Showing 3001 words to 6000 words out of 83387 words
din kowanne ya Hadu karshe yaji kayan Alatu,Babu abinda Babu a gidan irin na more rayuwa,gidan kamshi da kyalli kawai keyi maaikata na sintiri ta ko Ina,kowa da irin aikinsa,ga securities ko Ina Ana tsaro,garden da sweeming pool bangarensu daban a gidan.
Mami Pls kuyi sauri mu Isa Airport jirgin Ya ABDALLAH remain 5mnt yayi Landing Kuma kin San Ya Abdullah Bai son jira yau duk sai munci ubanmu a gidan Nan idan ya jira a Airport ba a zo daukansa ba,Mami tace ke karki yiwa Dana Sharri tuni securities sun Isa Airport Daddy ma Yana can tare dasu.
Cikin shiga ta Alfarma Dattijuwar daga ka ganta kaga marar mutunci tun a fuska tare da yaranta Afrah da Islam suka fito suna zuba kamshi,parking space suka Karasa inda iya kallonka motocine masu tsadar gaske iri iri ta ko Ina,Wasu Yan Mata ne da samari wasu suna shiga mota da Alamar fita zasuyi wasu Kuma sun dawo,wasu Kuma gasu Nan kowa da abinda yake, ganin su Afrah da Maminsu yasa aka fara gulmace gulmace Ana musu Habaici Ana Harare Harare,itama Mami da yaranta Basu fasa ramawa ba suna Maida martani da gani kasan ba a shiri da juna,itama Mamin da take Babba cewa tayi ki sharesu shegu yaran matsiyata,Alhaji shi ya jawo Daya kwaso iyayensu ya auresu,gida kamar kasuwa tsaki taja cike da Izza suka shige katafariyar mota Yar yayi Driver yaja su suka wuce airport.
Mami kyakyawar gaske ce ka rantse balarabiya ce Haka ma yaranta suke wannan na wane wannan a kyau sai Rashi kyan hali.
Suna karasawa Airport wani azababben Guy ya sakko daga steps din jirgi Yana janye da karamar Trolley dinsa ta Yan gayun gaske,Sanye yake cikin wata tsadajjiyar t-shirt silver color,da wando jean fari Kal pencil, rigar ta wuce Masa zuwa cinya ta Dan Zobe daga baya kalar ta mawakan turawa,hannunsa wani zoben azurfa me azabar tsada,ga agogonsa Gucci,Haka takalminsa ma fari Kal kamar canvas me shegen tsada Haka yake sai dai an budeshi ba a daure zaren ba ya wani bude kamar wani Justin Bieber zaiyi Waka,Sumarsa irin ta Larabawa baka wuluk Tasha wani aski na iban albarka,an kwashe gefe gefe kadan tsakiya daga gaba an tarata da yawa sannan an yarfota saman goshi tayi wani gaba kamar zata rufe Masa Ido,kowa kallonsa akeyi Dan ka rantse wani mawakine daga kasar London ya sauka a kasar,Amma fa ya Hadu karshe ta ko Ina Babu Wanda ya Isa ya kalleshi Bai Kara ba sabo da Masifar kyansa,gashi fari wani jajir dashi,da Dan sajensa kadan da gemu kuyas, fuskarsa ba me Fadi ba, ba ku ma me tsayi ba,Hancinsa Wai zarkadi kyan hancinsa ya baci,idanuwansa madaidaita lumsassu farare Kar Kar,girarsa me yawa,Haka gashin idonsa,komai nasa me kyau ne,shi ba me tsayi ba ba Kuma gajere ba,ga jikinsa dai dai babu kiba ba Kuma ramamme ba.
Wani taku yake na zaratan matasa Yan gayu,lips din Nan nasa masu kyau jajir dasu yake wani tsotsa Yana tauna Chewgum a hankali idan ba kula kayi ba baza kace tauna yake ba.
Wani Masifar gadara da yake abin ba acewa komai ga bala'in iyayi da jiji da Kai da yakeyi abin sai Wanda ya gani,Afrah da gudu taje tare da fadawa jikinsa,kamshinsa ya cika wajen.
Da sauri ya janyeta a jikinsa Yana hararata Yana Dan Murmushi kamar Dole yace Ke Zaki Samin Dirty,Baki bude suke kallonsa har Mami Amma sun San halin kayansu zai aikata me Hali baya fasawa.
