Showing 75001 words to 78000 words out of 224095 words

Chapter 26 - JEEDDAHTULKHAIR

06 Nov 2024

3781

tayi, tun ranan da suka fito daga wajen bayan ya nuna mata takarda bata sake bin hanyan ba, tsaye tayi tana ta kallon direction din, can dai ta karasa tana tafiya a hankali har ta isa kofar parlonsa ta bude tana lekan ciki, komai na parlon fess ko alamar datti bata gani ba sai wani kamshi ma da take ji, shiga parlon tayi tana bin ko ina da kallo gabanta ya dinga faduwa, can ta karasa wani kofa da ta gani, bude kofar tayi a hankali tana lekan ciki, daki ne da wani babban katifa da bedsheet a kai, babu abinda bbu a babban dakin, karasawa tayi ciki tana kallon wani table da jirgi a kai, xaro ido tayi tana kallon karamin jirgin, dauka tayi da hannu biyu tana jujjuyawa ta kai idonta tana leka d'an windows din jirgin, hotonsa ta gani jikin bangon dakin da fararen kaya ya rike hula tsaye kusa da wani katon jirgi, a ranta tunani ta shiga yi kilan shi ya ta6a ganin jirgi tunda gashi yayi hoto kusa da jirgin, ita dai a sama kawai suke hangosa dan mitsili, kallon fuskarsa ta dinga yi, lkci daya gabanta ya fadi tana ganin kamar xai iya magana a hoton, a hankali ta juya, taga wani kofa ta karasa ta bude ta ga wani makeken bandaki da abu kamar katon glass a ciki har tana iya hango ciki, kwata kwata bandakin ba irin nata bane, ga shi da girma sosai, ko ina a bushe yake sai kamshi bandakin yake, a hankali ta rufo kofar sannan ta bude wani kofar da ta gani daga can end, xaro ido tayi ganin view din, karamin balcony ne, ta dinga bin gidan da kallo daga kasa wanda ke shimfide da carpet grass ga wasu flowers a gefe, sosai wajen ya mata kyau ba kadan ba, ta kalli wani babban gidan dake opposite dinta suka yi ido hudu da wani dake xaune shi ma a balcony, laptop ne gabansa da drink, shi dai kallonta kawai yake, ta Sunkuyar da kanta da sauri ta juya ta koma ciki ta kulle kofar, da sauri da sauri ta koma dakinta. Daren ranan bayan isha Abuturrab na Abuja a gidansa sbda weather bai bari sun koma kano ba, Aneesah ce xaune kusa da shi a dakinsa, yace "Kince kina da lectures da safe, why not sleep now?" Ta hade rai tace "Toh ae it's not a crime idan nayi bouncing lectures din ko?" Ya gyada mata kai yace "Haka ne...." Lamo tayi ta lumshe ido kusa da shi, ya ci gaba da abinda yake, bayan few minutes ta bude ido tana kallonsa tace "In tambayeka mana captain" Yace "Ina jin ki" tace "This days kamar u are not longer eager being with me, why?" ya buda ido sosai yace "Why do u say so?" Ta marairaice tace "Haka naga alama, or do u have anything in mind?" Murmushi yyi yace "Yaushe rabon mu hadu? It's almost 10 days now" ya ja hancinta yace "And ke kin fiye ma mutum jan aji ne" Rungumesa tayi cike da shagwaba tace "Wallahi ba haka bane, ae kai din ne sai ka xo Abuja kake neman mutum" ya cire hulan kanta yace "Ohh really??" Dariya tayi tace "Aa wasa nake my captain ni kadai...." yyi murmushi yace "In few days time su Abbanmu xa su je gidanku in sha Allah" ta wara ido tace "Da gaske my captain?" Yace "In sha Allah" Rungumesa tayi tace "I can't wait Babynah" ya d'an hade rai yace "Baby kuma?" Dariya tayi sosai tace "Au.. to yi hakuri na manta baka son sunan, amma fa kada wataran ka xo kayi ta rokana in kiraka da Baby" yace "Sai kace wani jariri" Dariya kawai take tana kallonsa