙunshi gaba ɗaya ta tsofe , tare mukayi aure da wane ko wane ya rigani aure amma har yanzun matarshi kamar yanzu ya aurota , bata tsufa kullum "yar yarinya take komawa kaza׳ bayan kaine mugun , kuma kaine ka tsofar da ita , ka kuma ƙazantar da ita ta hanyar rashin bata duk irin kular daya kamata , shi kuma wanen da kake magana yana kula da matar tashi , yana tsaye akanta wurin ganin ya ciyar da ita ta yadda ya kamata , duk sabuwar atamfar data fito ko wani less janbaki sabon yayi saiya siyo ya kawoma matarshi , sai kuma akaci sa'a mai gayun ce da ansar wanka ba dole zata zama yarinyar ba ?
Ana haka sai kaga wata "yar budurwar tana wucewa da ƙyallinta , iyayenta suna tsaye kanta suna ta siyen fauda jagira da sutura basa gajiyawa , data wuce ku majalisa saita bar muku ƙamshinta , daga nan sai kace saika aurota , kaje kayita ɓarin kuɗi ka samota dakel itama ka kawota gidanka , kamar ta farkon itama haka zata bige saboda rashin kula kafin ka ankara ka tara mata kuma duk ka kasa riƙesu , babu sauran wurin dan haka saika fara harin na waje. Tunda su sun iya shafa fouda,
Bayan duk "yan shafe²n da sukeyi da ƙwalisar suna ɗaukar ido duk a aljihunanku suke tatsar kuɗaɗen , baka raya gida ba amma ka raya waje , baka siyawa matanka kayan shafa da sutura ba ka siyawa matan bariki wanda bakai kaɗai ne kake morarta ba , wasu kuma matan laifin nasu ne , a siyo a kawo musu amma basa dai gyarawar , matsalolin dai daban² ne , wasu rashin kula da mazajen