Mami ya mikawa hannu tare da rike Hannunta sai Kuma ya rungumeta Yana Dan Murmushinsa da Bai Kai cikin cokali ba a hankali yace Ina wuni Mami,ya gida? Lfy tace Son wannan wanka Haka wlh ban ganeka ba,Haka ka koma ka girma,ka ganka kuwa Abdallah, dariya kawai yayi Wanda mutane da dama maza da Mata sai da suka lalace wajen kallon wannan hadadden bawan Allah yafi uban kowa kyau duk gidansu albarka,ko a turai sai an tona samun kamarsa.
Islam wacce Bata Fi 10yrs ba ya dauka tare da dagata sama suna dariya yace cutie How u? I'm Good Bro,wurin Daddy ya nufa har kasa ya rusuna tare da gaidashi suna farin ciki gaba daya suka rankaya zuwa katafaren gidansu.
Tunda motoci suka tsaya a gidan Mutanen gidan bataliya guda kowa ya fito ganin gulma da tsegumi,har ta saman bene kowanne part Matan Yara da manyan tare da iyayensu Ana ta leke Ana tsegumin Abdallah.
Bayan Abdallah yaci abinci ya huta wanka yayi tare da fita ya shiga part part dake gidan Yana gaida matayen Babansa da yaransu suna amsawa,Yana fita za a fara gulma,Suma Su Mamin hakan take da yaranta Mata sai cewa suke wlh Dan Abdallah ne marar zuciya da mune ko part dinsu bazan kalla ba,Mami tace kyalesu Afrah a Haka zasu Kare na gaba yayi gaba,Can Kuma sauran suna cewa har ya fada Mana turai,muma yaranmu duk sunje can sukayi karatu me za a nuna Mana,ga yaron ma ya dawo a Dan iskansa,jibi askinsa wasu suce Wai su masu kyau shuwa Arab su fa Basu yarda ba Larabawa ne.
Mami Kuma da Afrah cewa suke yo mu da muke jinin arziki su kuwa duk matsiyata Daddy ya aurosu,ai wlh tukunnama sai sun ga matar da Abdallah zai aura,Ummi tace wlh kuwa Yar attajiri jinin sarauta Yar sarkin Ethiopia ga kyau ga Naira,Ai Mamanta ma ta Matsu ya Gama Masters Azo a Fara Maganar aure kwarya tabi kwarya,Dan Ma Abdallah banza ne Wai Humaira dince baya so to wlh sai ya aureta ko Zan tafi tsirara,Allah ya kawo Mana Dangin arziki zai watsa min kasa a Ido,Afrah tace karki yadda Mami Dole ya aureta,Mami tace kwarai ma kuwa yanzu ai ba a auren talauci,kana me kudi sai me kudi talaka sai talaka,Dana ya auri Yar Malam Shehu ai naji kunya,burina duniya tasan da zamana,so nake duniya tasan Dana ya auri Yar manya.
Mami Haka take ta kuri Babu ko sa Allah a ciki,duk abinda zaka dinga kuri ka Dora ranka Kai ba ruwanka da Allah to kuwa Allah zai iya kunyataka a idon duniya,Haka Kuma zai iya kyaleka ya baka abinda kake so ba ruwan Allah.
Garin Zamfara kauyen Nahuce Liman fa ya dukufa ya dage Dole sai yaga bayan su Khadija,tsafe tsafensa yake tayi akanta yarinya karama sabo da rashin Imani.
Khadija kuwa ta dage sai Kwangilarta take nemowa da yaranta suna aiki sosai,Haka Allah yake ko yaya kayi Abu idan yaso ya dafa ma sai asha mamaki,Khadija da kudin take ci dasu tufatarwa da kudin makaranta wa kannenta,Mama Sai mamaki takeyi kamar Wasa ga Khadija kuwa ta Zama 'yar Kwangilar harkar Noma, tayi katon asusu Ana Tara wasu kudin,ga samari yanda suke tururuwar sonta sabo da tsananin kyawun Khadija,indai kyau ne to a shafa Fatiha kawai a kanta,ga kyan sura da diri,skin dinta wata sumul sumul kasancewar babarsu Yar north Sundance farare ne kwal,Haka Babansu farin bafulatani ne,Khadija round face ne da ita,da hancinta madaidaici baiyi tsini da yawa ba,Idanunta Dara Dara,ga gashi har baya kusan tsakiya,hakoranta kanana kyawawa,ga dimple,girarta me yawa baka,Gata da uban Hips cinyoyi manya,gata da Da tsayi Amma ba can ba,kowa yaga Khadija yasan ta cika mace ta gaban kwatance,Haka su Merry ma kannanta kamar su sukayi kansu kyawawane sosai gwanin Sha'awa.