don tun ba yau ba tasan bai son irin wannan soyayyan da yawanci yake kiransa da na yarinta, ta daura kanta saman shoulder dinsa tana jin wani sabon sonsa na fixagarta... Karfe daya saura few minutes Abuturrab ya fito bedroom dinsa bayan yayi wanka ya shirya cikin jallabiya, xaunawa yyi parlor yyi dialing number ya kai kunne, sae da ya katse ba a dauka ba sannan ya kalli agogo, ajiye wayar yyi ya kwanta saman doguwar kujera ya lumshe ido... Throughout week din nan Jiddah bata ji kadaici sosai ba don ranan laraba ma sai da Maimoon ta xo gidan, A ranan kuma Abuturrab yyi niyyar dawowa amma cikin ikon Allah sai bai samu dawowan ba, ranan alhamis Maimoon ta kara xuwa tare da Ramlah da abinci wanda Umma ta basu su kawo ma Jiddar, sosai Jiddah ta sake da su don ba kadan suke debe mata kewa ba, Ramlah ta dinga mamaki kamar yanda Ahmad yyi ganin ashe dai Jiddah na magana haka, ga dariya kamar me, xuwan su ya sa har ta samu confidence din fita suka xaga cikin gidan gaba daya tare da su, a nan ne ma tasan da mai gadi da matarsa a gidan, sai bayan magrib Umma ta aika driver ya je ya daukosu, Jiddah ranta fess ta ci sauran abincin da suka rage sannan tayi wanka tayi isha ta shirya ta kwanta, nan da nan bacci ya dauketa. Karfe tara saura Abuturrab dake xaune hotel room dinsa a kano yyi dialing number nata, har ya gama ring bata daga ba, da mamaki ya dinga kallon wayar, ya sake kira nan ma no answer, sake kira yyi ya sake ringing ya gama ba a daga ba, da yamma ma ya kira sau biyu no answer, a lkcn kuma Jiddah na can compound tare da su Ramlah, ajiye wayar yyi, can ya mike ya shirya within few minutes ya dau makullin motarsa da jakar laptop dinsa ya fita dakin, abinda bai ta6a yi ba xai yi ranan, wato driving to kaduna at night, dama da asuba yyi niyyar komawa kaduna sbda throughout gobe ba shi da duty, amma yanxu yyi deciding din tafiya kawai, sai kusan sha biyu da wani abu Abuturrab ya shiga gida yyi parking mai gadi ya taho da sauri yyi masa sannu da xuwa, amsawa yyi ya wuce ciki, makulli ya ciro ya bude kofar dake a kulle, Jiddah bata mance warning din Ahmad na cewar duk wanda ya xo kar ta mance kulle gidan da makulli bayan ya tafi ba sannan ta boye makullin, bin parlon ya dinga yi da kallo, ya kashe wutan dake a kunne ya wuce sama, kofar dakinta ya bude, kwance ya ganta tana bacci cikin nutsuwa, karasawa cikin dakin yyi still looking at her da wani expression can ya juya ya fice daga dakin ya tafi bangarensa. Washegari da safe bayan Jiddah tayi wanka ta shirya ta fito daga dakinta, cak ta tsaya jin kamar tana jin murya a can daya part din, to ko tv ne a kunne, ko ma ita ce ta ta6a abu da ya kunna tvn ranan da ta shiga dakin bata sani ba, gabanta na faduwa ta fara tafiya xuwa can din a hankali, har ta isa sannan ta bude kofa cikin nutsuwa tana lekan parlon, babu wani tv dake a kunne ta dinga bin parlon da kallo, sai taji ba tv bane karatun qur'ani ne, har xata juya ta d'an yi jim kamar me shakkar shiga ciki, can dai ta karasa ciki tana kallon kofar bedroom din da ba a rufe ba gaba daya, tunani ta dinga yi ko ita ta bar kofar haka jiya, a hankali ta kutsa kai ciki, wani kara tayi a tsorace ganin mutum kwance with short and singlet yana bacci, ta juya da sauri ashe ta mayar da kofar ta ci karo da kofar, wani ihun ta kuma yi ta dafe forehead dinta....


