Showing 39001 words to 42000 words out of 93383 words

Chapter 14 - DUKAN RUWA

19 Oct 2024

10140

cewa ita ba ta soyayya, kuma ba ta sonsa ya rabu da ita.
Tunano hakan sai ta ji dariya ya kama ta, dakyar ta danne ta hanyar murmusawa. Wato dai yau din akwai kallo kenan. Ta kara duban Tasleem da ta sauya kaya zuwa wani leshinta ja mai ɗigon baƙi a jikinsa mai ɗan karen kyau, murmushin ta kara saki wannan karon har da sautin dariyar da ya sa su Raihana dubanta, suka kuma dubi junansu, sun tabbatar Fadeel ɗin Humaira ne a hanyar zuwa. Akwai dai matsala kenan.

©️Rufaida Umar.

*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645


Wayar Tasleem da ta ɗau ƙara ne ya sa ta saurin jifa da kwalbar turaren dake hannunta a saman gado, ta zari mayafinta da ya hau da leshin ɗan firit wanda ko kirjinta bai gama rufewa ba, ficewa a dakin ta yi bayan ta kara wayar a kunne tana fadin ga ta nan fitowa waje. Futuha ta mike ta bi bayanta wai za ta gani ko dagaske Tasleem din ta ke. Suna fita Humaira ta tuntsire da dariya har da faɗawa saman gado. Raihana da Ummita su ma dariyar suka shiga yi.

"Ni dama ya ce yana son nata dagaske ai da naji dadi, ko ba komai na huta da alaƙaƙai. Haba, ina dalili mutum ana korarsa yana mannewa sai ka ce mayen ƙarfe."

Ta ja guntun tsaki ta mike ta ci gaba da ninkin.

"Kai Humaira anya a duniya za ki yi aure kuwa? Wannan abu har ina wai? Duk kyau da kwalisa na saurayi ba kya sonsa? Meke damunki?"

Ummita ta ce tana duban ta, ji take kamar ta kai hannu ta buge ta tsabar haushi. Itama Raihana ta cafe

"Rabu da ita Ummita, ai kanta akwai alamar kuncewar notina. Da ace ma ni ce ke, ko don na nunawa Tasleem ita ɗin ba komai ba ce a wurin Fadeel ai wallahi da hannu bibbiyu zan tarbe shi, shima dai Fadeel din da ba shi da zuciya ya kyaleki ya ƙi, ya bari kina ta wulaƙanta shi son rai. Da ni ce shi ko?"

Ta yi ƙwafa amma ba ta ce komai ba, Humaira wacce tun soma maganarsu take kwaɗa musu harara, ta ja tsaki.

"Matsalarsa, ni dai ai ban yaudareshi ba, tun farko kuma na faɗamasa ya rabu da ni, ya ficemin a rayuwa amma ya ƙi. Aikuwa babu abin da zan ce mishi, ya je can ya ƙarata da Tasleem."

Ba su ce uffan ba sai kallon mamaki da suke mata, dagaske dai take ko a jikinta don ba su ga wani ɗigon kishi a saman fuskarta ba.

A ɓangaren Tasleem kuwa, tana ƙarasawa falon ta ci karo da Mami a zaune tana amsa waya. Ganin ta da shirin fita ya sanya ta yi sallama da abokiyar wayar ta dube ta dakyau.

"Ke kuma sai ina haka?"

"Mami baƙo fa nayi, bari na shigo da shi falon saukar baƙi sai na zo."

Ba ta ma kara jin abin da zai fito a bakin Mamin ba ta yi wuf ta fice, Mami ta yi kasake tana duban hanya, fitowar Futuha ya sanya ta maida akalar tambayar a kanta.

"Wannan wane baƙon ta ƙara yi a yanzu ne? Duka-duka yaushe shi Hamzan ya zo da har zai ƙara zuwa?"

Taɓe baki Futuha ta yi cike da jin kishin ƴar uwarta ta amsa.

"Uhum, wai fa abokin Ibb ne yake sonta shi ne take wannan rawar jikin."

Wani ɗan murmushi Mami ta yi.

"Wato dai ruwan ido ne abin nata kenan? Ya za ta yi da shi wanda ta yiwa iznin zuwa su gaisa da Abbanta?"