Khadija sabo da zaman kudu rawa wajenta kamar mazari Kuma na Yan kudu takeyi ayi ta girgiza mazaunai,a wani duka kasa tare da rike gefen Riga Babu kunya ko a gaban uban waye Haka suke rawa har Maryam Merry,A kauyen Khadija tana da kawa Abu,Abu yau tazo gidan ba Islamiyya ta samu Khadija da Merry har Ihsan tare da Ahmad sun kunna gidan radio an Sa wakar Wizkid suna ta tikar rawar suna ihu eh...eh...eh...sun cika gidan,yanda Khadija ke rawar zanku kamar kanwar Zlatan,Mama tana aikinta dake itama kudu ta ratsata sai cewa tayi Abu Bismillah ga rawa fa kiyi kema,kunya ta Kama Abu tace ban iya ba,Khairat ta wani duka tana eh....eh...chineke God ah...ah...we dey chill woooo let's dance Abu,Common eh...ehh Merry ma ta jawo hannun Abu Wai sai tayi rawa.
Mama tana kallonsu tana dariya harda gyarawa Ahmad rawar tana kalli yanda Khadija keyi maza ka koya kaima,Abu ta bude Baki Jin yanda Mama tace kunya ta rufe ta.
AsmaBaffa.
[12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: 🏵TUBABBIYA🏵
2
Official
By
AsmaBaffa
Auta, Asycool And Jannat page naku ne.
Khadija tana rawarta sai da Magrib tayi sukayi Sallah tare da cin Abinci suna ta Wasa tare da Abu Wai wasan Yar baby sukeyi Khadija ta Haihu Abu ce babarta suna ta abinsu,Khadija tace yawwa Abu Zaki koya min Hausa Ina so na iya sosai,Abu Kuma Yar Sokoto ce daga can suka dawo Zamfara gaba daya Hausar tasu data Zamfara ba irin ta kano da Kaduna bace,sabo da Hausar da banbanci idan sunji ta Kano da Kaduna sai suce Yan iska ne batsa sukeyi,su ma Yan Kano ko kd idan sunji tasu sai suce batsa ce,Dan Haka Khadija tace muje gindin bishiyar can,Abu tayi sauri tace ke Yar iska ce wallahi irin Yan Kano ce ke ba Haka ake cewa ba,Khadija tace ya ake cewa? Abu tace Gutsun bishiya ake cewa shine ba iskanci ba hhhh,Haka Abu duk tabi ta canjawa Khadija Hausarta ita Kuma Khadija ta rike ta gyara Dan Haka gaba daya hausarta idan Dan kd ko dan Kano yaji shima iskanci zai ce,Abu tace Khadija dare yayi Zan tafi gida Kinga mazan garin Nan fyade sukewa Mata,Khadija tace me fyade? Abu Kiri Kiri tace Ci ake cewa,wallah Wagga samari cin kaca zasu Miki sunka kamaki,Khadija tace oh raping da Hausa Abu da sauri tace Ci ake cewa shine ba iskanci ba,Khadija tace kamar Abinci? Gaskiya yayi dai dai chop chop,Abu tayi dariya tace Nima Zaki koya min Wagga turanci na lailayoshi ga mutanan wagga garin.