Don Allah no Reader should come and ask me of complete document na Jiddatul Khair plss, naga dai ba tsohon book bane da xaku dinga cewa sae an baku document xaku biya, snn shi page guda guda da ku ke karantawa ae ba kyauta bane shi ma, to don hka ko wacce ta ji da bashin dari biyat din mutane😏



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you


Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems

Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada

Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240


Bude ido Abuturrab yyi ya tashi xaune yana kallonta da mamaki, ta mike tsaye hannunta a goshinta, ko ina na jikinta rawa yake, duk ta daburce, xata bude kofar cikin tsawa yace "Me ya kawo ki nan??" Kin juyowa tayi hannunta na rawa ta bude kofar xata fita, wani tsawan ya kuma yi mata yace "Kar ki kuskura ki tsallaka bakin kofar nan" fashewa tayi da kuka amma taki juyowa kuma bata fita dakin ba, ya sauka daga saman gadon ya dau jallabiyansa ya saka sannnan ya nufeta, tana jin alamar ya sauka gadon ta juyo da sauri, ganinsa tayi tsaye gabanta, fuska daure yace "Me ya kawo ki bangarena?" Cikin rawan murya ta durkusa tace "Wllh kara naji shine na xo in ga meye, ban san ka dawo ba Allah" Ya rungume hannunsa yace "Wato har nan kike shigowa kenan idan bana nan kenan?" Ta fashe da matsanancin kuka tana girgixa kai tace "Aa bana shigowa, ni ba shigowa nake ba wllh" Yace "Toh ina ruwanki da koma me kika ji da xaki shigo min daki?" Hawayen dake makale idonta ya sakko ta girgixa masa kai kawai bata ce komai ba, yace "Toh tafi ki dauko abun shara, ki share tun daga cikin dakin har parlor sannan ki goge, ki wanke bandakin...." Ta sunkuyar da kanta don har ta ji hankalinta ya kwanta xatonta har marinta sai yyi yau, kofar balcony din dakin ya nufa ya bude yana nuna mata yace "Har nan xaki share kiyi mopping" Gyada masa kai kawai tayi, ya dau wayarsa har ya nufi kofa ya tsaya, ya juyo yana kallonta yace "Kar ki ga na kyaleki yau, billah idan kika sake shigo min bangarena ko da wasa xaki sha mamaki" Kai kawai ta gyada masa a sanyaye, ya juya ya fita, sai da ya fita parlon gaba daya sannan ta juya a hankali ta fita ita ma, downstairs ta sauka ta gansa xaune parlor ya kunna TV, ta wuce kitchen ya bi ta da kallo, abun sharan ta dauko da mopping bucket tare da mop with duster sannan ta wuce sama, aikin ta shiga yi babu ganda, har xanin gadon sai da ta sake shimfidawa, bayan ta gama da bedroom din ta tafi balcony, kallon inda taga mutumin ranan tayi duk da babu kowa wajen sai kujera amma sai take ganin kamar shi a wajen, ta fi minti biyu tsaye tana ta kallon wajen kafin ta fara share balcony din ta yi mopping ta dawo dakin ta kulle kofa, parlor ta tafi nan ma ta share ko ina ta goge har kayan kallon, tana gamawa ta koma bedroom din ta bude kofar da take tunani bandaki ne, kallon bracelet din hannunta me kyau tayi wanda yau ya kai kwana uku da ta saka shi, ta tafi gaban mirror dinsa ta cire sannan ta ajiye tana kallon turarrukan da ke gaban madubin, kwalabensu ne ya burgeta sosai, they look so unique, ta dau daya daga ciki ta bude ta kai hanci, rufe ido tayi sannan ta bude, da wannan kamshin ta sansa, babu kuma abinda ya fado mata sai lkcn da yake xuwa can wajenta a Hayin rigasa, ta dau murfin xata rufe turaren ya subuce daga hannunta duk kokarin ganin ta kama turaren kan ya kai kasa hakan ya faskara don tuni yayi landing kan tiles sbda irin faduwan da yayi kuma lkci daya ya tarwatse, a tsorace ta ja baya ta dafe kirjinta da ya hau bugawa, lkci daya ta fara yarfe hannu murya can kasa tace "Na shiga uku" hankali tashe take kallon turaren, ta ma rasa abun yi, can ta nufi kofa sai a sannan ta fashe da kuka ta fita part din, downstairs ta sauka ta makale jikin bango tana kallonsa gabanta na faduwa, jin footstep kuma bai ji ta karaso cikin parlon ba ya sa ya juya, sunkuyar da kanta tayi, ya mike yana kallonta ganin hawaye a idonta, satan kallonsa tayi ganin kallon da yake mata ta fashe masa da kuka tace "Don Allah kayi hakuri" kasa daina kallonta yyi, can yace "Me kika min a sama?" Ta kara rushe masa da kuka tace "Don Allah kayi hakuri nace" Ya wani hade rai yace "Me kika yi nace?" Kin cewa komai tayi, ya nufeta, da gudu ta bar wajen ta