"Mami, wannan fa ya fi Hamza kudi da haɗuwa, na tabbata abin da ya ruɗe ta kenan."

Mamin ba ta ce komai ba face Allah ya kyauta.

***
Yana zaune a cikin motar hankalinsa rankatakaf akan ƙaton ƙyauren gidan da Tasleem ta yi mishi kwatance, ji yake tamkar ya yi tsuntsuwa ya shiga ya yi ido huɗu da abar ƙaunarsa, ganin ya kwashi mintuna babu alamar Tasleem sai ya ji gaba ɗaya ya karaya. Kodai ba gidan ba ne? Waya ya fiddo da niyyar ƙara kiranta sai ya hange ta ta fito daga gidan. Da farko sam bai gane ta ganin tamkar wannan ɗin shirin fita unguwa ta yi, ga dukkan alamu ma ba gidan ba ne. Amma a hankali tana matsowa ya gane ita ce don haka ya sauke tinted glass din motar wanda ya katange ta daga ganinsa sai waige ta ke.

Tasleem kuwa yana saukewa ta ji numfashinta na barazanae ɗaukewa ba don tsoro ba sai domin tsananin burgeta da ya yi, ga kuma wani irin kyau da ya yi mata. Shadda ce a jikinsa coffee colour, ya ɗora hula a kansa, wannan karon babu gilashi a idanunsa don haka kyawun fuskar ya ƙara bayyana muraran. Ta kasa furta koda harafi har sai da don kansa ya fito daga motar ya rufe. Murmushi mai tsada ya sakar mata.

"Ashe kin iya kwatance."

Ta yi farr da idanu haɗi da sakarmasa nata kalar murmushin itama. Cike da yanga da kwarkwasa ta ce.

"Kai kuma kana da basira tunda har ka iya ganewa. Barka da zuwa, bismillah mu shiga daga ciki."

Ba musu ya karɓi tayinta, bayan sun gaisa da maigadi dake zaune a benci, tana gaba yana biye da ita yana ƙarewa gidan kallo. Hatta da gidan sai da ya ji kaunarsa a zuciya, ya kuma rantse albarkacin masoyiyar tasa ce.  Falon suka shiga ya zauna bayan ta mishi bismillah, sai ƙamshi kuwa ke tashi a ciki don dama tunda ya yi mata kiran farko ta ba mai wankin Abba dari biyu akan ya taimaka ya kara share mata a sa turaren wuta.

"Ina zuwa." Ganin ta furta haka tana niyyar ficewa sai bai ce mata uffan ba, ba ya son ya yi garaje da tambayarta Humairar, tunda har ta ce tana zuwa to ya sani ba zai wuce ita za ta rako ba.

Ya lumshe idanunsa kafin ya buɗe ya sauke saman hoton Abban dake maƙale jikin bangon. Ko wani bai faɗamasa ba, wannan mahaifin Humaira ne, kamannin ya ɓaci kwarai. Sai ya ji kaunar Abban ya lulluɓeshi, ƙauna dai kwatankwacin irin kaunarsa da Alhajinsa. Sallamar Tasleem din karo na biyu ya katse dukkan tunaninsa. Ganinta ɗauke da tray na kayan sanyi nan da nan ya ɗan ɗaure fuska, shi fa duk ba wannan ne a gabansa ba. Tana ajiyewa ya ga tana kokarin zama ya karya bille ya ce.

  "Where is she?"

Ta dube shi cikin rashin fahimta, ta yi ƙarfin hali ta ce.

"Who?"

Ya dauke kai daga kallonta, ya soma hasaso wani abun, ya gane ita ɗin manufarta daban, tunaninta ya tafi wani wajen. Mafarkinta daban.

"Wacce na zo domin ta, Humaira."

Kirjin Tasleem ya hau bugu, har ji ta yi ganinta ya ɗan dusashe. Miyan bakinta haka ta neme shi ta rasa, dakyar ta tattaro jarumta ta ce.

"Humaira kuma? Dama wajenta ka zo."

Sai a sannan ya dube ta tsakar ido.

"Yes, wurinta na zo. Ko sadda muka haɗu dama haka nace wujenki zan zo?"