Khadija ce Tasha wanka cikin rigarta da kadan ta wuce gwiwa doguwar rigar atamfa red Dan siririn gyale red ta daura a kanta dama su Basu Saba lullubi ba sai in zasu Islamiyya suke saka hijab Mama ce kawai ke yafa gyale,ta fito tana tafiyarta da sauri kamar yaren kudu ba wani yanga ko Jan aji kawai tafiya normal kamar maza ba saurarawa, kaurinta kitika kitika a waje sumul sumul,sai kallonta akeyi a garin Haka ta biya gidan su Abu wacce itama ta shirya cikin Riga da Zanin Atamfa ta yafa gyalenta Wai kasuwa zasu tafi can cikin city din Zamfara,Tasha suka je tare da shigewa mota,Khadija tana ta wakokinta da yaren Igbo,Har suka je suka yi siyayyarsu suna dawowa kauyen sai suka ga wata fyaleliyar mota a gefen Gona da wani Dattijo Kyakyawa dashi me kamala,Khadija tace hey...Abu wait for me ga Alaji can me kudi zanje ko Zan samu Kwangilar aikina,Abu tace to Khadija,da Gudu ta Karasa wajen Mutumin tace Alaji aiki za a ayi maki na gona Ina da Yara sunfi Twenty zamuyi ka biya mu,Alhaji ya kalleta yace Ke Amma ba yar arewa bace? Khadija uwar surutu nanfa ta Fara bashi labarinsu kamar Haka:
Cike da gwarancinta hausar da kyar take fita Tace Alaji mu Yan Asalin Zamfara ne Cikin kauyen Nan na Fulani a Karamar Hukumar Nahuce, Adam Shehu shine Babanmu shi kadai Iyayensa Suka Haifa,ya girma Yana aikin noma sosai har aikin ya bunkasa yake Kai Kayan masarufi state daban daban,ganin yafi samun kasuwanci a kudu Anambra state ya koma can da Zama Baki daya sai dai yazo Nan ya siyi kayan ya koma can,ya Dan Jima sai Allah ya hadashi da Iyayen Mamanmu Yan Asalin Sudan ne sakamakon yakin da akayi duk aka kashe Yan Uwan Mama tare da sauran dangi da yawa,da kyar Babanta ya samu Suka gudo Nigeria ya sauka a Anambra state.
Babanmu ya tausaya musu ya dinga taimaka musu Nan Suka ga mutumin kirki ne suka bashi auren Mama Saudat,Bata ko Haihu ba Allah ya yiwa Mahaifinta Rasuwa sakamakon Ciwon Koda,Sabo da bakin ciki Babar Saudat Mama kenan ta hadu da Hawan jini itama Bata Dade ba Allah ya Mata Rasuwa,Mama Bata da kowa sai Babanmu Adam Shehu,Danginta Kuma na Sudan da suka rage sun Manta da ita ma,itama Haka kasancewar dama ba dangi na jini bane shi yasa ba a zumunci.
Bayan Saudat ta Haifeni Nice Khadija Babba Wanda yanzu shekarata 16 sai Kanwata Maryam 14yrs,Ihsan 12yrs sai auta Ahmad 9yrs, duk da Babanmu ba Mai kudi bane amma mun taso cikin gata ga karatun boko Dana Arabic,ko a Anambra state a unguwar talakawa muke gaskiya sai dai ba rashin ci da Sha bare rashin sutura,makaranta me kyau muke zuwa, Muna Yara lokacin Ina Jss1 Babanmu Adam ya Allah ya Masa rasuwa a hanyar zuwa zamfara motarsu tayi Accident,Munsha bakin ciki Wanda sai da Mama ta kwanta a Hospital na 2wks,bayan komai ya lafa Sai Mama Ta Fara Sana'a sosai dama a gidan haya muke zaune a can,a Haka har naje ss2 Maryam Ana ce mata Merry tana jss3 Ihsan jss1 Ahmad Yana Primary 5 Mama Kudi suka Kare duk an siyar da gonakin gadonmu dake Zamfara,zaman Kudu ya fara gagararmu, me gidan Haya ma ya Kore mu, Dole Mama ta tattaro mu muka dawo kauye,cikin Dangin Adam Suka ce ga gidan Adam ne daya Gina kafin Ya koma Anambra sabo da Haka Muka gyarashi muke Zama a ciki,gidane na kasa rubabbe.
Wannan aikin Dana nema a wajenka Alaji dashi Muka dogara,Ina da Yara zasuyi maka aiki me kyau.
Jinjina kai Alhaji yayi gaskiya yaji tausayinsu, yace to karatun Addini fa kunyi? Khadija ta daga Masa Kai yace munyi Dan kadan dai dai gwargwado Wanda zamu bautawa Allah Amma bada yawa ba,sabo da halin da muka shiga shi yasa,To Maman Taki Bata yi aure ba ita?
Khadija tace nice na hanata gaskiya Ina kishin Dad namu,baka ga Mama ba Kyakyawa kamar ba ita ta haife mu ba,gata da masoya Niko nace baza tayi aure ba,Alaji yace to muje Naga gidan naku idan nazo aikin sai na kiraki,sannan ban yarda dake ba sai na tambayi Mamanki,Khadija ta jawo Abu suka tafi tana ta zubawa Alhaji surutu yana dariya Dan Hausarta da kyar takeyinta.