wuce sama, ya bi bayanta, tuni ta shige dakinta ta rufe kofan da karfi, part dinsa ya nufa tun bai shiga parlon ba ya soma jin kamshin turarensa, ya shiga parlon sannan ya bude kofar dakin, tsaye yayi bakin kofa ya rungume hannunsa yana kallon tsadadden turaren nasa a kasa, Jiddah dai sai zare ido take tana jiran jin ya shigo dakin amma bai shigo ba har sha daya na safe, sai a sannan ta fara jin yunwan da ya dameta, lamo tayi kan gado kamar xata yi kuka tana tsoron fita, tana nan a haka har kusan sha biyu, mikewa tayi daga karshe ta nufi kofarta ta bude a hankali, cikin sanda ta sauka downstairs bayan ta tabbatar baya kasa sannan ta wuce kitchen, indomie ta dauka ta fara dafawa a kitchen din, ko kadan bata yrda tayi making noise da xai sa a san tana kitchen din ba, yanda taga Ramlah ta dafa masu indomie jiya take yi, with ingredients, tana duba indomie da har ya dahu kamar ance ta juya ta gansa tsaye bakin kofa, sake murfin tukunyar tayi a rikice tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" end din kitchen din ta tafi ta tsaya tana kallonsa a tsorace kamar xata yi kuka, ya karasa gun gas din ya kashe na indomien, da kuma na kwai dake tafasa, tana ganin haka xata fita kitchen din da gudu, ya tare hanyar, hade hannunta tayi waje daya ta marairaice tace "Don Allah kayi hakuri" yana mata wani kallo yace "Laifi nawa kenan kika yi yau a gidan nan?" Ta hadiye abu da kyar tace "Biyu" yace "Wanne da wanne?" Tayi narai narai da ido ta ki cewa komai, ya hade rai yace "Ina jin ki" Cikin rawar murya tace "Na fasa maka turare" yace "Ehen, sai me?" Tace "Na ji kamar radio na magana shine naje sashinka ka kamani" Ya gyada kai yace "Good, kinsan nawa turaren nan da kika fasa min?" Ta bude ido tana kallonsa amma bata ce komai ba, yace "Toh ki sani cewar tara ki nake, turaren nan kuma sai kin biyani duk yanda za ki yi ba ruwana" a hankali tace "Toh ae ni bani da kudi" yace "Ehh nemosu xa kiyi duk inda xa ki nemo su" ta sauke idonta kasa, kallonta yake daga sama har kasa, ya sauke idonsa kan fingers dinta yaga babu farce alamar tana cirewa a kai kai, ya kalli fararen toes dinta, kallon fuskarta yyi yaga har sannan kasa take kallo, yace "Cire hular ki" sae a sannan ta daga kai ta kallesa amma taki cirewa, ya hade rai yace "Magana nake maki" a hankali ta xame hular, ya dinga kallon bakin gashin nata wanda sak na Fulani, amma duk ya takure waje daya duk da da ribbon ta dauresa a tsakiya ya sauka kasan wuyarta, tun gyaran gashin da Umma tayi mata har ranan bata ta6a gashin ba, ya yamutsa fuska yace "Meye wannan din?" Ta kallesa bata ce komai ba, ya mata tsawa yace "Ba tambayar ki nake ba" Cikin sanyin murya tace "Gashina ne" Yace "Ke kaxamar wace gari ce, gashin ki ne kika bari haka kamar na mahaukaciya?" Ita dai bata ce komai ba, ya koma baya yana sake kare ma gashin kallo da mamaki, satan kallonsa tayi ya mata wani shegen kallo yace "Sae na tsokale idonki kika sake kallona, kina mace da ke dubi ynda gashin ki ya koma kamar gashin jikin tinkiya?? What nonsense" Lkci daya hawaye ya kawo idonta, strictly yace "Ki gama cin abincin kiyi sllh ki jirani a parlor" Bata ce komai ba ya juya ya fice daga kitchen din, Jiddah bata wani ci abincin ba sae hawaye, daga karshe ta mayar kitchen ta rufe taje sama ta wanke bakinta ta dau gogaggen hijab dinta ta saka ta dawo parlor ta xauna fuskarta babu walwala, sae da ya dawo sallahn Juma'ah sannan ya dau makullin motarsa, ya isa bakin kofar fita sannan ya kalleta yace "In xo in dauko ki ne" mikewa tayi a sanyaye ta bi bayansa, gaban motar ta xauna don bata mance abinda yace mata ba last time da ta xauna a baya, wani saloon ya kai ta, yana xaune mota ya jira har aka gama sannan daya daga workers din ta fito ta sanar masa an gama ko xa ayi mata lalle, yace "Aa, nawa ne kudin gyaran gashin naku?" Ta fada masa ya ciro kudin ya mika mata tayi masa godiya ta koma ciki, ba a dau lkci ba sai ga Jiddah ta fito daga saloon din, walking slowly ta iso gun motar har sannan fuskarta babu walwala, ta bude gaban motar ta shiga, ta rufe bata ce komai ba, kallonta kawai yake da mamaki, gani yake kamar da kyar ta iya rabuwa da halin gidadanci, ya daga kafada don yasan yana

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login