Tasleem da har ta soma hawaye ta kasa magana, eh bai furta cewa wajenta zai zo ba, amma wane rainin hankali ne ya sa bai nemi kwatance daga Humaira ba sai a wurinta? Ta kuwa daure fuska tamau, ta rantse daga ita har Humairar sai dai su yi biyu babu. Kowa ya rasa don hana ta ce.

"Toh Humaira ban santa ba, asalima a wurin biki muka haɗu. Na yi zaton gidanmu kake nufin na kwatanta mana. Don haka babu Humaira a gidannan."

"Ko?" Ya furta idanunsa a saman hoton Abba, itama ta kalli hoton. Ranta ya ɓaci ainun, ta san kamannin Humaira muraran da ya gani a fuskar Abba ya sanya shi furta hakan. Ta mike tsaye ta  koma gefen Fadeel  ta zauna. Zuwa yanzu ransa ya kai maƙura wajen ɓaci amma yana tausar zuciyarsa da tunanin bai dace ba, ta ci alfarmar abin sonsa. Ko babu komai tace masa  mahaifinsu guda. Ita kuwa da muryar kuka ta soma magana.

"Wallahi ina sonka. Tun ganin farko da nayi maka zuciyata ta kamu da begenka. Me za ka yi da Humaira? Da me ta fi ni? Na rantse babu abin da za ta nunamin."

Ya runtse idanu, ransa ɓaci yake ya na kokarin danneshi, amma jin ana kushe abar sonsa ya bude idanunsa da suka yi jawur tarr a cikin nata. Sai da ta ji rishin kukan ya tsaya na ɗan lokaci tsabar fargabar kar ya shaƙo ta.

"Ki san kalaman da za ki faɗi a kanta. Idan kuma kina son kanki da mutunci, ki yakice ni a ranki. Ki sani kuma ki kara, Humaira ta fiyemin ire-irenki dubu. Kyau da sura ba su ne a gabana ba. Da ace su ne, na bar da yawansu a inda na fito, ba na sonki, ba kuma na son kowa sai ita ɗin. Idan za ki iya ki shiga ki yimin sallama da ita, idan ba ki iyawa ni zan sa a kira ta."

Da gudu Tasleem ta mike ta yi hanyar fita tana kuka sosai. Fadeel ya mike tsam ya fito farfajiyar gidan inda ya ci karo da Muhsin na wasa da keke. Ƙarasawa ya yi wurinsa ya ɗan durkusa daidai tsawon yaron yana murmushi kamar ba yanzun aka ɓata ransa ba.

"Boy, ya sunanka?"

"Muhsin."

Ya jinjina kai, da alama duka sunayen yan gidan su Humaira masu dadi ne, shi kam dadi yake mishi, ya ji ance Futuha, Tasleem yanzu kuma ga Muhsin.

Ganin yaron na shirin janye keken ya sanya shi saurin riƙe keken.

"Ɗan shiga ciki ka ce Humaira ta zo, Fadeel ya iso."

Jin haka Muhsin ya amsa da toh, ya juya kan kekensa bayan Fadeel ya saki ya wuce ciki.

***
A can kuwa, Mami da Futuha na zaune sai gani suka yi  Tasleem ta fado falon a guje, tana  zuwa ta zube cinyar Mamin tana kuka.

"Ke lafiya? Meyafaru?" Cewar Mami cikin ɗaga murya gaba daya ta ruɗe. Wannan ya yi sanadin fitowar su Humaira daga ɗaki sai a sannan Tasleem ta ɗago ta dubi Mami.

"Wai ba ki yake so ba, wajen Humaira ya zo."

Jin haka Futuha ta ji zuciyarta dan yi sanyi, ko ba komai Tasleem ba za ta ƙara hura mata hancin ta yi wanda ya fi Ibb ba kuma ta gane ba Ibb ne masoyin Humairar ba. Amma a gefe kuma kishi da tsanar Humaira ne ya kara mamaye ta, mene ne da ita wanda har namiji irin Fadeel zai gani ya maƙale mata, su da suke buzaye ma ta kasa shawo kan Ibb ya kaunace ta sai wata can bafulatanar ruga?

Mami kuwa gaba daya fuskarta ta sauya, kafin ta yi magana dai ga Muhsin a guje da kekensa ya shigo falon, yana cin karo da Humaira ya ce.

"Adda Humaira, ki je inji wani a waje."