Har gidansu suka zo ta shiga tare da Kiran Mama,Mama ta yafa gyalenta tare da Fitowa,Ai Alhaji Bai Zaci Haka matar take da shegen kyau ba,gata wayayya,Nan ya rude gaba daya,bayan sun gaisa yace Sunana Alhaji Tahir Amma anfi sanina da Alhaji Karami,ya tambayeta akan labarin Khadija, tace gaskiya ta fada Yace to sai Gobe zai dawo ya kirata suyi Masa aiki.
Murna wajen Khadija ba a magana har mota ta taka Alhaji ta dawo gida abinta,
Tunda Alhaji ya koma masaukinsa Hotel yake tunanin Saudat Mama,Allah ya Sa Masa sonta sosai,washe gari da wuri ya dawo kauyen har gida yaje Saudat ta fito Suka gaisa sannan Khadija ta bishi bayan ta gaidashi suka tafi gona tare,Alhaji Tahir yace Khadija Ina so muyi wata magana.
Khadija tace to Ina jinka Alaji,Yace idan nace Zan auri Mama Zaki yarda? Khadija kawai ta kalleshi sai ya Mata kwarjini ta kasa cewa a'a duk kishin Ubanta da takeyi sai ta samu kanta da yin shuru,Alhaji Karami yace Karki damu Khadija idan na auri Mamanki Zan tafi daku Gidana Zan kula daku kamar Yayan cikina,Khadija tace kana da aure? Yace ae matata daya Hajiya Hafsatu da yarana guda hudu,Nafisa 19yrs itace Babba,sai Hindu15yrs,Mubaraq 13yrs da Salis 10yrs, gidanmu estate gudane Kinga nida yayana ne Uwar mu daya ubanmu daya,shima a gidan yake da matansa da yaransa kowa da part dinsa,wlh Zan rikeku da Amana,ko me kuke so Zan muku.
Khadija tace to a wanne state kake? Kaduna state,Hmm to Allah ya taimaka na yarda sai ka tambayi Mama idan ta yarda,Ai murna wurin Alhaji Karami ba a cewa komai,da yamma wajen Mama ya koma,Bai Sha wahala ba ta Amince sabo da dama tana son auren Kuma gashi ta samu mutumin kirki asirinsu zai rufu gashi uwa uba Khadija ta yarda,Su Merry ma sun Amince Dan sunji me kudi ne zasu koma birni
Mama ta kalli Alhaji tace baka bani labarinka? Alhaji ya fara da mu Asalin Yan Adamawa ne,Fulanin Adamawa daga Ni sai Yayana Yousuf Balarabe Iyayen mu suka Haifa,tun Muna Yara Allah yayiwa iyayenmu Rasuwa sai dangi,munyi karatun Addini da na zamani,Yayana Shi Allah ya azurta,ya fara da kana Nan sana'a Munsha wahalar rayuwa har Allah ya budawa Yousuf ya auri Matarsa ta farko Rahmatu da yaranta Usman,Sarah,Ikhram,Nura,Omar,Zahra,Na'im da Naima Auta, sai Matarsa ta biyu Hajiya Zainabu yaranta biyu Aliyu da Nana Khadija,Matarsa ta uku Binta yaranta Sagir da Saleem sai ta Hudu Hajiya Aisha Kwara ce Wanda suke kamar Larabawa Haka suke tana da yaranta Abdallah 30yrs,Afrah 19yrs sai Islam auta 14yrs,sai Kuma Matan daya aura ya saki su Hudu ne Kuma duk suna da Yara wata biyu wata uku suna Nan a hannunsa sun girma,daga samari sai yan Mata a gidan,gidane Family House Amma ba takura kowa part dinsa daban,ko Ni part Dina daban ne da yarana kema Kuma part dinki za a Baki daban ke da yaranki,Sai dai kuyi hakuri gidan da zaku sai kun shirya domin Babu Wanda ke shiri da dan uwansa,kullum cikin tsegumi da Jan fada ake,Yayana Yousuf me kudin gaske ne,mun gaji sarauta a Adamawa,sannan Dan kasuwa ne,Dan siyasa ya rike mukamai da dama.
Shi yake min komai nawa da Sauran dangi,Mutumin kirki ne matsalarsa kawai aure aure domin ya auri Mata sama da goma Sha uku,Yaransa Kuma kaf Babu me Hankalin Abdallah sai dai gaskiya sai kunyi taka Tsantsan domin shi kanshi Abdallah watarana sai a hankali Bai son magana da hayaniya,ga Kunci,baya Dariya,ga iyayi sannan Bai son raini,Yana da gadara tare da shegen Iyayi,Uwarsu