"Ka je ka ce ba za ta fito ba! Kada ya kara gigin zuwa gidannan!"

Gaba daya suka dubi fuskar  kowannensu dauke da mamaki idan ka cire Humaira da kalaman ya yi mata dadi ainun, haba ta gaji da naci irin na Fadeel, shi bai san ba ta son komai da ya danganci saurayi ba. Meyasa ya ƙi fahimta? Ai gwara Mamin ta kora mata shi. A bangaren Raihana da Ummita kuwa tunaninsu daban da nata. Akan me Mami za ta ce Fadeel ya tafi? Wato don ba ya sin Tasleem shikenan kowa ma ya rasa? Tasleem da Futuha kuwa dadi ne ya mamaye su, wato dai uwa uwa ce, ta damu da yaranta. A farko sun yi zaton kwata-kwata Mamin ba ta kaunarsu ta fi kaunar ƴan riƙonta musamman ma Humaira. Amma a hukuncin da ta yi abin ya musu dadi, Tasleem ta ji gwara ma kowa ya rasa.

Muhsin kuwa tuni ya fice don cika umarnin Maminsa. Humaira dai ta juya zuwa daki don ci gaba da abin da ya rage na ninkin da take yi, ganin haka Ummita ta bi bayanta, Raihana kuwa da sauri ta bi bayan Muhsin. Futuha na kwala mata kira ta yi mata banza.

***
A can farfajiyar gidan kuwa, Muhsin ne ya karaso har kusa da Fadeel, yana shirin faɗin saƙon Mami da sauri Raihana ta kwala mishi kira.

"Kai Muhsin." Suka juya har Fadeel suka dube ta, ta karaso da sauri ta ce.

"Jeka zan faɗamasa." Ya kuwa tura kekensa ya ci gaba da zagaye a gidan yana waƙe-waƙensa da ake musu a boko. Ta gaida shi ya amsa, zuwa yanzu ya karaya da ganin Humaira.

"Suna na Raihana ƙanwa ce ga Humaira, don Allah ka yi hakuri ba za ka samu ganinta ba a yau sai dai ko watarana idan an ɗan kwana biyu."

Murmushin da bai kai zuci ba ya yi, ta tabbata shi kadai ke kiɗa da rawar sa, wacce ya ke yaƙin don ita ba ta san yana yi ba, ko kuma ya ce ta sani amma ra'ayinsu ya sha bamban.

"Kar ki damu, ba komai. Idan kin shiga ki ce ina gaishe ta, na kuma cika alƙawarin da na daukarwa kaina na zuwa gidansu. Amma hakan ba ya nufin ko a mafarki zan iya fita a rayuwarta. Ina sonta."

Daga nan ya juya ya fice. Raihana ta zuba masa idanu har ya fita daga gate din gidan, tausayi sosai ya ba ta, Humaira dai tana neman cutar da kanta. Samun masoyin gaske irin Fadeel abu ne mai matuƙar wahala. Ta ji haushin Humaira a zuciyarta kamar ta je ta rufe ta da duka. Gwuiwa a sake haka ta juya ta koma ciki.

***
Tun faruwar wannan lamarin Fadeel ya shiga damuwa ainun, yana da tabbacin shi yake so ba a sonsa, ya kuma shirya rungumar wannan jarrabawar ya yaƙe shi. A gefe ga mahaifansu da suka soma matsawa akan su fito da matan aure shi da Ibb. Satinsa guda bai kira ta ba balle ya aika mata saƙo, jarrabawa ya yi domin ya ga ko zai iya yakice ta a rai bisa shawarar Ibb amma sai ya ji kamar yanzun ne ma ya soma kaunarta. Ba kuma ya jin zai iya haƙura da ita. Ya miƙe daga saman gadon da yake kwance wanda tashinsa kenan daga bacci mai cike da mafarkan Humaira, kamar daga sama ya ji ana kwankwasa ƙofar falon, agogon dake maƙale a bangon ɗakin ya kalla, ƙarfe goma har ta gota. Ya ɗan ja ƙaramin tsaki, ya tuna yau suka yi da Alhaji zai soma zuwa kamfaninsa ya kama aiki, jin ƙarar kwankwasar yake har cikin kansa dake radadin ciwo, iya sati ɗaya zuciyarsa ta jigatu da rashin ji ko ganin Humaira, ta ina zai soma fidda ta daga rayuwarsa? Wannan abu ne da ba zai yiwu ba sam. A hankali ya miƙe daga shi sai vest da dogon wando ya fito falon.

"Waye?"

"Ni ce Yaya Fadeel, abin kari na kawomaka."

Guntun tsaki ya ja jin muryar Murja. Ƙofar kawai ya bude ya juya ba tare da ya ko kalle ta ba ya ce.

"Ki ajiye ki fice. Na gode."

Ta ji ciwon hakan amma da ta tuno da batun Malam na cewa idan har ya ci abinda ta girka da laƙanin da ya ba ta to fa ba makawa hankalinsa zai karkato gare ta. Ya yi mata gargadi akan lallai ta tabbata ya ci, idan kuwa bai ci ba to fa haka za ta kara narka uban kudade a yi mata wani sabon aikin. Don haka sai ta zauna a falon ta ƙi bin umarninsa, shi kuwa wanka ya shiga bayan sun yi waya da Alhaji ya buɗe mishi wuta akan rashin zuwansa ofis da wuri, hakuri ya dinga  a shi ya ce yana tafe. Suka yi sallama. Koda ya fito wankan a gaggauce ya shirya cikin kananun kaya, dark green din tshirt sai wandon jeans. Ya ɗaura agogo a tsintsiyar hannunsa, ya gyara sumar kansa. Fitowarsa falon ya ga mutum zaune, nan da nan ya tamke fuska, ita kuwa Murja da rawar jiki ta ce.

"Barka da safiya, bari na haɗa maka shayin."

Ba tare da ya kalle ta ba ya ce.

"No ki bar shi nayi latti, Alhaji na jirana. Ki je da su kawai."

Murja cikinta ya bada sautin kululu, ita dai ta shiga uku, wannan rashin sa'a har ina? Yanzu shikenan ta yi asarar dubu tamanin? Ita kuwa wa za ta je ya ba ta wasu kudaden a ƙara maimaicin aiki?

"Ba kya ji ne?"

Wannan karon ya yi maganar yana ji kamar ya ɗauke ta da mari hagu da dama, abu ɗaya da ya sa yake raga mata bai wuce na tunanin shi ɗin ma fa haka yake fama da soyayyar wata ba ta sonsa.

Ganin yanayinsa sai ta maida kayan kwandon ta dauka ta fice har da kwallarta. Fadeel yana so ya kashe ta, yanzun ma ji take kamar ta faɗa wannan faɗaɗɗan kirjin nasa ya yi mata rumfa da hannuwansa, sai dai kash! Wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Amma kuma komai nisan jifa ƙasa zai faɗo kuma sannu sannu ba ta hana zuwa, ta na ji a jikinta watarana haƙanta zai cimma ruwa.

***
Abba ne zaune fuskarsa cike da walwala, babu jimawa iyayen Hamza suka tafi bayan sun nemawa ɗansu auren Tasleem kuma ba musu ya amince ya ba su. Tasleem da kanta ta kira Hamza ta ce ya turo saboda bakin cikin abinda Fadeel ya yi mata, ga faɗan da suka yi da Futuha me  yi mata dariyar ta rasa shi, ita kuma don ta nunawa Futuha tana da mai sonta dagaske ba irin ita me bin Ibb ba ya sonta ba yasa ta kiran Hamza ta ce matukar dagaske yake toh ya turo a nema mishi aurenta a kwana uku, idan kuwa ya wuce haka to kaunar da yake mata a baki ne. Dama kuma shi abin da yake jira kenan, don haka sai kawai ya ba da kai bori ya hau.

Mami ta shigo itama fuskarta dauke da walwala ta zauna gefen Abba. Kafin ma ta ce wani abu ya riga ta.

"Maryama yau ina cike da farin ciki, ba ni da burin da ya wuce naga na aurar da yarannan mata lafiya kowaccensu ta tare a ɗakinta. Ina tsoron sharrin wannan zamani. Ita ma Futuha zan mata magana, ta fito da miji na haɗa aurensu baki ɗaya zai fi min. Karatun can su je su ƙarasa a ɗakin mazajensu, naji da kannensu masu tasowa."

Mami ta jinjina kai,

"Hakane Abban yara, in sha Allahu

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login